Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 48 Complete Novel
*ASM Bk2048*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………..Tafiya take bata san inda take wurga k’afafunta ba don sam bata cikin hayyacin ta a haka har Allah yasa ta fito cikin Asibitin tasan in taje pharmacy d’in asibitin ba za’a bata ba tunda ba Doctor ya turo ba hakan yasa ta yanke zuwa d’aya daga cikin pharmacies d’in dake wajen Asibitin tana ta tafiya gani take tafiyar ma bata sauri tamkar maidota baya ake hakan yasa ta yanke hawa Napep duk da ba wani nesa bane tama kusa isa, bayan ta tsaida ta fad’i mashi inda zai kaita shima mai Napep d’in har saida ya d’anyi mamaki yace mata nan wajen gate tace eh amman zai jira zata siyo abu ne sai ya maido ta makaranta yace nan school of nursing tace mashi eh yace to ta hau, bayan sun tsaya ta nufi cikin pharmacy d’in gabanta sai fad’uwa yake har ta kusa rubzawa k’atuwar kwalbatin dake wurin batare da ta ankare da slab din ya fashe ba mai Napep d’in ne ya d’an d’aga murya yace tabi a hankali don ya lura duk a firgice take ta d’aga mashi kai kawae, bayan ta shiga ta fad’i abunda za’a bata ba 6ata lokaci aka d’aukko mata ta je wurin biya ta bada d’ari biyar ta juyo saida cashier d’in yace mata canjin ta fa sannan ta juya ya bata ta amsa ta fito bayan ta hau Napep d’in suka komo Asibitin, a bakin gate ya aje ta ta mik’a mashi duka sauran canjin dake hannunta ta juya, ganin a rud’e take yasa yay tunanin ko bata san nawa ta bashi ba ya tsaidata yace kud’in sun yi yawa tazo ta amshi canji hannu kawae ta d’an girgiza mashi alamar ya bassu ta nufi ciki yana ta kallonta gashi dai baisan wacece ba don ta rufe face d’inta amman dae ta bashi tausayi don tabbas da gani akwai abunda ke damunta k’arshe yay mata Addu’a yaja napep din ya tafi, nan da nan ta iso d’akin su ta shige bayan ta cire nik’ab d’in zaune tay a gefen gado tana ta zare ido wani irin tashin hankali take ciki tsoronta ta gwada taga cikin ne can wata Zuciyar ta bata shawarar ta daure ta gwadan in ma shine tunda wuri ba sai taje ta siyo allurar zubda ciki ba tay ma kanta, sosae hakan yay mata ba tare da tayi tunanin wata matsala ba ta mik’e saida ta samu wani d’an murfi sannan ta fita zuwa toilet d’in su bada jimawa ba ta fito ko kallabi babu a kanta haka taje tayo fitsarin, a bakin windown d’akin ta tsaya ta d’aura robar fitsarin ta koma bakin gado ta d’aukko ledar pt d’in ta dawo, tsaye tay cike da fargaba take kallon fitsarin ba don komai sai Allah ya k’addara ba da iya tashin hankalin da take ciki ya isa yasa in ma cikin ne ya zube, can zuciyarta ta raya mata time fa na tafiya gashi yau Friday tayi abunda yakamata da sauri tasa hannu ta cizge ledan hannu na rawa ta fiddo tsinken gwajin ta tsoma shi a cikin fitsarin kaman yadda ake yi bayan ta fiddo ta aje ledar data fiddo shi a ciki ta d’aura tsinken flat hannunta nata k’akkarwa, a hankali ya fara washewa idonta akan shi tun ma kafin ya gama ta fara girgiza kai had’i da gumtse baki a haka har ya gama jajayen layuka biyu suka bayyana daro daro alamar akwae cikin, kwata kwata ta kasa yin kuka sai faman girgiza kai take tana fitar da numfashi da k’arfi da karfi ga jikinta dake ta kerma da k’yar ta kai jikin bango kusa da window d’in ta jingina bayanta sai lokacin kwalla suka fara zubo mata masu d’umi cikin wata irin murya ta fara fad’in “ciki ne da ni! Ciki….Na shiga ukku na lalace na bani! Mi maye ni Fatuu na mutu, Ya Haisam ka cuce ni, kaci amanata na shiga ukkuna in gwaggo taji wannan Maganar nasan mutuwa zatayi wllh…” tana Maganar tana Jujjuya kai, tana cikin wannan halin taji motsin kaman ana tunkaro d’akin bata gama gasgatawa ba taji muryar wata tana fad’in “Fauzy kema kin dawo kenan” Fauzyn ta bata amsa da “Eh wllh Maryam toilet ya koro ni” ta