Uncategorized

Macijine Shi Page 9-10 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Page 9/10

__________________Nan da nan fusatattun rugar suka nufi gidan malam bukar ,dan aiwatar da ƙudirin lamiɗo.

Allah Sarki fattu kuwa a wanann lokacin tana ɗakinta cikin jimami da tunanin abinda ta  gani yau ɗin nan,haka nan ta tsinci kanta da son sanin menene wannan abubuwan dake motsi aƙasan wuyan maciji? wanda tun daɗewa bata taɓa ganinsu ba sai yau,waya sani ma ko wani akayiwa asiri ajikin macijin ?tabbas zatayi iya ƙoƙarin ta dan ganin ta raba macijin nan da wannan abubuwan ,ta yadda koda wani aka yiwa asiri  ta hanyar macijin, to asirin zai karye .sannan tana fargabar gwogwgo ta gano cewar tana gidan kuma bata ɗebo ruwan ba.kuma ahalin da ake ciki yanzu bazata iya komawa rafin nan ba ,.dan ta tsorata dasu jauro .

Hayaniyar mutane ce ta cika gidan  nasu fattu ,wanda haka yasa gwogwgo hansai fitowa dole badan ta soba, Dan har lokacin nan ita da yaranta ba wanda yayi sallar asuba.

“Kai su waye haka suka zo suka cika mana gida da  ihu kamar ana yaƙi?”cewar gwogwgo hansai tana gyara daurin ƙirjinta dake ƙoƙarin kuncewa bayan ta fito daga ɗakin.

“Aa meye hakan arɗo ?lafiya na Ganku da yawanku kun shigo?ta tambaya lokacin da idanunta ya sauka akan mutanen da suka cika gidan,kusan duk mazan garin ne.

Cikin masifa wanda aka kira da arɗo yace “wllh yau saimun ɗauki mataki akan bukar da fattu ,haka kawai yarinya ta fara kashe mutane ,kuma ta rasa ta kan wa zata fara sai ɗan gidan lamiɗo ?wllh yau sai mun kashe Shegiyar yarinyar nan”ya faɗa yana wani zazzaro idanu kamar zararre.

Eh wllh afito mana da ita kawai mukaita gurin lamiɗo ya bamu izini mu kashe mayya.gaba ɗayan mutanen gurin suka faɗi haka cikin nuna fusata da ƙosawa abasu fattun .

Wani irin farin ciki da jin daɗine ya kama gwogwgo hansai ,shikenan zata rabu da alaƙaƙai cikin sauƙi Allah yasa akasheta kowa ya huta ,dama su haɗa da bukar ɗin da yake ɗaurewa fattu gindi ,koba komai shanunsa sun zama nata.gwogwgo hansai ta faɗa cikin ranta.kafin ta kalli arɗo da sauran mutanen tace “aikuwa idan aka kasheta an kyauta ,dan nima nan wllh so take ta cinyeni nida yarana, jiya da kyar mukasha data maƙuremin wuya wai saita cinyeni, ku ɗan jira kaɗan yanzu zaku ganta shegiya gantalalliya,banma san inda ta tafiba, dama haka takeyi kullum inta fice yawon iskanci bata dawowa da wuri,tana can gurin maza”gwogwgo hansai ta ƙarasa maganarta tana mai buga hannu acinya.

“Aikuwa yanzu zamuje mu nemota ko ina ta shiga,wasu sutafi bakin rafin wasu sushiga jeji, mukuma zamu jira ana “cewar arɗo kenan yana kafe sandarsa akasa,sannan ya gyara tsayuwarsa.

Duk wannan abunda ke faruwa akan kunnen fattu, tana jin komai ,saidai tashin hankali,firgici tsoro da kuma ruɗewa sun hanata koda yin kwakwkwaran motsine .

Numfashinta ma da ƙyar yake fita tsabar ruɗewa.

Ta shiga uku !shikenan yanzu kasheta za’ayi?laifin me tayi da za’a kasheta?me baffanta yayi ake nemansa shima? Dama jauron mutuwa yayi ? innalillahi !!!yanzu ya zatayi.

Wani kukane ya kubce mata cikin sauri ta toshe bakinta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,ji take dama tana da ikon ɓacewa, tabbas da ba abinda zai hanata ɓacewa ta bar duniyar ma gaba ɗaya.

Ahankali ta miƙe cikin sanɗa ta leƙo da kanta ,ba ƙaramin tsoro tajiba lokacin da taga mutanen da suka zo tafiya da ita.shikena kawai ta mutu,yanzu shikenan bazata cika burinta na ganin innarta ba?wayyo “Allah ka kawomin ɗauki “ta faɗa cikin raunananiyar  muryarta mai cike da tsantsar  tsoro.

Ahankali ta ƙara leƙo da kanta waje ,cikin rashin Sa’a kuwa sukayi ido huɗu da dan gidan gwogwgo hansai umaru.wanda hayaniyar mutane tasa suma suka farka.

