Mijin Marigayiya Page 28 Hausa Novel
Ya ajiye wayar yana harararta yana cewa ‘Yanzu zan je na shirya, kema ki shirya sai mu fita gaba daya ko kuma idan na kaisu sai na dawo kafin nan kin karasa sai mu wuce.’Tace ‘Um, ka ga babu komai fa, zaku iya tafiya ma sai na wuce kawai ba sai na gayawa Baffan ba.’Ya kakkafeta da ido yana harararta har sai da ta sunkuyar da nata idanun, ya juya yana cewa ‘Ki shirya nace.’Ya fice ya barta a nan.Tayi dariya ta cigaba da aikinta.Bata da zabi haka ta shirya suka fita tare, kuma daga wannan lokacin ya zama ko da wanne lokaci zata makaranta haka yake barin abinda yakeyi ya zo ya kaita. Sai dai idan ta gama abinda takeyi kawai sai ta hawo motar haya ta dawo……..A zaune yake a parlor din Ahaji, yayinda Hajia take zaune a kusa da Alhajin. Zuwa yayi musu da labrin auren yana son ya kara don har ma yana gaya musu sati me zuwa yake so aje a kai kudin aure.Cikin walwala Alhaji yace ‘Ai kwanaki da mukayi magana da kai da na jika shiru na zata ka fasa.’Yayi ‘yar dariya ‘Ba fasawa nayi ba Alhaji, na dai dan tsaya ne na kara shiryawa, na gaya maka zan sayi gida ai. To dama tsayawa nayi a samo gidan, kuma yanzu an samo, cinikin ne ma bai fada ba saboda ina so su dan yi min ragi. Amma in sha Allahu ina sa ran zamu daidaita shi yasa nake son yanzu a kai kudin auren.’Murmushin Alhaji ya kara fadi, ya dubi Hajia sannan ya dubi Mustapha yace ‘To ma sha Allahu. Wannan ai sai dai mu sa albarka kawai. Kaje ka sami babanka Safiyanu kayi masa bayanin ita yarinyar idan ya gama bincikensa ya tabbatar gidan mutunci ne ai sai suje su kai kudin. Allah ya sa albarka, Allah ya kara budi.’Suka hada baki shi da Hajia suka ce ‘Amin.’Hajia tace ‘To ka gayawa Khadeejan ko? Me tace?’Ya shafa kai yana murmushi ‘Ban gaya mata ba tukunna, amma in sha Allahu zan gaya mata. So nake sai an gama magana tukunna idan ya zama saura kamar sati uku ko hudu sai na gaya mata ko don saboda gudun fitina. Kafin nan na siya gidan mun koma.’Alhaji yace ‘Eh, to hakan ma yayi. Sai dai kuma Allah ya sa kada mata su rigaka gaya mata.’Hajia tace ‘A’a babu wanda zai gaya mata, kayi abinka a hankali idan ka shirya ka gaya mata.’Nan suka kare hirarrakinsu daga baya yayi musu sallama ya kama hanya.………. Abu daya ne yake ciwa Khadeeja tuwo a kwarya rashin haihuwa, domin har yanzu tun bayan cikin da ta samu ya bare bata sake ko da batan wata ba. Gashi yanzu har sun shiga final year amma babu wani labari. Duk lokacin da tayi yunkurin zuwa asibiti Mustapha sai ya nuna halim ko in kula ko kuma yace lafiyarta kalau zata je ta fara neman fitna, don haka ta tattara ta hakura. Sai dai ta yanke kanta hukuncin cewa da zarar ta gama final exam zata je asibiti a dubata a tabbatar mata da abinda ya hanata samun ciki; ko babu komai itama tana so taga ta haifi dan cikinta. Tunda idan ta gama karatu bata san lokacin da zata sami aiki ba. Haka ta hakura ta mayar da hankali a kan karatunta tana addu’a.Zamanta da yaran Mustapha kadai ya isa ya sa ta ji tana son haihuwa; domin yanzu yaran sun girma tunda Shukra auta ma tana primary 1 yayinda Afaf take SS. Kusan gaba daya yaran yanzu ba dadinsu take ji ba, domin abinda suka ga dama sukeyi. Habib ne ma kawai wanda ya damu da rayuwarta kuma yake neman shawara a wajenta kamar uwa, amma Afaf da Nasreen ma bata san wanene yake basu shawara ba. Ta dai san duk wani abu na wulakanci da sukeyi mata da sa hannun Yaya Jidda. Ga wani mahimmanci da Musttapha yake bawa Afafa ta yanda ko da sun gama magana da Khadeejan Afaf tana iya saka shi ya canza. Duk abinda ya shafi yaran kuma ko da Khadeeja ce ta gaya masa to a karshe da Afafa din zai yi shawara. Hatta kitchen din gidan ya zama kamar na mata biyu; domin a lokuta da damam sai ta gama girka abinda kowa zai ci ta fita daga kitchen din sai Afaf ta shiga itama ta dafa abinda ta ga dama tace bata cin wanda Khadeejan ta dafa. Tayi magana har ta gaji, tunda Mustaphan ya fara nuna tana so ta takurawa Afaf ne saboda ba ita ta haifeta ba. ……… Tana kwance a dakinta tana jiyo hayaniyar yaran a parlor; Afaf ta shigo ta sameta ta mika mata waya tana cewa ‘Anti Abba ne yake waya yace yana kiran wayarki bata shiga.’Ta tashi zaune ta karba ta dan kalli wayar taga whatsapp call ne, sannan ta kara a kunnenta.Yace ‘Ina kika shiga ne anke kiran wayarki ana ta cewa not reachable?’Tayi yar dariya tace ‘Sai dai ko idan network ne don ga wayar ma a hannuna.’