Health

Yadda za a magance tabo da kurajen fuska insha Allahu

Assalamu alaikum jama’a barkanku da wannan lokaci ayau insha Allahu zan sanar da ku hanyoyin da za a magance tabo da kuma kurajen fuska.

Mafiya yawan wadanda wannan matsalar ta fi shafa su ne matasa, maza da mata.

Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska amman sai tabo ya ƙi ɓacewa.

Hakika rashin ɓacewar tabo na ɓata kwalliya. Sau da yawa ‘yan mata basa son shiga cikin taron mutane saboda taɓon da ke fuskarsu.

 

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

Masu wannan matsalar kan gwada mayukan kanti, domin dai rabuwa da wannan matsala ta tabon fuska, wasu kan samu nasara ya ɓace amman wasu kuwa baya ɓacewa.

Ayau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a sani cewa ɗaya za a zaɓa daga cikin hanyoyin da za mu yi bayani, kada a kuskura a haɗa su. Domin yin hakan zai ƙara lahanta fuska ne.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

Hanya ta farko a samu gayen dogonyaro, sai a haɗa shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan ɗumi.

Hanya ta Biyu za a iya shafa markaɗaɗɗen dankalin turawa akan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa gabaɗaya.

Hanya ta Uku ita ce, a daka tafarnuwa sai a shafa akan tabo. Duk da tana da wari, amman tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

Allah Ya sa a dace.

 

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

Ina matan dake fama da matsalar fesowar kuraje musamman a fuska, ga tsaraba na kawo muku yadda ake magance kurajen fuska.

Yawancin yan mata ne ake samu da fitowar kuraje a fuska galibi farkon balaga. Don yawanci an fi samun mata daga shekara 14 zuwa 20 da kuraje ke fito musu a fuska.

Don kawar da kuraje, ku samu wadannan abubuwa kamar haka;

 

  • Man Habbatussauda cokali 1
  • Man tea tree
  • Garin Masara cokali 1

 

Yadda Ake Hadawa 

A samu man habbatus sauda mai laushi cokali ɗaya a gaurayi shi a cikin man tea tree, tare da garin masara cokali ɗaya kullum, sai a shafe shi gabaɗaya a fuska ta hanyar lullube fuskar baki daya na tsawon awa ɗaya sannan a wanke da ruwan dumi da sabulu, sannan kuma a maimaita haka har tsawon sati daya.

Yana da  kyau idan kika kara da shan man habbatus sauda a cikin ruwan dumi.

Allah ya baiwa duk wasu marasa lafiya, Lafiya

Back to top button