Hausa novels

Zakuna Biyar Page 3 By Princess Teema

5:30AM AGOGON AZURE BARRACK TA BUGA. Gabaɗaya matasan sun haɗe a filin nan, da yake akwai tsari da natsuwa sai dik suka shiga cikin layi mai kyau.Kowannensu yana abin da yake yi, ZAYNASH and VASH hira suke ta yi da juna gwanin burgewa, tamkar sun jima da sabawa da juna, shi kuma NIRASH sai duba wata ƴar takardan hannunsa yake yi yana tsaye a can jefe bai shiga sahun layi da su ba. Sai lokacin da Captain ya kariso wajen ne NIRASH ya nufo in da sauran matasan suke, a gaba ya tsaya tare da rufe takardan hannun nasa, da yake ƴar karama ce sai ya turata cikin aljihu, dik suka mayar da hankali kan Captain dake tsaye a gabansu. ——————🔥Yana tsaka da barcin da ta ɗauko ɗanɗano da daɗi, har mafarkin sisters ɗinsa yake yi, ya saba kwanciya a saman laps ɗinsu yai barci har ya tashi ba zasu saukesa ba, yau yana kewa, gadon gidan soja bata yi kama da cinyar sisters ɗinsa ba. Ya yi nisa a cikin mafarkin da yake yi tamkar saukar aradu haka ya ji an takasa da wannan shegiyar takalmar tasu, da karfi Commander ya takasa har sai da ya faɗo ƙasan gadon. Ko a fuska kuka ga commander kuka ga Captain kun san Captain Onbish ya fi imani da tausayi, Commander ko kaɗan babu ALLAH a lamuransa, bakin mugu ne da ya ga jiya ya ga yau a GIDA SOJA, in taƙaice maku shi ya horar da su Captain Onbish ɗin ma! Kunga kuwa dole wannan ba zai yi tausayi ba!. Ƴar kara Noor ya saka tare da waro idanunsa. Ganin mutum a tsaye a kansa fuska babu alamar annuri yasa yai mahaukacin razana, dan shi fa ya manta a GIDAN SOJA yake. Ihu ya kurma sai kuma lokaci guda ya ɗauke wuta ɗiff alamar ya kame ko ya suma, kar ku manta irin ciwon da yake da shi.Daddynsa ya ɓoyewa GIDAN SOJA wannan batu, kuma magana ake ta ba dik kai ke zuwa wannan gida ba, kunga magana ake ta daddynsa na da daloli, dan haka ba zasu zurfafa ba!. A maimakon Commander ya tausaya mashi ganin ya suma, sai ya sake sanya kafarsa ya take nasa kafafun yana ce mashi ya tashi ya fita wajen horo cikin ɗaga murya. Sai dai dik tsawar da ya yi a banza, dan Noor bai motsa ba. Hakan yasa ya ɗan duƙa a gabansa, nan ya tabbatar da ya suma. Siririn tsaki ya ja tare da kwalawa wasu jaratan sojoji biyu kira, dama tare suke bin ɗaku-ɗakuna suna tashin sauran basu tashi ba!.Da wani irin gudu kamar gangsters waɗan nan sojoji suka shigo room ɗin. Da hannu ya nuna masu Noor game da cewa. “Ku zuba mashi ruwa kafin ku ɗaukesa zuwa wajen horo”. BABBAR MAGANA, watau ba ɗaga kafa babu tausayi!. Da sauri soja ɗaya ya matsa kusa da shi, hannu yasa ya cicciɓesa sai saman shoulders ɗinsa. Shi kuma Commander ya fita zuwa sauran ɗakunan dan tabbatar da kowa ya fita. Waɗan nan sojoji babu tausayi babu tausayawa suka kai Noor wajen babban tap na barrack ɗin. A kan fuskansa suka kunna tap ɗin. Ai ruwan nan na taɓa fatansa a wani irin gigice ya farka yana ambatar sunan Aunty Lusi, da alama ta fi kula da shi a gidansu. Janyesa daga wajen tap ɗin suka yi ganin yana neman sake rasa numfashinsa, suka tsayar da shi a kan kafafunsa, sai ƙoƙarin tangaɗi yake kamar zai faɗi. Sai dai yana waro idanunsa take ya shiga natsuwarsa, dan ganin waɗan nan sojoji yasa ya tuna ashe fa GIDAN SOJA yake, sai ya ji ya kara tsanan aikin fiye da yadda ake zato.Basu bari ya samu damar tinani ba ɗaya ya daka mashi tsawar da ya sanya shi firgita, in a harsh way suka ce ya wuce wajen horo kafin jikinsa ya gaya mashi, bashi da zaɓin da ya wuci ya wuce da sauri, dan bai ga alamar wasa a wannan waje ba! Waɗan nan sojoji tsab zasu iya cinyesa ɗanye a cewansa.Haka ya wuce zuciyansa na tsananta bugu da razana saboda tsawan da suka yi mashi ya tsorata sosai. Shi ko wanka bai yi ba, ga jikinsa a jike da ruwa, babu damar ya koma ɗaki bare ya canza kaya!. ——————–🔥Cikin kakkaifar murya Captain ya ce da matasan. “Ready!!”. Take dik suka buka ƙafafuwan a kasa, at the same time suka ɗaga hannu suka sara mashi alamar gaisuwa. Kai ya jinjina masu haɗe da sake cewa. “1, 2, 3 start!” Cikin ɗaga murya.Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA…… “We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom’s call, for justice true, Our oath is strong, we’ll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!”. (My people ya kuke tinani idan za’a rera taken nan da gangar ƴan BB? Uhm.)Jinjina kai Captain yai tare da cewa. “Kamar yadda kuka sani ne dole yau zamu fara horonmu, yakamata tin last week zamu fara amma abubuwa suka ɗan shiga cikin lamarin wanda already kun sani ba sai na tsaya dogon bayani ba, yanzu zamu fara da matakin farko, dole ne ku yi tafiya da sauri cikin tsari na tsawon mil biyu domin gwada ƙarfin jiki a fannin safiyar nan, so get ready again!”