Hausa novels

Wace Ce Ita (Who Is She) Chapter 55 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                             FIFTY-FIVE📍

 

 

“Na dace dake! Kin dace dani! Ki bude idonki ki fuskanci masoyinki wanda bakida kamarsa a duniya!”

“Idan kika kini na gwammaci in kasheki kowa ya huta!”…

Wayen’nan sune sakonni guda biyu da aka turo mata a jere da unknown number, sakon farko ne ya bata mamaki na biyun kuma ya bata tsoro, saidai duk a cikin lulubenta ta gagara gano wanda ze iya mata message din…

Maimata sakon tayi sau uku kafin tayi deleting messages din sannan tayi blocking number….

A sanyaye ta mike ta fara shiri tana kara maimata sakon aranta, wai ta bude idonta ta fuskanci masoyinta da bata da kamarsa a duniya, toh tana da babban masoyin daya wuce khaleel ne? Mutumin daya sota tin batasan kanta ba? Babu flaws dinta dabe sani ba amma ko sau daya be taba nuna gazawarsa a kaunarta ba, ta tina lokacin da zeta rokonta akan ta dena shan codeine amma tana sa masa kuka shikenan ze bata, toh akwai soyayyar da tafi mutum yaso abinda kakeso? Bata kara tabbatar da khaleel na sonta ba saida deen ya shigo rayuwarta, ya shigo rayuwarta da wasu irin abubuwa da batasan yanda zata fassara ba, ya hargitsa mata tinaninta da nitsuwarta da shegen takurarsa da muguntarsa, a lokacin ne ta gane khaleel rare gem ne saboda a gurinsa kadai take samun farinciki idan deen ya bata mata rai, duk da haka tana ganin kimar deen sosai wanda tasan ko shi baze yarda ba, bakomai bane yasa take ganin kimarsa ba illa sadata  da mahaifanta dayayi sannan haka kawai bata san abinda ze cutar dashi, batasan da hakan ba kuma sai lokacin da akazo za’a kashesu yace taja motar ta tafi shi ze ji dasu dukda yasan za’a kashesa, wannan abun ya kasa barin ranta har yau, wayennan abubuwa guda biyu ne sukasa take ganin kimarsa, amma fa hakan bashi zesa ta bari ya takata yanda yaso ba……. Tabbas bata son khaleel at first but as time goes on ta gane bata da kamarsa shiyasa ta koyawa zuciyarta sonsa, and yanzu tana jin she can do anything for him, she just wants to see him happy too……

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

Watsar da zancen tayi ta shirya cikin wata fitted bubu silk fibre, sai da ta gama feshe jikinta da turaruka masu kamshi sannan ta saka rigar, tsayawa tayi a gaban mirror tana tinanin meya kamata tayiwa fuskarta, ita ba gwanar kwalliya bace but she wants to look good for her honey, tuno yanda mami ta mata last time da zata gurin Abby yasata daukan kwalli tasa a hankali being cautious karya tsokane  mata ido, eye liner ta dauko ta gwada lining saidai ganin yanda hannunta ke rawa kawai ta hakura dashi, mascara tasa ta taje long natural lashes dinta sai hakan ya kara fito dasu gwanin sha’awa, girarta ta taje da brush sannan ta saka lipgloss baki yayita maiko gwanin sha’awa, daidai nan khaleel ya kirata yace mata gashi a kofar gida yana jiranta, veil dinta ta yafa sannan ta sake feshe jikinta da turaruka, matching bag da shoes ta shafa ta kara gyara zaman veil dinta sannan ta fita, ko kafin ta bar corridor din sama veil din har ya dawo tsakiyar kanta saboda tsantsin gashinta da yalwarsa, ko a jikinta ta cigaba da tafiya batareda ta sallami su umm ba…..

Direct hospital dinsa ya wuce bayan ya budewa umm inda ya kulle billy, ya sani sarai bazasu kwashe ta dadi ba idan taga irin dukan da yayiwa yarinyar shiyasa kawai ya fece saboda ransa a bace yake bayasan a kara masa wani bacin ran…..

