Hausa novels

Ruwan Zuma Page 45 Hausa Novel

(45) Madu sai yamma ya dawo gida kamar kullum in aka tashi daga kasuwa, Hajja ce ta shiga sashenshi ta samu yana waya wanda sai daya gama ta mishi sannu da zuwa tare da tsiyaya mishi ruwa a kofi ya sha. “Ya gida ya yaran? Ban ga babana ba.” Yayi maganan yana washe baki wanda ya bata mamakin meya sameshi haka. “Cewa nayi su barka ka huta sai zuwa anjima su shigo su maka sannu da zuwa.” “Hakan yayi. Nikam kinji yaron nan ya saki Laila ko?” Ya fad’i hakan annurin fuskarshi na k’aruwa. Hajja da a yanzu ta daina mamakin tsanar da Madu yake yiwa Laila tace, “D’azu na shiga sashen Ummii naji labarin. Abun bai yi dad’i ba.” “Maganinta kenan, in banda son zuciya irin nata me zai sa ta auri yaron da ta kusan haifa? Duk abunda ya biyo baya laifinta ne kuma Allah ne ya kamata data yaudari Alhaji Abdul. In banda rashin mutunci a ranar aurensu tace wai ta fasa? Ai wannan babu abunda ya kaishi cin fuska.” Ya k’arishe maganan cikin 6acin rai. Shiru Hajja tayi domin a yanzu ta daina kare Laila a gurin Madu dalilin fad’an da suke yi muddin ta nuna Laila ta fishi gaskiya. Sanin halinsa yasa ta koyi karatun zama dashi domin tasan sun fi kusa tunda uwa d’aya uba d’aya suke, kenan ita ce bare. Sai a lokacin ta tuno da sak’on Jamila ta fad’a mishi. “Jamila kam ba kwana uku da suka wuce ta tafi garinsu ba? Me kuma ya dawo da ita kuma ta k’ara tafiya? Jeki ki d’auko mini.” Ya fad’i hakan cikin mamakin wannan al’amari. Hajja fita tayi zuwa d’akin Jamila, kayan falonta komai yana nan sai dai cikin d’akinta ne a wargaje suturunta a k’asa ta watsar. Ta6e baki Hajja tayi tana mamakin wannan abu domin Jamila bata ta6a barin d’akinta a bud’e ba in zata yi tafiya, amma wannan karon gashi har key ta bari a jikin k’ofar falonta. Wardrobe ta bud’e taga babu komai a jiki sai wata katuwar envelope ta d’auko ta fito da ita zuwa sashen Madu, taso ta bud’e amma wata zuciyar ta haneta ta kai mishi ya k’ar6a yana cewa, “Me wannan d’in kenan?” “Wallahi nima ban sani ba don ban bud’e ba.” Ta zauna a gefenshi. Cikin d’aurewar kai ya bud’e envelope d’in ya zaro wasik’a, hotuna da kuma Disk. Hotunan ya fara dubawa ya danna wata muguwar ashar yana mik’ewa tsaye ganin Jamila matarsa ta sunnah kwance a k’irjin Alhaji Abdul wanda yake bacci bai ma san an d’aukeshi ba. Wani hoton ya duba yaga bai fito sosai ba amma Alhaji Abdul ne tsirara akan mace wacce ya tabbatar Jamila ce ganin kod’add’un k’afafunta da yayi a gefe da gefen Alhaji Abdul, kenan video ne aka mayar dashi hoto. Haka yaci gaba da ganin sauran hotunan zufa na keto mishi a goshinsa yayin da zuciyarsa ta tsananta bugawa yana jin kamar ya mutu tsabar takaicin da yake ciki. Watsar da hotunan yayi kana ya jawo wasik’ar ya fara karantawa kamar haka, ‘Nasan kafin kaga wannan wasik’ar nayi nisa a duniya inda baza ka ta6a samuna ba, so don’t even try. Kafin ka aureni ni budurwar Abdul ce wacce take bashi jikinta da kuma zuciyarta a duk lokacin daya buk’ata sai dai ashe shi ba zai ta6a sona ba. Saboda irin son dana ke mishi ya had’amu har ka aureni ba tare dana daina kwana a gadonshi ba, sannan ba tare daka gane ba. Sai dai irin son da yake yiwa k’anwarka yasa na gane har abada bazan samu soyayyarsa ba shiyasa na yanke shawarar rabuwa da kai da kuma shi. Kamar yanda aka had’a baki da kai ake cutar Laila haka muka had’a baki muke cutar da kai yana baka kud’i kana k’ara mishi aiki. Na tafi na barka idan kaga dama ka sakeni in kaga dama kar ka sakeni domin dama ban d’auki aurenka a bakin komai ba. Video da hotuna kuma dama ina ajiye dasu don 6acin rana irin haka, sannan ganinsu zai sa ka tabbatar da abunda nake fad’a.’ Hajja tunda ta lek’a taga abunda hoton ya k’unsa tayi shiru da bakinta bata ce kanzil ba, domin dama tana lura kamar Jamila na huld’a da maza duk da bata zaton cewa Alhaji Abdul ne, saboda tsoron kar aurenta ya mutu ne yasa ta barwa Allah komai ta kuma cigaba da hak’urin zama da Madu domin baza taso ta barwa Jamila tarbiyyar ‘yayanta ba. Domin Madu yana son Jamila baya son abunda zai 6ata mata rai, sau da dama in suka samu matsala Jamila yake bawa gaskiya. Wannan dalili yasa take zama a gidan Madu ba don tana jin dad’insa ba. A gigice ya isa bakin kayan kallonshi ya saka dvd d’in ya kunna suka fara kallon abunda za’a iya kira da blue film amma wannan na Jamila da Alhaji Abdul. Videos ne kala-kala wanda wani tsayinshi bai fi seconds talatin ba wani ma k’asa da haka domin gudun kar Alhaji Abdul ya gane tana aikata hakan, kenan shima ta shammaceshi ne. Sai daya gama kallon duk abunda yake ciki wanda ya d’auki tsawon minti goma yana hawaye yana huci kamar zaki. Hajja da take gefe ita ke rufe idanunta idan taga wani abun yayi yawa domin kayan aikin Alhaji Abdul da ake nunawa. “Ina take?!” Madu yayi k’araji yana duban Hajja. “Tun da hantsi ta tafi bata dawo ba.” Ta bashi amsa cikin tsorita da yanayinsa. “Sai na kashesu, sai na kashesu dukansu. Sun ci amanata kuma wallahi ba zan barsu ba.” Ya fad’i hakan cikin k’unan rai yana ficewa daga falon kamar zai tashi sama. Hajja na ganin ya fita ta tattara abubuwan gudun kar ‘yayanta su gani ta kai mishi d’akinshi ta ajiye domin bata son tayi laifi. Amma a zuciyarta taji dad’in abunda ya faru ko ba komai alhakinta dana Laila ne ya kamashi, saboda tana sane da k’untatawa Laila da yake yi da kuma mata sharrin aikata alfasha ba don tana yi ba, wai yana hakan ne duk don tayi zuciya ta auri Alhaji Abdul. To yau ya gane waye fasik’i tsakanin Laila da wanda yake marawa baya, tunda iskancin Alhaji Abdul bai tsaya a kan kowa ba sai matarsa ta sunnah. Fatan Hajja a yanzu shine Allah yasa Jamila bata saka musu cutar HIV ba domin infection kam suna dashi dukansu, kuma magani ya gagara aiki don Madu yace ba zai je asibiti ba. Madu yana fita gidan Alhaji Abdul ya nufa bayan ya 6oye wata shafceciyar katako a cikin babbar rigarsa, ana kiran magriba ya isa gidan sai dai abun bak’in ciki maigadi ya fad’a masa cewa baya nan yayi tafiya Abuja. “Yaushe zai dawo?”Madu ya tambaya kamar zai mutu a gurin tsabar takaici da bak’in ciki. “Wallahi bai fad’a mini ba domin cikin gaggawa yayi tafiyar.” Maigadin ya k’ara bashi amsa don yasan Madu abokin uban gidanshi ne. A zuciye ya koma cikin motarshi ya daki siterin ya fashe da kuka kamar k’aramin yaro, wanda zai iya cewa ko ubanshi daya mutu bai mishi kuka irin haka ba. Ya kai minti goma a haka sannan yayi tunanin kiran Alhaji Abdul yaji ko yasan abunda Jamila tayi, in bai sani ba kuwa