. Ya kai karshe yana rarraba idanunsa a kansu, da yake wajen akwai haske sosai. Sai da ya tabbatar da kowa ya hallara a wajen, aka kira sunan kowa dake rubuce a document, suka amsa, sannan ya ɗan yi gyaran murya.Kara haɗe natsuwarsu waje guda suka yi, da karfi Captain ɗin ya ce masu start. Sai da suka sake sara mashi kafin su fara tafiya cikin tsari da natsuwa amma da sauri, a lokacin su Zaynash basu lura da Noor a wajen ba, dan a baya ya tsaya da ya zo.Sai daka hamma yake yi, saboda shi har ga ALLAH barci bai ishe shi ba, ba dan wannan Commander maras imanin nan ba ALLAH da ba zai tashi ba.Hannayensa NIRASH ya zura cikin aljihun wandonsa suka cigaba da tafiya har na tsawon wannan bil biyun, suna tafiya wasu suna hira, wasu suna cewa ashe ma aikin sojan ba wahala, shi ne sai tsoratasu ake yi, ashe iya wannan ɗan tafiya ne, ai wannan sai su kwana suna yi.Haka a tinanin Noor ma shikenan zasu koma ɗaki su yi barci daga wannan ƴar tafiya, sai kuma me? Suna kai daidai gaɓar mil biyu wata hanya ta rabe a wannan waje, nan fa Captain dake biye da su amma ta gefe ba’a cikin layinsu ba ya umarcesu da su sauka daga kan wannan hanya su bi ɗayar. Nan da Noor ya gane lallai already wannan hanya an shiryata ne ma dan horar da su, shi fa wlh bai shirya aikin soja ba, kawai daddynsa ya ja mashi balai yana zaune cikin sisters ɗinsa gwanin burgewa, da yanzu ko shirin tashi barci bai yi ba. A daidai wannan lokacin ne kuma su Zaynash suka lura da shi, da sauri suka isa in da yake, Vash ne ya fara cewa. “Noor yana ga jikinka dik ruwa? Baka canza kaya ba! Kana son mura ta kamaka ne?”. Zaysh (Zaynash) ne ya ce. “Meyasa baka cire wannan kaya ba? Zaka yi ciwo!”. Cike da kulawa game da tausayawa haɗe da gaskiyarsu suka faɗa. Amma Noor sai ya dallah masu harara, a fusace ya ce. “Kada ku sake yi mun magana, mugaye kawai, ai kun san me aka mun da zaku wani zo ku nuna kuna sona!”. Da sauri Zaysh ya ce. “Wlh bamu san me aka yi maka ba”. Vash ya amsa da. “Noor muna sonka mana”…… A kufule ya amsa da. “Da kuna sona da baku bari waɗan can azzaluman sun azabtar dani ba, dan haka karku sake yi mun magana”. Ya kai karshe tare da wucewa. Captain dake kallonsu ya so yi masu magana a kan cewa ba’a tsayawa magana da juna haka, amma kasancewar ranarsu ta farko ce sai ya kyalesu. Jiki ba kwari suka bi bayansa, dan wlh ya basu tausayi tin ma basu san me matsalarsa ba. Tafiya mai ɗan nisa suka yi a wannan hanya da suka sauka kafin su isa wani tapkeken fili mai girman gaske wanda ya fi hall ɗinsu sau goma, fili ne mai cike da duwatsu, tsaunuka da shinge, daga karshen filin wani dogon bene ne mai step-step sun kai 100 zuwa 150, tsawon staricase ɗin nan ya yi mugun basu mamaki, kuma ba ɗaki bane, just steps ɗin ne kawai aka yi har sama, kuma saman ma babu komai, dan horon gwarin gwiwa kawai aka yi wanna bene.A bakin wannan fili Captain ya umarcesu da su dakata, dik tsayawa suka yi suna mai da nunfashi a hankali-hankali. Sai dai Captain bai bari sun huta ba ya yi cauting from one to 3 ya ce su je da gudun gaske su isa wancan steps ɗin. Da yake har yanzu da ɗan sauran karfinsu sai suka kwasa da gudu sosai, Noor shi ne na karshen zuwa wannan waje, dan tsabar ragwanta da barci da yake kansa, ga ruwan da ya sha, while NIRASH and ZAYSH sun rigasu isa wajen. Shi kuma Captain cikin zafa ya ɗan taka har ya isa wajen, hakan ya basu damar ɗan hutawa kafin ya iso. Dan yana zuwa ya umarcesu da su tattakawa su haura wannan steps har sama a cikin mintuna ƙasa da biyar su kuma sauƙo.Ai zazzaro idanu Noor ya yi, cike da damuwa ya matsa kusa da VASH tare da cewa. “Bro I’m tied wlh, ba zan iya ba, hawa sama fa, no, my legs done tied over”. Bawan ALLAH fushinsa na ɗan lokaci ne, har ya manta ya ce kada su sake yi mashi magana ma. Ganin ya nuna manta da kalamansa na ɗazun ne yasa suma suka manta, Vash ya ce mashi. “Noor this is just the beginning for our training, saboda yau ranarmu ta farko na karɓar horone ma yasa kake ga ake mana ƙananan abubuwa, i promised you in the next one week dik wannan tafiya for two mil zai canza zuwa 10 mil to up, dik horo zai ninka kansa, kawai abin da zance shi ne, kada ka kunyata daddynka, kaga ni na shiga soja ne for my dad, kafin ya mutu kullum maganansa ɗanya in zama soja, shiyasa granny ɗina ya horar da zuciyata da kaunar aikin, i will do all my best dan ganin na cika burin daddyna, i wish yana raye a lokacin da zai ganni da kaki, amma ba komai”. Tin da ya fara magana idanun Noor suka cika da kwallah. “Sorry for the rashin dad bro”. Jinjina kai kawai ya yi kafin ya rike hannun Noor da kyau….. “Be strong, zaka iya my brother”. Noor da yasan ba zai iya jurewa bane ya ce. “I will try, but not sure zan iya”. Jansa ya yi suka fara tattaka steps ɗin da sauri yana faɗin. “By the grace of God zamu fito da good result mai kyau and a rukuni guda zamu fito, zamu yi aiki a tare”. “I wish that”. Noor ya faɗa tare da zaro idanunsa waje, dan yaga NIRASH har ya hau yana saukowa su yanzu suka yi rabi, mamaki ne ya kamasu daga shi har VASH, yanzu ya kara tabbatarwa da gaske NIRASH yake wannan aiki ba wasa ba. Haka suka sha faman hayewa sama da kyar suka sauko, suna saukowa Noor ya durkushe kasa a waje yana wani irin haki da ɗan karfi-karfi. Hutun five mins Captain dake tsaye yana kallonsu ya basu kafin ya sake umartansu da su yi gudu sosai zuwa wajen waɗan nan duwatsu da tsaunuka, ba musu suka dallah da gudu suka nufi wajen, amma fa a wannan karon ma Noor ne na karshen zuwa, dan shi wlh bai huta bama Captain ya sake tashinsu, ga shi idan baka tashi ba wasu zaratan sojojin huɗu dake binku a baya da manyan bulalu su baka a jikinka. Da suka isa sai da suka ɗan jira Captain, hakan ya kara basu damar hutawa kaɗan. Yana zuwa ya umarcesu da su fara tsallaka ƙananan tsaunika da duwatsun nan. Nan fa Noor ya