Tinda ya shiga asibitin ake ta gaishesa amma babu wanda ya kula kawai ya shige office dinsa ya shedawa secretary dinsa bayasan ganin kowa…..

Zama yayi a office chair dinsa zuciyarsa duk a jagule, sai kuma a lokacin yaji yana san sanin result din tests din, gashi babu wanda yace masa komai, kodai anyi nasara ne? Sai kuma yaja tsaki yace;

“And so? Ina ruwana?!”….

Sai ya jingina da bangon kujerar yana lissafin yanda ze tsara rayuwarsa, beje ko ina ba tinaninta ya masa kutse a cikin tinaninsa….

“Has she eaten? Nasan batasan cin abinci”…

Ya fada kamar shi da wani ne a gurin…..

Sai kuma ya kwashe da dariya yace;

“For real? Wai itama tasan soyayya? No this is not funny!”….

Ya fada yana gimtse fuska…..

Haka yayita tinaninta, wani abun ya sashi murmushi, wani abun ya sashi watsar da abubuwan da yake kan table din, a haka duk saida ya hargitsa office din be sani ba….

Sai da yaji ana kiran sallar magriba sannan ya tashi ya tafi masjid din hospital din dan yayi sallah , koda cleaner din dataje gyara office din taga yanda office din yayi kacha kacha tayi mamaki sosai, sai kace wanda yayi dambe da kayan office din, haka dai taja bakinta tayi shiru tayi abinda ya kaita….

Ko bayan an idar da sallah be tashi daga masallacin ba sai ma Al-qur’ani daya dauko ya fara karantawa, a hankali ko yaji zuciyarsa ta fara masa sanyi, bacin ran daya kwasa yau na gushewa, karatun ya cigaba dayi har akayi sallar isha, saida ya sake kara 30mins yana karatu baya an idar da sallar isha sannan ya tashi ya wuce gida…….

Har ze shige part dinsa yaji baze iya bacci idan besan halin da take ciki ba, yasan kuma ba lallai taci abinci ba, gwara yaje ya tasata a gaba taci, ya kuma bigi ruwan cikinta yaji labarin tests din dan abin ya kasa barin ransa……

Yana shiga parlourn yaji ko ina tsit sai karar ac, har zai haura sama yaji wani fitinennan kamshin turare ya daki hancinsa, ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido at the same time yana kara bude hancinsa dan ya shaki kamshin turaren da kyau, sai kuma yaji takun takalmi dass dass alamun ana tawowa, guri ya samu daga chan gefe ya zauna yana jiran yaga waye haka dan yanada tabbacin me shine ya cika turare haka…….

Kamar a mafarki ya hangota tana saukowa daga kan step sadap sadap jikinta sai motsawa yake a cikin silk rigarta, murza ido yayi dan ya tabbatar ita din yake gani ko kuwa, mamaki ne ya kamasa ganin da gaske ita dince, sake baki yayi yana kallonta kamar ya hadiyeta daga zaune, sosai ta mishi kyau kamar ya saceta ya boyeta yana ganinta ita kadai, ya rasa meyasa kome tasa yake mata kyau, ga bakinnan sai maiko yake yana daga masa hankali, kasa jurewa yayi ya zaro wayarsa ya hau yi mata hotuna da videos, ita ko batasan yanayi ba dan bata ma ganshi ba, burinta kawai ta fice batareda kowa ya sani ba, deen kuma yanaso ya dakatar da ita amma inaa hankalinsa ya riga ya gushe a wajan kallonta, saida ta kai daidai bakin kofa yaji kamar an tsikaresa, da sauri ya ajye wayar ya daka mata wani mugun tsawa yace;

“Kehhhhh!!!!”…..

Har ta dora hannunta zata bude kofa taji muryarsa ta daki kunnenta, a gigice ta cire hannunta daga kan kofar ta juyo tana neman inda yake, sai a lokacin ta gane yana parlourn tin data fito kenan…..

Wayarsa ya dauka yana kallon hotunan daya mata a cikin wayar a dake yace;

“Koma inda kika fito!”….

