Mejo Najeeb Page 43 By Autar Alheri
“Akan gadon tahango isseta kwance tana rawar ɗari cikin sauri ta ƙarasa gareta tareda yaye blanket ɗin… subhanallah shine abinda ya fito daga bakin Hajiya mama ganin yadda isseta ke karkarwa jikinta na fitarda wani irin hucin zafi kamar wuta. Ahankali ta ɗagota domin ta tadata zaune, wani irin ihu tasaki tana ƙanƙame hannun Hajiya mama domin ta ɗauka mejo ne cikin Muryar shagwaɓa da kuka tace ‘”nashiga ukku wayyoo Allah yah najeeb please kabarni wlh bazan iya tashi ba nagayama, taƙasara zancen tare da komawa takwata tana karkarwa. Atake Hajiya mama tafahimci inda abun yadosa cikin ranta tace “ikon Allah wato najeeb muyarenawa hankali betaɓa kusantar yayinyar nan ba seyanzu amma yace yayi, Humm ai shikenan tunda ita kazaɓa nikaina nafi son yazauna da wannan ɗin domin hankalina yafi kwanciya da ita, da wannan tunanin hartazo general perlor ɗin, suna nan zaune inda ta barsu anty hawwa ce kawai batanan. Wayarta ta ɗauka tashiga kiranshi bugu ɗaya ya daga, batajira mizeceba tace “kana ina najeeb? Banji miyace mataba tace okay kazo yanzu, daga hakan tayanke wayar tare da komawa pert ɗin nashi….koda yashigo a perlor yasameta zaune cikin haɗe huska tace “seka ɗauketa kakaimin ita bathroom domin bazan iya daukar taba…bece komaiba yawuce tare da ɗaukar ta yakaita bathroom ɗin yadawo bedroom yazauna…itako Hajiya mama kayan gyaran data ɗauko ɗakinta tasaka a bath ɗin bayan ta tara ruwa masu ɗimi aciki kana tazuba kayan maganin tatemakawa isseta tashiga, sosai Hajiya mama tagasa isseta tare da temakon waƴannan magun gunnan…hakan yasa dasuka gama tafito da ƙafarta dudda cewar bata takawa dede amma taji daɗin jikinta sosai…da kallo yabisu seda Hajiya mama ta watsamai harara kana yamiƙe yana murmushi yafice daga bedroom ɗin….dakanta ta temaka mata tashirya kana tariƙo hannunta suka fito domin suje hospital sedai fa dasukazo matattakalar dazata sadasu da general perlor takasa takawa, seda Hajiya mama tace yazo yaɗauketa yasakata a mota tunda shine sanadin komaiCakin sauri yazo ya ɗauketa kamar baby yanufi waje da ita. Abba yace “subhanallah abin haryakai hakan? To Allah yabata lpy konazo mutafi?? “Ah’ah base kazoba Alhaji aima yanzu zamu dawo in sha Allah…to shikenan Allah yabata lpy yawwa munir kuje kakaisu hospital matar najeeb ce balafiya, yafaɗa yana kallon munir ɗin da shigowarshi kenan..to Abba cewar Munir yanabin bayan su.Hajiya umma kuwa cikin mugun tashin hankali da firgici wanda makircinta yakasa ɓoyeshi tamiƙe tanufi bedroom ɗinta kamar zata tashi sama aranta kuwa se fatar takeyi Allah yasa ba kusantar isseta najeeb yayiba yau dakuwa ƙaryarta taƙare inkuwa hakane to setayi ajalinsu sedai dukkansu surasa, ahakan tafaɗa ɗakinta na sirri ido rufe sedai kiran duniya tayiwa tsijuju amma yaƙi zuwa hakan yasa doli ta haƙura har zuwa anjima ta ƙara kiranshi.Suna zuwa asibitin aka karɓeta amma juyin duniya mejo yaƙi bari namiji yadubata kala Hajiya mama na faɗa harta dawo lallaɓashi amma firr yaƙi yadda ahaka doctor Ziyad yazo wurinshi amma yahaɗe fuska