ce shi ba zai iya bafa, dan kafafunsa zafi suke yi mashi, abinku da renon madara and ice cream. Hannunsa VASH ya ja yana faɗin. “Wlh a wannan gida babu tausayi babu tausayawa, shiyasa idan soja yakama mutum babu imani yake jibgar bawa, a wannan horo dakake ganin mun fara ake cire masu dik wata tausayi da imani, saboda bakin azaban da suke sha, in har baka tashi ba, wlh Captain na iya sanya wannan shegiyar takalmar tasa ya tattakaka, ko kaɗan ba zasu tausaya maka ba, so is better for you to stand up”. Tabbas Noor yasan gaskiya VASH yake faɗa mashi, saboda yasan dokokin gidan soja, yakaranta komai ya kuma cika komai, dan haka babu uwa, babu uba, babu ƴan uwa, wlh ya yi gardama mugun azaba da bakin duka zai ci, kuma a banza ya daku in an dakesa, babu mai tausaya mashi daga cikin manyan sojojin nan, su gama dukansa su haɗa shi da horo mai azaba, a haka zai goge, ya fi mashi sauƙi ya miƙe ya bi umarni kawai.Idanunsa sun cicciko da kwallah haka ya miƙe ya nufi waɗan nan duwatsu ƙanana dake gefen manya-manyan, da kyar Noor yake iya tsallakasu. A wannan waje good 20 mins Captain ya basu suka yi wannan aiki kafin ya wuce da su wajen wasu igiyoyi dake ɗaɗɗaure, kasansu ruwan taɓone mai ɗan zurfi.Cikin kakkausar murya ya ce. “Zaku rarrafa cikin ruwan nan ne a kasa da minti biyu ku fita ta gefen can, kada wanda ya bari kansa ya taɓa igoyiyin nan, idan kanka ya taɓasu tabbas zaka sako ne daga farko, kuma kada wanda ya bari kansa ya taɓa ruwan!!”. TOH FAH!Ai dukkansu bin ruwan da kallo suka yi, yana da tsawon taku 30, sannan suka ga igiyoyin da aka ce kada kansu ya taɓa, lallai aiki ne babba. UHM BASU SAN AIKI BABBA MA YANA GABA BA, AI YANZU MATAKIN PRIMARY SUKE, SAI GABA.Wasu kuma takaici suke yi na fararen t-shirt dake jikinsu, yanzu shikenan rigarsu ya tashi a aiki kenan? Ga shi basu ga alamar fuska a wajen Captain ba bare su ce ya yi hakuri ya bari sai gobe zasu shiga kada kayansu ya ɓaci, gobe sai su sako bakaken kaya, ba hali, dole suka ɗaura ɗamara, sun fi su 100 a wajen, amma mutane uku ne suka fara faɗawa cikin ruwan kai tsaye, ciki harda NIRASH wanda shi ne farkon faɗawa bayan ya ajiye littafin da yake karantawa ɗazun da watch dake ɗaure a hannunsa a gefe kusa da Captain, ya faɗa cikin ruwa ya fara rarrrafawa da gwiwowinsa. Zaysh ya rufa mashi baya, sai wani kyakkyawan chocolate guy dake tsaye a kusa da su shi ma ya faɗa.Shi kansa VASH a wannan karon tsayawa ya yi yana kallon Noor cike da tashin hankali, dan wlh bai kawo a ransa zasu shiga ruwa ba, ga balain sanyi da ake yi. Muryar Captain ce ta karaɗe kunnuwansu da cewa. “Mintuna biyu gareku, dik wanda minti biyu ta gota bai fito ba sai ya sake farowa, zai yi ta farowa har sai ya fito a mintuna biyu ko ƙasa da hakan”…… Ai tin kafin ya rufe baki mutasa sun kai 30 suka faffaɗa, still dai Noor and VASH suna tsaye, saboda sun gaji. Ɗaya bayan ɗaya matasan nan kaf suka faɗa saura su biyu, suka ci minti ɗaya a tsaye a wajen, sai da sukaga babu wani sarki sai ALLAH sannan suka faɗa cikin ruwan suna aikin haɗe rai. Sai dai ko tsakiya basu kai ba mintuna biyu suka cika, Captain ya yi wa waɗan da suka fito kafin mintuna biyu alama da su ja baya, su sun tsira. Waɗan da basu fito ba har mintuna biyu ya cika suna fitowa aka ce su sake farawa, tamkar zasu yi kuka haka suka sake komawa, a karo na biyu ma Noor and VASH basu fito a mintina biyun ba, kun ga rarrafe ba kamar tafiya a ƙafa bane. Hakan yasa aka sake mayar da su, da dai VASH yaga babu mai iya kwatarsa a wannan gida, Mama no dey baba no dey fa sai ya zage a karo na uku ya fito a ƙasa da mintina biyu. Shi kuma Noor tin yana da sauran karfi har ya gaza, amma bai iya fita a kasa da mintuna biyu ba. A tinaninsa taimaka mashi za’ayi idan ya gaza, ina ai sai ya ga akasin haka, dan a horon soja ba’a taimako, shiyasa zaku ga suna tashi a marasa tausayi, to ba’a gwada masu tausayi da imani ba a yayin horo, ubansu suke ci har zuƙatansu su bushe ba kaɗan ba. Ai Noor bai tashi sanin a GIDAN SOJA GIDAN WUTA yake ba sai da ya ji saukar wannan uwar kwandorom ɗin takalman Captain a tsakiyar bayansa, ya takashi da karfi a cikin ruwan yana daka mashi tsawan ya yi sauri, dan kowa ya fita saura shi kaɗai, yana ɓata masu lokaci. Dole tasa Noor ya cije, yana zafafan hawaye ya fara iyo a cikin ruwan nan, da kyar da suɗin goshi, ya maimaita sama da sau biyar, sannan ya iya fitowa a mintuna biyu daidai. Da ya fito a tinaninsa barinsa zasu yi ya huta, sai fa ya ga akasin haka, domin kuwa sake zangon tafiya suka fara yi dan komawa ainahin cikin Barrack in da suka fito kenan, a lokacin karfe 7 daidai ta buga, sun ɗauki awa ɗaya da rabi a wannan waje kenan suna horo. Da kyar Noor ya iya kai labari, ya ja kafafunsa suka karisa wajen, suna zuwa suka tsaitsaya a wannan katan fili da suka tsaya bayan fitowarsu daga ɗakunansu, a nan ne Captain ya ce. “Mintuna 30 gareku na yin wanka da canza kaya, 7:30 daidai zaku fara breakfast, zuwa 8 dole kun gama, 30 mins na ɗan hutawa dan kuna sabbin zuwa, 8:30 zaku fara gwada horon hannun zuwa 11 zaku shiga class! Lokacinku ya fara daga yanzu!”