Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 30 Hausa Novel

**Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?”**Da wani irin amo sautin muryarshi ke dawo mata a sadda yake faɗa farkawarta daga shan piya-piya, ashe da biyu yake yi mata irin wannan faɗan? Ashe shima duniyar ba daaɗi tayi mishi ba? Wasu irin ruwan hawaye ne ke bin fuskarta babu kakkautawa, sai taji har gwara ita ma da shi kaman ƙaddarar ta ya fi nashi sauƙi tunda tana kwanciya tayi bacci lafiya ƙalau, kuka kawai take yi duk yadda mammi ta so tayi shiru ta ƙi, sai da tayi ma’ishi Mammi ta bata ruwa ta sha kan ta ɗago ta kalli Mammi bata ce komai ba.”Za ki iya cewa Meyasa ban bashi Abeeha ko Jannah ba ko? Har raina na ɗauki Saraki ɗan da na tsuguna na haifa ne shiyasa har abada na haramta mishi auren ‘ya’yana, uba yake a gare su a yanzu da basu da wani uba shi ya raine su bayan yana jinya na, shi ya basu tarbiya cikakkiya da har in sun fita ana sha’awar su. Wannan dalili ya sa ko da wasa wannan tunani bai taɓa darsar min ba don har in mutu bana fata ko sau ɗaya Saraki yayi tunanin don ba ni na haife shi ba zan iya ɓata mishi…”A hankali Afeefah da idanunta suka sauya ainun ta riƙe hannun Mammi “Ke mutumiyar kirki ce Mammi, kina daga cikin sahun ‘yan aljanna in shaa Allah… Hakika kina da zuciya mai kyau wanda Allah ne yayi miki kyautar shi don samun irinki sai an tona”Murmushi kaɗan kawai Mammi tayi zata yi magana Afeefah tayi saurin cewa “Mammi ki bar roƙo na kin yarda da ni ni kuma in shaa Allahu ba zan ba ki kunya ba, wlh har raina na amince kuma zan yi iya kokarina in ga na ba da abinda ake so”Rungumeta kawai Mammi tayi cikin farin cikin da yake ratsa zuciyarta.****Shi kam Rayyan daga masallaci ya mayar da Saleem gida bayan yayi ta mishi tuni akan mahaifiyarshi da ‘yan uwanshi irin muhimmancin su a rayuwarshi duk yana ji amma amsawar wani iri, bai damu sossai ba don shima zai taya abokin nashi da Adu’a yana kuma da yakinin duk abinda yayi farko yana da ƙarshe musamman abinda ba don Allah aka yi shi ba.Daga nan gidan Jannah ya wuce, tana zaune kawai ta ji ana knocking ta tashi taje ta buɗe sai ta ganshi tsaye, murmushi ta saki tana mishi sannu da zuwa ya amsa yadda ya saba musu ya shiga ya samu wuri ya zauna, cikin mintuna kaɗan ta cika gabanshi da kalolin abubuwa su snacks da su abinci kan ta dawo ta zauna “Barka da juma’a Yaya””Barka dai ya gidan?”Ta amsa da farin ciki”Lafiya ƙalau ya su Mammi?””Alhamdulillah”Ya faɗa yana shan zobo don yana matuƙar kaunar zobo bayan ya sauƙe cup ɗin ya kalleta “ba ki da wani damuwa ko?”Kai ta gyaɗa “Babu komai Yaya”Ya ce”Masha Allah”Miƙewa yayi ya zare kudi ya ajiye mata dukda tana aiki godiya tayi ta mishi ta raka shi har mota ya tafi ta dawo tana murmushi ya kan yi hakan tun bayan aurenta, haka kawai sai ta ganshi zai zo ya duba ta ya tabbatar tana lafiya ya ajiye mata kudi ya tafi.Gida ya nufa kai tsaye, bai je Sashenshi ba don la’asar ya kusa yana so ya duba Mammi kan ya fita yayi sallah sai ya dawo ya huta gabaɗaya, ko da ya shiga yanayin wurin ya ɗan zubawa ido Dukda ya fahimci Mammi ta yi hawaye sai dai idanunshi da suka shiga cikin nata ya ɗan ji wani yanayi da har bai ɓuya ba, seconds ya kwashe yana kallonta kan ya ɗauke kai sai ta miƙe ta zo zata fita muryarta na cracking tace “Sannu da dawowa”Bata jira amsarshi ba ta wuce don ganinshi kaɗai tausayi yake bata.