Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 13 Complete Novel

*ASM Bk2013*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

………Ganin ta zuba mashi Ido tak’i cewa komae gashi kuma tana son tay Magana yasa ya d’an matsa hannuwanta da har lokacin yake ruk’e dasu, firgit tay ta dawo daga zancen zucin da take ta d’aura idanunta kanshi lokaci guda Maganganun su Haulat da Kawu Amadu suka fara mata yawo a kai, gaba d’ayansu Maganganunsu iri d’aya ne kowa cewa yake Kota gaya mashi Hakuri zai bata kuma zai daina ganin k’imarta ga kuma Maganar da ita kanta taji ya Fad’a da Bakinshi na baya ra’ayin mata biyu ga kuma zancen kwanciyar Fanan Asibiti don yace bazai Aureta ba to ita ma kenan da take yar uwarshi yace bazai Aureta ba inaga ita da bata had’a komae dashi ba, lokaci guda tsoron fad’i mashi gaskiya ya kamata murya na rawa tace “da..dama banji dad’i ba zaka tafi don baka ta6a fad’a man zakai Aure ba shiyasa duk na damu” shiru tay ta sunkuyar da kanta don kar ya gane k’arya take, sigh yay ya saki hannuwanta ta jingina gefen jikinshi da kujera,tabbas bata yi k’arya ba bai ta6a Maganar Aurenshi da ita ba a tunaninshi baiga Amfanin yin wannan zancen da ita ba, nisawa yay Calmly ya fara Magana “am really sorry about dat Zaraah,u know Fanan is my sis so a hakan naci gaba da d’aukanta though we were engaged,ina ganin bashi da wani muhimmanci in ta Maganar aure tunda lokacin bai yi ba not knowing hakan zai iya zama matsala……” da sauri ta katseshi tace “a’a Ya Haisam ba wani abu bane kawae nayi zaton Maganar da muka ta6a yi da kai na zamu rayu tare gaskiya ne banyi zaton zakai aure ka tafi ba kwata kwata shiyasa banjin dad’i” zuba mata ido yay yana kallon yadda take Maganar fuskarshi a sake, nisawa yay cikin cool voice d’inshi yace “am so sorry Zaraah i caused u worries, amman don nayi aure ai ba yana nufin zamu rabu ba, mun zama family now ko bananan zamu kasance a tare hakan is so simple ko kin manta miye aikin Yayanki ne?” shiru tayi tana bin shi da ido hakanan sai taji ta samu wata irin Natsuwa,

“We’re leaving On Friday so ki shirya zamu tafi tare” taji ya fad’a, d’an far far tayi da idanu yanayin fuskarta ya canja ita dae bata son zuwa bikin hakan yasa ta fara tunanin mafita ganin haka yasa yace mata taji abunda yace ta bud’e baki cikin disasshiyar Murya tace “ai bazan samu zuwa bikin ba” wani iri yaji Maganar har saida ya taso ya zauna daidai ya tambayeta dalili, tace “Saboda Next week zamu fara papers d’in Practical kuma ran Friday d’in da ake Auren ranar zamu fara jarabawar gaba d’aya” da k’yar ta samu ta gama Maganar saboda faduwar da k’irjinta yake don tasan k’arya ce take shirga mashi sai Upper Week zasu fara jarabawar ma,shiru yay fuskarshi da experassion dake nuna baiji dad’in Maganar tata ba don ya yarda da duk abunda ta fad’a nan take ya k’ara yin tunanin harda hakan yasa ta damu sosae, cikin muryar lallashi yace “Ok, but banji dad’in hakan ba best friend d’in Groom bazatay attending ba” d’an tura baki tay jin ya kirata da best friend hakan yasa ya d’anyi Murmushi kafin yace “u shouldn’t worry about dat ki maida hankali kan karatu sosae don ki passing exams and Maganar biki da komae in kinaso zaki ga komae live koda baki je ba i can arrange dat for u” d’an bud’a ido tay alamar mamaki da d’an Murmushi yace “ko baki so?” a sanyaye tace “amman ai hakan sai an kashe kud’i ko, ace komae na bikin zan rink’a gani” yar dariya yay ya koma ya jingina yace “to dama ba don a kashe su ake nema ba?”,

tace “to ai kaida kake da hidima”

 