A darare tace;

“Fita zamuyi ni da khaleel fa”….

Ai besan sanda ya cilla mata throw pillow din dake kusa dashi ba sannan a hassale yace;

“Khaleel din ubanki ne da zaki fita tare dashi karfe taran dare?!”……

“Toh ba anbashi ni ba kuma mun kusa aure”….

Ta fada a shagwape….

Kamar ze duketa yace;

“Sai ki jira in kunyi shashashan auren sai ku fita ko tsakiyar dare ne, now koma ciki mara kunya fitsararriya!!!”……

“Yana fa waje yanzu, bari inje ince mishi ya bari gobe toh”…..

“Wai me yake damun brain dinki ne zahrah? When will you start differentiating between right and wrong? Kin cika turare kamar kampanin turaren ne zakije gurin saurayi? Kalli kayan dake jikinki dan Allah? Haka zaki tafi kina tallan jikinki ko wani jack and jill ya kalla kenan?! Mayafin kuma da kinsani cillarwa kikayi dan dashi da babu duk daya, bansan meyasa mami da umm ke barinki kina shiga anyhow ba, zaki wuce sama ko sai na karya miki kasusuwa?, stupid girl kawai!”….

Deen ya fada cike da takaici, shi yanzu baya ma ganin lefinta sosai, umm da mami ne suka barta take saka matsattsun kaya, toh wallahi za’ayi yaki dashi a gidan nan akan haka dan baze lamunta ba…..

Kamar zatayi kuka ta marairaice tace;

“Yaya dan Allah koda 5mins ne in fita mu gaisa kaga babu dadi yazo kuma ince ya tafi bamu haduba”….

Wayar da yake hannunsa ya saita daidai bakinta daya iya tsara kalamai idan yaso, harda wani yayan munafurci, sanda yake binta tace masa yaya ai ki tayi sai yanzu saboda wani gardi, ba shiri ta matsa wayar ta fadi ta fashe a take, sai kuma taga ya nufota gadan gadan, da sauri ta kwasa a guje tayi sama, bedroom din daya koma mallakinta ta shige da sauri ta rufe kofa…

Kwafa yayi ya dauki wayarsa daga kasa, kallon screen din yayi yaja tsaki yace;

“Foolish girl kinyi min asarar pictures dinki, dole ma in gyara wayar!”…..

Zira wayar yayi a aljihunsa ya haura sama, be bi takan bedroom dinta ba ya shige na umm, be sameta a ciki ba sai ya tafi na mami, knocking yayi ya shiga bakinsa dauke da sallama, amsa masa mami da umm dake tattaunawa sukayi, mami zatayi magana yayi saurin rigata da fadin;

“Ina zahrah?”…..

“Inaga tayi bacci dan tace min isha zatayi ta kwanta”….

Umm ta bashi amsa….

Kallonsu daya bayan daya yayi sannan yace;

“Kuna zaune ta saka matsattsun kaya zata fita da saurayi baku sani ba!”….

Harararsa mami tayi tace;

“Wa din?”….

“Wacece banda baby tee? “…..

“Baby tee din da bata da lafiya? Meyasa bakasan zaman lafiya ne deen?”…

“Toh aje a dubata mana”…..

Mikewa sukayi dukansu suka fita daga dakin, suna fita sukaji wani irin kamshin turare ya dakesu, kwafa deen yayi yace;

“Kunji kamshi ko? Toh duk uban kamshin nan itace ta fesa turaren”….

Basu tankashi ba har suka karasa dakinta, sai da sukayi knocking sau uku sannan ta taso ta bude, a shirye suka ganta cikin kayan bacci, kwata kwata batayi kama da wacce ke shirin fita ba, hasali ma harta kashe fitila, ba karamin gogewa deen hadda tayi ba saboda yanda tayi maza ta wanke fuska ta chanja kaya, zeyi magana mami ta dakatar dashi tana kallon baby tee tace;

“Wai kin fita daughter?”…

Cikin yanayi irin na me bacci ta girgiza kai tace;

“A’a, ni bacci nakeyi”….