Ɗan shiru yayi kan ya taɓe baki yana ɗaga Kafada ya isa wurin Mammi “Mammi why did you cry? Yarinyar chan ne ko?””Ni ce dai na sakata kuka ba ita ta saka ni ba, ka dawo?”Bai ja zaren zancen ba yace “Eh, hope baki ji yunwa ba?””No ban ji ba, na san ma Abeeha ta kusa shigowa ko na ji ma zata zo ta sama min wani abin you should rest”Kai ya gyaɗa ya ɗan jingina da kujera yana lumshe ido “Ni ko ina son yin wata magana da kai”Buɗe idanun yayi yana kallonta “Saraki ka tuna kai ka ce in zaɓa maka mata ko ma wacece za ka aureta in dai ni ce na zaɓa?”Ɗan shiru yayi kan chan dai ya gyaɗa kai.”Toh mun samu Mata Saraki”Bai wani nuna ya ji daaɗi ko zumudi ba sai ma runtse idanu da yayi ya ɗan buɗe.”Baka tambayi wace ba kuma a ina?””Mammi ke fa kika shirya wannan aure duk abubuwan nan ba lallai sai na ji ba ayi duk abinda ya dace kawai””haka za ka aureta baku fahimci juna ba? Ai ba’a haka dole za ka nuna mata itama macece kaman sauran mata ka bata darajar ta na neman soyayya da ma kyautatawa da kan shiga tsakanin saurayi da budurwa”Idanunshi kawai ya zubawa Mammi don jinta kawai yake baya tunanin zai iya yin ko abu guda cikin wanda ta lissafo.”Mammi kin fa san duk ba zan iya wannan ba””Toh na ji amma ka san wacece yarinyar? Ka dai san ba zan zaɓa maka wacce na san bata dace da kai ba ko? Kuma ka yi min alkawarin ƙarbar ta yadda take ko?”Ya ɗan matsa kaɗan ya riƙe hannunta “Mammi duk zagaye-zagayen nan na menene? Kin fa san yadda na ɗauki girman alkawari wallahi zan amince, wacece?”Yadda take ta zagayen ne yasa ma yaji yana son sanin wacece haka.”Afeefah ce!”Ɗan shiru yayi yana tunani don sai ya ji kaman ma bai san sunan ba, amma duk inda ya zagaya a kwakwalwarshi mace ɗaya tak ya sani da wannan suna, mace ɗaya da ya sani kuma buduruwar abokinshi ce salim. Da sauri ya kalli Mammin yana girgiza kai”A’a Mammi ki samo wata ba wannan ba”Da zuciya ɗaya yayi maganan kuma kai tsaye.”Ban gane in samo wata ba, Meyasa?””Mammi ni wannan ta yi min yarinya wlh ba na son hauka da raini, sannan Mammi buduruwar saleem ce fa! Ta ya zan fara zaman aure da ita?”Murmushi Mammi tayi a maganan nashi na farko “Ina saleem ɗin? Ina yana chan yayi aure yana zaune da matar shi? Ko ma bai yi aure ba ba zan amincewa Afeefah ta auri saleem ba ba kuma don shi a karan kanshi ba sai don mahaifiyarshi ba zan so ta koma inda zata sha wahala ba shiyasa na zaɓa mata kai ina da yakinin za ka kula da ita har karshen numfashi”Tayi maganan cikin tabbatarwa, duk ya ɗan ruɗe mata kaman zai yi kuka ya fara magiyar ta chanza wata shi dai wannan yarinya bata mishi ba.”Ba fa zan fasa ba Saraki sai ka bani kwakwarar hujjar da zan gamsu ban da buduruwar saleem, ban da kuma baka sonta itama bata son ka dukkanku za ku koyi son juna idan zama ya haɗa ku, banda kuma tayi yarinya don kaima ka san ba yarinyar bace”Hangota kawai yake a idanunshi yana son tuna menene kuma aibunta wannan idanu farare manya da take zarowa duk sadda yayi magana yake hangowa kawai, da ɗan sauri yace “Mammi baƙa ce!”Dariya Mammi ta fara tana girgiza kai ya kwaɓe fuska shi da gaske yake “Yaushe kuma ka fara zaɓar kala? Kenan ni da babanku bai aureni ba kenan ko kuma da Su Jannah ba za su auru ba””To ai ku daban ne ita daban Mammi””Ka san