“Wannan ai angama komae kinga sauran kud’in sai akashe kawae” d’an yamutsa fuska tay tace “to amman ai ba iya hidiman bikinne ba kawae in aka yi Amarya ma kud’i ake kashewa sosae in kuma suka k’are ya zaka yi” sosae yake jin dad’in yadda take mashi Magana, d’an bud’a ido yay yace “still bayan uban kud’in dana kashe kuma in akayi auren ma sai na kashe wasu to mi kuma za’ai dasu kenan?” tura mashi baki tay tace “Kayan dad’i ake siya su kaza…..” cak ta dakata don ita kanta sai taji she sounds foolish, ganin kallon da yake mata yasa ta yamutsa fuska kaman zata sa kuka kawae sai taga yasa dariya har fararen hakoransa sun bayyana da sauri tasa bayan hannunta ta rufe fuskarta tana yamutsa baki alamar zatayi kuka, a cikin ranshi ya ayyana wannan itace zaraah da ya sani a fili kuma sai cewa yay “Zaraah ko kina son cin kaza ne?” da sauri ta bud’e fuskar kaman zata yi kuka tace “nifa bason ci nike ba, ai haka ake yi ko in akayi aure aita cin kayan dad’i” dariyar ya k’ara yi ya d’age kanshi yana kallon sama da alama dai ba k’aramin dadin firar yake ji ba ita kuma sai kallon fuskarshi take abubuwa na mata kai kawo a cikin zuciya, juyowa yay suka had’a ido da Murmushi yace “kar ki damu da wannan ai itama Amaryar tana da kud’i sai ta d’auki nauyin wannan ni kuma zanyi ma beloved sis d’ina what would make her happy da nawa” d’an Murmushi tayi tace ba sai yayi hakan ba in su gwaggo suka dawo ta ga komae a wayan a Kawu Amadu dan ta6e baki yay yace “Ok in hakan yayi maki, but kema yakamata by now kina da Waya”, tace “ai gwaggo bata son in ruke wayan tace sai zan cigaba da karatu sannan” shiru ya d’anyi sai kuma yace mata to taya zasu rink’a communicating in ya tafi tace ko ta kawu Amadu ko ta gwaggo,

 

“No, suma suna da uzurinsu bai kamata a takura su ba, ba kaman Uncle d’inki shima yanzu yana karatu dole yana using phone d’in sosae so i will talk to her ta bari ki rike” jinjina mashi kai tay don tana son dama itama ta fara ruk’e wayar, can kuma sai tace “Nagode Allah ya saka da Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuria nagari” d’an bud’a ido yay da Murmushi ya amsa da Ameen idonshi akanta yace “kinma tuna man kince inna yi aure matana ta haihu zaki rinka goya baby d’in ki mashi wasa right??” hannu tasa ta rufe baki tunawa da lokacin da tayi Maganar sai kuma ta cire ta yarfa hannuwa tace “to ai ba anan zaku zauna ba dana yi hakan?”

 

“To ko in tafi dake??” waro ido tay baki bud’e tace “kasar wajen?” lumshe ido yay ya jinjina mata kai yace “sai kiyi karatun likitan acan” da sauri ta girgiza mashi kai tace “a’a so kake Aunty Fanan tace na lik’e ma mijinta ta koro ni a wurgo ni Nigeria gwara in zauna nan in yi karatuna kuma ma ni banson in rabu dasu gwaggo” sigh yay still da Murmushi kan fuskar tashi yace mata Fanan bazatayi mata hakan ba ta d’an ta6e baki tace “uhmm ya haisam baka san kishin mata bane idon mutum rufewa yake kuma ita nasan zata yi kishinka sosae” ita kanta bata san ya akai ma tayi Maganar ba ganin ya zuba mata ido yasa ta sha jinin jikinta kamar daga sama taji yace ya akai tasan zata yi kishi sosae a dabarbarce tace “kawae naga tana sonka ne sosae” tana kai Maganar ta sunnar da kai, jin bai k’ara cewa komae ba yasa ta saci kallonshi kawae sai taga ita yake ta kallo hakan yasa itama ta taci gaba da kallon nashi sun d’an d’auki lokaci haka kafin ya janye idonshi ya kai hannu ya shafi forehead d’inshi Calmly yace “last Sunday i need help to park my stuff nace da Zaraah bata gujeni ba nasan zata man wannan” taji fada a tausashe d’an murmushi tay tana tura baki tace “ni fa ba gudun ka nai ba” ya d’an ta6e baki taci gaba da cewa “to in kana so sai in tattara maka ko gobe ko kuma yanzu inje in fad’i ma gwaggo sai in dawo in had’a maka” shiru yay yana kallon yadda take Maganar har saida tace mashi “kaji” sannan yace “TK have done dat” gyad’a kai tay still da d’an Murmushi akan fuskarta yace “sarkin kuka kawae” dariya tayi wannan karon ta kai gefen jikinta itama jikin kujerar kaman yadda yayi,