zai barshi a duhu har sai ya dawo ya masa lahani kamar yanda yaci buri. Kiran wayarshi yayi wacce ringing biyu Alhaji Abdul ya d’auka ba tare daya san me yake faruwa ba yace, “Madu ya aka yi?”Sai a lokacin Madu ya fara ganin rashin girma da Alhaji Abdul yake gwada mishi, saisaita muryarsa yayi kana ya amsa, “Na zo gidanka ance ka tafi Abuja, yaushe zaka dawo?” “Yanzu ma haka ina kan hanyar dawowa zan ganka nan bada jimawa ba, sannan ina tafe da albishir wanda zaku yi mamaki.” Ya fad’i hakan with excitement in his voice. “Nima akwai abunda zan maka albishir dashi idan ka dawo.” Fad’in Madu yana ji kamar ya shiga wayar ya kasheshi nan take. “To Allah ya kaimu.” Alhaji Abdul ya amsa ba tare daya kawo komai cikin ranshi ba domin shi yama manta da wata Jamila. Yinin ranar sukuku su Laila suka yi ta, magana wannan wahala yake bata sai addu’a kawai da take tayi tana danne zuciyarta dalilin su Ummii sun hanata kuka. Mas’ud kuwa tun daya kawo musu labarin cewa bai samu Haydar ba ya k’ara fita bai dawo ba sai bayan magriba. A nan ya samu Ammi na cewa zata koma gidanta. “Ba zan sake barin kiyi nisa damu ba, a nan zaki cigaba da zama har Haydar ya bayyana. Sai dai anjima in anyi sallar isha Mas’ud zai kaiki gidan ki d’auko kayanki da zaki buk’ata.” Ammi bata yi musu ba ganin Ummii ta gama yanke shawara, Mas’ud guri ya samu ya zauna yana tambayar lafiyarsu suka amsa da ‘Alhamdulillah.’ “Shiru har yanzu babu d’uriyarsa ko?” Ammi tayi tambayar ga Mas’ud with hopeful eyes. Girgiza kanshi yayi yace, “Wallahi duk inda nake tsammani bai je ba, ga wayarshi bata shiga. Ammi ki kwantar da hankalinki Haydar ba yaro bane, idan ya sauk’o zai dawo gida Insha Allah.” “Allah yasa amma ina tsoron zuciyar Ali duk da cewa yana da hak’uri, amma wannan karon abun ya taru ya mishi yawa ne.” Laila na jin hakan ta sunkuyar da kanta k’asa domin ko ba’a fad’a ba tasan har da laifinta a 6acewar Haydar. Babu wanda ya k’ara cewa komai falon ya k’ara yin shiru kowa da tunanin da yake yi a zuciyarshi. A nan ne Mas’ud ya d’auko wayarshi ya shiga whatsapp don turawa Haydar sak’o amma sai yaga messages da yawa a family group d’insu wanda ‘yayan Ummii da surakananta mata ne kad’ai a ciki babu yara. A nan yaci karo da munanan hotuna da videos d’in da Jamila ta tura bata ko kunyar cewa itama za’a kalli tsiraicinta, don muradin asirin Alhaji Abdul da Madu ya tonu bata damu da a ga jikinta ba after all dama karuwa ce. “Subhanallah.” Mas’ud ya furta yana karanta dogon rubutun da Jamila ta bari wanda yake bayyana duk kullace-kullacen da Alhaji Abdul yayi da kuma wanda Madu yayi. “Lafiya Mas’ud?” Ummii ta tambayeshi tana dubanshi. “Ha…. fad’a ake yi a wani gari aka turo hotunan a group. Kalti duba wayarki ki gani.” Yayi k’arya don baya son Ummii taji wannan k’azantar daya k’ara faruwa da zuriyarsu. Laila bata motsa ba balle ta kai hankalinta kansu, hakan yasa Mas’ud ya kira sunanta da d’an k’arfi ta d’ago ido tana kallonshi fuskarta blank kamar wacce bata da emotion. “Check our family whatsapp group please, it’s important.” Ya zuba mata ido wanda hakan yasa ta gane abunda yake son ta gani mai muhimmanci ne. D’auka wayar tayi ta kunna data kana ta shiga ta fara cin karo da duk abunda Mas’ud ya gani tana