Cikin mamakin karyar data shimfida deen yace;

“Karya kike! In bacci kike tundazu wannan kamshin na menene?”…..

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

Kallonshi tayi tana wani munafukin murmushi, dama tasan za’a rina tinda taji ya ambaci sunansu tasan sai yaje ya musu magana, shiyasa tana shiga tayiwa khaleel text message din bazata samu fitowa ba sannan ta kashe waya, da sauri ta cire kayan jikinta ta jefa a washing machine ta hau wanke fuskarta, Allah ya taimaketa bawani abun azo a gani ta shafa a fuska ba…..  Murya kasa kasa kamar na wacce ta fara baccin dagaske tace;

“Tun dazu na fesa, turaren ne me karfi”…..

Ze kara magana mami ta nuna mishi kofa tace;

“Sai da safe Deeni! Yarinya na baccinta kawai kasa mun zo mun tashe ta”…..

Kallon rashin yarda umm tabi baby tee dashi saboda tasan haka kawai bazata masa magana a nitse ba amma kuma yanda takeyi din babu wanda zece ba daga bacci ta taso ba, kawai ta kada kai tace;

“Allah ya kyauta!”….

Sannan ta bar gurin….

Duk yanda deen yaso yiwa mami magiya akan a binciki baby tee shi yasan za’a samu sheda ki tayi, takaici ya isheshi wayarsa ta fashe bare ya nunawa mami hoton daya mata, yanaji yana ganin mami tace baby tee ta koma ta kwanta sannan shi kuma ta tasashi a gaba da fada har saida ya bar part din sannan ta rufe kofa ta koma gurin umm suka cigaba da zancensu…..

Wani tinani ne yazowa deen akan yaje ya duba ko khaleel na nan ya sauke haushinsa akansa, saidai yana fita yaga babu khaleel babu alamarsa, haka ya koma yaje ya kwanta ransa wasai tinda dai bata fita khaleel ya ganta a haka ba, shi da yasan su umm ma basu sani ba da be tona mata asiri ba tinda bata fitan ba, yanzu gashi makircinta yasa suna ganin kamar karya ya mata……

Bayan ya idar da sallahr asuba direct part din su mami deen ya tafi, a bude ya samu kofar kamar yanda yayi expecting dan da asuba suke budewa, dakin mami ya fara zuwa ya tarar da ita tana lazimi, gaisheta yayi ta gyada masa kai sannan ya tashi ya tafi dakin umm, akan sallaya ya tarar da itama ya tsuguna har kasa ya gaisheta, amsa masa tayi da tambayarsa ya ya tashi, lafiya kalau yace sannan ya tambayeta ko baby tee tayi sallah, ce masa tayi yanzu ta bar dakin ma, ok kawai yace ya fita daga dakin….. Bin shi da kallo tayi tana sake sake aranta….

Tana zaune akan sallaya, qur’ani dauke a hannunta tana karatu a zuciya taji knocking, izini ta bayar Deen ya shigo bakinsa dauke da sallama, tana ganin shine ta mike da sauri zata shige toilet, ruko hannunta yayi a tausashe yace;

“I’m not gonna hurt you baby girl!”….

Sai a sannan taji hankalinta ya kwanta, sakin hannunta yayi ya dauki Al-qur’anin ya mika mata yace;

“Dama nazo muyi karatu ne, let’s go downstairs”….

Ba musu ta karba sannan tayi gaba, bin bayanta yayi yana irga takunta dinta yana kuma kare mata kallo ta cikin hijab dinta….

Guri ya nuna mata ta zauna sannan shima ya zauna yana facing dinta, nitsuwa tayi sosai harda sunkuyar da kai kamar a islamiyya aransa yace ‘sai kace ta Allah’…..

Gyaran murya yayi yace;

“Daga yau duk bayan asuba zamuna karatu anan! Kada ki yadda in shigo ban sameki a gurinnan ba, kinji ko?”…..

Cike da ladabi tace;

“Toh”…

Hmmm kawai yace aransa sannan seriously yace;

“Daga fatiha zamu fara ko? Dan nasan babu abinda kika iya”….