“Laaaah aradu gwogwgo ga fattun can cikin ɗakinta tana leƙowa”ya faɗa yana nuna ɗakin da Fattu ke ciki

.cikin hanzari fattu ta koma cikin ɗakin tana mai runtse idonta ,tare da dafe ƙirjinta.”shikenan sun ganni wayyo Allah na baffa,wayyo MACIJINA kana ina  kazo ka taimakeni zasu kasheni wayyo ni fattu”fattu ta faɗa tana mai leƙa hanyar nan da macijin Kebi idan zai bar ɗakin nata inya zo kamar Zariya  haka take bankada hanyar macijin da hannunta.

“Munafuka ,mayya dama kina ji ana neman ki shine kika ɓuya nan?to fito yau dubunki ta cika ,mutuwa zakiyi wllh saikin bar duniyar nan yau nima na huta da ganinki ,maza arɗo zoka tafi ta ita gata nan”gwogwgo hansai ke faɗin wannan maganar tana daga bakin ƙofar dakin Fattu,dan tun lokacin nan da tasha matsa agurin  maciji bata ƙara shiga ɗakin Fattun ba.

Aikuwa kafin ta rufe baki su arɗo sukayo kan Fattu suna janta.

“Wayyo Allah gwogwgo karki bari su tafi dani zasu kasheni ,wllh ban aikata komai ba wayyo Allah na gwogwgo ki taimaka min”abinda Fattu ke faɗi kenan tana miƙawa gwogwgo hannu cikin kuka mai tsanani.

“Ai wllh dana taimakeki gara hannuna ya karye Shegiyar yarinya ,kutafi da ita  can ku kashe banza” gwogwgo ta faɗa tana  kaɗa hannu irin yadda ake korar kaji ,cikin farin ciki take maganar.

Ihu Fattu keyi tana kuka,amma haka suke janta  kamar akuya aƙasa, suna cikin tafiya ne ,saiga baffa aguje yazo gabansuu ya tsaya riƙe da sanda yana ta haki,dan yana can bayan gari ya sami labarin abinda ke faruwa acikin garin da gidansa,shine ya rugo yazo .

Aikuwa Fattu na ganin baffa ta ƙara fasa ihu tana cewa” wayyo baffana ka taimakeni zasu kasheni” ta faɗa tana miƙa masa hannu,abin tausayi dukta susuce tayi buju buju da jiƙaƙkiyar ƙasa.kallonta baffa yayi 

Cikin bacin rai mai tsanani ya ce.

“Sakarmin yarinya arɗo,  kona rotsa maka sandar nan akanka” baffa ya faɗa cikin hargowa da ƙaraji,

Kasancewar baffa kowa  ya sanshi arugar mutumin kirki ne ,sam ba ruwansa da shiga harkar wani,sanan kuma shine ke ja musu jam’i ,hakan yasa suke ɗan ganin girma da mutuncinsa, dan haka cikin Turo baki da hura hanci  arɗo yasaki hannun Fattu wanda ke mata azabar ciwo da raɗaɗi,yana mai cewa”ato lamiɗo ne dai yace mu taho daku,dan haka ya zama dole ayiwa lamiɗo biyayya”ya faɗa yana hararar gefensa, dan yaji haushin sakin wannan hannun na Fattu mai shegen laushi da daɗin taɓawa da baffa yasa yayi.lol

Fattu kuwa yana sakar mata hannu ,da rarrafe ta ƙara so gurin baffa ta rirriƙe shi tana kuka da faɗin”wllh baffa ba abinda na aikata,ban kashe jauro ba ” ta faɗa cikin matsanancin kuka da tsoro, jikin ta sai rawa yake.

Riƙota baffa yayi cikin tausayawa yace “na sani Fattuna,baki kashe jauro ba ,kuma ba wanda zai kasheki, Allah na tare dake kinji”?ya faɗa cikin sigar rarashi,sannan ya kalli arɗo yace”kai arɗo ka kiyayeni ,karka ƙara ƙoƙarin  sake aikata irin wannan dabbacin akan ƴata, saboda baka da hankali shine zaka rinƙa janta aƙasa. Kamar wata dabba ?jahilan banza jahilin hofi,muje gurin mai garin zanji idan shiyasaka wannan ɗanyen aikin”baffa ya faɗa cikin mugun bacin rai yana mai riƙe Fattu suka nufi faɗa.

Lamiɗo na hangosu ya fara lasar baki ya kure fattu da idanu kamar maye , yana kissima abubuwa da dama cikin ransa….

Manage please yau ina busy,Dan banyi niyar typing bama yau wllh.

Masu karatu me lamiɗo ke nufine shima?

Hmmmmmm kubiyoni mu hade bayan sallah     danjin yadda zata kaya.

Kafin nan ina mana fatan yin salla lafiya,sannan aci Nama ahankali kar azo ana …….

Taku anty mammy 

Mrs babi,💘💘💘

Back to top button