k’arasa Maganar tana dariya jin muryar Fauzy yasa a firgice Fatuu ta kai hannu ta rarumi ledar strip d’in da tsinken gwajin ta nufi gado a sukwane taja bargo ta lullu6e har kan ta, tana gama rufe jikin Fauzy na shigowa ta bita da ido sam bata kawo idonta biyu ba ta duk’a ta d’aukko bucket ta fita don flushing d’in su bai yi saidae mutum ya cika bucket da ruwa ya shek’a, tana jin lokacin data fita amman bata bud’e jikinta ba don tasan da ta ga fuskarta zata zargi wani abu tay lamo tafin hannunta toshe da bakinta, after some minutes saiga Fauzyn ta dawo ta maida bucket d’in k’ark’ashin bed tana kokarin mik’ewa kwatsam idanunta suka sauka akan pt strip d’in dake yashe a k’asa wanda sam Fatuu bata san ya fad’i ba iya ledar ce a hannunta, slowly Fauzy ta kai hannu ta d’aukko shi ganin abunda ke a jikin shi yasa ba shiri ta mik’e idanunta still na akan shi tana kallo da tsananin Al’ajabi had’i da mamaki ta d’an gyad’a kai cikin ranta ta ayyana pt strip kuma a d’akinsu mai nuna akwae ciki to waya kawo shi??? A wani irin slow ta d’ago ta kalli Fatuu dake kudundune lokaci guda kirjinta ya buga jin zuciyarta na raya mata kodae itace tunda ai ba kowa a d’akin sai ita kuma duk sauran students na Class hannu ta kai ta rufe bakinta gabanta na cigaba da fad’uwa can kuma ta cire hannun murya na rawa ta kira sunan Fatun amman bata amsa ba bata kuma nuna idonta biyu ba hakan yasa ta k’ara kiran sunan da k’arfi nan ma still bata amsa ba nan take Fauzy ta shiga girgiza kai cikin murya mai nuni da tashin hankali tace “Zarah I know u’r not asleep idonki biyu to ki tashi don na riga nasan abunda kike 6oyewa gashi ma a hannuna!!” runtse ido Fatuu tay sosae ta kasa gane mi Fauzy ke magana akai tana haka taji Muryata tana fad’in “Ki tashi Zarah ina son sanin wannan abun na waye!” Jin haka yasa a kidi’me ta yaye bargon tana juyowa idanunta suka sauka akan abunda Fauzy ta d’aga tana nuna mata wani abu Fatuu ta had’iye Kutt sai zare idanunta da sukae jawur take yanayin fuskar ta kadae ya tabbatar ma da Fauzy abunda take zargi, ganin irin kallon da take mata ne yasa cikin rawar murya Fatuu tace “m….miye wannan d’in…?” Wani d’an murmushin takaici Fauzy tay kafin tace “abun ki ne da kikai amfani dashi, yanzu ashe da gaske ciki ne da ke Zarah!!” A razane Fatuu ta hau girgiza mata kai tana fad’in ita fa bata san mi take magana ba akai ya za’ai wannan ya zama nata ita da tasan ba aure ne da ita ba, Fauzy tace “Yes Zarah ba aure ne dake ba amman kina da ciki ai ba dole sai ta aure ake samun shi ba ko” Fatuu na jin haka ta saka mata kuka tana fad’in sharri zata ja mata ita data san halinta ko samari bata saurara, duk yadda Fauzy ta so ta fad’a mata gaskiya abun yaci tura k’arshe ma sai cewa tay ta sani ko sharri ake son ja mata tunda dama anata fad’in ciki ne da ita jin wannan Maganar yasa Fauzy ta d’an sauko ta fara tunanin zai iya yuwuwa hakan ne to amman abun da d’aure kai mi ta tsare ma wani da har za’a mata sharri irin wannan ita da take zaune da kowa lafiya sannan kuma ana k’aruwa da ita sosae Saboda k’ok’arin ta, kan Fauzy ya gama d’aurewa ta rasa tunanin da zatai sai kallon Fatuu da ta duk’e kanta tana kuka take can ta juya gefe idanunta suka sauka akan hijab da nikab d’in da Fatuu ta ajiye slowly ta nufe su tasa hannu ta d’aga nikab d’in wanda nata ne kuma a cikin Akwatin kayanta tasan ta ajiye shi to miya fiddo shi? bata kaiga ba kanta amsa ba idanunta suka sake sauka a kan robar fitsarin da Fatuu tay amfani da shi harda sauran fitsarin ganin shi ya tabbatar ma da Fauzy gaskiyar Al’amari cike da tashin hankali ta juyo tana kallon Fatuu yayin da acikin ranta ta furta innalillahi Wa’inna ilaihir raji’un! Kiran sunan Fatuu tay ta d’ago da jajayen idanunta ta kalleta jiki a mace ta nuna mata robar