kawar da kanta, don ita kam ta kasa playing videos d’in tayi saurin scrolling k’asa zuwa dogon rubutun. Tana karantawa hawaye ya fara gangarowa daga idanunta zuwa k’uncinta tana jin bak’in ciki da kuma takaicin aka yi ta kasa gane cewa duk wani 6atanci da ake yiwa rayuwarta laifin wad’annan mutane biyun ne. Wani irin tsana suke yi mata da har zasu yi sanadiyyar lalacewar d’anta? Wannan shine son da Alhaji Abdul yake cewa yana yi mata? Sannan meyasa Madu ya tsaneta tun tasowarta? Laifin me ta mishi? Mas’ud ne yayi mata alama da ido kan su fita waje, shi ya fara fita Laila tabi bayanshi zuwa farfajiyar gidan inda suka yi parking d’in motocinsu. “Mas’ud wani laifi muka yi muke ganin bak’in ciki irin wannan a rayuwarmu? Anya kuwa ba asiri aka yiwa zuriyarmu ya fad’i a kaina nake shiga garari da tashin hankali ba? Me wannan? Don girman Allah menene wannan? Matar yayana fa take zina da wanda ya nemi aurena! Wanda tun farko an d’aura auren nasu ne don kawai a samu galaba a kaina. Wayyo ni Laila ina zan sa kaina?!” Ta k’arisa maganan tana durk’ushewa a gurin tana kuka kamar ranta zai fita. Sai a lokacin ta samu tayi kukan rashin Haydar da kuma duk abunda yake nuk’urk’usanta duk tsawon wannan lokaci da take yawo dashi with a brave face. Mas’ud bai ce komai ba illa isa gurinta da yayi ya dafa kafad’arta yana mugun jin tausayinta a ranshi. Gaskiya ne yayarshi tana cikin jarrabawa sai dai ya mata addu’an Allah yasa taci. Sai da tayi mai isarta sannan ya mik’a mata hannu ta tashi yana bata hak’uri. “I’m sorry da duk abunda yake faruwa a rayuwarki and I hope you’ll be strong, a yanzu da asirinsu ya tonu baza su sake gigin aikata wani abun ba. Sai dai baza mu barsu haka ba, zamu kai k’ararsu hukuma a kwato miki hak’k’inki duk da cewa hakan zai sa a ta6a Madu.” Girgiza kai Laila tayi da sauri tana share hawayen fuskarta tace, “Babu k’ararsu da zan kai domin duk hukuncin da za’a yanke a kansu ba zai kai rabin illar da suka yiwa rayuwata ba. Sun mini cutan da in ba Allah ba babu wanda zai kwato mini hak’k’ina. Wallahi na barsu da Allah saboda sun mini zaluncin da babu wanda ya ta6a mini irinshi. Sun cuceni cuta mafi muni Mas’ud, wallahi ban yafe musu ba.” Gyad’a kai yayi cikin yarda da magananta domin tayi gaskiya. Sai dai zasu iya yiwa Alhaji Abdul abunda ya yiwa Laila ta hanyar watsa hotunansu a yanar gizo. “Zan watsa hotunan shima yaji abunda kika ji.” “Karka yi don Allah, saboda duk wanda yaga tsiraicinsu kana da kason zunubi, Allah kuma babu ruwanshi da cewa ramawa kayi saboda ka yad’a alfasha ne a gurinshi. Tunda muka barsu dashi nasan gaba zai saka mini.” “Allah ya k’ara miki hak’uri.” Ya mata addu’a cikin ganin jajircewarta don tayi tawakkali ba kad’an ba. “Amin. Ka kira su Yaya Ajidde dasu Safa ka fad’a musu su goge sannan kar su fad’awa Ummii don wannan abun zai iya tayar mata da ciwonta, yau ma nayi mamakin da babu abunda ya faru.” A gabanta Mas’ud ya kira ‘yan uwan nasu ya sanar dasu halin da ake ciki tare da hukuncin da suka yanke, Marwa da dama tuntuni ta gani tace, “Ni dana gani tsoro naji na kasa kiranku.” Yayarsu Ajidde da dama bata damu da shiga whatsapp d’in ba tambayar lafiyar Ummii ta fara yi don a tunaninta kota sani, Mas’ud ya sanar mata cewa baza su