Ajiya A Duhu Book 1 Page 16 Complete Novel
🅿️➖1️⃣6️⃣……….“Haka muke tunani Yaya. Tunda bamu taɓa ganin Mamma ta haɗa kaya tabar gidan nan ba dan sun samu matsala da Daddy.” Basira ta bashi amsa cikin kuka. A take zufa ta gama wanke masa jiki, harma ya gagara cewa komai. Badiyya ce ta sake katse masa tunani da faɗin, “Yaya kuma wlhy koma minene ya faru da sanya hannun waccan munafukar matar a ciki. Dan tana a sashen Daddyn komai ya faru, ko sanda Mamma zata tafi da muka je kiran sa itace ta hanashi”. Cikin mamaki ya ce, “Ita wa?”. Kai tsaye ta bashi amsa da, “Amaryarsa mana”.Hararar daya zuba mata ya sata kame bakinta tana turashi gaba. Dama sun san ai bazai yarda ba tunda agolan ƴarta ce budurwarsa. Bai sake cewa komai ba ya miƙe, sai da ya kusa kaiwa ƙofa ya juyo yana kallonsu. “Kutashi kuje ku kwanta zuwa da safe koma miza’ai sai ayi. Ku kulle nan ɗin”. Wasu sun amsa masa da to, wasu ko da hararar ƙasan idanu suka rakashi dan sun san babu damar yi a zahiri mutum yaci dukan banza a daren nan balle ma babu Mamma….. ★★★ Washe gari koda Yazeed yazo ganawa da Daddy sai ya samu har ya fita. Sashen Ammie ya nufa, inda ya taddata zaune jihum alamar tana tare da damuwa harma da ɓacin rai. Gaisheta yay da girmamawa kamar yanda ya saba. Itama ta amsa masa cikin kulawa tana danne damuwarta. “Yanzu ka iso ne?”. “A’a tun da daddare. Around eleven na samu kunyi barci shiyyasa na haƙura har sai da safe. Yanzu kuma naje sashen nashi naga alamar a rufe yake”. “Nima nazo na haɗa masa breakfast na koma naga yabar gidan. Ka ganni tun ɗazun nake kiransa yana rejecting daga ƙarshe ma ya kashe wayarsa gaba ɗaya.” “Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un”. Yazeed ya shiga ambata yana mai dafe kansa da dukka hannayensa biyu. “Yazeed nikam da zakaji daka haƙura da batun auren nan na Maanal. Dan idan zamu duba gaskiya duk batunsane tushen wannan matsalar. Kayima Hajiya biyayya ALLAH sai ya baka wadda tafi Maanal”. “Amma Ammie ina sonta, wlhy matuƙar so nakema Maanal dan ALLAH kar kice haka, ke da Daddy ne ƙwarin gwiwata. Sannan shima Daddy ai yanada hakki a kaina kuma yana son auren. Miyasa Mamma bazata fahimta ba. Miyyasa bazata fahimci Aunty Sabuwa tana zugatane kawai saboda ta samu biyan tata buƙatar na auri tata ƴar bane?”. “Amma Yazeed ƴar uwartace fa, uwa ɗaya uba ɗaya. Taya bazata tayata son abinda take so ba.” “Amma wlhy Ammie akwai manufa a zuciyar Aunty Sabuwa. Mamma ɗin ce kawai ta kasa fahimta”. Rasa abincewa Ammie tayi, dan itakam wannan cakwakiya ta ma fara gundurarta wlhy. Tabbas tana matuƙar son Maanal ta auri Yazeed kodan ƙyawawan halayyar yaron. Sai dai tana tsoron halin Hajiya Yaya gaskiya. Sannan tana tausayi da fargabar jefa rayuwar yarinyarta mai raunin ciwo a cikin wani hali. Yazeed shi kaɗai ke son auren nan sai mahaifinsa. Amma ƴan uwansa da mahaifiyarsa da mafi yawan danginta basa so sam….. ________________★ “ALLAH nazata wasa kikeyi da kikace min gaki nan tahowa Zaria fa.” “hhhh aina fahimci hakan a muryarki. Bazaki ganeba fitowar ta dole ce. Gidanmu ne keci da wuta na gasken gaske kwana biyun nan”. “Tofa wuta kuma Aminiya tami?”. “Uhhm ke dai bari, tushen matsalar daga auren agolar gidanmu ne da maigidan yace zai ƙulla kusan shekara uku kenan…..” “Kar kice na katseki wai ƴar amaryar ku? To da wa?”. “Ita fa, dawa kike tunani idan ba ɗan sonsa Yazeed ba. Tunda fa akai maganar dama uwar tasa tace bata yarda ba. Shi kuma Daddyn Huznah bai maida kai ba yarinyar dai tana cigaba da karatu, shi kuma Yazeed yana manne da yarinya. Bayan ta kammala karatun akaso tada zancen bansan miya faru ba dai kuma aka dakata ta wuce service. Indai taƙaice miki batu ta gama service ɗin ne yanzu zancen ya sake tasowa shine aketa dam-barwa. Ita uwar ɗan tace bafa za’ai ba, kwana takwas da suka shige sukazo itada ƴar barikin ƙanwar nan tata sabuwa suka cima uwar ƴar mutunci randa muka bar nan kenan shine itakuma yarinyar ta yanke jiki ta faɗi ta kama aman jini”. “Aman jini kuma?”