 

“Pls Zaraah bana son irin damuwar nan, when u have problem just feel free to tell me” yay Maganar yana tabbatar mata da abunda yace da kanshi ta d’aga mashi kai alamar to, kawae sai taga ya mik’o mata dogon yatsanshi manuni bin shi tay da kallo tun kafin tace wani abu yace “Promise zamu k’ulla bazaki k’ara shiga damuwa haka ba” nan take ta gane dalilin da yasa yayi hakan wato abunda ta ta6a yi mashi a Mota akan rashin cin abinci data ce su kulla Alkawari in yaje wurin aiki zai ci tunawa da hakan yasa tasa dariya sosae har gyalenta ya idasa zamewa shima dariyar yake yak’i janye hannun alamar sai sun k’ulla cikin dariyar tace mashi ba sai sunyi hakan ba wato amsar daya bata a lokacin itama ta bashi, sosae yaji dad’in ganin ta warware dama da biyu yayi hakan, wayarshi ya d’auka ya duba time lokaci guda ya mik’e yace mata yana zuwa ta d’aga mashi kai ya nufi hanyar beedroom ta bishi da kallo, yana shiga Corridor ya d’ago mata hannu ba tare daya juyo ba alamar yasan kallonshi take Murmushi kawae tay ta maida kanta ta kwantar jikin kujerar cikin ranta take ayyana shikenan ta dae rasa Ya Handsome saidae kuma ta wani bangaren taji dad’i sosae yadda ya damu da ita,bata yi tunanin yana ganiyar angwancewa ba zai wani damu da damuwarta haka dan Murmushi tayi kawae, bada jimawa ba ya fito hannuwanshi duka biyun ruk’e da manyan Akwatuna Maroon color da ratsin baki sun matuk’ar yin kyau da gani kuma ba sai an fad’a ba masu kudi ne sosae ya nufo cikin parlon ya aje a gabanta kafin ya sake komawa ya d’aukko wani madaidaici kaman trolley mahad’insu yana zuwa yace tayi amfani dasu tana kallonshi tayi mashi godiya yace mata ta tashi suje ya rakata ta mik’e, manyan da ya fara kawowa ya d’auka yace ta d’aukko k’aramin tace shi ya d’auka ya bata babba d’aya ganin abun zai zamar masu gardama yasa ya bata na biyun ya d’auki k’aramin suka tafi.

 