. With harsh voice ya faɗa. Ai da gudu suka fara watsewa, ji kake dam! Dam! Dam! Suna taka kasa, dik suka watse ya rage Noor da baya iya tafiya da kafafunsa sosai. Da gudu VASH ya dawo baya ya zo ya taimaka mashi suka koma room ɗinsu. Da yake suna girmama lokacin, dayawansu cikin kasa da mintuna 15 suka kammala shiri except Noor da suna shiga ɗaki ma bajewa ya yi a kasa yana jan doguwar numfashi game da saukewa a hankali-hankali, har su VASH suka gama wanka, dik suka shirya cikin wandunan jeans and t-shirts masu balain kyau shi yana zaune. Vash ne ya ce. “Noor 30 mins garemu fa, kasan dokoki da tsare-tsaren gidan nan, ba’a kauce lokaci!”…. Yana kwaɓe fuska ya ce. “Ni babu in da zan sake zuwa!”…….. “Noor baka son lafiyar jikinka na lura, gara maka fa ka tashi, dan wlh in muka gama breakfast ko baka yi ba lokacin horo dole Captain ya fito da kai da duka”. Noor zai sake yin magana, Leo ya riga shi da cewa. “Make sure you clean this floor before I come back”. Maganansa ta farko a garesu keman. A natse ya yi magana, yana da murya mai sanyi da kaifi ga balain daɗin saurara, yana gama faɗa bai jira amsarsu ba, infact bai ɗaga ido ya kalli in da suke ba ya sa kai ya wuce da sauri abinsa, dan ya kammala shirinsa cikin wasu zafafan kayan dake nuna shi ɗan royal family ne, kansa sanye da army p-cap…….. Yana yawan sanya p-cap ne saboda baya son kallo, in dai zai bar gashin kansa a buɗe sai an dinga kallonsa ko ina ya juya, shiyasa yake yawan rufewa, bugu da kari p-cap ɗin na ɗan hana ganin face ɗinsa sosai, ya huta da idanun jama’a a kansa, ga kuma kitso a kansa da ya yi, ai dole ayi ta kallonsa, kyan gashi kyan kitso da kyan halitta. Say Masha ALLAH.Bayansa suka bi da kallo. ZAYSH ne ya ce. “This guy acting like he’s our parents, ji yadda yake bamu umarni”. ……… VASH ne ya ce. “I don’t know why I like his character”………. “Same to me bro, and I like his sharp voice, ji yadda ya yi magana yanzu fa, like wow”. Noor ya faɗa yana cigaba da kwaɓe fuska. “Yeah, yana da tsari mai kyau for his life, but why baya mana magana bayan we’re together in the same room?”. Cewar ZAYSH da abin ke bawa haushi….. “That’s why a like his style, he don’t want to talk, and hakan girmama kai ne, amma dai yakamata ace yana yi mana magana like friends tinda we’re the same now, and kuma ba wani finmu shekaru ya yi ba fa”. Cewar VASH. “We lost 5 mins again, ba lokacin wasa bane yanzu, let’s go guys”. Zaysh ne ya faɗa. Da sauri Vash ya ce. “Noor I don’t want to see you in this situation, please tashi ka yi wanka, kaga dattin jikinka ya ɓata mana floor har wannan mai fuska irin na gangsters ɗin yana baka command na ka gyara masa waje ko?”. “Ai ba zan gyara ba, da wani nuna isa da iyayin nan nasa”. Noor ya faɗa yana ɗaure fuska kafin ya daure ya miƙe, da kyar yana tangaɗi ya afka cikin toilet. “Bari in taimaka mashi in gyara wajen”. Cewar Vash yaro mai saukin kai, kuma iyayensa manyan kai ne, amma yana da sauki sosai. Da sauri Zaysh ya ce. “Don’t do that, ku bar wajen haka in ga uban me wancan ɗan rainin hankalin zai yi idan ya dawo, ba ya wani ce mu gyara mashi waje ba? To ku bari mu ga me zai iya”. Ɗan zazzaro idanu Vash ya yi. “But not for him kawai ai, cleaning the place is for our healthy all”…….. “I know that, but for now ka bari mu ga gudun ruwan shi, me zai iya yi mana, kasan fa idan bamu gwada mashi muma guraye bane ba zamu zauna lafiya da shi ba, yana wani ɗaga mana kai like ya fimu ne, idan ya yi wasa ma muka gama horon nan result ya fito a karkashinmu zai yi aiki”. Noor da ya fito yanzu ɗaure da towel ne ya jingina da jikin bangon wajen toilet ɗin tare da cewa. “Da kuwa ya gane kuransa, ni dan in bashi wahala har takalmata zai rinƙa wankewa”. “Zaysh, Noor kuna da matsala, idan aka biye ta ku zamu ɓata breakfast time ɗinmu a nan”. Vash ya faɗa……. Karisowa ciki Noor ya yi, da sauri ya hau shiryawa yana tinanin yadda zai rinƙa gujewa horon nan. Waje Zaynash ya nufa yana jin haushin Leo a ransa, saboda yadda yake nuna masu shariya. Hall na cin abincinsu ya nufa, yadda tsarin hall ɗin yake wajen cin abinci ne da kowani table yake ɗauƙe da four chairs, kuma kowani table da number ɗakin mutane a jiki, kamar su Leo da ɗakinsu yake room number 1, to haka table ɗinsu ma yake da number 1 a jiki, su huɗu ne a ɗakin kazalika chairs huɗu ne a wajen. Zaune Zaynash ya isko Leo yana cin abincinsa cikin natsuwa da tsari yana kuma ɗan naɗe yatsun hannunsa kamar yana tasbihi, ya duƙar da kai ƙasa, dikkan sauran matasan ma suna zazzaune suna cin nasu abincin cikin tsari da natsuwa. Saman chair Zaynash ya zauna tare da jawo plate ɗinsa dake rufe ya buɗe.Wake ne da ƙwai dafaffa domin ƙarfafa jikinsu da ƙara masu kuzari, sai black tea mara madara, dan madara tana sanya kasala, su kuma ba’a buƙatarsu da kasala, ga bread a gefe, sannan ga lemu guda ɗaya domin kuzari da rage gajiya. Waken Zaysh ya fara ci yana ɗan satar kallon yadda Leo yake cin abincinsa tamkar baya son motsa baki, shi da yake namiji ma sai da abin ta burgesa bare mace.A lokacin cin abincinsu fa ba a yarda a yi magana ba. Kowa yana ci da gaggawa, saboda su gama cikin 30 zuwa kasa kacal! Idan soja ya yi kuskure ko ya kasa gama cin abincinsa a cikin waɗan nan ƴan mintocin, to za a tura shi ya yi tsalle kwaɗo guda 100 ko gudu na musamman kafin a bar shi ya tafi, kuma ba zai cinye sauran abincinsa ba. A haka su Noor suka kariso suka sami su Leo, zama suka yi suka hau cin abincin suma a cikin gaggawa, dan saura 5 mins 30 mins da aka ɗeba masu ya cika. Kafin 8 ya cika sun kammala cin abincin nasu, a nan Captain ya umarcesu da su tashi su nufi wajen da aka tanada dan ɗan miƙe kafafunsu kafin 8:30 ya cika. Da sauri suka miƙe suka nufi wajen. Zama suka yi Zaysh and Vash suna ta gulmar Leo, kai Vash har da cewa. “Tun da ya zo yana wani naɗe yatsu ko me yake yi haka oho?”