fad’a mata ba sannan ya sanar da ita duk halin da ake ciki har na bayyanar Ammi ‘yar kawunsu. “Don meyasa tuntuni baku sanar dani ba? Ina take yanzu?” “Wallahi ita Ammin ce ta hana a fad’awa kowa akan cewa tafi son ta fara zuwa Maiduguri su ganta. Ba laifina bane kiyi hak’uri, ke d’in ma karki fad’awa kowa.” Bayan sun gama waya ya kira Naana matarsa itama yace ta goge chats d’in duka. Daga nan magana Laila da Mas’ud suka yi mai tsayi akan abubuwan da suka faru da kuma damuwar da Laila take ciki akan Haydar, sosai ya kwantar mata da hankali domin yanzu tausayinta yake ji bana wasa ba. “Come for a warm hug.” Yace da ita yana ware hannayensa domin yasan she likes someone to hug her idan damuwa ya mata yawa. Bata musa ba ta isa yayi caging d’inta da hannayensa ta rufe idanunta tana Ajiyar zuciya. “You don’t smell like him.” Tace da Mas’ud tana barin jikinshi. Murmushi yayi yace, “Saboda ni k’aninki ne ba Haydar ba. Kuma next time don’t expect a hug from me.” Itama murmushin tayi tana kallon k’anin nata cikin k’aunarshi saboda no matter what baya ta6a fushi da ita na tsawon lokaci, kuma duk abunda tayi ko bai mara mata baya a lokacin ba daga baya he’ll support her. Mas’ud shine meaning na ‘who got your back’. Motarshi ya shiga kana yace, “Ki fad’awa Ammi ta fito in kaita gida ta d’auko kayan nata.” Laila tana shiga ta sanar da Ammi sak’on Mas’ud tana k’asa da kai cike da kunyar abunda ta aikatawa d’anta, sannan har lokacin Ammi bata mata maganar cikin ba balle ta nuna ranta ya 6aci. Minti talatin da fitansu Mas’ud suka dawo gida, a nan suka tarar da Ummii na yiwa Laila fad’a kamar dama jira take yi su fita. Tana ganinsu tayi shiru amma bata bar hararar Laila ba, ganin haka yasa Ammi ta fara magana, “Kalti ki daina mata fad’a tunda abunda ya faru ya riga daya faru, sannan ku bakwa ganin girman laifinshi ne daya saketa? Wallahi nafi ganin laifin Ali fiye dana Laila duk da cewa itama bata kyauta ba. Sannan shi da kanshi yayi niyyar tafiya babu wanda yace ya tafi, kenan duk lokacin da yaji ya huce zai dawo babu wanda ya sani. Ba zai ta6a yin nisa ya barni ba duk da cewa nima na mishi laifi, saboda Ali yana sona kuma yana tausayina ya kuma san zan shiga damuwa idan baya kusa dani. Insha Allah ba zai jima ba zai dawo, Insha Allah.” Tana gama fad’in hakan ta shige d’akin Ummii dalilin hawayen daya taru a idanunta, don wannan maganar da tayi kamar tana jaddadawa kanta ne basu ba. Laila da tasan zaman gidan ba zai mata dad’i ba k’arfe goma ta fara neman inda jakarta yake zata koma gida, a d’aki ta samu su Ummii da Ammi suna magana ta musu sallama ta dawo falo gurin Mas’ud zasu tafi. A nan suka ji wasu maza na sallama a tsakar gida Mas’ud ya amsa yana cewa, “Bismillah ku iso.” Alhaji Abdul suka fara gani ya shigo sannan bayanshi babanshi ne wanda ya tsufa amma da sauran k’arfi a jikinshi. Sanin daraja irin ta manya yasa Laila da Mas’ud basu yiwa Alhaji Abdul rashin mutunci ba, ko ba komai yaci albarkacin ubanshi. Gaisheshi suka yi suna hararar Alhaji Abdul kana Laila ta shiga d’aki ta fad’awa Ummii tayi bak’i, Ummii bata jima ba ta fito tana musu maraba tana tuna cewa rabonta da Baban Abdul tun rasuwar mijinta da yazo ya mata ta’aziyya. Bayan sun gaisa d’akin yayi