. “Uhm kin san sunce wai ai tana da ciwon zuciya”. “Tirƙashi, eh lallai dole kice gidanku naci da wuta. Ke nan yanzu yaya ake ciki kuma?”. “Yarinyar na asibiti a Abuja yanzu haka. Ba shine nake faɗa miki nakoma Abuja ba nima harma naga ƙanin Majdiya”. “Oh ƙwarai anyi haka. Ko shiyyasa itama taje Abujan ita da yara duka dan gulma shine suka wuce gidan Yaseerah wai ganin ɗaki. Aiko sai da na mata tujara daga ita har mijin nata data dawo”. Dariya sosai suka kwashe da ita suna tafawa. Hajiya Basariyya ta ce, “Ai kinmin dai-dai wlhy. Kinga gobe ai ta kiyaye”. “Karma ta kiyaye na koya mata hankali. Mu munafuncin kishiya wanne bamu sani ba kuma”. “Wlhy kuwa. Sai dai wanda kuma aka ɓoye a zuciya. Yanzu kin san miya sani zuwa Zaria ɗin?”. “A’a sai kin faɗa”. “Jiya uwar gadaran gidan namu ce ta wuce gida harda kaya cike da akwatina. Dan ya hanata girki a gidan sai mu biyu mukeyi, shine jiya girkin ita shegiyar ne ita kuma taje ta samesu tai musu ɗibar karan mahaukaciya. To ban sani ba ko sakinta yayi shine ta kwashi kaya ta tafi, dan naga ɗan ma ya dawo jiya da dare su kuma matan sunata kuka. Yau kuma tunda safe mai gidan ya fice rai a ɓace matar son nasa itama dai duk ta koma sukuku. Dan haka malam nakeso ki kira mana nan ina son a ƙarama wutar fetur ne ya sake birkice musu. Sai kuma batun Huznah da yaron nan da suka haɗu a Abuja. Na fahimci kamar itace ta damu da shi, dan sai ta yini kiransa a waya bai ma amsa mata ba sai ya gadama. Ina son a riƙe masa wuta gaskiya san bana son nima ta rasashi. Nayi binciken yaron shi kansa bama ubansa ba wani shege ne. Dan Companys ne da shi na abubuwa. Ga shima uban nasa sune ƙasar. Hakama ƴan uwansa biyu kowa ƙwaron kansa ne duk da dai shi ƙanin ya fisu komai.” “Humm wato ƙawata kina matuƙar birgeni, sam ke baki da wasa akan abu. Sha yanzu magani yanzu kikema komai shiyyasa da wahala asha gabanki”. “Yo ai babu zama ƙawata. Lamarin rayuwar nan kana sakaci sai a tafi a barka a ƙarshe bare mu dake zagaye da shegun kishiyoyi, tako ina da hari ake kawo mana mune na tsaka. Kinga ko dole mutum ya nemo garkuwa da takobin kai nasa harin ai.” “Wannan gaskiya ne. Yanzu dai bara nasa Zaituna ta kira mana shi ta falon baya. Kin san gidan namu dai cike yake da ƴan sa ido. Damma maigidan baya gari ne jiya da yamma yay tafiya.” “Ato ai ansha hidima dole a koma nema kuma. ALLAH ya taimaki ƴan baya suma haka dai dan wlhy rashin auren yaran nan ya fara tada min hankalina. Rigi-rigi sai samari sunzo kamar za’ayi sai ki nemesu ki rasa”. “To ke kuwa maƙiya cike da gida za’a barsu haka ne. Ke dai kin san yaƙi da gwagwarmayar da nasha Kafin auren nan na Yaseerah ya yiwu. Yanzu saura Zaituna itama dai wani ya biyota a ƴan bikin so nake na huta gajiyar nan na fara aiki a kansa. Dan babu wasa”. Dariya suka kwashe da ita su duka suna mai taɓawa. Hajiya Basariyya ta ce, “Haka nake fata a nawa gidan. Dan sai yaran nan sun gama aure kaf kafin yaran ɗakin gadararriyar can suyi sa. Na riga na shirya yaƙarta ta wannan fanin”. “Wlhy ina bayanki. Shegu ai idan sunce su mugunta suka iya gidan suka taras….” _________★ Kwanakin Maanal goma sha shida a asibiti sannan aka bata sallama. Dai-dai da cikar Hajiya Yaya kwana tara a gidansu. Daddy dai tun wannan fitar da yay daga gida a washe garin zuwan Yazeed bai koma ba. Sai daga baya suka fahimci yama bar ƙasar ne sabgar gabansa. Dan kwanansa biyu da tafiya yasa Hajiya Basariyya tabisa can. Komai Ammie