fitsarin tace itama kawo ta akai? Wani abu Fatuu ta had’iya cikin kuka ta hau rantse rantsen itafa ba ita tay amfani dasu ba k’ilan tana cikin bacci wata ta shigo d’akin don kar a kamata tayi amfani dasu anan still Fauzy tay tana kallonta kawae jin wata magana ta rashin hankali duk wuraren dake da akwae a Hostel d’in sai wata tazo d’akinsu duk da ga Fatun kwance tay hakan, ta lura in ba da gaske tay ma Fatuu ba bazata fad’i mata gaskiya ba duk da ta riga ta gama yarda itace tay amfani dasu kawae tana son taji daga bakinta ne, sauke nannauyar ajiyar zuciya tay tace “Ok fine tunda kince bake kika yi amfani dashi ba kin k’i ki fad’a man gaskiya I know what to do” tana gama Maganar ta juya zata fita da sauri Fatuu ta mik’e ta sha gabanta fuskarta jage jage cikin rawar murya tace mi zatayi d’an murmushi Fauzy tay tace ina ruwanta ta bata hanya, k’in kaucewa Fatun tay duk tay zuru zuru sai motsa baki take ta rasa abunda zata ce ganin haka yasa Fauzy cewa “tunda kina son ki sani to bari in fad’a maki, daga nan in na fita gidan ku zan wuce zan je in kai ma gwaggo wannan pt strip d’in in mata bayanin komae harda ciwon da kike tayi ba tare da saninta ba kin fake da baki son hankalinta ya tashi alhali ba haka bane sai yanzu na gano dalili” tana k’arasawa ta fara kokarin ra6awa ta gefen Fatun ta wuce da sauri ta kamata tana girgiza mata kai cikin kuka tace “Fauzy don’t do dis to me na fad’a maki bani nayi amfani dashi ba nan fa Hostel room ne kowa zai iya shigowa kuma ai bani kad’ai ce a d’akin ba ko” ita kanta Fatun bata san mi take fad’a ba, d’an murmushin takaici Fauzy tay tace “Yess Zarah u’r not d only one a cikin d’akin ni dake ne so in kina tunanin ko sharri zan maki duk abun mai sauk’i ne yanzu ki sako Hijab d’in ki mu fara zuwa gidan Aunty Mareeya akai mata pt strip d’in sannan mu wuce gidan ku akai ma gwaggo kin ga duk sai a taru a tuhume mu baki d’aya” zuru Fatuu tay tana ta motsa baki cikin d’aure Fuska Fauzy tace taje ta sako Hijab d’in su tafi mana, yarfa hannu Fatuu ta fara yi ta shiga fad’in ta shiga ukku ta lalace karta yi mata haka don Allah ganin zata 6ata mata lokaci yasa Fauzy tureta gefe ta wuce har ta kai kopa taji muryar Fatun tace “ki dawo zan fad’a maki gaskiya to” cakk Fauzy ta tsaya ta runtse ido wani irin tashi hankalinta ya k’ara yi jiki a mace ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye bayanta tana ta kuka cike da Al’ajabi tace “so it’s true Zarah u’r pregnant?” Jinjina mata kai tay alamar eh wani irin jiri ne ya kwashi Fauzy da sauri ta dafe kanta tana salati kafin da k’yar ta nufi gadonta ta zaune idonta akan Fatuu dake tsaye can itama ta lalla6a ta koma gefen nata gadon ta zauna suna facing juna, sun d’an d’auki lokaci a haka kwata kwata Fauzy ta kasa magana Saboda tsabar rud’ewa baki bud’e take kallon Fatuu abun ya matuk’ar tada mata hankali wai Zarah data sani bata ko kula samari bare ayi zancen soyayya ko aure itace da ciki, how on earth?” Fatuu dae sai kuka take ta sadda kai can Fauzy ta sauke ajiyar zuciya rai a 6ace ta kira sunan Fatun ta d’ago ta kalleta a kausashe tace “am highly disappointed in you Zarah, ina hankalin ki da na sani ina tunanin ki ya tafi, duk irin kamun kan ki da na sani har kika iya ba wani dama ya ku sance ki ba tare da kinyi tunanin girman zunubin hakan ba, to ko dama kina aikatawa mu kika lullu6e….” Da sauri Fatuu tace “Don girman Allah Fauzy ki daina fad’in hakan wallahi tallahi billahillazi ba hali na bane yadda kika d’auke ni haka nike, Fauzy k’addara ce ta fad’a man nima ba da son rai na ba hakan ta faru wllh fyad’e aka man” zaro ido Fauzy tay baki bud’e ta maimaita fyade aka mata da sauri Fatuu ta d’aga mata kai alamar eh salati Fauzy ta shiga yi hannunta dafe da goshinta can ta cire tace “amman ke ya akai har