Halysaah Page 102 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 102…Khaleesat ta mike zaune a fusace tana kallonsa cikin kuka tace “Ni dai ka fitar min, i don’t want to see you” Daga sama har kasa ya kalleta yace “Baki san na fi rashin son ganin ki ba, who do you think you are? As far as I am concern I have no business with you” Wani sabon kukan ta rushe da shi ta mayar da kanta saman pillow tana ganin kamar an gama cutar ta a rayuwa, har cikin ranta taji dama kawai Abdul aka mayar ma aurenta tunda har aka hanata Jay, ta yaya za a hanata Jay kuma a aura mata Ajay, how? she can’t even explain what she is feeling right now realizing she is not Jay’s wife, juyawa Ajay yayi ya fice daga dakin ya kullo kofar, sai yanxu yake sake sabon bakin cikin wannan auren da Abbansa yayi masa, coping with this girl shi ne abu na karshe da yake jin zai iya a rayuwa, he became so sad, don kawai gani yake wani babban burden Mai martaba ya dora masa, Aunty Farida na briefing ma Mai martaba ainahin garinsu a Niger da sunan family din su a can ta dalilin tambayarta da yayi, ba abinda ta boye masa game da asalin su, bata yi tunanin saukin kansa ya kai haka ba, don yayi stooping kansa to her level har yake sauraronta yana kara yi mata wasu tambayoyin, tayi mamaki da yace ya san Sarkin garinsu, don har ya kira mata sunansa, dai dai nan Ajay ya fito daki, Aunty Farida ta daga kai ta kallesa, ya sauke idonsa ya zauna kan Carpet yace “Tana fitowa” The parlor was silent for the next 5 minutes, can dai Ajay ya kalli Aunty Farida a hankali yace “Aunty ko za ki duba ko ta gama shiryawa” Aunty Farida tace “Toh bari in duba” Mikewa tayi ta nufi Bedroom din ta bude kofar ta shiga da sallama, bata yi mamakin ganin Khaleesat kwance tana rera kuka a dakin ba kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ta kulle kofar tana kallonta, can tayi kasa da murya tace “Har yanxu kukan kike yi kenan? Me yasa kike haka ne Khaleesat?” Khaleesat ta mike zaune cikin kuka tace “Ni wallahi Aunty bazan iya zaman gidan nan ba, me yasa za a min aure da wanda ban ce ina so ba? Dama haka ake yi ban sani ba?” Aunty Farida ta mata wani kallo tace “Ina shi wanda kika ce kina son? Wani ne ya hana auren naku da shi ko kuma Mahaifiyarsa? Tunda uwarsa tace bata so in mu ba mayu bane ai ya ci mu hakura da Jawwad, Jawwad abun so ne amma tunda abubuwa suka zo da haka ba sai a hakura ba kuma, Ke baki san gata ma Sarki yayi maki da ya makala ma Junaid ke bai ji ba bai gani ba tunda shi ma bai ce yana so ba biyayya kawai yayi, amma saboda baki da mutunci kike cewa baki son sa, to shi yace son naki yake? Wato ke kin fi karfin ki yi mana biyayya yanda shi ma yayi ma mahaifinsa biyayya, har kike da bakin cewa baki son sa” Cikin kuka Khaleesat tace “To Aunty ta yaya zance ina son sa bayan yayansa nake so ba shi ba, idan nace ma ina son sa ba sai ku ji tsorona ba, ta yaya zan so yaya da kani? ni wallahi bana son sa da aure gaskiya bazan iya ba, a matsayi daban na daukesa a zuciyata amma ban taba masa kallon ya zama mijina wataran ba, tun da aurenmu da Housemate dina bai yiwu ba da kawai an maida ma Abdul aure na, ai nasan shi ma yana so na kuma bazai sake min abinda yayi min ba” Sake baki Aunty Farida tayi tana kallon Khaleesat don bata yi expecting kalmominta ba, Khaleesat