batace ba akan hakan, damuwarta fushin da yake da ita da batasan laifinta ba. Gefe kuma ga yaran Hajiya Yaya sun tasota da rashin kunya da rashin mutucin a gidan. Sai idan Yazeed na gidan ne take samun sauƙin su. Dai-dai da su Hameed sun takurawa da zagi da duka. Wannan dalilin ya saka yau koda su Shahidah suka kirata akan sallamar Maanal tace Maanal ɗin ta zauna anan gidan Shahidah kawai. Nene sai ta biyo su Amaal ta dawo. Hakan yayma Maanal daɗi dan dama bata son komawa Kadunan. Sai dai ita Nene ta fahimci akwai matsalane amma batace komai ba ta shanye a ranta har sai ta koma. Dama tanata mamakin abinda ya hana Ammie sake dawowa Abujan. Kullum sai dai suyi video call safe da yamma. Takance suyi haƙuri da rashin daowarta akwai abinda take yi ne. Badan Maanal tasoba ta yarda RK yay musu rakkiya har gidan Shahidah. Cikin farin ciki su Munaya sukazo suka rungumeta. Itama haɗasu tai ta rungume tana mai jin kewarsu dan sau ɗaya sukaje dubata asibiti aka hana zuwa dasu saboda bata son hayaniya a lokacin. Har cikin falo suna manne da ita. Kafin su fara rige-rigen zuwa ɗakko mata gift da kowa ya tanada mata. “I love you yarana”. Ta faɗa a hankali tana rungumesu….“Kina da son yara kamar haka, amma kiketa ɓata mana lokaci”. RK dake gefen kujerar da take ya faɗa a hankali ta yanda itace kawai taji. Ɗago yaran kawai tai daga jikinta batare da ta kallesa ba. Shima sai ya basar saboda isowar Amal ɗauke da ƙaramin tire ta haɗo masa abin sha. Godiya yay mata hankalinsa kwance ya ɓalle ruwa ya tsiyaya a kofi ya hau sha. Ita Maanal ma sai ƙarfin halin nasa ya ɗaure mata kai. Kasa jurewa tai sai da ta ɗan zuba masa ido. Yanda take kallon nasa ne ya sashi sauke kofin daga bakinsa shima yana kallonta. Sai kuma ya wani ɗan ƙyaƙyƙyafta idanunsa. Nata idanun ta ɗauke tana ɗan yamutse fuska da faɗin, “Kai ko kunya baka ji?”.. “Ikon ALLAH kunyar mi zanji?. Gidan yayata nake fa. Idan kuma so kike na fara jin kunyar ki bani damar sakaki a gidana na miki alƙawarin ko’ina naje aka bani ko miye bazanci ba sai naki”. Kallo ta jefa masa mai kama da harara sai kuma ta girgiza kai kawai ta miƙe. Harta gama hayewa upstairs idonsa a kanta, sai da takai step ɗin ƙarshe itama ta ɗan juyo dan tana jin kaifafan idanunsa na yawo a kanta. Da sauri ya ɗauke kansa ya basar. Ita kuma taja ƙaramin tsaki ta ida hayewa. Daga haka bata sake sanin sanda yabar gidan ba. Dan wanka ta samu tayi a ɗakin Shahidah tai kwanciyarta sai barci. Dama sunce zata dinga samun isashen barci yanzu hakan ne zai dawo da kuzarinta data rasa… Bayan sallar la’asar Nene dasu Amaal suka wuce. Sai suka koma daga ita sai Shahidah da mijinta da yaranta biyu a gidan kawai. Sai kuma masu aikinta guda biyu. Jitai kuma duk babu daɗi, dan tana matuƙar son ta gansu su duka a waje ɗaya hakan na sakata a farin ciki. Sai dai yaya ta iya aure ya rarrabasu. Hira suke da Shahidah, koma ace Shahidah ke hiran dan Maanal dai daga guntun murmushi sai eh ko a’a ne nata. Muneff ne ya shigo da ɗan gudunsa, autan Shahidah, dan daga shi dai har yanzu bata sake ba ko tana hutawane ko ta tsaya oho mata. “Muneff ban hanaka wannan guje-gujen ba wai nikam?”. Shahidah ta faɗa cikin taka masa birki. Yaron bai damu ba ya ce, “Mamy Uncle Yazeed ne yazo”. “Uncle Yazeed na kd?”. “Eh Mamy. Yana waje ma”. Kallon Maanal Shahidah tayi. Itama Maanal ɗin ita take kallo. “Kije ki shigo da shi”. “Ni Didi ƙafata ke ciwo”. Kai kawai Shahidah ta girgiza tana miƙewa. Hijjab ɗinta da takan ajiye a falo saboda baƙi irin haka ta ɗauka ta saka sannan ta fita. Babu wani jimawa sai gata ta dawo Yazeed biye da ita. Yana shigowa idonsa akan Maanal ya fara sauka. Itako ta ƙurama television ido kamar bata san da shigowar tasa ba………✍️