kika bari hakan ta faru ina kika je har aka maki hakan kuma waye yay raping en ki??” yarfa hannu Fatuu tay ta langa6ar da kai tace “Don Allah Fauzy kada ki man wannan tambayar nasan kin yarda dani to ki yadda wllh raping ne bada son raina bane” jinjina kai Fauzy tay tace “tabbas na yarda dake Zarah amman taya daga kin fad’i man rape in ki akai sai in kama bacin baki fad’i man yadda akai ba” Magiya Fatuu ta shiga yi mata kan ba sai taji yadda akai ba kawae ta taimaka mata ta san yadda zata rabu da shi amman fir Fauzy ta k’i amincewa tace lallae fa sai ta fad’i mata yadda akai har a kai raping inta in ba haka ba to da son ranta a kai kuma ba makawa sai taje gidan su ta fad’a, kuka wiwi Fatuu ta ke yi hakanan bata son ta fad’i mata wanda yay mata hakan don duk da haushin shi da take ji sai taji bata son Mutuncin shi ya zube a idon mutane gwara ta rufa mashi Asiri, k’arshe da Fauzy taga ta kafe tak’i fad’i sai ran ta ya 6aci sosae ta mik’e Fatuu na ganin haka itama ta mik’e da sauri ta nufeta ta kama hannunta guda tana kuka tana mata Magiya a fusace Fauzy tace “Wllh tllh Zarah ko kukan jini zaki indae baki fad’i man wanda yay maki hakan ba Allah a yau d’innan sai gwaggo tasan halin da ake ciki wato shi baiji komae ba yay maki hakan sai kece zaki kare shi da alama dae magana ta na akan hanya da son ran ki komae ya faru” tana rufe baki ta fara k’ok’arin k’wace hannunta daga ruk’on da Fatun tay mata cikin k’araji Fatuu ta fara fad’in “to don Allah Fauzy ki tsaya zan fad’i maki” bin ta tay da wani kallo kafin tace to ta sakar mata hannu bayan ta saki ta koma gadonta ta zauna itama ta zauna a bakin nata ganin yadda Fauzy ta kafeta da ido yasa ta fara motsa baki tana d’an nishin kuka ta rasa ta ina ma zata fara Fauzy dake kallonta tace “am listening Zarah, tell me who impregnated u??” Ba alamar wasa a fuskarta tay Maganar saida Fatuu ta had’iyi wani wahalallan yawu kafin da k’yar ta bud’e baki tace “zan fad’a maki Fauzy amman don Allah don son Annabi ki man alk’awarin bazaki fad’a ma kowa ba koda gwaggo ce kuma zaki taimaka man” kai Fauzy ta d’aga mata alamar eh hakanan taji gabanta ya fara fad’uwa tun bata ji wanene ba don ta gane Fatun na jin nauyin ta fad’i ko waye, ce mata tay ta fad’i tayi alk’awarin da bakinta Fauzyn ta bud’e baki tace tayi mata alk’awarin hakan suka zuba ma juna ido da k’yar murya na rawa Fatuu tace “Y….YA HAISAM NE!!!” Kaman saukan aradu haka Fauzy taji Maganar gaba d’aya ta zaro ido waje baki bud’e k’irjinta ya fara wani irin bugu k’arshe ta mik’e da sauri ta nufi kopar d’akin ta d’aga labulan ta d’an lek’a wajen ta tabbatar ba kowa sannan ta maido kan ta ciki tasa hannu ta tura kopar cikin tashin Hankali ta dawo ta zauna inda ta tashi a kidi’me tace “Zarah kina da hankali kuwa? have u gone mad! Saboda na matsa maki sai kin fad’a mani wanda yay maki hakan shine zaki raina man hankali don ki kare kan ki, mi Ya Haisam yay maki da ya cancanci wannan bak’in k’azafi daga gare ki???” Jujjuya kai Fatuu ta shiga yi ita dama tasan zai yi wuya duk wanda yaji Maganar nan ya yarda da ita tana sheshsheka tace “Wllh Fauzy da gaske nike shine yay rapi….” Tun kan ta k’arasa Fauzy tay mata yar tsawa tace “Enough Zarah, enough pls wannan Maganar taki ba abu bane da hankali zai d’auka wllh haba how on earth ace mutum kaman ya Haisam wai shine yay raping d’in ki, kawae na gane kina mashi sharri ne don ai saurin barin Maganar amman wllh kin ban mamaki mi ya Haisam yay maki da zaki mashi bak’in k’azafi?” Cikin kuka tace “Fauzy akan wane dalili zan mashi k’azafi miya man tunda nike dashi in ba Alkhairi ba ba abunda yake shiga tsakanin mu sai yanzu da yay man wannan mummunan abun shiyasa tun farko kika ga na kasa fad’i maki wanda yay man d’in Wallahi tallahi kinji na rantse shine