ta goge idonta ta kauda kai don ita har ranta take fadin abinda ya fito bakinta, ta yaya za a aura mata Ajay, da wani idon Jay zai dinga ganinta tare da Ajay a matsayin mijinta bayan irin bond din da tasan suna da shi, inaa ai bazai ma yiwu ba, dama su Aunty Farida na barin gidan nan ita ma zata yi tafıyarta don bazata zauna ba” Aunty Farida tace “Lallai baki da hankali sai yanxu na sake tabbatar da hakan Khaleesat, mu kike son ki ja ma magana da abun fade a gidan nan ko? Nuna ma yan gidan zaki yi ai kin fi karfinmu, to in kin fasa…. Khaleesat dai taki cewa komai don ma bata san suna tafiya zata bi bayansu ba, Aunty Farida ta hade rai tace “Kuma idan kin ga dama ki tashi ki gyara fuskarki sarki na parlor yana jiran ki tun daxu, kuma ki bari in sake dawowa in maki magana ki ga ikon Allah tunda ke baki da mutunci baki san mutunci ba” Daga haka Aunty Farida ta juya ta bude kofar dakin ta fita ta kullo…. Khaleesat na zaune parlor ta kwantar da kanta jikin kujera hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, she was really heartbroken and sad, so take ta bara baki tayi kuka ko zata ji sanyi amma babu daman yin haka gaba Mai martaba, tun daga sanda Sarki ya fara magana har ya idar da maganganun nasa cikin natsuwa babu wanda ya daga kai ya kallesa a parlon, Ajay kam wasn’t even Concentrating to all what his father was saying don yayi nisa tunanin da yake, daga karshe Sarki yayi masu nasiha da fatan zaman lafıya ya kuma yi masu addu’a sannan ya mike, sai a sannan Ajay ya daga kansa a hankali, Aunty Farida tace “Allah ya kara girma ranka shi dade” Ajay ya mike ya bi bayan Abbansa suka fita daga parlon, Aunty Farida dai kallon Khaleesat kawai take, can tace “Allah ya sa duk kin ji kuma kin dauka, don ke zai yi ma amfani ba wani ba, kamar yanda Sarki ya fada Allah bai kaddara auren ku da Jawwad ba, ni nasan ko da kin auri Jawwad wallahi baza ki ji dadin zama da shi ba saboda mahaifiyarsa sannan ga kishiya er uwarsa kuma warce uwarsa take so, until when kike son ki samu natsuwa da kwanciyar hankali a aure? Ko burin ki kenan kiyi ta aure ana gasa maki Aya a hannu? Ga shi naga alamar Gimbiya Shafa’atu ce kadai tayi na’am da batun auro ki a duk fadin gidan nan, and I learnt bata ma zaman kasar nan sosai, amma sauran ta ciki na ciki ban ga alamar mutanen kwarai bane, shi kansa auren Junaid ba wai mun ce kin tsira bane amma Challenges dinsa akan na Jawwad mai sauki ne, na Jawwad abun yayi yawa, ga uwa bata son ki, ga kishiya cousin dinsa, ga duk yan gidan nan ba yin ki su ke ba, duk abinda kika ga ya faru a rayuwar nan dama rubutattce ne daga Allah Khaleesat, don haka kiyi accepting hakan with good faith, da ace Jawwad ne mijin ki babu abinda zai hana ki aurensa sai dai ki je kiyi ta facing duk Challenges din auren nasa ko da kuwa it will take forever, but Allah ya dubeki ya musanya maki da inda Challenges din zai zo maki da sauki, wallahi ko don addu’an da Umma take maki ba dare ba rana ni nasan baza ki tabe ba Khaleesat” Ita dai Khaleesat kuka kawai take don in duk jikinta kunnuwa ne bata jin Aunty Farida zata iya convincing dinta in anyway, mikewa Aunty Farida tayi tace “In kin dau abubuwan da sarki ya fada maki da wanda na kara maki yanxu su maki amfani, in kuma kika yi fatali da su don kanki, zuwa anjima duk neman mu