………. Zaysh ya ce. “Ni ban yarda da shi ba, daga gani daga familyn gangsters ya fito, ji wani kitso dake kansa ta bayan wuya fa”. Da sauri Noor da Vash suka kai kallonsu kan bayan wuyansa ta ƙasan p-cap ɗin, a nan suka lura yana da wani abu a wajen dab gashin kansa tamkar wani zanen fuskar wani abu haka, kurawa wajen idanu Vash ya yi.Shi kuma Noor da ɗan ba ruwana ne sai ya ɗauke kallonsa daga wajen tare da cewa. “Kuma kyakkyawa ne sosai wlh guys”…….. “Ana cin kyau ne?”. Zaysh ya faɗa a kufule. Murmushi kaɗan Noor ya yi wacce ta kara fito da kyansa. “To ai kaima Zaysh kyakkyawa ne, ni wlh suna mun kama da Vash ma wani zubin”…… Vash ɗin ne ne ya yi sauri cewa. “Noor banda kalaman yaudara, ta ina muke kama?”. “Seriously kun mun kama”. Cewar Noor. Da sauri Vash ya sake cewa. “Baka son gaskiya dai”…….. Zaysh ne ya ce. “Ku daina wannan zancen muyi focusing akan abin dake gabanmu na horo”. Kun san wani abu? Shi fa Zaynash so yake yi ya zama na ɗaya, yana jajircewa ne sosai dan ya tsallake horo lafiya ya fita da result mai kayu da karfi, ya fita a babban soja, to ya ga kuma dik ƙoƙarinsa Leo yana wucesa, ya yi iya yinsa ya isa waje sai ya samu Leo ya rigasa, to wannan abin ne yasa yake jin haushin Leo ba komai ba, yana son idan suka kammala horon nan ya zamana shi zai fito da matsayin shugaban rukuninsu, dik matasan sojijin nan su zama a karkashin ikonsa, amma yaga Leo na ƙoƙarin kawo mashi cikas. Kuma a cikin wannan rukuni na horon shekarar nan, su uku ne zakwaƙurai wanɗan da tin a horon farkon nan manyan sojojin suka gane hakan, da Leo, Zaynash sai wani ɗan Nigeria mai suna Unays a room number 2 yake, suna da jajircewa matuƙa, dan dik horon da suka yi yau su ukun nan ne a gaba, sai dai da alama za’ayi zazzafan gasa a tsakanin su ukun nan wajen tsai da goni ɗaya, saboda yadda suke jin haushin juna, Zaynash yana jin haushin Unays da Leo, while Leo baka gane ainahin ina ma ya dosa, yana jin haushinsu ko baya ji dik ba’a gane mashi, shi ma Unays haushin Zaynash and Leo yake ji, saboda suna zuwa daidai da shi, ya so ace ya fi kowa, ga shi ɗakinsu makwabtan juna ne. KAI AKWAI KALLO FA A GIDAN SOJA WLH, ZAZZAFAR GASA, KU DAI MU JE ZUWA.8:30 daidai Captain ya dawo hannunsa rike da wata sharɓeɓiyar bulala wacce ganinta kawai tashin hankali ne. A saman stage dake wajen ya tsaya yana faɗin. “Ready! Zaku fara horon daidaito a yanzu, zaku koyi yadda za ku tsaya da ƙafafunku ba tare da fargaba ba a lokacin harbi ko farmaki ƴan ta’adda”. Mimmiƙewa tsaye suka yi, sai suka fara kallon juna. Muryan Captain ɗin ne ya katse masu kallon da suke yi da cewa. “Kowannenku ya kama abonkin matsaya a tare”…….. Basu gane nufinsa ba, hakan yasa suka sake binsa da kallo.Ɗan gyara murya ya yi tare da sake cewa. “Ku shiga rukuni guda, dik ƴan ɗaki ɗaya su kasance a tare waje guda, zaku tsaya ne da kafafunku ɗaya a kasa, ɗaya zaku ɗangalesa a sama, dik wanda ya saki kafansa ɗayan kafin lokaci ta cika, to dikka saura mutane ukun da suke ɗaki guda zasu je da gudun gaske su taɓa wancan post dake can, wanda ya yi karshen dawowa kuma zai karɓi bulalu guda biyu masu kyau”. A miliyan suka juya suka kalli post ɗin da yake magana a kai, mugun nisa ne da shi, suka sake juyowa suka kalli bulala dake hannunsa, lallai fa babban aiki, kuma dikka wannan ace farko ne ake masu kaɗan-kaɗan? Tab gaba sai yaya kenan? Kallon juna suka sake yi, a fili Noor ya ce. “Wani kaddara ya kawoni aikin soja ne wai?”. Yana kwaɓe fuska ya faɗa. Sai kuma ya juyo da kallonsa a kan Vash, Zaynash da kuma oga Leo. Wani irin kallo Leo ya wurga mashi har sai da ya ji maƙoshinsa ta bushe yana buƙatar ruwa, in a cool way sosai Leo ya ce. “If you people cause us to fail, then what?”. Then he went silent as if they already knew what would come next.”Ready”. Captain ya faɗa yana kallonsu. “Start”……. Da sauri dik suka ɗaɗɗage kafafunsu ɗaya sama suna bubbuɗe hannaye tamkar zasu tashi sama. Zubawa lokacin ido Captain ya yi a agogon dake hannunsa, lokacinsu ya fara daga yanzu kenan. Unexpected from nowhere suka ji karar harbi da bindiga, ai kusan rabi da kwatan waɗan dake wajen sai da suka sauke kafafunsu, wasu ma har ƙoƙarin gudu suka yi, su da ake koyawa yadda zasu saita natsuwarsu a lokacin yaki, amma sune suka razana har haka daga jin karar bindiga, tab da aiki kenan, da gangan aka buga bindigar dan a gwadasu dama. Nan fa Captain ya sanyasu gudu zuwa taɓa post, bayan sun dawo waɗan da suka yi last a kowani team suka sha bulalu bibbiyu a gadan baya, haka ya sake cewa su ɗage kafafunsu, Leo and Zaynash da Unays makocinsu sun jajirce sosai, ko da wasa basu sauke kafafunsu a lokacin karar bindigar ba, dik da cewa sun ɗan razana.A karo na biyu suna ɗage kafafu da ƴan mintuna aka sake buga bindigar da karfi, a yanzu ma dai su dayawa suka sauke ƙafafuwa suka kuma razana, haka suka