tsit ana jiran aji dame suka zo. Su Laila kuwa fargaba suka shiga dalilin basa so Ummii tasan abunda yake faruwa na matar Madu, suna kuma mamakin tsaurin ido na Alhaji Abdul da ya iya shigowa gidan bayan cin amanar daya musu, ba tare da sun san cewa shi bashi da masaniya akan abunda Jamila tayi ba. Baban Abdul ne ya fara magana bayan yayi gyaran murya yace, “D’azu Abdul yaje Abuja yake gwada mini wani recording wanda na gane d’ayan muryar Matata ce.” Cikin rashin fahimta suka bishi da kallo suna tunanin me had’insu da wannan magana? Saboda It doesn’t even make sense. Ummii ta dubeshi tace, “Alhaji ban gane ba.” “Suwaiba ‘yarki matata ce sannan Haydar d’ana ne. Na gane hakan ne bayan naji murya da kuma labarinta data baku a yau, don Allah idan tana kusa ku kira mini ita in tabbatar ita ce kuma ba mafarki nake yi ba.” Salati da kuma Innalillahi ne ya tashi a falon Ummii har tana tafa hannu kana ta kwalawa Ammi kira wacce tun shigowarsu ta gane muryar mijinta amma ta k’i fitowa tsabar kukan daya ci k’arfinta, da kuma tsoron abunda zai faru gaba idan matarsa taji ta dawo cikin rayuwarsa. Shin yau wace irin rana ce da abubuwa suke bayyana kamar dama jiranta ake yi? “Lu’alu’a.” Baba ya kira Ammi da sunan daya rad’a mata tun a wancan zamanin soyayyarsu. K’in fitowa tayi haka bata amsa duk kiran da ake mata ba. Laila da abun ya fara mata yawa taji kanta na juyawa tana neman gurin kwanciya. Mas’ud ne ya lura da hakan yayi saurin zama a hannun kujeran da take zaune ta kwantar da kanta a jikinshi hawaye na silalowa a fuskarta, wai Haydar d’inta k’anin Abdul ne? Wani irin kwamacala ne wannan auren nasu ya bankad’o? Ummii ce da kanta ta tashi ta shiga d’akin ta yiwa Ammi magana sannan ta fito ta samu guri ta zauna ba tare data kalli kowa ba. Hakan yasa Baba ya kira sunanta, “Lu’a.” Yanayinsa kamar mai shirin zubar da hawaye. Ammi ta d’ago idanunta sai kuma wani kukan ya kwace mata tana girgiza kanta tana cewa, “Don Allah kar kace ka ganmu, zata saka a kashe mini yaro.” “Wacce kike magana a kanta ta rasu tun da jimawa bayan ta fad’a mini abunda ta aikata, sannan ta bani wasiyyar duk lokacin dana ganki in nema mata yafiyarki da fatan zaki yafe mata domin tayi nadaman abunda ta aikata a gareki da d’an cikinki. Ina d’ana yake Lu’alu’a? Ban ganshi a tare daku ba sannan tun d’azu Abdul yake gwada kiranshi wayar bata shiga. Ina son ganinshi, ku kira mini shi yazo yaga babanshi.” Ya k’arisa maganan cikin tsantsar farin ciki yana kallon Ammi kamar yaje ya d’auketa. “Bayan ya saurari tarihin rayuwata ya tafi bamu san ina ya shiga ba.” Difff annurin fuskar Baba ya d’auke ya sunkuyar da kanshi k’asa yana addu’an kar Allah ya maimaita mishi 6atan iyalinshi. Ihun da Laila tayi yasa kowa ya d’ago ido yana kallonta tana nuna bakin k’ofa da hannunta bakinta ya kasa magana, suna juyawa suka hango Madu ya kaiwa Alhaji Abdul duka a bayanshi da wani k’aton katako, Alhaji Abdul cikin kid’imewa ya tare da hannunshi ya bada wani k’ara ‘katttt’ alamar hannun ta karye. Mas’ud ya tashi da gudu yana kiran sunan Madu zai kwace katakon hannunshi amma kafin ya isa Madu ya k’ara laftawa Alhaji Abdul a goshinshi, nan da nan jini ya fara zuba yayi azaman tashi yana neman gurin 6uya. “Yaya Madu baka da