Ba shiri ta dago ta kallesa tana zaro ido….

Wani irin tashi tsikar jikinsa tayi saboda yanda ta ware idonta a kansa, shi ze iya cewa besan haka idanuwanta suke da girma ba sai yau saboda kullum a lumshe suke, wani yanayi yaji ya fara shiga ya harareta yana zare mata ido shima yace;

“Dena kallona!”….

Dauke idonta tayi tana turo baki tace;

“Toh ba kaine kace ban iya komai ba”….

Kallon dan bakin da take turowa yayi, murmushi ya sabuce masa yace;

“Toh kin iya dinne?”….

“Eh mana, na fa yi sauka, kuma nayi hadda ma”……

“Saukar izu biyu da haddar izu daya ko?”…..

Bata rai tayi bata kara cewa komai ba….

Dariya yayi kasa kasa yace;

“Toh shikenan muyi tilawa toh kafin na tsara mana yanda zamuna karatun da kuma littatafan daya kamata munayi”….

Mika masa qur’anin tayi tace;

“Ungo ka ji min haddata”….

Hancinta yaja yana murmushi ya ajye qur’anin a gefe yace;

“Iyee good girl ina jinki toh”…..

Bismillah tayi ta fara karanta suratul fatiha cikin kwarewa da bawa ko wani harafi hakkinsa……

 

Wani irin sanyi da nitsuwa deen yaji yana saukar masa saboda yanda sautin muryarta me dadi ke karatu cikin kira’a me dadi cike da kwarewa, koda wasa be taba tinanin zata iya karatu haka ba, ya dade beji murya me karatu me dadi irin nata ba, amma be yadda ya sakankance ba dan yana kiyaye duk wani harafi da take fitarwa har ta fara karanta suratul baqarah cikin tattausar muryarta……

Sai da ta karanta izu biyu yaji muryarta ta farayin kasa kamar me jin bacci sannan ya dakatar da ita yana murmushi yace;

“Masha Allah mallama zahrah, anya bazan bude miki islamiyya ki fara karantarwa ba kuwa?”….

Dariya tayi tana rufe fuska….

“Honesty I’m really impressed baby girl! Allah yayi albarka, tashi kije ki kwanta”….

Ya fada yana kallonta lovingly, dagaske bata taba burgeshi ba irin ranar……

Mikewa tayi tayi masa sallama ta tafi, ita dakanta sai take jinta wani iri saboda yau ce rana ta farko da suka taba rabuwa lafiya ba fada ba tsawa ba komai, sai taji hakan ya mata dadi….

Da farinciki yan gidan suka tashi saboda sanarwan zuwan mutan maiduguri da su uncle A mutan Dubai….. Sosai gidan ya kachame da gyare gyare da girke girke kamar wani babban taro za’ayi, ita kanta baby tee farinciki take sosai kamar ta sansu……

Tinda safe suka fita da mami da umm lokacin saif yana bacci be sani ba, fashion house din mami suka fara zuwa mami tace baby tee ta zabi duk wani choice of kaya da takeso, kasa zaba tayi mami tace kawai ayi mata packaging duk wani sabon design din kaya da yake gurin including varieties of abaya, tafiya sukayi saboda kayan sunyi yawa gashi sai an rage mata wasu, wasu kuma sai an kara kawai mami tace a kawo gida later, daga nan mall din umm sukayi, nan ma shopping spree umm tace tayi ta zabi duk abinda takeso kana daga kan turaruruka, undies, chocolates da komai da komai…… Daga nan kuma suka wuce wani beauty parlor aka musu manicure da pedicure, gyaran kai da kiso, babu yanda umm batayi ba akan akayiwa baby tee kitso tace ita bataso a mata gyaran gashin kawai, karshe da taga umm ta takura tace ita jan lalle takeso, ai kuwa aka mata irin me yankan celotape me shegen kyau na hannu da kafa, ana gama lalle tace ita a cire tagaji, umm tace bata isa ba ai tinda tace tanaso sai yayi awa daya sannan za’a cire, tanaji tana gani sai gurin la’asar aka cire tukunna, ba karamin kyau lallen yayi akan farar fatarta ba, sai ya kara fito da kyan hannayenta da kafafunta, suda kansu masu lallen sai koda lallen sukeyi, su umm ma saida sukace masha Allah dan ba karya lalle yayi kyau….. Sallah sukayi sannan suka wuce gida……

