Hausa novels

Ruwan Zuma Page 19 Hausa Novel

(19) “Ali!!�? Ammi ta kwa6eshi tana bugin k’afarshi ranta a 6ace. “Ki fad’a mata Hajiya Laila.�? Ya zuba mata ido yayinda ita kuma take kallon gefe fuskarta babu wannan fara’ar. “Ali ka tashi ka fice mini a gida tunda ba zaka iya yin shiru ba. Ita Hajiyar sa’arka ce da zaka dinga mata irin wannan wasan? Ban ce kar in saka jin ka tayar da zancen nan ba? Menene bata maka? Sannan don rashin kunya da rashin sanin girman mutum sai ka tunkareta da shirmen nan? Ali zan 6ata maka rai yanda baka tsammani, wallahi ka shiga hankalinka kasan da wa kake magana.�? Wannan fad’in Ammi ce cikin 6acin rai tana nuna Haydar da yatsa shi kuma yana kallon Laila. Laila ta dubi yanda Ammi ke huci sai taji tausayin Haydar ba kad’an ba ya k’ara shiganta, tace, “Shiyasa naso na masa aure tun kwanaki saboda a tunanina rashin aurensa ne ya kawo wannan zancen. Haydar kaji da kunnenka abunda Ammi tace ko?�? Girgiza kai yayi kana yayi d’an murmushi kamar bashi aka yiwa rufdugu ana yiwa fad’a ba. Yace. “Ina son miki wata tambaya d’aya kuma ina son ki fad’i tsakaninki da Allah.�? Ammi zata yi magana Laila ta katseta da cewa, “Ammi zan amsa masa tambayarsa, saboda ina son a yau a kawo k’arshen wannan maganan.�? “Kinyi alkawarin zaki fad’i tsakaninki da Allah?�? Murmushi Laila tayi don tasan zata iya fad’a mishi koma menene don bata shakkarshi ko wani abu. “Nayi.�? Ta furta tana masa kallon yaro mai tarin yarinta. “Idan daa za’a ce Ammi zata yarda ki aureni sannan mutanen duniya baza suyi zund’enki ba, shin zaki aureni Hajiya Laila? Karki manta kince zaki fad’i gaskiya!�? Wannan karon sunkuyar da kanta k’asa tayi na sakanni biyar kana ta d’ago tana ganin yanda dashi da mahaifiyarshi suka zuba mata ido suna jiran amsarta. “I don’t know Haydar.�? Shine kad’ai amsar data bashi kana ta mik’e tsaye tana gyara laffayanta tana cewa. “Ammi zan tafi.�? “Baki bani amsa ba.�? Ya furta shima yana mik’ewa tsaye. Ajiyar zuciya Laila ta sauk’e kana ta dubeshi cikin ido tace, “Kamar yanda kwanaki na fad’a maka cewa tarayya tsakanina da kai ba zai ta6a yiwuwa ba yau ma zan k’ara maimaita maka, domin kuwa na girmeka wanda nasan ban haifeka ba amma nayi k’ani da kai Haydar. Me amfanin auren da za’ayi jama’a na jiki da kuma na gefe na kushewa suna Allah wadai? Ai ana barin halal don kunya. Ka cire wannan magana a ranka ka nemi daidai kai ka aura, domin nan da sati biyu zan d’aura aure.�? Ta fad’i hakan wai duk don ya gane cewa baza ta iya aurenshi ba. Wannan magana tata ta k’arshe ba k’aramin k’ona zuciyar Haydar tayi ba. Laila ta auri wani bashi ba? A zuciye ya maida dubanshi kan Ammi yana cewa, “Ammi kinji amsarki ko? Ba wai nine bata so ba, a’a maganan da mutane zasu yi take tsoro. Sannan ki sani wallahi idan kinga kin auri wani bani ba ki tabbatar ni Haydar ba so nake miki na gaskiya ba.