Novel Document

Tambarin Sarauta Hausa Novel Document

Description/Story:

Tambarin Sarauta Hausa Novel Complete Document Written By Farida Bashir

Description

“Sauri takeyi domin ganin ta k’arasa gida, dan tasan yanzun *kaka* tana can hankalinta a tashe ganin lokacin dawowarta islamiya har ya wuce,
kallon agogon hannunta tayi, taga 7:30pm.

Jan wani dogon ajiyar zuciya had’ida k’ara yin sauri harda d’an gudunta domin ganin sallar isha’i ake neman akira yanzun.”

taja wani dogon tsaki ta juyawa ta kalli k’awarta Maryam da itama ganin *Afnan* d’in na sauri hankalinta a tashe ya sanyata itama yin saurin.”

Sannan Tace “Maryam duk kece kika b’ata mana lokaci wurin biyan haddarki, gashi yanzun dare yamana a hanya kuma bayan kinsan kaka ta tsani na kai magariba bana gida, ni yanzun bansan yanda zan cemata ba idan na koma gidan.”

Maryam tace “kiyi hak’uri Afnan bada son raina muka kai iyanzun bamu koma gidaba, koma meye laifin malam *Nura* ne da ya tsayar damu a cewarsa sai mun iya karatunshi sannan zamu dawo gida.”

*Afnan* bata kuma tankawa *Maryam* ba, domin batason yawan suruto, magana d’aya biyu takeyi sai tayi shuru,
da zarar da cika magana sosai,
ko kuma ana yawan yi mata surutu a akai to kanta ciyo yakeyi.”

Wannan dalilin ne yasanya ko k’awaye bata dasu, k’awarta d’aya ce *Maryam* itama unguwarsu d’aya kuma mak’otane sosai domin gida biyu ne a tsaninsu,
Tare suke zuwa makaranta Arabic da Boko.”

sauri kawai sukeyi ba Wanda ya kuma yiwa d’an uwanshi magana domin *Maryam* tasan halin *Afnan* sarai bata son yawan suruto

Karya kwanar da zasuyi, da zata b’ullewa dasu gaban gidansu,

saiji sukayi anja burkin mota da k’arfi.”

A razane suka firgita musamman *Afnan* gaban ne yashiga fad’uwa jikinta na rawa,

domin tasan kwanar gidansu mota bata fiya shuguwa ba, ga kuma duhun dare da somayi ba kowa ne mutum ke yawan wucewa ta wurinba.”

Kashe mata ido akayi da fitilar motar hankalinta ya kuma tashi idonta ta cika da hawaye, taja gefe d’aya ta tsaya tana jiran kowaye ya wuce sannan suma suwuce.”

Ganin motar tak’i tafiya kuma ankashe masu ido da fitila,
Maryam kuma na ganin hakan taja da baya da baya a tsorace ta antaya da gudu ta barta nan.”

Wani saurayi tagani yafito daga motar da alama a buge yake da giya, sai tangad’i yakeyi yanufota gadan gadan.”

*Afnan* naganin wurinta ya nufo, a tsora ce, ta k’ank’ame jikinta tadin ja da baya da baya cike da tsoro a fuskarta.”

Shima biyarta yakeyi yana kallonta yana murmushi.”

itama kallonsa takeyi domin bata tab’a ganin kalar wannan fuskar tashiba,
amma alamu sun nuna cewa d’an sarkine diba da tayi da kalar shigar da yayi da kuma hularshi mai *Tambarin sarautar* masarautar sarki Ahmad Moh”d,
Sai kuma alkibbarshi dake rataye a kafad’arshi,

” *Bassam* kenan d’an sarki maiji da kud’i da mulki ya taka duk Wanda yakeso a garin yanda yaga dama.”

nufarta yakeyi da wani kalar murmushi a fuskarshi,
domin ganinta yakeyi sak kamar budurwanshi *Basma* wanda suka rabu da ita yanzun a club.”

Kamota yakeso yayi ya rungume amma besamu sa’ar yin hakanba, sai yashiga fad’in “haba *Basma* yau kuma guduna kikeyi?” Yana nuna kanshi cike da maye.”

ita kuma tana ja da baya cikin tashin hankali,
Tana zubarda hawaye “wannan bala’i daya keso ya tunkarota cikin daren nan, gashi unguwarsu mutune basu cika wucewa ba idan dare yayi hakan.”

Wannan dalilin ne yasanya *Kaka* bata barinta fita waje, da zarar suntaso daga makarantar islamiya k’arfe shida, to bata barinta Zuwa ko ina sai kuma gobe.”

“Amma yau gashi kaddara takirata har isha’i tana waje, gata yanzun ta had’u da wannan bala’i a gabanta,

“Tasan yanzun wannan mashayin ko kasheta zaiyi ba Wanda zai fito ya taimaketa.”

Ta kuma fashewa da kuka mai sauti tana addu’a a zuciyarta “Allah yakawo mata d’auki.”

cigaba tayi da Jada baya shima yana kuma kusan tota, har takawo jikin wani shago dake kulle taja ta tsaya, had’ida runtse idonta tana zubar da hawaye, tana addu’oi.”

Yana zuwa daf da ita ya kuma ganin takoma mashi *Basma*shi sak,👌🏼 ya kuma sakin wani murmushi irin na mashaya, yarik’o hannunta ya murzashi yace “haba *Basma* baki ganeni bane kike guduna?”
Wata gyatsa yasaki mai d’auke da warin giya, da tsami.”

*Afnan* tayi saurin toshe hancinta, cike da tsoro da kuma b’acin rai, “domin tunda Allah ya halinceta babu namijin da yatab’a rik’a mata hannu sai yau.”

Bata ankaraba saijinsa tayi ya rungumeta yana fad’in *Basma*yau ni kike toshewa hanci?” Warina kikeji ?”

Aikuwa wani k’arfi ya zo mata,
cike da b’acin rai ta tureshi daga jikinta tasanya hannu biyu ta kwad’a mashi lafiyayyen mari mai kyau a kuncinshi, wadda sai da ya kusan dawowa hankalinshi,

Hakan yayi dai dai dawowar wutar Nepa, *Prince Bassam* rik’e da kunci yayi tsaye tsam, ya kurawa *Afnan* ido ko gyaftawa bayayi kamar wanda ke tunanin wani abun.”

Bata ankaraba taji muryan *Maryam* tareda mahaifinta Malam *Iro*,

Malam *Iro* yace “kinyimin dai dai *Afnan* dakika mari wannan mutumin Wanda besan darajar d’an Adam ba.”
yanunashi da yatsa👉🏻

 

File Name   Tambarin Sarauta… Hausa Novel Doc.
Title   Tambarin Sarauta Complete
Author   Farida Bashir
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    16/07/2024
File Size    500Kb
Format Size     TXT
Phone No      NIL
Download Tambarin Sarauta Complete Novel Document By Farida Bashir

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button