zaki yi ki rasa a gidan nan sai mu ga wanda zai gaya maki gaskiya” Daga haka Aunty Farida ta fita daga parlon, Khaleesat ta fashe da matsanancin kuka tana tuno kalaman karshe da Jay yayi mata ranan da ya zo gidan Aunty Murja da daddare tare da Ajay, kuka sosai take tana jin ranta na mata zafı. Mai martaba na zaune parlon Hajja tare da Ajay, tun daxu Hajja ta sauka garin amma bata yarda taje masarauta ba instead ta sauka a gidanta, shi ne sarki ya bar duk abinda yake aka yi masa rakiya zuwa gidan don ya gaida mahaifiyar tasa, ba kasafai take sauka gidan nata ba don duk zuwa idan tayi a masarauta take sauka amma wannan karan taki zuwa can alamar akwai magana, tun da Ajay ya gaisheta tare da Gimbiya Firdausi da kilishi dake zaune parlon ya mike zai fita daga parlon Hajja tace “A’a dawo kayi zaman ka, ina kuma zaka je Yarima” Komawa yayi ya zauna ba tare da ya kalleta ba, dai dai nan aka bude kofar parlon Jay ya shigo da sallama, Ajay ya daga kai yana kallonsa, Jay ya karasa cikin parlon ya duka kasa ya gaida Sarki kansa a kasa, Mai martaba ya amsa gaisuwansa sannan yace “When did you come back?” Hajja zata yi magana, Gimbiya Firdausi tayi mata alamar tayi shiru, shi dai Jay bai dago kansa ba yace “I came back yesterday ur Highness” Mai martaba yace “Who did you tell you were leaving before you left?” Jay yayi shiru bai ce komai ba, Sarki ya jinjina kai yace “To sannu da dawowa” a hankali Jay yace “Allah ya taimake ka, tuba nake, a gafarce ni” Hajja tace “Da kayi me zaka tuba? Ai ba wani abu bane don mutum yayi bulaguro ganin an dena yin sa a waje, gafarar me kuma zaka nema?” Mai martaba ya juya ya kalli mahaifiyar tasa da ta daure fuska, can ta gyara zama tace “To ranka shi dade ya fama da al’umma? Ya kuma bayan saduwa?” Calmly Sarki yace “Alhamdulillah” tace “To Madallah, na kuma ji auren da ka daura ma wannan yaron Junaid, Wanda ni ban san da daurin auren ba ma, don iya na Jawwad kawai na sani, shi ma ranan daurin auren ya samu matar ashe har kayi masa aure?” Mai martaba yace “Eh haka ne Hajiya, dama jiran isowarki nake sai in maki bayani, shi yasa bayan daurin auren na kira ki na tambayi yaushe zaki iso” Hajja tayi wani murmushi ta juya ta kalli Gimbiya Firdausi, ita dai kilishi sai wani kallo take ma Ajay daga sama har kasa, Shekaru biyar Gimbiya Firdausi ta ba Mai martaba kuma Stepsister dinsa ce, sannan ita ce babba a gidan a yanxu, Jay ya mike zai fita daga parlon Hajja tace “A’a koma ka zauna Ahmad, koma kayi zaman ka Gimbiya Firdausi na kallon sarki cikin nutsuwa tace “Ranka shi dade duk mun samu labarin abinda ya wakana a kan auren Jawwad, and am sorry to say Mai martaba we are all highly disappointed at what happened” Sarki na kallonta ya gyada kai yace “Ohk” Gimbiya Firdausi ta ci gaba tace “Sannan duk tunaninmu ai daga Junaid har Jawwad daya suke a wajen ka babu wani bambanci, kuma mu duk a haka muka san ka” Sarki ya girgiza kai with calmness yace “In this case, Fulani Aseeyah ta nuna ba daya bane, sannan shi ma Ahmad din ya nuna maganar mahaifiyarsa ta fi muhimmanci akan wanda ni zan yi ko kuma akan abinda na yanke” Mami ce ta shigo parlon da sallama babu yabo babu fallasa ta nemi waje ta zauna ta gaida sarki, ya juya yana kallonta, tace “A gafarce ni, amma ranka shi dade babu ta yanda zaka ce maganata