sha gudu suka kuma sha bulala. Sai a karo na uku ne suka fahimci lallai wannan bindigar saboda su ake bugawa, dan haka sai basu sake razana ba, suka tsaya, a karo na huɗu aka sake buga bindigar, nan ma dai suka tsaya cak, abin ya yi mugun burge Captain, lallai ya shaida suna da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin gane abu, sun fahimci saboda su ake buga gun ɗin har sun ɗauki mataki, lallai suna da jajircewa da zafi nama, ya jinjina masu. Lokacin da suka saba da karar bindigar suka gano saboda su ake yi, sai suka tsaya kyam tamkar saƙaguguna, ana buga bindigar ko a jikinsu, sai dai kuma basu fi minti uku da fara tsayawa cak ko da karar bindigar ba Noor ya sake ɗayan kafansa yana faɗin. “Wlh na gaji”…….. Zaysh and Leo a tare suka haɗiyi wani irin yawun takaici, dan dikkansu burinsu team nasu ya zo na ɗaya, ransu ya sosu. Vash ma ya ji haushin sake kafa da Noor ya yi. A tare dikkansu suka sauke kafafunsu suna ɗaure fuska, juyawa suka yi da gudu su ukun, suka nufi wannan post ɗin, shi kuma Noor ya sake ɗaga kafansa ɗaya sama bisa umarnin Captain.Leo ne ya fara dawowa da gudu sai Zaysh ke take mashi baya, Vash ne last ɗin dawowa, ya karɓi bulalu biyu masu lafiya a gadan bayansa. Sake komawa suka yi suka tsaya suna kwaɓe fuska, Zaysh ne yake faɗi a ransa dole a canzawa Noor ɗaki, a raba shi da su tin da rago ne, su kuma ɗakinsu dikka jarumai ne!. A karo na biyu Noor ya sake sauke kafafunsa har da durkushewa kasa yana numfashi sama-sama. Ai tamkar Zaysh ya rufe shi da duka haka suke ji. Ajiyar zuciya Leo ya sauke tare da kai hannu yana ɗan shafa kirjinsa kafin ya sauke kafafunsa ya juya da gudu ya nufi wajen post ɗin, Zaysh ya rufa mashi baya, sannan Vash. Kamar ɗazun yanzu ma Vash ne ya sha bulala guda biyu, tamkar zai cinye Noor da harara haka suka sake komawa suka tsaya. Ina short kafin a tashi wannan horon sau uku Noor yana sasu gudu, yasa Vash karɓar bulala. Da suka kammala sai faɗa Vash yake yi mashi, yana ta zaginsa wai ya cika ragonta, shi dai ban da ALLAH wadarai da aikin soja babu abin da yake faɗi. Shi kuwa Unays wannan faɗuwa ta Noor ta yi mashi daɗi, koba komai a yanzu team ɗinsu ta zo na farko tin da su ko ɗaya babu nasu da ya faɗi, abin ya yi mashi daɗi sosai, ji yake tamkar ya baiwa Noor kyauta. —————————-TIME🔥 Karfe 11 daidai suka hallara a katafaren class ɗinsu, class ɗin ya tsaru sosai, tamkar secondary set haka, suna da Ac, tables ɗinsu mai shegen kyau da loca, chairs ɗinsu mai kyau, kowa da kujerarsa. Captain Onbish ne ya hallara a gaban class ɗin nasu hannunsa rike da wata katuwar littafi. Fuskansa babu alamar annuri ko wasa, a saman table dake kusa da smartboard ya ajiye takardan hannunsa, yana sanye da kaki a jikinsa. Rubutu ya ɗan yi a smartboard ɗin da makar kamar haka FIREARMS kafin ya juyo ya kallesu, while dik shi suke kallo. Dikkansu sun fitar da note books ɗinsu, a natse cikin kakkaifar voice ya fara da faɗin.”Firearms, watau rabe-raben makamai, yau zamu fara ne da rabe-raben makamai kafin ku san menene makaman na gaske”. Ya ɗan dakata yana rarraba idanu a kansu kafin ya cigaba da cewa. “Bindigogi sun rabu rukuni 5 ne, na farko akwai pistols, watau ƙananan bindigogi waɗan da za’a iya rikewa da hannu ɗaya, sannan ana amfani da su ne daga kusa. Misalan pistols akwai glock 17, beretta M9, colt m1911, SIG sauer P226, jimilla nau’ikan kala 10 na pistols gun”. Dafe kai Noor ya yi, a ransa ya ce. “Da sunan waɗan nan makamai kawai idan aka barka sai su kasheka ko ka shiga doguwar suma, kana jin wasu sunaye tamkar na horori wai bindigu, ni dai na shiga uku tin da na shigo aikin soja!”. A fili kuwa ya mayar da hankalinsa kan sauraron Captain Onbish da abin da yake faɗe. Leo, Zaynash and Unays sun natsu sosai karatun yana shiga kansu, saboda sun sanya a ransu zasu zama manyan sojoji masu ji da lafiya dan bawa duniya gabaɗaya tsaro su kori ƴan ta’adda, sun yi alkawarin a dik ranar da suka sanya kaki mai ƴanci, ma’ana suka tsallake horo suka zama sojoji, to tabbas ba za’a sake samun wani ɗan ta’adda a duniya ba kasarsu kawai ba, wannan alƙawari ne suka ɗaukarwa kansu. SHIN WANNAN ALKAWARI NASU ZAI CIKA? ZASU YI NASARAR TSALLAKE HORO SU ZAMA SOJOJI?.Cigaba Captain ya yi da cewa. “Na biyu akwai rifles, bindigogi masu dogon murfi, ana amfani da su daga nesa, kuma suna da ƙarfi da daidaito sosai. Suna da nau’ika kamar haka, bolt-Action rifles, kamar mosin-nagant, kar98k, sai semi-automatic rifles, kamar m1 garand, SKS, da kuma assault rifles, kamar AK-47, M16, FN SCAR, G36, F2000, suna da nau’ikandai fiye da 30, amma ana koyar da nau’i 10 zuwa 12 a wannan Barrack ɗin, ba’a cika amfani da sauran nau’ikan ba”. (Sai ga jami’ai na musamman ake koya sauran nau’ikan, misali idan suka gama karɓar horo, yanzu haka manyansu suna nan suna kula da dik wani motsinsu, idan suka kammala aiki za’a zaƙulo jarumai kuma ƴan baiwa, sai a sake basu horon da a nan ne zasu zama manyan jami’ai na sirri dana ambata maku a farko, za’a koya masu harbi na musamman wanda ko a ina ne a faɗin duniya komai nisan da suke zasu iya saita mutum su yi harbi kai tsaye.)Ya ɗan dakata ya basu 2 mins suka rubuta abin da yake karanta masu, dan shi ma yana bayani yana ɗan kara rubutawa ne. “Na uku muna da machine