Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 23 Complete Novel

🐅MATAR DAMISA🐅
(The Wife Of Tiger)

Written and story by
Asma’u Muhammad Auwal

( ASMEETAH NOVEL✍️✍️)

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ——-> 65 & 66 <——-

“Please banzo gidan ku don ki dameni ba fa?”
ya ƙarisa maganar yana zaro mata manya-manyan idanunsa,
turɓune fuska tayi tana faman masa muzurai, kaiwa hannu yayi zai doke bakin cikin zafin rai tayi saurin tare wa da hannun ta, “get out inside my car” yana nuna mata alamar fita da ɗan yatsar sa,
“dan Allah Oga Junaid ka saurare ni mana…”
kafin ta kai ƙarshen maganar ya katseta da cewa “before i count one to three leave my car, if not you’ll see what am going to do” ba shiri Lailah tabar cikin motar da sauri domin ta riga da tasan halin mutumin yanzu zai iya hargutsewa.

fitar ta cikin motar yajaa wani dogon tsuka ya cigaba da wasan game a wayar sa,
da gudu Lailah tayi cikin compound tana rera kuka haka ta wuce su Dr da Ayush a falo suna shan hira ganinta yasa suka tsayar da hirar suka bita da kallo, shi dai Dr yasan dalilin yin kukan ta kawai ya share miƙewa Ayush tayi tare da faɗin “Dr zan wuce Yaya Junaid yana jira na”
“ok tam muje na rakaki gimbiya” ya ƙarisa maganar dai den lokacin da ya miƙe shima yana ƙareta da kallo domin ba ƙaramin kyau tayi mishi ba,
tana sanye da after dress black mai duwatsu ata front ɗin rigar an jera su, gyalen rigar tayi rolling ɗinsa akanta tana riƙe da handbag.
ita ta soma yin gaba tana taku a hankali cikin nutsuwa shi kuwa yana biye da ita, da haka har suka fito harabar gidan suka nufi yanda Junaid yayi parking da motar,
tana zuwa gurin ta buɗe murfin motar ta shige shi kuwa Dr zagaya wa yayi ta yanda Junaid yake drave ya yi knocking yana cewa “well done Ogah kana shaƙar hayaƙi fa, inba busa ba ɗaga hannu ne.” wanda yake cikin motar kuwa a hankali ya sauƙar da glass ɗin motor da murmushi a face ɗinsa yanda yake motsa bakin kai kace abu yake ci duk hakan cikin ji da kai ne kamar bazai yi magana ba after some minute da ƙyar ya buɗe baki yana faɗin “how is ur body” murmushin takaici Dr ya yi sannan shima ya maida masa martani “Hmm! Am ok..” abunda Dr ya faɗa kenam idonsa akan Ayush wacce take ta wasa ta jakar hannun ta duk abunda suke yi tana jinsu, already tasan akwai ƴer tsama a tsakanin su amma a ranta tana jinjina irin girman kai na Junaid, “kai kaji wa mutum ciwo amma gaishe shi da jiki sai ya zamo aiki” magana take a ranta idonta akan Junaid dai den lokacin da zai karya kwana da sitiyarin motar ya miƙi hanyar da zai sada shi da gate, sai da ta waiwaya bayanta tana kallon Dr yanda yake jan ƙafarsa da ƙyar yake tafiya abun tausayi, sai da kwalla ta kusan yanke mata da sauri ta tare fuskarta da hannu kar Junaid ya fahimci wata matsala.