‘Kin san Ali Ahmed ko? Abokina da muke zuwa zance tare.’‘Eh na san shi mana.’‘Yauwa da Allah shine ya shigo gari nan da kamar awa daya zamu zo gidan, me zaki iya dafa masa sai muyi dinner tare. Yana dai son tuwo’‘Ok, to sai ayi tuwon ai. Amma dai ka bari na duba freezer tukunna naga yawan kazarmu yada za samu kuma ayi muku peppersoup ko?’‘Eh, kwarai kuwa da zobo ma please. Duba idan babu kazar sai na bayar a kawo miki yanzu, rike wayar ki duba ki bani amsa.’Ta mike ta dubi Afaf da take tsaye tana jiran wayarta ta nufi kitchen. Suna fitowa parlor Afaf din taga Nasreen ta canza channel ta mayar Disney Junior, da sauri tayi kanta tana cewa ‘Wane mara kunyan ne ya canza min channel ban gama kallo. Anti idan kin gama wayar ina nan.’Ta shige kitceh ta barsu.Tana shiga ta karasa ta bude freezer ta duba sannan ta ce masa ‘Zata isa ma, amma dai idan zaka dawo sai ka siyo wata don gaba daya zan kwashe na dafa muku yanzun.’Suka yi sallama ta katse wayar.Sunan da ta gani a jerin chats din kan wayar shi ya ja hankalinta ta fasa fitowa daga kitchen din tana karewa sunan kallo; Anti Naja aka rubuta da alamar zuciya ta emoji. Daga haka da take kallon hoton da yake kan sunan kuma tabbas Naja ce sakatariyar Abbansu. Ba tare da tayi wani tunani ba ta danna kan sunan ya bude mata chats din, har zata yi sama sai kuma wani sako da yake cikin jerin sakunan dake kasa ya ja hankalinta. Afaf ce ta turawa Naja sakon kamar haka“Congrats Anti, Abba ya ce min an kawo kudin auren ko?”“Eh my girl, sun kawo harda sadaki ma. Saura kawai ya gama gyaran sabon gida mu shikenan.”“I can’t wait to have you here with us Anti.”“Soon my girl. Amma dai ta daina baki matsala ko?”“Ta daina, tunda ta ga babu riba. Yanzu ba sosai ma take kulani ba dama ni haka nake so. Habib ne kawai sarkin rawar kai ya manne mata.”“Kada ki damu kwanan nan zan zo na gyara mata zama.”Motsin da Khadeejan ta jiyo ne ya sa tayi sauri ta rufe sakinnin ta dire wayar a kan teburin da yake kusa da freezer din ta kama murfin freezer din ta daga kamar a lokacin ta rufe.‘Anti ina wayar?’ Afaf ta fada bayan da ta karasa shigowa kitchen din.‘Kin ganta nan a kan tebur, dauki.’Ta karasa ta dauki wayarta ta fice ta koma parlor din.Cikin sanyin jiki Khadeeja ta tsaya a ta jigina da freezer din ta kafa tagumi. Kusan wata takwas da suka wuce Mustapha ya kalli tsabar idon Baffa da Mommy yace musu ba auren Naja zai yi ba, amma gashi daga wadannan chats din da ta karanta yanzu har an kai kudin aure da sadaki. Wato ma Afaf ta san komai itace kawai bata san mijinta zai kara aure ba kenan; kuma kamar dai bashi ma da niyyar gaya mata. To me ta yiwa Mustapha ne? me yake tunanin zata yi a akna kara aurensa da yake boye mata? Ita dama da ya kai ta gidan da ya siya yanda taga gidan ta san sai ya kara aure, kawai dai bata zata Naja zai auro ba don kwata-kwata bata sake ganin wata alama da take nuna yana tare da Naja ba tun bayan da suka je wajen Baffa. Wato dama da take zargin Yaya Jidda ce take hure mata kunnen yara ashe Naja ce, tunda gashi nan ta gani har tana gayawa Afaf cewa zata shigo ta gyara mata zama. Ta jijjiga kai, ta goge gumin da ya fara tsattsafowa daga goshinta sannan ta tuna ce mata fa yayi nan da awa daya zasu zo.Jikinta a sanyaye ta koma cikin gidan ta kirawo Rashida sannan suka fito suka kama aiki. Haka ta hadiye duk wani bacin rai tayi ta haba-haba da abokinsa, sai bayan sallar isha’i sannan yayi musu sallama ya tafi.Ta san cewa ya kula da yanayinta yanda ya sauya, amma bai yi mata magana ba. Duk da dai ko da yayi mata maganar ma zata gaya masa gajiya ce kawai. Haka dai suka kwana shi yana baccinsa ita kuma Khadeeja duk lokacin da tayi juyi sai ta kalleshi tana tambayar kanta wai me tayi masa ne yake mata abubuwa kamar wata wadda aka aura ba don soyayya ba?