Lokacin da suka je gidan atare suka shiga tana gaba yana biye da ita da sallama ya shiga saidae ba’a amsa ba Fatuu tace ya shigo suka shiga Falo kowa ya aje akwatin hannunshi kafin suka zauna sai kuma ta mik’e tace bari tayi ma gwaggon Magana ya d’aga mata kai,a daki ta isketa ta bud’e wardrobe tana shirya kaya tace mata ga Ya Haisam yazo tace to ta dakata da abunda take tabi bayanta suka nufi falon, da fara’a ta shiga ta zauna kan kujera ya gaishe da ita ta amsa tace mashi ya shirye shirye shima ya amsa mata da Alhamdulillah, bayan sun gama gaisawan Fatuu ta nuna mata akwatinan dake aje gefe tace gashi nan ya bata, hannu gwaggo tasa ganin dandatsa dandatsan akwatinan kafin ta kalleshi tace “d’ana Haisam baka gajiya ne, haka aka cika Amadu da kaya ran lahadi Tukur ya kawo mashi” da d’an Murmushi yace mata “ba wani abu” Addu’oi ta shiga yi mashi yana amsawa a hankali can ta mik’e tace bari ta zubo mashi Abinci ba tare data jira cewarshi ba ta fice, bada jimawa ba ta shigo ruk’e da babban tray ta d’auro plate d’in abincin rufe da wani ta aje Fatuu ta mik’e ta nufi Fridge ta d’aukko mashi ruwa da lemu ta aje mashi a gefe ta koma ta zauna, ganin yak’i saukkowa yasa tayi mashi Magana ya kalleta kafin ya saukko k’asa kan Carpet ya mik’ar da k’afafunshi ta yadda tray d’in ke gefenshi, hannu Fatuu ta kai ta bud’e mashi Abincin wanda farar taliya da macaroni ne sai miyan alaiyahu abincin gwanin kyau a ido sai kamshi ke tashi, hannu ya kai ya d’auki fork d’in ciki a nutse ya fara ci ita kuma tana zaune gefenshi ganin ya fara ci yasa ta maida idonta kan Tv can ta juyo suka had’a ido tayi mashi Murmushi hakan yasa ya dakata yace mata ita taci Abincinne tace ta fara ci ya aiko kiranta shine ta aje yace taje ta d’aukko ba musu ta mik’e ta fita,hannunta ruk’e da plate d’in Abincin nata ta dawo ta koma inda ta tashi ta zauna kawae sai gani tai ya mik’a hannu ya d’auki abincin nata ya k’ara mata cikin nashi ya maida mata tana dae ta kallonshi bayan ya aje ya kalleta yace yar rigen cinyewa zasuyi tana jin haka ta waro ido alamar mamaki tana guntse Murmushi wato abunda ta ta6a yi da Hajiya a gabanshi shine yace suyi da alama dae duk rayuwarsu da ita bai manta ba, alama yay mata na su fara ta kai hannu ta d’auki Fork d’in ta fara ci, tun tana ci a hankali har ta fara sauri sai gashi ta wuce shi ganin hakan yasa ya fara d’iba da yawa saidae rashin sabo da yin lomar yasa da ya kai Abincin wurin bakinshi duk sai ya zubo Allah ma yasa riga mai duhu ce a jikinshi daba k’aramin 6aci kayanshi zasu yi ba, Fatuu ko mi zatayi in ba Dariya ba sosae take kyalkyata mashi dariya ba 6ata lokaci sai gashi ta cinye nata lokacin nashi da saura da d’an yawa, aje fork d’in yay yana kallonta sai faman Dariya take mashi harda d’an kwantawa bata ta6a tunanin zaice suyi hakan ba, baisan ko shi kadae ke ganin hakan ba amman ba k’aramin kyau dariya ke mata ba hakan yasa sai yay ta kallonta wani lokacin in tana yi,hannu ya kai kan kujera ya d’aukko wayarsa yana dubawa can ya d’ago yay mata alamar ta matso da hannu ta d’an matsa kusa dashi kawae sai gani tay ya d’aga wayar ashe Camera ya shiga da d’an mamaki ta juya ta kalleshi don tasan ba ma’abocin son yan d’auke d’auken hotuna bane, alamar ta kalli Camera d’in yay mata da ido ta juya har zai d’auka kawae tasa dariya ganin taliya a gaban rigarshi a haka ya d’auki hoton kuma yay kyau sosae bayan ya aje wayan yace ko zata idasa sauran Abincin nashi tay mashi wani kallo tace Allah bata yarda ba bashi yace ai yar rigen ba dole shima ya cinye ya jinjina mata kai yaci gaba da ci har ya cinye, bayan ya sha tace lemun fa yace ya bar mata daga haka ya mik’e alamar zai tafi itama ta mik’e suka fito daga falon tare saida taje ta sanar ma gwaggo ta fito sukae sallama sannan suka fita tare, A daidai shagon Amadu ya tsaya yace mata ta koma dare yayi tace to ya juya ya tafi tay tsaye tana kallonshi yayin da sautin busar sarewa na wak’ar india ke tashi bada k’ara ba sosae daga cikin shagon Amadu lokaci guda idanunta suka d’an ciko da kwalla da sauri ta maidasu ta juya ta shige gida. Yana isa part d’inshi wayarshi tay k’ara ya duba mai kiran yaga Hajiya ce bayan yay picking take tambayarshi k’ara fita yay bai shigo yaci Abinci ba yace mata yaje gidansu Zarah ne kuma yaci Abinci acan daga haka sukae ma juna saida safe ya wuce Bedroom bayan ya rage hasken parlon, yana shiga ya aje wayar kan side drawer ya wuce cikin laundry duk da bai jima da yayi wanka ba bayan ya dawo gym saida ya k’ara yin wani saboda Abincin daya zubar mashi a jiki, sanye da bathrobe ya fito yana tsane gashinshi da wani farin short towel ya nufi cikin Bedroom din, shiryawa yay cikin Sleeping dress yasa turare ba mai k’arfi ba don su kansu kayan da ya sa sakin k’amshi suke ya goga roll-on kafin ya nufi wurin switch ya kashe hasken d’akin ya kunna bedside lamp guda daya ya haye gadon yana kallon ceiling lokaci guda zuciyarshi ta fara tariyo mashi abunda ya faru tsakanin shi da Fatuu, Murmushi kawae yake saki yana jin zuciyarshi Fresh can ya kai hannu ya d’aukko wayarshi,hoton da suka yi da ita ya bud’o ya k’ura mata ido yana kallon yadda ta washe baki tayi Dariya dimples d’inta sun lotsa sosae, murmushi kawae yake saki kafin ya maida wayan ya aje ya lumshe ido…………………

 

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button