hankali ne?” “Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun.” “Mas’ud rik’eshi karka bari ya isa gurinshi.” “Abdul ka fita daga gidan an rik’eshi.” “Kar ka ta6ashi nace, Madu nace karka ta6ashi.” “Ummii ki hanashi kar ya kasheshi.” “Zai kasheni, bashi da hankali ku rik’eshi.” “Madu ni nake maka magana ka nitsu ka saurareni.” “Wannan wani irin tashin hankali ne yake faruwa damu?” Haka d’akin ya kacame da ihun mutanen cikinsa, Alhaji Abdul yana dafe da goshinsa dake zubar da jini ga Madu na k’ok’arin yin kanshi Laila da Mas’ud sun rik’eshi, Ammi ta kwace katakon hannunshi tana tare Alhaji Abdul wanda yake 6uya a bayanta. Ummi kuma magana take yi tana son nitsar da Madu yayin da Baba yake gefe yana kallon wannan abu kamar a mafarki ya rasa me zai yi d’aya. “Ku barni in kasheshi in kashe banza, matata yake zina da ita a bayan idona. Nace ku sakeni in kasheshi.” Fad’in Madu yana yin kan Alhaji Abdul wanda Ammi ke tarewa tana son fitar dashi waje. Ai kuwa yana samun hanya ya fice daga gidan da gudu zuciyarsa na azalzalarshi bisa wannan kayan takaici da kunyan daya sameshi. Baba na ganin haka shima ya fita yana cewa, “Bari mu kaishi asibiti.” Sai da Mas’ud ya tabbatar sun bar gidan sun yi nisa sannan ya sake Madu wanda ya samu guri ya zauna idanunshi sun kad’a sun yi jaa kamar garwashi sai huci yake yi kamar zai ci babu. Nan kowa ya samu guri ya zauna amma banda Ummii da take tsaye a kanshi tana kallonshi. Sai da numfashinsa ya daidaita sannan Ummii ta fara tambayarshi cikin sanyin murya, “Madu me yake faruwa ne? Meyasa ka aikata wannan abun kunya da rashin hankalin?” “Munafuki ne Ummii, ashe tun kafin in had’u da Jamila suke watsewarsu tare har muka yi aure basu daina ba. Ita da kanta ta bayyana bayan ta gudu.” Shiru d’akin ya sake yi baka jin k’aran komai sai na fanka kad’ai. Ummii ce ta ja ajiyar zuciya kana ta nisa tace, “Na gane Jamila na bin maza sai dai ban ta6a tsammanin da abokinka zata k’are ba. Kwanaki da kuka yi tafiya da Hajja bak’in cikin abunda naji take fad’a a waya yasa na kwanta rashin lafiya har gadon asibiti, shiyasa daka dawo na ganka nayi hawaye don tausayinka da nake ji. Bani da tabbacin abunda take aikatawa shiyasa ban ta6a yiwa wani daga cikinku maganan ba, sai addu’a dana dage a kai kan cewa Allah ya tona asirin duk mai cutar da iyalina. Yanzu gashi Allah yasa ta bayyana ita da kanta ba tare da an mata dole ba.” “Ummii addu’ar taki ce ta kar6u shiyasa da Jamila ta tashi tonon asirin bata tsaya a nata ba sai da ta fad’i irin tuggu da makircin da Madu da Abdul suka yi ta kullawa akan Kalti.” Fad’in Mas’ud yana yiwa Madu kallon tsana da takaici. “Mas’ud nace kar ka kuskura ka d’auko magana nan.” Fad’in Laila tana girgiza kai. Cikin rashin fahimta Ummii ta dubi Mas’ud tace, “Wani tuggu suka had’a mata?” “Mas’ud don girman Allah kar mu d’auko wannan maganar a yau. Abubuwan da suka faru sun isa kar mu k’ara, wallahi na gaji, na gaji da komai ina son in kwanta kar in tashi har abada.” Ta k’arishe maganan tana yarfe hannayenta idanunta sun kasa zubar da hawaye tsabar ta gaji, saboda tun safe shi take yi. “Mas’ud fad’a mini komai kar ka 6oye mini.” Ummii ta bashi umarni fuskarta babu alamun wasa. Mas’ud kallon Laila yayi wacce ke