kuma in zaki lura ke kan ki rannan ba sai da kika tambaye ni wai lafiya kika ga ban ciki Maganar shi ba yanzu kuma ko waya baki ganin muna yi kaman da har nace maki hankalin shi ne ba kwance ba tunda jinyar mahaifin shi yake to kawae na fad’a maki ne don abar Maganar wllh” da alama mutuwar zaune Fauzy tay ko idonta bai motsi ba k’aramar razana tay da jin zancen ba k’irjinta kai kace ana mata daka a wurin, ba wai bata yarda da zancen Fatun bane kawae ta kasa believing Haisam zai iya aikata wannan d’anyen aikin ga wata ma ba Fatuu ba, ta d’auki lokaci bata ce uffan ba sai da aka d’an jima sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Fatuu tace ta fad’a mata ya akai hakan ta faru nan Fatun ta shiga bata labari tiryan tiryan bata 6oye mata komae ba har yadda ta kasa hanashi da farko da kuma yadda har ya aikata mata hakan tana gamawa ta fashe da matsanancin kuka tana Fad’in ya cuceta ya gama da rayuwarta gashi yanzu yaja mata abun kunya, itama Fauzy kuka ta saka suka taru sukai tayi aka rasa mai rarrashin wani da k’yar Fauzy ta mik’e ya nufi gadon Fatun ta hau ta jawota jikinta ta shiga rarrashinta tana cewa ta daina fad’in abunda take fad’i akan shi daga jin yadda abun ya faru bada niyya bane kawae kaddara ce da sharrin shaid’an jin hakan yasa Fatuu d’agowa cikin kuka tace “duk da hakan harda son zuciya Fauzy dama yanzu na fahimci yana man wasu abubuwa da bai saba ba rannan fa a parlorn shi kama shi nay yana kallon man boobs ena gashi yay ta yawan ta6a ni bai jin komae ranar da zai koma wancan zuwan da yayi harda hugging ena fa yayi kawae na fahimci ya fara sha’awata ne shiyasa ya kasa daurewa duk da magiyar da na rink’a mashi amman saida ya cutar da ni” shiru Fauzy tay kaman tana nazarin wani abu Fatun ta maida kanta jikinta don wani irin Sara mata yake can bayan wani lokaci Fauzy tace “Yanzu miye abun yi don ni wllh kaina ya riga ya k’ulle saboda wannan ba k’aramin Al’amari bane ba kowace zuciya zata iya d’auka ba” da sauri Fatuu ta d’ago ta kama hannuwanta cikin muryar kuka tace “mu zubar da shi kawae Fauzy ba tare da kowa ya ji ba” waro ido Fauzy tay a razane tace “abortion kuma keda kan ki kike fad’ar hakan sai kace baki san tarin illolin shi ba……” Katseta Fatuu tay “Eh nasani Fauzy amman shi kadae ne mafita wllh in ba haka ba ba k’aramar matsala cikin nan zai jawo ba na farko kinga da an sani za’a kore ni daga school d’in nan kuma bazan k’ara samun damar yin karatu anan ba ga suna na da zai 6aci, duk ba ma wannan ba gwaggo nafi ji wllh taji zancen nan zuciyarta na iya bugawa ta mutu kinga Saboda fa wanda za’a aura man d’in nan ba shiryayye bane yana neman mata ta kasa natsuwa har da su ciwo to ina ga yanzu in taji ina d’auke da cikin shege….” tana kai k’arshen Maganar ta fad’a jikin Fauzy tana cigaba da yin kukan, shiru Fauzy tay ita dae har ga Allah tsoron abortion take can tace “ni gaskiya Zarah ban goyon bayan ki abortion Saboda abunda kan iya faruwa duk da ba fata ake ba za’a iya samun matsalar da asirin mu kuma zai zo ya tonu kinga anyi ba ai ba kenan ga laifin kisan kai kuma a wurin Ubangiji gaskiya dae muyi tunanin wata mafitar ba wannan ba”,
Fatuu da ta d’ago daga jikinta tace “wace mafita kike tunani data fi wannan Fauzy, in ba hakan muka yi ba duk abunda zamuyi asirinmu tonuwa zai yi ni kuma abunda ban so kenan kar ki manta akwae aminci mai k’arfi tsakanin Gwaggo da Hajiyar su shekaru masu yawa suna zumunci na tabbatar in wannan abun ya bayyana sai zumuncin nan ya lalace abubuwa da yawa Al’amarin nan zai shafa don Allah Fauzy ki bani goyon baya in sha Allahu ba wata matsala da za’a samu kuma Allah zai yafe man tunda yasan ba da son raina hakan ta faru ba sannan cikin kinga k’arami ne ko kwana arba’in bai yi ba duka watan shi guda” shiru kawae Fauzy tay