direct super market suka nufa zasu yo shopping ɗin dresses da kuma shoes with handbag and others.
duk siyayyar nan a Ayush za’ayi su, duk wasu abubuwa na amfani wanda mace zata yi using dasu gaba ɗaga za’a siyesu.
tafiya suke ba wanda ya kula kowa a cikin su, ya turɓune fuska gira a haɗe cikin ɓacin rai ya daki sitiyarin ɗin motar ya soma wasa akan titi yana jujjuyar da kan motar da ƙarfin gaske yake danna kan sitiarin wani irin ƙara motar take yi, ganin haka yasa Ayush ta toshe kunnuwan ta da hannenta biyu tana ihu “dan Allah Yaya Junaid kar ka kashe mu, kayi hakuri” tayi matuƙar tsorita sosai jikinta har ɓari yake, wani irin burki ya danna gaba ɗayanta ta tafo fuskan nan ya daki gaban motar ta ciki nan kuwa bakin ta ya fashe sai jini dake tsiyayo wa, tsayar da motar yayi yana faɗin “now tell me meyasa kika daɗe da Dr Hasheem a cikin ɗakinsa?”
bai ma lura da jinin dake bleeding a bakin ta ba, tsabar ƙololuwar baƙin ciki ko kulashi bata yi ba. jin shuru yasa ransa ya ƙara hargutsuwa cikin zafin nama ya wani daka mata tsawa “baa magana nake miki baaa” a razane ta juyo tana kallonsa ga hawayen da ya wanke mata fuska tana ƙoƙarin tare jinin dake tsiyaya daga bakin ta da hannu tace “shin zargina kake yi ne ?
kallon ta yayi ta wutsiryar ido yana cizan laɓɓensa, ya ciro farin handkerchief ya miƙa mata, hannu na kakkarwa ta karɓa tana goge bakin ta, shi kuwa jan motar ya yi a hankali suka ƙarisa shop…
Junaid gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi ganin jini a bakinta, sai dai bai kalli yanda take ba saboda a tunaninsa kar ta raina shi, buɗe murfin motar yayi ya fito yana shan kanwa, itama fito wa tayi idonta cike da kwalla suka nufi cikin shop, shigar su keda wuya anan Ayush ta fara kalle-kallen abubuwan more rayuwa, ga shagon yanda yake ta wal-wal da haske kala-kala! baki ta sake tana kallon ikon god, ita fa har ta manta abunda ya faru a tsakaninta da Junaid fuskar ta ya yi wasar sai faman washe white teeth ɗin ta take, bata ankara ba taji Junaid yace “ke ƴer village je ki dubo abubuwan da kike so wanda zaki yi amfani dashi..” fuskarta ta haɗe ta turo ƙaramin bakin ta ita bata ji daɗi ba yanda ya ƙirata da ƴer ƙauye a gaban mutanen wajen wasu har da dariyar su.
shige wa tayi rai a ɓace direct wajen kayayyakin sakawa tayi ta fara zaɓar dogwayen riguna masu bala’in kyau ga tsada, sai data ɗauki kala 20 na abayoyi, Suez lace kala 5, gizner 5, materials 5, laces 15, atamfa 15, ƙananun kaya suma sun kai 15, da sauran abubuwan da ba’a lissafo ba, takalma da duk abubuwanda take so komai da komai duk abunda tasan zata nema to sun siye su, banda mayuka da turaruka sukam ba’a magana domin kala kala gasu nan har da nasu gyaran gashi….
aka zo gun lissafin kayan da Ayush ta ɗauka, 5.500millions
zaro ido Ayush tayi tana nanatawa batayi tunanin ta ɗauki abubuwa har haka ba,
ƙwayar idonta ta kai kan Junaid tana son ganin irin reach ɗin da zai bayyana akan fuskarsa abun mamaki baiji komai ba sai hannunsa daya sa a aljihunsa ya ciro check yayi rubuce-rubucensa sannan ya miƙa wa manager na super market, ma’aikatan gurin ne suka saka kayayyakin a bayan booth…!
shiga cikin motar sukayi Junaid yayi drived ɗin su sai gida,
isar su kenam gidan ita kuma Mommy tana shirin fita tana sanye da kayan likitoci a jikinta, ganin su Junaid sun dawo yasa ta fasa shiga cikin motar tata tana faɗin “aa’a kaga manyan gari kun dawo ne?” da gudu Ayush tayo kan Mommy tana dariya zuciyar ta fam yake da farin ciki ganin lodi-lodin kayan data jido, “Mommy mun siyo kayayyakin kin gansu kuwa sunyi kyau sosai” tana magana baki ya gagara rufuwa, murmushi mommy tayi sannan tace “Hummm Ayusher kenam ke iya wannan kawai kika gani, ku ƙarasa shiga ciki Junaid ya kai ki room ɗinki zaki sha mamaki,
ni kinga sauri nake zan wuce hospital ana nema na” ta shafa sumar kan Ayush tare da manna mata kiss a goshi, tayo kan Junaid shima ta manna masa muach a kan goshin sa tana faɗin “saina dawo” da sauri ta shige cikin motarta ta miƙi doguwar hanyar dazai sadata da gate kafin ta isa already maigadi ya buɗe mata gate, tayi ficewar ta…