�? Yana fad’in hakan ya fice daga gidan tamkar zai tashi sama. Idanu cike da kwalla Laila tabi bayansa da kallo tana jin d’aci a zuciyarta. Ajiyar zuciya ta sauk’e kana ta koma ta zauna kan kujeran tsugunnon tana jin jikinta babu kuzari ko kad’an. “Ammi kiyi hak’uri amma ban san ya aka yi har Haydar ya fara tunanin aurena ba. Zan yi aure domin nima a gida an matsa mini inyi saboda zamana babu miji yasa ake mini zargin fasik’anci.�? “Meyasa kika k’i yin aure har na tsawon shekaru ashirin kamar yanda Ali ya bani labari?�? Kallon Ammi Laila tayi sai taga ta yarda da ita kuma zata iya fad’a mata wani abu na daga rayuwarta. “Ina yiwa mijina so na hak’ik’a wanda har ta kai nake tayashi kishin kaina wanda hakan shine ya hanani aure da kuma tarayya da kowanne d’a namiji. Ammi koda zanyi auren bazan auri Haydar ba domin bazan ci zamanina sannan inci nashi ba, a daa Allah yasa na cika burina na auri wanda nake so, a yanzu kuma bazan iya hakan ba domin aurena da Haydar zai jawo mini magana a cikin zuri’ata da kuma mutanen duniya. Ki bashi hak’uri ya nemi budurwa ya aura.�? “Kenan da gaske ne ba Alin ne bakya so ba, maganar mutane kike gudu.�? Fad’in Ammi tana murmushi kad’an. Laila bata tsammaci hakan ba, kuma a tunaninta bata yi furucin da zai nunawa Ammi cewa tana son Haydar ba. “Ammi wannan ba gaskiya bane. Ina son Haydar amma ba soyayya ta aure ba, sannan ina shanye duk abunda yake mini ne saboda Allah ya had’a jinina da nashi.�? “Kafin ki tafi bari na fad’a miki wata magana ko zaki yi amfani dashi.�? Fad’in Ammi ganin Laila ta tashi zata tafi a karo na biyu. “Ina jinki Ammi.�? Ta furta tana mai d’aukan jakarta don ganin har magriba ya kunno kai. “A rayuwa karki takura kanki akan maganan mutane domin duk yanda kika kai da taka tsan-tsan wani sai ya tofa albarkacin bakinsa. Idan har kina son auren Ali ni bazan hana ba kuma zan baku goyon baya d’ari bisa d’ari domin kuwa nasan zafin rabuwa da masoyi, wanda nake tunanin hakan ya faru ne da Allah ya kamani akan wasu laifuka dana aikata a baya. Sannan Alina ba shege bane idan ma kina tsoron auren wanda bashi da uba ne.�? “Ammi ki bar zancen nan haka domin kuwa babu aure tsakanina da Haydar, ni abun kunya ma yake bani. Mu kwana lafiya.�? “Shikenan, Allah ya had’aku da abokan zama nagari.�? “Amin.�? Da haka suka yi sallama Laila ta fitar da sayayyar data mata yaran unguwa suka shiga dashi cikin gidan. Tana isa gida ana kiran sallar magriba, kai tsaye d’akinta ta shiga tayi sallarta kana ta zauna a gurin tana tunanin abubuwan da suka faru a yau. Wa zata za6a a cikin masu son aurenta? Shine abunda yafi damunta kenan saboda bata son tayi dana sani daga baya. Za6an wanda zata yi rayuwar aure dashi duk wuya duk rintsi har k’arshen rayuwarta ba k’aramin abu bane. Wa zata za6a? Ta k’ara tambayar kanta a karo na ba adadi. Kwankwasa k’ofarta aka yi tare da sallama ta amsa Mas’ud ya shigo hannunsa d’auke da envelope. Guri ya samu ya zauna tana tambayarshi ko lafiya taga jikinshi duk a sake. “Last time da aka turawa Madu hotunanki da Haydar shi ya kawo gidan nan yana masifa har kika shigo kika samemu. Ko bayan hakan Kalti ba’a daina turowa ba sai dai nine bana nuna miki na kuma hana maigadi ya baki har sai na dawo in kar6a. Duba nan ki gani.