girgiza mishi kai kana ya fara magana, “I’m sorry Kalti don bazan tsallake umurninta ba. Ummii Jamila ce ta turo hotuna marasa dad’in gani a whatsapp family group d’inmu wanda yake nunata tare da Abdul a hali na kaico. Daga nan kuma tayi rubutu kamar haka;….” Ya zaro wayarsa daga aljihunshi ya fara karantawa… ‘Na dad’e ina jiran rana mai kamar ta yau da saurayina Alhaji Abdul zai juya mini baya in gwada mishi wacece ni, aurena da Madu shi ya had’a ba tare da Madu ya san cewa ni dadironsa ba ce. An yi auren ne don in zama mai fad’awa Abdul duk abunda yake faruwa a zuriyarku musamman a kan Laila wacce yake yiwa soyayya mai had’e da mugunta. Abdul shi ya ta6a fad’awa Madu cewa Laila na bin maza wanda ba tare da yayi bincike ba ya d’auru a kan hakan saboda tsanar da yake mata tun a daa. Hakan yasa duk inda ya zauna ko kuma ya had’u da ita yake jifarta da k’azafin zina har Uwarku ma ta fara yarda da hakan tana matsa mata da maganan aure, wanda hakan shine burin nashi. Duk yanda Madu ya kai ga binciken rayuwar Laila don ya kamata a halin fasik’anci ya gagara, hakan yasa Haydar yana shigowa rayuwarta yasa aka fara bibiyarta ana d’aukansu a hoto yana tura mata duk don ya tsoritata ta nemi aure wanda suka tabbatar Alhaji Abdul zata za6a a k’arshe. Sai dai da yake Allah ya fisu, Laila da Haydar basu rabu ba. Alhaji Abdul shi ya bawa Micheal abokin Abul kud’i don ya kaishi club yasha giya, hakan yasa bayan yayi caca yayi losing aka dakeshi aka kira Alhaji Abdul yazo ya d’aukeshi. Ina hankalinku yake da kuka kasa gane wannan makircin? Ya za’ayi su samu number Alhaji Abdul kuma su kirashi kai tsaye yaje ya d’auko Abul? Da alama kuma bakwa amfani da iliminku. Ban san ya aka yi aka gane halin Alhaji Abdul a ranar aurensa da Laila ba, abunda na sani shine; umurninshi ne da aka saka kwaya a jakar Abul bayan ya gudu a ranar auren, haka yasa aka yi ta bibiyarsa har rayuwarsa ta lalace sannan ya tura Haydar Abuja ya kuma aikeshi ya kar6o mishi wani aika a kasuwan dasu Abul suke kwadago don ya ganshi ya dawo dashi gida, saboda ya lura da cewa bayan Abul ya 6ace Laila bata shiga damuwar da zai 6ata aurenta ba wanda dama hakan shine target d’insa. Abdul shi ya biya mutumin da yake sayarwa Abul kayan maye kan ya musu k’azafin sata sannan ya musu duka don ya lura Haydar na bibiyar Abul, kuma yasan da yaji abunda ya faru zai dawo dashi gida wanda hakan zai k’ara hatsaniya tsakanin Laila da Haydar. Wani abunda baku sani ba shine, Abdul ya k’arawa Haydar matsayi ne a office d’insu don su sakar mishi aiki ya dinga wahala sannan daga baya suna k’ok’arin mishi k’azafin satan kud’in company wanda zai kaishi prison, sai dai hakan bai faru ba saboda lokacin da suke shirin yin hakan bai zo ba. Sannan a yau Madu ya sanar da Abdul mutuwar auren Laila wanda cikin murnar hakan ya koreni a rayuwarsa saboda na gama aikina. A k’arshe Madu yana yiwa Abdul aiki ne don kud’i da yake bashi wanda shi kuma yake kaiwa marayun daya cinye dukiyar mahaifinsu wato ubangidanshi. Da ni da Abul an yi amfani damu ne don wargaza wannan zuriya kuma a k’arshe basu ci sa’a ba. Wannan kad’an kenan daga cikin sharri da makircin da wad’annan mutane biyun suka k’ulla. Na barku lafiya.’

Mum Fateey 👌

Back to top button