guns, bindigogi masu harbi da yawa a lokaci guda, ana amfani da su wajen mamaye wuri, suna harba bullets da yawa a lokaci ɗaya. Sannan suna da nau’ika kamar haka, akwai light machine guns (LMG) RPK, M249 SAW sai general purpose MGs PKM, FN MAG, akwai heavy MGs DShK, browning M2 .50 Cal, suma sun kai kala 10”. Nan ma ya ɗan dakata ya basu damar rubuta wannan karatun kafin ya cigaba da cewa. “Na huɗu muna da shotguns, watau bindiga mai fashewar bullets, suna amfani da pellets ko slug, masu amfani daga kusa. Misali remington 870, mossberg 500, benelli M4, winchester model 1897, a taƙaice irinsu 6 zuwa 10 ne kawai da aka fi sani”. “A karshe muna da sniper rifles, bindigar kwantena masu harbin nesa, suna da tsawo da ƙwarewar harbi daga nesa sosai, misalinsu akwai dragunov SVD, barrett M82 .50 cal, M24 sniper weapon system, L96A1, cheyTac M200, su 8 ne zuwa 12 da aka fi amfani da su”. “Amma akwai sauran makamai masu harbi irinsu submachine guns SMG kamar MP5, Uzi, PPSh-41, grenade launchers, kamar M203, GP-25, Rocket launchers, RPG-7, AT4, anti-material rifles, NTW-20, denel mechem, flamethrowers, kaɗan ake amfani da su yanzu, kamar M2. nau’ukan bindigogin, a taƙaice gasu kamar haka pistols 10, rifles duk nau’i 30, machine guns 10, shotguns 8, snipers10, gabaɗaya sama da 80 zuwa100 na nau’i bindigogi ake koyarwa a aji na nan GIDAN SOJA, amma ana mayar da hankali kan 25–30 na asali ne wanda kuma shi ne kuma zaku fi mayar da hankali, yau ku rike na’ikan da na faɗa maku, gobe zamu fara duba ne daga kan menene pistols gun da yadda suke, yadda ake amfani da su!”. Ya dakata yana sauke numfashi a hankali.Shi dai Noor gabaɗaya sunan makaman ma kawai sun hargitsa mashi lissafin ƙwaƙwalwa ne, wai sunan makaman kawai ma ai sai su sa mutum ya mutu da ransa, dan haka shi wlh ragonta zai dinga nuna masu har a gama horon ya fito bai samu result ba ko za’a barshi ya koma gida. Cike da wannan tinani a ransa har suka kammala class, suka tashi around 1 na rana, a nan ne kuma musulman cikinsu suka nufi masallaci dan yin sallah. Bayan sun fito daga sallah suka wuce hall ɗin cin abinci dan yin lunch. Kamar dai ɗazu group-group suka zauna kowane da ƴan ɗakinsu suka ci abincin su, sannan aka basu hutun 30 minutes kamar ɗazu. Dik wani motsin matasan sojojin nan a kan idanun manyansu suke yi, kun san meyasa ake saka masu ido sosai?. Saboda a yanzu ne ake zaƙulo sojijin ɓangare na musamman, a yanzu ne ake ciro sojoji masu kaifin barisa, suna lura da su ne dan su ga su waye suka fi kaifin basira ta yadda ko sun kammala horo za’a sake basu horo na musamman na sirri dan zama zakwaƙuran kuma su kasance masu iya gano mai laifi da kallo ɗaya, shiyasa ake saka masu ido sosai a wannan lokaci.Karfe 2:30 Captain ya umarcesu da su tsaya bisa tsari, sannan su yi tafiya a kan tsari izuwa wani katafaren fili mai girman gaske wanda shi ma a cikin GIDAN SOJAN yake. Bayan sun isa wajen a nan Captain ya fara karantar da su me ake nufi da discipline da ladabi, yadda zasu kasance masu ladabi da girmama manyansu, bin umarni ba tare da gardama ba, tsabtace kaya da gyaran ɗakunansu, tsari a rayuwa, da tsarkin jiki. Ai ya zame masu dole su yi ladabi da tsabta ne ma, idan ba haka ba su gwammaci mutuwa!!.Sun yi wannan horo na discipline har zuwa karfe 4 na yamma, sannan suka wuce masallaci. Bayan sun yi sallah sun dawo suka ɗaura da horon gwajin ƙarfin hannu, ana koya musu yadda ake riƙe makami da ɗagawa ba tare da gajiya ba, amma ba kai tsaye shi aka koya masu ba, domin yau ne ranar farkonsu ko makaman basu gani da ido ba, kawai gwada karfin hannayen nasu aka fara yi ta hanyar haɗa mutane biyu, zasu rike hannun juna, dik wanda ya kwantar da hannun ɗan uwansa shi ya yi nasara, kai da baka yi kokarin ba za’a sake haɗaka da wasu har sau uku, idan baka yi ba yau za’a ɗaga maka kafa tin da ranar farko ce, daga gobe ka sake aka yi winning a kanka zaka karɓi wani horon ne na daban!. Sun yi wannan horo zuwa karfe 5 na yamma, daga nan aka basu hutun 30min, bayan sun huta suka ɗaura da horon daidaito, aka koya musu yadda za su tsaya da ƙafafunsu ba tare da fargaba ba a lokacin harbi ko farmaki.Dik horon da suka yi yau Noor shi yake cariying last, kwata-kwata babu alamar zai yi abin arziki a rayuwarsu na matasan sojoji, shi fata ma yake yi a koresa daga school ɗin shiyasa yaki mayar da hankali.Sarai Captain ya lura da shi, kuma da daddynsa ya karɓa mashi Form ɗin ya kawosa ya faɗawa G.A.T a bashi horo na musamman, dan haka shi kuma ya sanar da Captain cewa ya saka ido kan Noor ya tabbatar da cewa horo na musamman ya bashi, daddyn Noor suna da kyakkyawar alaƙa da GAT, Dan haka ya ce kada ya barsa ya yi lalaci dan renon mata ne shi.Da misalin ƙarfe 6 aka basu horon zuciya, karatu da darussa kan jarumta, sadaukarwa, da ƙaunar ƙasa, aka zafafa masu kan batun kaunar kasa da yin komai a kan ƙasa da aikinsu, aka nuna masu cewa rai ba’a bakin komai yake ba, su kashe ko a kashesu, Captain ya zafafa masu cewa karaya ba halin namiji bane, tsoro ba dabi’a bace, jajircewa ita ce mutum, su tsaya tsayin daka dan kare kasa, ko sun mutu ƙasa zata yi alfahari da su. Sosai zafafan kalaman Captain suka fasa zuƙatan dayawa daga ciki, shi kansa Noor ya ɗan ji kamar zai yi aikin, amma idan