tana bin ta da ido ita dae hakanan hankalin ta bai kwanta da a zubar da cikin ba ba kamar wasu abubuwa da take nazari, magiya Fatuu ta shiga yi mata kan azubar d’in can ta nisa tace “kin gane Zarah ni wllh raina bai kwanta da a zubar da shi ba ba kamar dana yi la’akari da wasu abubuwa shin Ya Haisam ya ta6a kai ki gidan tunda kuke dashi?” a hankali ta girgiza mata kai alamar a’a shiru Fauzy tay tana sake yin nazari tsawon shekara biyar da suka san juna amman bai ta6a kaita gidan ba sai yanzu sannan tace yana yawan ta6a ta ba tare daya ji komae ba wanda a yadda ta bata labari a da sam bai mata haka hasali ma bai son su ke6e su biyu to miyasa yanzu yake mata hakan? wata Zuciyar ta raya mata k’ilan don yanzu ta girma ta zama cikakkar budurwa shiyasa ya fara jin sha’awarta kamar yadda itama Fatun take tunani can kuma nazarinta ya gangaro kan Alkhairin da yake mata wanda harda su wayar miliyan hakanan ba dangin iya bana baba nan ma wata zuciyar ta sake raya mata wannan ai daman ya saba yi mata Alkhairin kuma zai iya yuwuwa ko ya fara son ta ne shiyasa har Yay mata irin kyautar, k’arshe dae kan Fauzy ya k’ulle tamau ta kasa yin tunanin wani kwakkwaran dalili don komae a bud’e yake amman tana jin kaman something is amissing k’arshe dole ta bar ma ranta kawae kaddarar su ce a hakan, kallon Fatuu tay tace “zan amince a zubar kamar yadda kike so amman da sharad’i guda” da sauri Fatuu tace miye sharad’in Fauzy taci gaba “Dole Ya Haisam yasan da cikin nan kafin mu zubar d’in” wani kallo Fatuu tay mata a marairaice tace “miyasa za’a sanar mashi Fauzy abunda shi baima damu da abun da yay man ba kina gani tunda hakan ya faru sau biyu ya kirani ban d’aga ba daga nan fa bai sake kira ba dama shima kiran sai kusan da akai 2 weeks sannan don Allah mu rabu dashi kawae ni nasan ba wani abunda zai yi” d’an girgiza kai Fauzy tay tace “karda idon ki ya rufe Zarah zubda ciki fa ba k’aramin abu bane da za’a ce ayi ba tare da mai shi ya sani ba yanzu ba fata nike ba azo Asiri ya tonu wurin zubarwar taya zamu kare kan mu tunda shi ba sanin da cikin yay ba think about it Zarah” d’an shiru Fatuu tay duk ranta bai so ba tace mata ita tana ganin in sha Allahu ba abunda zai faru ai cikin k’arami ne they should just go ahead and do d abortion ba tare da ya sani ba amman Fauzyn ta kafe kan ita dae a sanar mashi don bata tunanin hakanan yak’i kiranta dole da dalili Fatun tace to taya zata sanar mashi shi da bai nan kuma dae ai bai dace ta kira shi yana can wurin jinyar ba, d’an jimm Fauzy tay sai kuma tace “mi zai hana ki kira Kawu Amadu ki tambayi ko sun dawo baki sani ba” gyad’a kai tay ta juya can kusa da pillow ta d’aukko wayar ta fara k’ok’arin kiran Amadun ringing biyu ya d’aga ta gaishe shi ya amsa ya tambayeta ta dawo gida ne don shi yana Makaranta tace mashi a’a sai anjima d’an shiru tay jin hakan yasa ya tambayeta da wani abu ne tace a’a kawae tana son ta tambaye shi ko Hajiyar Sanata ta dawo ne, yar dariya yay yace “ke dai fad’i gaskia kodae ran ki ne ya baki Romeo d’in ki ya dawo shine kike son ki tabbatar” d’an yamutsa fuska tay tace “kai Kawu Amadu ni don Allah ka fad’a man ai Hajiya dae na tambaye ka ba wani ba ko” tana jiyo dariyar shi kafin yace mata eh ta dawo jiya da yamma harda ma Romeo d’in nata, ko sallama bata yi mashi ba ta katse kiran da ta kalli Fauzy har bata san tayi d’an murmushi ba tace mata ya dawo jiya itama murmushin tayi tace “yauwa kinga Allah ya taimake mu komae zai zo da Sauk’i in sha Allah” cike da farinciki Fatuu ta fad’a jikinta tana Fad’in “Thank u so much Fauzy u’r more like my blood sis than Friend, Nagode ma Allah da yake had’a ni da k’awaye Nagari wanda duk in ina cikin damuwa suma suke shiga damuwa har su bani shawara mai kyau da zata fitar dani” d’agota Fauzy tay