damma karyaga damarshi…murmushi doctor Ziyad yayi afili yace “saranka inuwa ƴallaɓai mejo nibazance namiji yaduba maka mataba wata doctor ce nakira dudda bata hospital ɗin amma tana zuwa yanzu, yaƙarasa zancen yana murmushi. Se alokacin yaɗan saki ranshi Munir kuwa se dariya yake musu aɓoye….lokacin da doctor deejah tazo tayi mugun mamakin ganin raunin dake jikin isseta cikin tashin hankali tace “innalillahi wa’innailaihi raji’un har mutun nawa sukayi Mata fyaɗe hakan Hajiya? Tatambayi Hajiya mama bayan ta fito…cikinjin kunya Hajiya mama tace “wlh ba fyaɗe aka mataba mijintane yayi mata hakan..ido doctor deejah tawaro tace “miji dai?? “Wlh kuwa kinsan halin yaran yanzu abunka kuma ga soja sedai Allah ya kyauta ina fatar dai be illatataba? “Humm lallai ma dan yana soja se’akace Mishi fagen yaƙi ne? Ina yake mijin nata? “Yana waje cewar Hajiya mama cikin rauni… tashi doctor deejah tayi tafito wajen tasamu Munir zaune yana danna wayarshi shiko gogan yana ɗan nesa dasu kaɗan shida doctor Ziyad. “Haba ɗana wannan wacce irin aika aika ce hakan? Kasamu ƴar mutane sekaje afagen yaƙi kake? Waya gayama anayiwa mace hakan? Abu kamar namuji goma sukayi anfani da ita wlh baka kyauta ba kuma kasani kaida ita sebayan wata biyu yanzu ma ɗinki zamu mata maza karɓi kakawo mana wannan kayan domin wlh se an mata dinki har huɗu wannan wanne irin rashin imanine da tausayi. “Sororo Munir yayi yama kasa karɓar takardar yana sauraren yadda doctor deejah ke surhuta Mishi masifa kamar shine mijin nata…sukuwa dagacan da suke tsaye doctor Ziyad yahangi doctor deejah kamar ranta a ɓace yake hakan yasa sukazo wurin..suna ƙarasowa Munir nakarɓar ta kaddar zebar wurin. “Miyafaru ne doctor? Cewar doctor Ziyad.. “aikomima yafaru Ziyad wannan marar imaninne nakeyiwa faɗa mana yasamu yarinya ƙarama sekace wanda akace filin yaƙine aka bashi inda ta nakasa aikanka kayiwa..tunkamin takai ƙarshe yadokawa Munir wata muguwar harara hakan yasa yabi bayansu yawuce yana dariya, faɗar yakeyi toni miye nawa aciki big bro kaine kayi ɓarna kasha daɗinka kuma anzo ana tuhumata kaikuwa kanamin wannan harar taka me tada hankali.Anan kuwa murmushi doctor Ziyad yayi kana yace “wanda kikeyiwa faɗa bafa shine mijintaba doctor Kinga mugun nan yafaɗa yana nuna mejo dayawani haɗe rai kamar besan minene dariyaba…juyawa doctor deejah tayi ta kalleshi sekuma yayi mata kwarjini amma dukka hakan seda ta balbaleshi da faɗa inda tace kuma seta gayawa iyayenshi kar abashi ita setayi wata biyu tawarke tukunnah….shidai bece komaiba illa ƙasa dayayi da kanshi yanajin tausayin Maryam ɗinshi…ba’ajimaba Munir yakawo kayan aikin,,,hakan akayiwa isseta ɗinki har huɗu abun tausayi,,, gaskiya mejo bekimantaba awannan gaɓar😢 bayan angama komai suka nufi gida…tun a harabar gidan sajad kemata sannu domin koyanzu ɗaukota mejo yayi. Shikuwa yana shirin biyar su hospital ɗinne segasu sundawo.”Kai najeeb pert ɗina zaka Kaita cewar Hajiya mama lokacinda yanufi pert ɗinshi da ita…jiyowa yayi tare da narke fuska kamar zeyi kuka yabuɗe baki zeyi magana kenan ta ɗaga