ya tuna wannan ɗan banzan wahalar da suka sha yau, kuma a haka ma wai ranarsu ta farko ce, yana tuna wannan zai ce kai shi ina, sai ya ji zafafan kalaman Captain sun goge a kansa. Karfe 7 daidai suka tashi daga horon jarumta, Captain ya basu 5mins su yi alwala zuwa masallacin soji. Haka kuwa aka yi, bayan sun yi sallar mangariba da ishai karfe 8 suka haɗu a dinner hall suka yi dinner, karfe 8:30 suka kammala, a nan ne Captain ya umarcesu da kowa ya wuce room ɗinsu, suna da damar yin wanka su kwanta, kada su manta gobe 4:30 na asuba zasu tashi. Daga nan ya hura usir kowa ya nufi room ɗinsa.Noor ya riko shoulder ɗin Vash yana ta faman haki yana nishi sama-sama alamar shi ya yi matuƙar gajiya, shi ma Vash ɗin nishi sama-sama yake sai faman kwaɓe fuska suke yi. Kai tsaye room ɗinsu suka nufa, sai dai kuma suna shiga suka tsaya turus ganin Leo a tsaye a tsakiyar ɗakin hannunsa rike da waist ɗinsa yana kallon wajen da Noor ya ɓata da taɓo ɗazun. Leo ya tsani datti komai ƙanƙantarta, baya zama wajen ƙazanta, wlh idan ya ga ƙazanta a waje ya dinga shirga amai kenan, yana da bala’in kyankyani sosai, zuciyansa ta yi ta tashi idan ya ga ƙazanta.Ganin yana tsaye yana kallon wajen ne yasa Vash and Noor suka ɗan sha jinin jikinsu, shi kuma Zaysh ya wani ɗale kan gadonsa yana ɗaure fuska tamau irin shi ma no respect ɗin nan. Wucewa Noor ya yi zai nufi toilet sanyayyar sexy voice ɗin Leo ya daki dodannin kunnuwansu da cewa. “Come over here”. Sosai sun ji shakkarsa, amma Zaynash da ya yake dake ne ya ce. “Yana kiranku ai sai kuzo”. Ya faɗa ba tare da ya kalli Leo ba, saboda shakka da tsoronsa, kuma gatse yai masu, ina irin ubanku na kiranku ai sai ku je. Zazzare ido Noor ya yi, da sauri ya saki Vash yana faɗin. “Yanzu zamu goge wajen mancewa na yi”……. Da sauri Vash ya amsa da cewa. “To dama meyasa baka goge ba?”. Mamaki ne ya kama Noor, wai ba su suka ce kada ya goge ba ɗazun? Yanzu kuma sun juya mashi baya. Wucewa Vash ya yi da sauri ya nufi wajen bed ɗinsa. Jakansa ya zaro zai kwashi kayan wanka irinsu lotions da soap ya wuce toilet, bai bi ta kan Noor ba, sai da ma ya ciro katon biscuits mai daɗi ya fasa ya ɗan ci rabi, ya mayar da sauran cikin kayan motsa bakinsa, daga nan ya miƙe tare da kwasan kayan amfaninsa ya wuce toilet.Back to their age, Zaysh kamar Leo haka yake 23, Vash bai wuci 22 ba, Noor 20, Amma kansu kusan ɗaya, Leo dai ya fisu tsawo ne, Pamira people suna da tsawo sosai!. Yanzu Noor yagama gane dikkansu suna tsoron Leo, sai ya kudurta a ransa sai ya ƙullah alaƙa da Leo su shaƙu sosai ko dan su Zaysh su daina raina mashi wayau.Mopper room ɗin nasu ya ɗauko, ya zo ya goge ko’ina tsab, ya kara share masu ɗakin kafin ya nufi wajen bed ɗinsa, shiru suka zazzauna cike da al’ajabin farkon ranarsu a GIDAN SOJA, wannan abu ya tsayawa Noor a rai, ba su taɓa zatan haka ba. Ni kuwa na ce abin da baku taɓa zata ba ai yana nan dayawa kuma yana kan hanyar iso ku, GIDAN SOJA ya zarce yadda kuka ɗauka mutanen! har gobe dai inai maku fatan kammala horo lafiya har ku fara aiki!.Suna zaune shiru har Leo ya fito daga wanka sanye da bathrobe white kala mai shegen kyau, ya haɗe kitson kansa waje guda, yana ɗaure da karamar white towel a saman kan nasa, lokaci guda kamahin soap and shower gel ɗinsa ya buɗe ko’ina a cikin ɗakin nasu.Mamaki ne ya kama Noor dake saman bed ɗinsa, a fili ya ce. “Wannan kamshi tamkar na soap ɗin Companynmu”. Basu ji me ya faɗa ba, dan haka babu wanda ya tanka shi.A saman bed ɗinsa Leo ya zauna tare da kawo jakarsa, ya fito da lotions na companyn STARS LADIES BODY LUSH. Kayan kamfanin kala biyu ne, na maza ya kasance da sunan STARS BODY LUSH, na mata STARS LADIES BODY LUSH. Fito da su Leo ya yi, a natse ya fara murza mayukan a jikinsa, take kamshinsu ya kara bule ko’ina a ɗaki, kura mashi ido Noor ya yi yana mamakin yadda aka yi kayan kamfanin daddynsa ya shiga duniya har nan. Like wow, yanzu ya yarda da cewa Leo ba karamin kai bane, dan ba kowa ya isa amfani da kayan kamfaninsu ba , saboda balain tsadarta, abu mai kyau da inganci ai dole ta yi tsada!.Robar lotion da Leo yake shafawa a yanzu pic ɗin Noor ne a jiki, dan kyansa yasa su suke yi wa Companynsu tallah, a robar mata hotunan sister ɗinsa ne a jiki, ai na faɗa maku Noor yana da kyakkyawar jiki kamar madara, ga kyan fuska, amma Leo tsabar iskanci bai gane Noor bane a jikin hoton, dan bai taɓa bi ta kan hoton jikin ba!.Suna gani Leo ya kamma shirinsa cikin pj’s tsab, ya haye gado ya kwanta, sannan ya jawo littafinsa na nazarin makamai na lacture ɗin da suka yi ɗazun ya fara karantawa, ya sanya Bluetooth a kunne yadda ma kada ya ji wani motsi ko magana. Shiru ɗakin ya yi, suna son yin gulma suna tsoron ya ji su, haka suka yi tsit, daga karshen kowannensu ya tashi ya yi wanka, suka zo suka shirya yare da hayewa gado, kwanciya suka yi suka hau barcin gajiya, jiki dik tsamin wahalar horo, shiyasa suna kwanciya ba jimawa sai barci, amma ban da Zaysh, shi bai rintsa ba, sai da ya bari suka yi barci sannan ya diro ƙasan bed ɗinsa, ya fito da……..Masu tambayata batu kan Dr and ƴarta ku dai kara hakuri, zamu waiwayi wajen a next page In Sha ALLAH, akwai dalilin ɗan janyewa!.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️

Back to top button