�? Ya mik’a mata envelope d’in ta kar6a hannunta na rawa ta bud’e ta fara cin karo da hotunanta da Haydar a gurare daban daban wanda duk yake mata kallon k’auna tamkar itace kad’ai abun dubawa a duniya. “Ya Allah.�? Ta furta a hankali tana duba hotunan d’aya bayan d’aya. “Wanda aka d’aukeku a bikin Sabrin ni kaina bai mini dad’i ba Kalti, amma ban sani ba ko photoshop ne.�? Yana fad’in hakan ta iso kan hoton wanda suka d’auka bayan an d’aura aure, Haydar ne rik’e da k’ugunta ya rankwafo jikinta kad’an tamkar fuskarsu zata had’e guri guda. Ita kanta tasan wannan ba photoshop bane domin hakan ya faru babu k’arya. Tana tunawa ana d’aukan hotuna irin wanda ake yi bayan d’aurin aure, Haydar na can tsaye a gefe sai murmushi kawai yake doka mata idan suka had’a ido. Tana tunawa da kallon ya isheta ta yafutoshi da hannu ya zo tace masa ya tsaya su d’auki hoto. Ya tsaya a gefenta akan za’a d’aukesu aka tunkud’oshi jikinta ya d’aura hannayensa a k’ugunta don kar su fad’i duka. Sai dai da tureshi da rik’entan da yayi ko sakan biyu bai kai ba ya cire hannusa a jikinta tamkar wanda ya ta6a wuta. Waya turesa? Shine basu ga wannan mutumin ba daga ita har shi. K’arshe a wani irin yanayi na kunya da takaici aka d’aukesu hoto guda d’aya, ana d’auka Haydar yayi saurin barin gurin ya fita daga gidan ma gaba d’aya, bata sake ganinshi ba sai da su Nazifi da Alhaji Mukhtar suka zo Mas’ud ya aikeshi sayo musu ruwa. Tamabayar a nan shine wayene yake binta yana d’aukansu a hoto? Me yake nufi da hakan kuma menene burinsa a kanta? “Waye ne?�? Shine farkon abunda ta furta tana cigaba da kallon sauran. “Kenan zuwan da nayi gidansu yau ma anyi snapping?�? Ta fad’i hakan tana nunawa Mas’ud. Gyad’a kai yayi kana ya k’ar6e hotunan daga hannunta ya mayar dasu cikin envelope yana cewa, “Kalti bamu san wa yake haka ba kuma bamu san menene nufinsa a kanki ba, na d’auka duk mai aikata hakan zai hak’ura idan yaga bamu damu da abunda yake yi ba, shiyasa ko da an turo bana nuna miki nake ajiyewa a gurina. Amma wanda aka turo yau ya 6ata mini rai dalilin it’s like baki da privacy, duk inda kika je suna binki suna d’aukanki a hoto for what reason? Abunda yafi dacewa yanzu shine mu kai k’ara police station a binciko duk wanda yake wannan aikin a gurfanar dashi a gaban kotu.�? Ya k’arisa maganan cikin 6acin rai har idanunshi na sauya kala zuwa ja. “Wa kake tunanin zai mini haka?�? Ta tambayeshi tana zama akan gadonta. “Shine ban sani ba Kalti kuma kaina ya kulle. Duk wanda nake zaton zai miki haka sai inga sonki yake yi da aure kuma bazai so ya zubar da mutuncinki ba. Waye kike zato?�? Babu 6ata lokaci tace, “Abul.�? “What?!�? Shine abunda Mas’ud ya furta da k’arfi yana kallonta. Laila bata dubeshi ba domin gefe take kallo yayinda zuciyarta ke tafarfasa sanin cewa Abul ne yake aikata mata haka. “Abul ba zai ta6a yin hakan ba Kalti. He would never do that.�? Ya fad’i hakan yana dafe kanshi da hannunsa duka biyu. “Yasan duk wani shiga da ficena, kuma baya shakkar fad’a mini cewa yasan naje gidansu Haydar a duk ranar da naje. Wa zai mini haka in ba Abul ba wanda yake da zafin kai da bak’ar zuciya. Ya yiwa Haydar tsanan da baka tsammani Mas’ud domin a kan maganarshi Abul ya yarda wai inyi aure. Abun bai baka mamaki ba?