tana murmushi tace “What are Friends for, haka yakamata aboki na gaskiya ya kasance wani lokacin in kai dacen aboki sai kaji ma har yafi maka wani dan’uwan naka na jini hakan nake ji a tattare dake Zarah” k’ara fad’awa tay jikinta tana murmushi can taji Fauzyn tace “How I wish ace cikin nan na halak ne lokacin da zamu gama makaranta kuna da d’an yaron ku ko yaranku in twins ne lokacin nasan har sun d’an tasa ma, wai za’a ga ruwan kyau dae wllh amman ba komae komi Allah yay mai kyau ne fatana dae ya shige mana gaba a duk abunda zamu yi” Fatun ta amsa mata da Amin a hankali Fauzyn tace mata to ta tashi tay wanka ta shirya sai taje ita kuma zata jirata har ta dawo bazata tafi weekend ba, sosae Fatuu taji dad’i ta mik’e, ba’a d’au wani lokaci ba tayo wankan ta zura doguwar riga bak’a ta yafa gyalenta Saboda zumud’i har ta ma manta da ita mara lafiya ce, tare suka fito har wajen gate cikin sa’a suka samu Napep da Fatuu zata shiga Fauzy ta kama hannunta tace “kiyi man alk’awari nima zaki same shi kiyi mashi Maganar” kai ta d’aga mata tace “nayi maki Alk’awari kuma in zan dawo zan taho da allurar sai kiyi man” d’an jimm Fauzy tay kafin ta gyad’a mata kai tace shikenan amman dae ta tabbatar sun fara yin Magana da shi daga haka ta shige Fauzy na d’aga mata hannu suka tafi.
Tunda suka shigo Unguwar gabanta ke fad’uwa har d’an rufe fuskarta take don kada gwaggo ko Kawu Amadu wani ya ganta Saboda bazata shiga gidan su ba don kada gwaggon ta gano halin da take ciki ba kamar da ta tuna Maganar data yi mata rannan, har bakin gate mai Napep d’in ya kai ta bayan ta biya shi tana ruk’e da yar purse d’inta ta tunkari gate d’in Office yay mata ya Makaranta ta amsa bayan ta gaishe da shi ta shige, part d’in Hajiya tay tunanin fara zuwa don tayi mata ya mai jiki kuma k’ilan ma ta iske Haisam d’in a can tunda yau Friday, lokacin data shiga Hajiyar na zaune a parlor tayi gayun Juma’a bak’i tayi bayan ta dawo daga Masallaci basu dad’e da tafiya ba ta zauna tana kallo idanunta sanye da medical glasses d’inta, tunda Fatuu tay sallama ta maido idanunta kanta tana kallonta har ta k’araso cikin parlon ta zauna kujerar dake opposite da ita da d’an murmushi tace “Hajiya ina wuni an dawo lafiya” still kallonta take fuska a sake ta amsa mata, Fatun ta sake cewa Ya mai jiki, d’an girgiza kai Hajiya tay tace “mai jiki sai dae mu ce Alhamdulillah don an sha jiki kam amman cikin hukuncin Allah ya warke garas abunda ake gudu Allah ya tak’aita faruwar shi” itama Fatun Alhamdulillah tace kafin tay Addu’ar Allah ya k’ara mashi lafiya Hajiya ta amsa, d’an shiru sukae Fatun ta lura da Hajiyar sai kallonta take hakan yasa tasha jinin jikinta ta sadda kai tana wasa da yatsunta can ta d’ago tace ma Hajiyar Ya Haisam na part d’in shi ne zata mashi ya mai jiki d’an girgiza kai ta k’ara yi tace “bai nan tun jiya da muka dawo yana G.r.a da yake har yanzu shi kaman jikin nashi bai idasa warwarewa ba” shiru Fatuu tay tana maimaita abunda tace a cikin ranta can ta tambaye ta bai lafiya ne, Hajiyar ta ruk’e ha6a tace “ai ciwo yasha shima a can jinya biyu akai wllh dama dae tun da muka bar nan zamu Kano na lura da yanayin shi har na tambaye shi sai yace man fever ke damun shi to da yake mutum ne mai k’arfin hali a hakan har suka fita da Mahaifin na su da yake mu sai daga baya muka bi bayan su Germany d’in, to a can ma bai samu ya huta ba bayan sun je aikuwa sai ciwo ya buge shi wani irin zazza6i mai zafi da ciwon kai suka taru suka rufe shi dama kuma shi yana dad’ewa bai yi ciwo ba, amman fa duk randa ya kwanta yana jin jiki wllh don ni bazan iya tuna ma yaushe yay irin wannan ciwon ba amman dae Alhamdulillah ya samu sauk’i sosae nayi ma tunanin zai wuce can U.s d’in da yake suma su Fanan d’in sun zo nan Germany kusan ita tay jinyar