da gudu Ayush tayi cikin babban falo tana baza idanuwa taga inane ɗakinta, domin akwai ɗakuna sosai ata cikin falo sai wanda ka zaɓa, ganin har yanzu Junaid bai shugo ba yasa ta faɗin “i can’t wait gaskiya” ɗakuna ta fara buɗe wa tana lelleƙawa duk wanda ta buɗe sai ta ga wayam iya kujeru ne kawai, wasu ɗakunan baƙi ne, ba ɗakin da bata shiga ba amma bata ga ɗakin ta ba, tsayawa tayi tana tunanin “to ina ne ɗakina? kodai ba’a cikin falon nan yake ba”, tana cikin wannan tunanin taji shugowar Junaid yana faɗin “ku shugo da kayan” wasu matasa biyu ne daya kira don su shugo da kayan da suka siyo cikin ɗakin Ayush,
Ayush zuba eyes tayi taga ina zasu kai kayan don tana da tabbacin yanda zasu kai kayan nan ne ɗakinta,
ƙwatanta musu ɗakin Junaid ya yi!
kamar yanda ya gaya musu haka suka hau upstairs suna taka matakala kamar zasuyi ɗakin Junaid sai suka karya ƙwana ta ɓangaren hagun nan ne ɗakin Ayush kusan a jere dana Oga Junaid, sai dai shi nasa kana haurowa upstairs zakayi right hand ɗakin Ayush kuma ɓangaren hagun, Ayush ce itama tayi gaba zata bi bayan su bata ankara ba taji an riƙo hannun ta yayi wani irin juyi da ita kafin ya jawota jikinsa, suna fuskantar juna gashin kanta ne ya hautsino gaba duk ya rufe mata fuska, tsayawa yayi yana kallonta daga bisani ya kai hannunsa kan sumar kanta yana ture mata gashin, kyakykyawar fuskarta ne ya bayyana idonta a lumshe ga zara-zaran gashin ido suma sun kwanta sai sheƙi suke, hannunsa ya kai gefen fuskar ta yana shafa face ɗinta mai shegen laushi ga tafin hannunsa shima ba ƙaramin laushi ne dashi ba sai abun ya bada citta,
a hankali yake kai wa fuskar sa saitin nata tana jin yanda numfashin su yake hargutsuwa amma ta kasa buɗe eyes ɗinta, yana shirin kaiwa maroon lips ɗinsa kan ɗan ƙaramin bakinta yaji an katse masa hanzarin sa waɗanda suka shigar da kayan ne suka fito suna faɗin “Ogah mun kai, mun kammala shirya komai…”
Ok kawai yace tare da faɗin “send me your bank account”
washe baki sukayi suna godiya suka tura mishi, fita suka yi da murna domin sun san ba kuɗi kaɗan zai tura musu ba, kafin su fita daga harabar gidan kuwa har suka ji alert da sauri suka duba zaro ido suka yi baki ya gagara rufuwa baki a haɗe wajen cewa “five thousand and hundrend naira?? wow oga Allah ya ƙarawa rayuwa albarka wallahi, mutumin ya iya kyauta mai tsoka,” haka suka bar gidan suna yabonsa….

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

GASKIYA BA CHAJI A WAYATA BARI NA BARKU HAKA SABODA DA 4% NAKE USING YANZU HAKA, KU BIYONI BASHI
NEXT PAGE MORE TYPING ZANYI DANA WANNAN PAGE….

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*.

Back to top button