�? “Bashi bane.�? Mas’ud ya fad’a yana tashi tsaye ya fita daga d’akin nata. Laila ta bishi a baya tana cewa, “Kar ka kai k’ara gurin police bincike ya dawo cikin gidana Mas’ud, domin hakan zai fi mini tonon asiri a idon duniya. Ka kira mini shi yazo.�? Zai yi magana tace, “Kayi yanda nace Don Allah.�? Bayan minti sha biyar Abul ya shigo yana tambayar ko lafiya. Ganin mamanshi a zaune lafiyanta kalau yasa yayi ajiyar zuciya ya samu guri kusa da ita ya zauna yana cewa, “Uncle Mas’ud ai zaku bani tsoro da irin wannan kiran gaggawan. Mama lafiya?�? Ya tambayeta yana murmusawa kad’an. “Abul kaine kake turo mini sak’on hotuna?�? Ta tambayeshi fuskarta a tsuke tamkar bata ta6a dariya ba. Wannan tambaya data masa yasa ya nuna kanshi da yatsa cikin rashin yarda da abunda ya fito daga bakinta yace, “Ni kuma Mama?�? Gyad’a masa kai tayi tana kallon yanayinsa yanda lokaci d’aya ya canja tamkar bashi ne ya shigo da fara’a ba. “Kalti na fad’a miki ba Abul bane. Ki tashi mu tafi office d’in ‘yan sanda.�? Fad’in Mas’ud yana mik’ewa tsaye. “Ka barshi ya bani amsa da bakinsa.�? “Yanzu Mama har zaki yi tunanin ni d’anki na cikinki zan aikata haka? Me nake nema da zan miki haka? Wallahi bani bane. Ya ma za’ayi ki fara wannan tunanin a kaina?�? Ya fad’in hakan cikin takaici da bak’in ciki. “Ya aka yi kullum naje gidansu Haydar kake da labari Abul? Ka fad’a mini gaskiya bana son k’arya.�? Shiru yayi ya sadda kanshi a k’asa kana ya d’ago yace, “Ina da aboki d’an makarantarmu da yake wannan unguwan. Shine Idan yaga motarki sai ya fad’a mini.�? “You are lying Abul, ina gane k’arya a maganarka.�? “Mama ko da hakan k’arya ne wallahi tallahi bani nake miki hotuna kuma nake turo miki ba.�? Yayi wannan maganan idanunshi na cikowa da kwalla. “You are still lying Abul. Meyasa kake da taurin kai da kuma k’arya?�? Ta tambayeshi itama cikin bak’in ciki domin tasan shi yake duk wannan abun. Hawaye ne suka gangaro kan fuskarsa ya tashi tsaye a zuciye jikinshi har kyarma yake yi yana cewa, “Tun lokacin da yaron na ya shigo cikin rayuwarki kika canja Mama, kuma kika daina spending time dani kika daina aikana kina fad’awa mutane cewa bana miki aiki da wuri ina zuwa yawon banza. Baki sanshi ba, baki san daga ina ya fito ba haka kuma baki san ainihin manufarshi a kanki ba saboda soyayyarsa ta rufe miki ido.�? “Abul!!!�? Ta daka matsa tsawa amma bai saurareta ba yaci gaba. “Duk mun gani Mama, babu wanda bai san cewa kina son yaron nan ba sai dai babu wanda ya iya fitowa ne ya fad’a miki.�? “Abul ka rufe bakinka.�? Mas’ud ne wannan karon ya daka mishi tsawa yana nunashi da yatsa. “Kina ta bibiyarshi kamar wata k’aramar yarinya yana ta wasa da hankalinki kuma kin k’i sauraran kowa kina ganin kin fimu sanin halinshi. Wallahi baki san waye shi ba Mama domin kuwa nina fiki sanin waye shi da kuma manufarshi a kanki. Kar ki bari soyayyar k’aramin yaro ya rufe miki ido har kiyi sanadin wargajewar iyalinki da kuma mutuncinki.