Allah idan ba legit hujja zaka kawo ba, maganan nan babu fashi ka fara shiri… Saboda yanayin jiki na ba za mu ɗauko wani hidima ba ɗaura aure kawai za’a yi ayi walima kowa ya shaida ta tare”Duk yadda ya so ya zamewa Mammi ya kasa, don komai ya ce tana da amsa har aka kira la’asar ya tashi ya tafi, ta bishi da kallo tana murmushi idan ta ga yana hira da ita haka hakan na yi mata matukar daaɗi a rai, ta kan rasa Meyasa baya son Magana alhali ya iya ba bai iya ba, kawai dai ya zauna shiru ya fi mishi ko mahaifin su Jannah da yana raye sai dai ya ji dariyar ta ba zai ji maganan Sarakin nata ba yayi ta tsokanarsu kenan tana shigarwa Sarakin don shi bayan ita wasa da sakin fuskanshi babu mai gani gwara ma saleem da suka shaku sossai shima don salim ɗin ya karanci halayenshi ne tsaff kuma ya iya zama dashi.Tana fata ko ba yanzu ba ya so Afeefah ya sake mata fiye da yadda ita take ganin wannan side ɗin nashi, hannu ta ɗaga tana roƙon Allah ya nuna mata wannan rana da zata miƙa shi ɗakin matarshi.Daga nan ta miƙe ta shige don alwalar la’asar, bata yi ƙasa a gwiwa ba da daren ta sa driver ya kaita gidan ƙanin mahaifinta Uncle Musa dattijo ne sossai shima kuma natsatse mai tarin ilimin boko da arabi yana da zuri’a kuma duk zaman lafiya suke da su Mammi, sossai ta mishi bayanin Afeefah ta kuma roƙi da su je su nema mata aure a wurin dangin mahaifinta don a fita hakkin su, bata so su bada komai amma tana son A karɓi auren Afeefah daga shakikanta. Ya gamsu shima kuma yayi na’am da hakan sun yi hira sossai don tana kwana biyu bata je ba sbd jikinta shi ne ma ya kan zo har gida ya duba ta haka yaranshi da wasu jikokinshi, bata bar gidan ba sai da suka tsayar zai yi tattaki da kanshi da babban danshi su tafi Dutsen-wai su nemi a basu ranar auren daga nan sai a fara shiri.****Mommy ce kwance a kan gado tsabar damuwa da tunani da ta sakawa kanta ne ya sa jininta hawa sossai, su Samha ke zagaye da ita a yanzu ɗin ma hawaye take zubarwa na tausayin Saleem da damuwar halin da yake ciki wanda ta yarda laifin ta ne amma me yasa su Yaya za su rama alkhairinta da mugunta? Me ta musu da zafi haka?Bata gama tunanin ba Sabrina ta shigo ɗakin ta samu wuri ta zauna “Sannu Hajiya mommy ashe kuma jiki ya ƙi?”Mommy ta danne tace “Eh amma Alhamdulillah””Toh Allah ya kara sauƙi dama Saleem ne ya aiko ni”Yadda ta kira sunan sai da suka daga kai duk suka kalleta.”Wai cewa yayi ku koma wanchan tsohon gidan na gado ya riga ya tashi ‘yan hayan yana son yayi renovating nan, kin ga yanzu mun yi yawa ga iyali zai fara tarawa ga su Gaje gininsun ya tsofe cikin ko wani minti zai iya rufta musu suma dai duk nan za su dawo”Galala suke kallonta da kyar mommy ta iya cewa “Saleem ɗin ne yace haka?””Ai kin san ban san yan hayan ba bare in tashe su, shine yayi komai kuma ya tabbatar min kar ku wuce yau don gobe masu aikin za su fara zuwa”Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga sulmiyo wa mommy da su Samha, Sameera ce ta iya daurewa ta miƙe tsaye ta fara hada kayan mommyn don ba zasu zauna ba, gwara su tafi ɗin babban matsalar dukkansu babu mai aiki cikinsu karatu suke yi, mommyn sai kallonta take tana jin tururin zafi a zuciyarta tuni Sabrina ta fice, mommy tashi tayi ta fito kai tsaye ta haura saman su ta buga, su Samha duk suka bi bayanta jikinsu