tafi taka muhimmanci a wajen Jawwad, kan nayi masa magana sau daya ya dauka ya dau naka sau ba adadi, sannan hukunci nawa ka yanke kan Jawwad na taba daga kai na ce don me? Wannan ma kasan ai babu yanda zan yi idan ka yanke hukuncin yi masa abinda yake so” Mai martaba dai kallonta kawai yake, can ya dan yi murmushi ya dauke kansa yaki cewa komai, after some minutes Mai martaba ya kalli Jay yace “Kai jawwad, the third time u came to my Chamber me kace min?” Jay dai bai dago kansa ba, Mami tace “Allah ya taimake ka, amma bazai yiwu ka saka masa magana a baki ba, ko ma me yace maka ai kai ubansa ne baza ka daka ta tasa ba, beside all those time he was only trying to please me, Wanda da ka nuna mana bamu isa da ni da shi ba ai hakan ya zauna babu kuma yanda za mu yi, yau ace ka aura masa yarinyar nan idan aka kawo masa ita ba dai koranta zan yi ba duk abu na” Cikin kuka Mami ta kare maganar, Sarki ya kalleta calmly yace “Ke ki ji tsoron Allah Fulani, kuma ki bude baki ki maimaita duk abinda kika shigo Parlor na kika gaya min yanxu ko kuma kowa ya tashi ya bar min parlon nan banda Hajiya…. Apart from Hajiya i don’t think anyone is in the rightful place to question me in the first place, since from day 1 I have known you to be a manipulator” Mikewa Mai martaba yayi yace “Duk ku fita ku bar min parlon nan” Sai kuma ya juya ya kalli Gimbiya Firdausi yace “Yaya, zan zo in sameki a daki idan nayi magana da Hajiya, for now I need to be alone with Hajiya” Zaunawa Mai martaba yayi bayan parlon ya rage daga shi sae Hajja, Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace “Ko me zaka gaya min ba lallai ya shigeni ba Yusufa, jikina yayi matukar sanyi da abun nan da ka aikata wanda ni nasan ba halin ka bane tunzura ka aka yi, amma Jawwad bai cancanci haka daga gare ka ba don shi ya kamata ka duba, gashi a yanda na fahimta yana son yarinyar nan sosai, ko abinci yaron nan baya ci wallahi ya dau damuwar duniya ya dora ma kansa shi yasa hankalin uwar ya tashi don ba saboda Allah bane wannan tashin hankalin da ta shiga, me ya kai ka duba mahaukaciyar uwarsa Yusufa? Yanxu kenan ka fito ka nuna ma duniya ba kai ka haifesa ba ga naka dan kenan, don kuwa babu wanda zai maka uxuri ya duba baya, mahaifinsa fa wan ka ne uwarku daya uban ku daya, har ya koma ga Allah ba shi da tamkarka kai ma ka sani, kai ma kuma baka da tamkarsa….” Mai martaba yace “Kafin in yi ma Junaid abu daya nayi ma Jawwad babu adadi, Jawwad bai taso fully a gabana ba tunda uwar taki barin haka amma kusan duk harkokina Jawwad ne a kai ba wai don Junaid isn’t capable ba, I put Jawwad first before Junaid in everything, I trust jawwad more than I trust Junaid, Amma duk uwarsa bata gani saboda abinda ta dauka ta saka a ranta daban, ni kuma nasan soyayyan mahaifinsa ne na mayar kansa, yanda na so sa ko Junaid ban nuna masa wannan son ba….” Hajja ta sauke ajiyar zuciya don har cikin ranta taji takaicin wannan abu da ya faru kuma ita dai tasan ba halin sarki bane nuna bambanci tunxurasa aka yi, Mai martaba yace “Ban taba tunanin nada Junaid Yarima ba banda ke da su Baba Tafida da kuka sa dole nayi hakan, bond din da nake da shi da Jawwad babu wannan Bond din tsakanina da Junaid wallahi, don ma Allah yayi Junaid mai hakuri da kauda kai sannan he have a clean heart, dai dai