mijin nata har ya samu sauk’i to da zamu dawo ne ita ta wuce can shi kuma muka dawo dashi” duk sai jikin Fatuu yay d’an sanyi a hankali tace Allah ya k’ara basu lafiya Hajiyar ta amsa har zata mik’e taji tace “amman kema dae Fateema kaman baki lafiyar ko?” Damm gabanta ya fadi a dabarbarce tace mata eh itama malaria ke damunta, Hajiyar tace to taga likita ko don fuskarta ta fad’a da yawa gashi tayi fayau kamar mara jini da sauri tace mata eh taje taga likita har test an yi mata an kuma bata magunguna yanzu haka tana cikin sha ma Hajiya tace to Allah ya k’ara lafiya ta amsa da Amin had’i da mik’ewa zata tafi Hajiyar tace ba ta bari taci Abinci tace a’a ta k’oshi taci Abinci daga haka sukai sallama ta nufi hanyar fita, lokacin data fito har saida ta saki yar ajiyar zuciya bayan ta fito wajen gate sai taji dama ta san bai nan da bata bari mai Napep d’in ya tafi ba, ta bayan gidan Hajiyar ta bi saida ta kusa bakin titi sannan ta samu mai Napep ta fad’i mashi G.r.a zai kaita yace to ta hau suka tafi, bayan sun iso ya tambayeta road d’in da zai kaita tace bata san sunan road d’in ba da yake sau d’aya ta ta6a zuwa kuma da daddare ne amman zata rink’a nuna mashi hanya yace to, da yake G.r.a ba kaman geto bace sam Fatuu ta kasa gane gidan sai faman uban zagaye layuka suke a kokarin ta na ta gano, sun d’auki lokaci tana dudduba gidajen Unguwar har dae mai Napep d’in ya gaji ya parker a gefen hanya yace mata gaskiya fa ba lallae su gane gidan ba tunda bata san sunan layin da yake ba k’arshe zasu yi ta yin wahala ne, shiru tay da alamun damuwa bata son ta koma ba tare data gano gidan ba don ta san k’arshe ba lalle Fauzy ta bata goyon baya ba ganin yadda ta damu yasa mai Napep d’in tambayarta bata san sunan mai gidan bane d’an Jim tay ta tuno da Haisam yace ai gidan baban shi ne hakan yasa tace ta sani gidan Senator Alee Adamu Zakee ne yace to bari yaga in za’a samu wanda za’a tambaya da sauri tace to ya fita daga cikin Napep d’in yana duba hanya can saiga wata Mota ta taho ya d’aga ma mai Motar hannu cikin sa’a ya tsaya daga d’an gaban Napep d’in ya nufi Motar da sauri, slowly glass d’in driver side ya sauka wani Alhaji ne a ciki mai Napep d’in ya gaishe da shi bayan ya amsa yace don Allah tambaya suke yace to Allah yasa ya sani mai Napep d’in yace “dama wani gida ne muke ta nema mun kasa ganewa gidan wani Senator Alee…..” kakarewa yay yana niyyar d’aga kai ya tambayi Fatuu yaji Alhajin yace gidan Senator Alee Adamu Zakee da sauri mai Napep d’in yace yauwa eh nan, kwatance yay mashi mai Napep d’in ya gane yay mashi godiya yaja Motar shi kuma ya koma Napep d’in Fatuu ta tambaye shi an gane gidan yace eh sosae taji dad’i duk da fargabar da ta cika ta, suna shiga titin layin da aka masu kwatance Fatuu ta hango gidan ta nuna ma mai Napep d’in ya tunkare shi, a gaban tangamemen gate d’in ya parker ta fito su Officer na zaune a saman benci ta nufe su idanun su a kanta har ta k’arasa ta tsaya daga d’an gaban su, bayan ta gaishe dasu tace don Allah ko Ya Haisam na nan d’ayan Officern da tunda ya ganta ya ganeta yace mata eh yana nan, d’an shiru tay ganin haka yasa shi ce mata ba wurin shi tazo bane tace eh yace to ta shiga, juyawa tay ta koma wurin mai Keke Napep d’in tace don Allah ya jirata ba dad’ewa zatay ba sai su koma yace ba matsala hajjaju a fito lafiya harda ce mata wai ta taho mashi da lemu mai sanyi mak’oshin shi ya bushe Saboda yawon da suka sha ta d’aga mashi kai kawae, ta k’aramar kopa ta bi ta shiga gidan tunda ta tunkari ginin gabanta ke fad’uwa abubuwan da suka faru rannan suka shiga dawo mata, saida tay yar tafiya mai d’an tsawo ta isa ginin gidan ta shiga Parlon kafin ta bi ta Corridor ta nufi kopar Bedroom d’in shi………
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.