a matuƙar sanyaye sai da tayi mintuna biyu kan aka bude saleem ta ƙura wa ido sama da seconds goma kan tace “kai ka ba matarka saƙo ta ba mu?”Kai ya gyaɗa “Duk abinda tace haka ne!”Jiri ne ya kwashe ta ya yunkura zai tare ta ta ture hannunshi ta juya da sauri ta sauƙa su Samha ta cewa su hada kayansu duk suka hada suka fito a motar sadiqa suka zuba duk abubuwan buƙatar su ta ja suka fice daga gidan dukkansu suna kuka, basu sake jin tashin hankali ba sai da suka iso gidan duk ‘yan haya sun lalata shi komai dai sai a hankali kuma dakuna biyu ne da parlor sai kitchen duk jiki a sanyaye suka zauna a parlorn mommy na dafe da kanta har lokacin kuka take yi.”Mommy..!”Sameera ta kira sunanta.Sai ta ɗago ta kalleta “Kina jin zafi a ranki ko? Kina jin ciwo da raɗaɗi ko? Kina jin baƙin ciki da tsantsar damuwa da tashin hankali ko?”Mommy tace”Ba sai na faɗa ba Sameera abin da nake ji ba zai misaltu ba ni saleem ya ɗaga daga gidan shi zai dawo da surukanshi? Ni fah? Ko a mafarki ban taɓa zato ko tsammanin saleem zai iya juya min baya a kan mace ba””Mommy in faɗa miki gaskiya? Laifin ki ne, dukkanmu muna da laifi a abin da ya faru… Mommy kin yi tunanin inda Afeefah ta nufa da muka kore ta? Gwara mu muna da nan kuma ko ba komai muna da junanmu amma ita kaɗai ta fita bata da kowa bata da inda zata je, kin tuna irin wulakancin da muka mata? Ashe alhakin da muka raina zai iya bibiyarmu, kin tsane ta ne saboda saleem yana son ta kina ganin son nan da yake mata zai sa ya bijire miki kika zaɓa mishi wacce kike ganin ke ce da riba sai kuma akasin hakan ya faru. har yanzu kina ganin laifin Yaya da kika mishi dolen karbar wacce bai taba so ba? Kina ganin laifin Yaya da ƙarfi da yaji yana kuka yana komai kika raba shi da Masoyiyar shi? Mommy ina jin zafi ina jin ciwo ina ji a zuciyata cewa duk wannan abinda ya farun alhakin yarinyar nan ne, Allah ya jarabceni da azabar so na ji yadda itama ta ji a sadda muka raba ta da nata savior ɗin, na ji kwatar abinda yaya ya ji a kanta amma muka hadu muka nufeta da sharri har da ƙagen lalata da samari wlh idan ba mu neme ta mun nemi yafiyarta ba to kadan kenan muka fara gani”Dukkansu maganganun sameeran sun shige su barin ma mommy da Samha dake ta kuka, gaskiya Sameera ta faɗa bata kyauta ba kuma duk laifin ta ne da tun farko ta kwaɓe su ba zasu yi ba amma bakin alƙalami ya riga ya bushe sai dai su tari gaba, tana tuna irin abubuwan da suka mata tana tuna irin yadda taje ta haɗa ta da maza don tayi rayuwa saboda kawai an ce ne ita Mayya ce sai ka ce jahilai waenda basu yi karatun islama ba sun ci zarafinta baiwar Allah, sai gashi Allah ya nuna musu ɗan Adam ko ya yake mai daraja ne a gareshi, ya nuna musu ikon shi a kan bayinsa.”A ina za mu sameta mu nemi yafiyarta a ina zan ganta Sameera?””Wannan sai Allah mommy, yanzu ina so ki daina yiwa yaya kuka mu dukufa Adu’a da sadaka Allah ya karkato da hankalinshi mommy adu’ar ki karɓaɓɓiya ce a gareshi ke kika ɓata ke ya kamata ki dukufa ki gyara”Ta gamsu sossai kuma ta fahimci karatun duniyar, ta fahimci ayar da Allah ya nuna a kanta don haka gwagwalanta ta cire ta ba sadiqa akan su je su sayar su musu sayayyan duk abinda za su buƙata haka suka fice kasuwa suka bar su su biyu da Samha da har lokacin jikinta kaman an zuba mata ƙanƙara.

Back to top button