�? Tass!!! Ta d’ebe Abul da mari yayi tangad’i kamar zai fad’i amma ya tsaya yana kallonta ido cikin ido yana murmushi wanda hakan ba k’aramin kad’a hanjin Laila yayi ba. Me yake damun Abul? Hauka ya fara yi? “Ka gani ko Uncle Mas’ud? A akan saurayinta ta mari k’anwata yau ma gashi nima ta mareni. A hakan ne kike cewa kina sonmu?�? Wannan karon hawaye ne ya gangaro kan fuskarshi amma bai daina magana ba yaci gaba. “Daa za’a bani za6in waye zai mutu tsakanin Ubana dake da wallahi ke zan ce a d’auka bashi ba!!Baki ta6a son Babana ba haka ni da k’anwata ma bakya sonmu, k’arya kike yi.�? Kuka Laila ta saka tana kallon Abul wanda ya rikid’e ya koma wani mutum daban wanda bata ta6a sani ba. Mas’ud ne ya iso gurinshi tamkar walkiya ya kifeshi da mari wacce tafi ta Laila k’arfi, hakan yasa Abul ya zube a k’asa yana dafe da k’uncinsa. “Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un.�? Shine abunda Laila take maimaitawa tana jin duniyan na juya mata. Mas’ud ya cakumo Abul ya mik’ar dashi tsaye, cikin tsawa tamkar zai d’aga gidan ya fara magana. “Uban me kake tunani da kake furtawa mahaifiyarka irin wannan maganan? Kanka d’aya kuwa ko shaye-shaye ka fara? Ka fad’a mini me kake yi?�? Yana fad’in hakan yana jijjiga Abul wanda bakinshi da hancinsa ke fitar da jini, yayinda idanunsa kuma ke tsiyayyar hawaye. Abul yaja jinin bakinshi ya tofar a tsakiyar falon ya kallesu zuciyarsa a k’ek’ashe yace, “Ka tambayi mai bin yara k’anana.�? Mas’ud zai k’ara kai mishi mari Laila ta rik’e hannunshi ta baya tana cewa, “Barshi Mas’ud. Sakeshi.�? “Kalti ki barni in koya yaron nan hankali don abun nashi ya zama hauka.�? “Ka barshi nace maka.�? Tana fad’in hakan ta 6an6are hannunsa daga kafad’ar Abul. Yana jin an sakeshi ya fita daga gidan cikin sauri Laila na kiranshi amma bai ko waiwayeta ba. “Na shiga uku. Na shiga uku! Na lalata tarbiyyar d’ana da kaina.�? Ta fad’i hakan tana zama a kan kujera daga baya ma ta sauk’o k’asa tana dafe da k’irjinta wanda yake mata rad’ad’i tamkar ana soyawa. “Kalti babu laifinki a cikin canjawar Abul. Ki d’auki hakan a matsayin jarabawa da Allah yake gwada miki.�? “Duk laifina ne dana kasa yin aure ya tashi ba uba. Daa na sani daa na barwa Umma ta raineshi ya tashi da Nazifi a matsayin mahaifinsa. Meyasa na kasa tunanin hakan zai iya faruwa na kafe sai da nayi rayuwa dasu? Me hakan ya tsinana mini in ba bak’in ciki da dana sani ba?�? Zai yi magana ta tashi tsaye tace, “Kaje ka samu Alhaji Abdul kace na amince a d’aura mana aure rana ita yau, Jumma’a kenan.�? Zai k’ara magana ta k’ara katseshi tana cewa, “Mas’ud zan rasa Abul idan har ban yi auren nan ba. Kayi yanda nace kawai.�? Cikin tausayawa ya bita da ido har ta shige d’akinta kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Tana shigewa ya ciro wayarsa a aljihunsa ya danna kira yace, “Naana za’a iya aura mini ke cikin kwana uku?�? Amsa aka bashi a d’ayan gefen yace, “Ki fad’a a gida gobe zan turo manya gidanku sannan ina son ayi auren a cikin kwana uku.

Mum Fateey 👌

Back to top button