Mishi hannu…hakan yawuce da ita pert ɗin Hajiya mama dukkansu suna zaune a perlor su ukku, da kallo suka bishi cikin mamaki…shiko ko takansu bebiba yawuce da ita har bedroom ɗin Hajiya mama ya kwantar da ita kana ya manna mata kiss a lips ɗinta yafito, hakan yawucesu cikin tafiyarshi me jan hankalin ƴammata, seda yariƙa Handel ɗin ƙofar zebuɗe yafice cikin sauri anty hawwa tace “yaya najeeb kamar yadda taji ummi nakiranshi. Cak ya tsaya badan komaiba sedan yanason sanin wacece wannan memishi katsalan ɗan acikin al’amarinshi….itako wani mugun daɗi taji ganin yatsaya dudda bejuyoba…ahankali tatako hartazo inda yake cikin kissa tace “please yaya najeeb inaso zanyi magana dakaine idan badamuwa. Bece mata komai ba amma yajiyo yana fuskantarta…wani irin kwarjininshi anty hawwa tagani hakan yasa tashiga kame kame kafin tasamu zarafin cewa “dama nace inaso naɗan rinƙa yima wasu hidimarne kozan samu lada amatsayina na matarka, taƙarasa zancen kanta aƙasa….shiko gogan wani ɗan iskan kallo yake Binta dashi aranshi yake maimaita kallimar mata, kafin bayanan su Abba sudawo mai nacewa aida yarinya biyu aka ɗaura mai aure. Sajen fuskarshi yashafa yana sakin wani ɗan iskan murmushi kafin ta ɗage gira ɗaya cikin wani ɗan iskan sexy voice yace “au really? Aiban sankibane amma zaki iya zuwa pert na ummi kikaita daga hakan yajuya yabar perlor…wani irin ihu anty hawwa rasaki tare da juyi tana rawa tace “wlh seni hawwa’u nasan ba namijin daze ɗauke kanshi daga gareni sedai marar lafiya, tafaɗa cikin isa da nuna cewar ita ɗin wata ce…itadai Ummi tuni tabar wurin tanufi bedroom ɗin mama gun Isseta…juwaira kuwa wani uban tsaki taja tana barin perlor..Gombe stateYau garin Gombe sun tashi da baƙon al’amari domin ta ko ina shirin tarbar baƙon dazasuyi sukeyi wannan kuma umurnin megirma gwamna ne…damisalin karfe ɗaya narana jirgin dake ɗauke da baƙon yasauka, sedai dagani kowaye wannan babban mutun ne duba da yadda jami’an tsaro suka cika airport ɗin tako ina…nashi security ne suka fara saukowa manyan sojojin ƙasar Niger kowanne ɗauke da bindigarshi kana shi uban tafiyar yasauko,,, kyakkyawan dattijo buzun asali mecikar haiba da kamala gakuma kwarjini wannan baƙon bakowa bane face Alhaji abdussalam idis shugaban kasar Niger shine yadira Nigeria dakanshi neman ƴarshi a garin Gombe…..megirma gwamna dakanshi yazo tarbarshi cikin farin ciki da girmamawa…hakan yasa doli yashiga motocin da gwamna yazo dasu beshiga tasu sapwan ba…cikin girmamawa suma wasu security suka buɗe musu wata dalleliyar mota suka shiga sapwan da nazeer….cikin wadda Alhaji abdussalam yashiga kuwa ita hajiya Hannah tashiga. Yanzu kam babu zancen sauka hotel gidan gwamna kawai suka nufa..LagosWanka yayi yafito perlor bayan ya gama shirinshi yazauna yana wayada general Faruk.. sallama sukayi itada ummi suka sahigo, cikin sauri Ummi tace “ina wuni yah najeeb wai anty hawwa tace kace nakawota pert ɗinka,,, tafaɗa cikin fargaba kar anty hawwa taja mata duka idan bashine yaceba…kai kawai ya ɗaga mata tare da nuna mata hanyar barin pert ɗin…..!