da rana daya bai taba kishi da dan uwansa ba ko yaji haushin why I put Jawwad first always” Hajja ta sauke wani ajiyar zuciyan tace “Wannan gaskiya ne don a baya can na sha kawo maka rashin jin dadin yanda ake banzantar da Junaid a Masarauta komai ace Jawwad duk da har cikin raina ina son dukan su, shi Junaid ko uwar da zai gani yaji dadi ma ba shi da ita ga Matarka bata ja sa jiki ba shi yasa nake matukar tausayin sa, Jawwad kuwa gata garesa kaca kaca ta ko ina, Yarima da muka tilasta maka ka nada Junaid a maimakon Jawwad da kake da ra’ayi ba don komai yasa na dage ayi hakan ba sai don Aseeyah, sam bata ganin kowa da gashi a masarautar nan kai ma sai taga dama take raga maka, dubi yanda ta maka magana yanxu ba da’a, kuma ace ga dan ta na jiran gadon sarauta ai mun banu kuma sai yanda muka ga, idan ba ayi hankali ba ma ita ce zata yi mulkin don juyasa zata yi ta yi akan mulki, shi yasa kaga muka hade maka kai lallai ka ba Junaid don dama shi ne asalin me jiran gadon” Mai martaba yace “A cikin maganganun da ta gaya min har cewa tayi ni na kashe dan uwana saboda mulki, tunda ni ne mutum na karshe da ya bar parlonsa, and he was hale and hearty then, Ina raga ma Aseeya saboda abubuwa da yawa Hajiya” Hajja da ta bude baki tana kallonsa tsabar shock ta kasa cewa komai, can ta girgiza kai tace “To Allah ya wadaran ta, wallahi banda Jawwad da tuni mun yi watsi da matar nan don ba matar kirki bace, wannan magana kuma kayi hakuri ka bar sa a ranka ba sai ka kara gaya ma kowa ba, ka kyaleta da halinta ta ci gaba da cin albarkacin dan ta, sannan ina son sanin dalilin da zai sa ka aura ma yarinyar Junaid a maimakon a fasa auren kawai Yusufa?” Mai martaba yace “Saboda babu wanda zai maida ni karamin mutum don girma na, shi ma Junaid din ban yi shawara da shi ba nayi abinda nayi saboda ina ga na isa da shi, yau ace Walid na kirki ne shi zan aura ma ko don in cusa ma Fulani Hafsah takaici, don sarai nasan ita ke kara zuga Aseeyah, kuma ita ma zan yi maganinta nan ba da dadewa ba kuwa….” Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace “To amma dai kam ka bar baya da kura, ko ka mance tsakanin Jawwad da Junaid ne?” Tun da Ajay yayi attempting yi ma Jay magana ya ga yaki tsayawa balle har ya sauraresa ya shige daki ya kulle kofar, Ajay ya bar gidan ya koma palace, zai tafi part dinsa sai ga Jakadiyar Aunty tare da Khaleesat a walkway din suna tafiya, sau daya Khaleesat ta kallesa ta kauda kai, Jakadiyar ta duka tana gaishesa cikin girmamawa, har zai wuce sai kuma ya tsaya yace “Ina za ki da ita?” Da ladabi Jakadiya tace “Fulani ta ce a taho da ita bangarenta ranka shi dade” Zagayowa yayi gabansu yace “Ki ce mata zan kawo ta when I am ready Daga haka ya kalli Khaleesat da ta hade rai yace “Juya mu tafi” Jakadiya ta risina tace “To ranka shi dade, bara in je in sanar mata, Allah ya ja zamanin ka Daga haka ta bar wajen da sauri, ya daure fuska yana kallon Khaleesat yace “Baza ki juya mu tafi ba” ta juya masa baya tace “Ni dai kawai ka kyaleni, just leave me alone” hannunta ya fixgo ya fara tafiya zuwa part dinsa, tana zaro ido tace “Meye haka, ni ka sake min hannu, do you want me to fall down” Har ya isa bangarensa bai sake hannunta ba kuma bai fasa jan ta ba, ya bude kofar parlon ya turata ciki yana kallonta yace “Silly Brat”…