Deen tin sha biyu yake zarya a part din su mami basu dawo ba, gashi kiran duniya ya musu sunki daga waya, su kuma suna sane dan sun san tsap ze iya biyosa shiyasa kawai suka share shi…… Har yaje yayi sallahr azahar ya dawo basu dawo ba, lokacin ya zama so frustrated har ya fara wurgi da throw pillows, yana cikin wannan hali yaji wayarsa na ringing, da sauri ya dauka duk a tunaninsa su umm ne kawai yaga number sudais ta Nigeria, tsaki yayi ya dauka yasa a speaker yace;

“Kai kuma yaushe ka shigo kasar?”….

Kwashewa da dariya sudais yayi yace;

“Kai kuma waya taboka haka? Gaskiya ka rage zuciga man”…..

“Bazan rage zuciyar ba dan ubanka!”….

Wata dariyar sudais ya kara fashewa dashi yace;

“Dan uwan babarka ka zaga ni ba ruwana”….

“Kai kasan wannan, idan dariya ka kirani kayi zan kashe wayata”….

Saita muryarsa sudais yayi yace;

“Allah ya wuci zuciyar dan gaban goshin umm da anna da bappa, ni dama kiranka nayi in sheda maka muna tafe yanzu”….

Da mamaki deen yace;

“Kuna tafe ina?”….

“Abuja mana, anna da bappa sun sako mutane a gaba, anna harda cewa duk wanda beje yaga jikarta ba Allah ya isa, kaga ko dole mu ajye aiki mu tawo”…

Tashi zaune deen yayi yace;

“Are you for real? Kowa da kowa sai yazo? Kana nufin su imran su abbass duka tace sai sunzo?”…..

“Ni nazo ma bare su? Ta fa rantse kowa na familyn shuwa sai yazo ya ganta, duk wanda kaga be zo ba tace uzuri babba ya bayar, shima kuma sai taga damar amsa, a hakan ma da alkawarin zuwa ko ba yanzu bane”…….

“Ikon Allah amma su bappa sun shammace ni, dana ce musu kar suyi gayya cemin sukayi fa toh”….

“Taaab lallai sun saka a kwalba, anna harda cewa kafi kowa imani a familyn dan tinda aka tsinci yarinyar ka tare a abuja”…..

Sudais ya fada yana dariya…..

Girgiza kai kawai deen yayi zuciyar na buguwa, haka kawai yaji bayasan gayyar nan gabadaya, kuma daya sani da sai yasan yanda yayi ya dakatar dasu, amma ko a hakanma ze gwada sa’arsa yagani…..

“Will call you later sudais”…..

Ya fada yana kashe wayar……

Number bappa ya fara kira amma sai ringing take ba’a dauka ba, sai ya maida akalar kiransa zuwa number anna, itako a kashe ya sameta ma, sosai yaji hankalinsa ya kara tashi ya cigaba da kiran bappa still ba’a dauka ba…….

Yana cikin wannan hali yaji sallamar baby tee, da sauri ya dago yana kallonta, ganinta ita kadai rai a bace yace;

“Zo nan! Ke kadai kika fita dama?”….

“A’a”….

Itama ta bashi amsa tana shan kamshi….

Zeyi magana kenan idonsa ya sauka akan lallen hannunta, sosai lallen ya tafi da imaninsa har yaji maganar da yakesan yi ta makale, a hankali ya nuna mata gefensa yace;

“Sit here baby girl”….

Zama tayi tana mamakin abinda ya sauyasa lokaci daya….

Hannunta ya kamo yace;

“Waya miki abinnan? Dama haka yake da kyau?”…

Shiru tayi batace komai ba, kawai taga ya saka yatsunta na tsakiya guda biyu a baki yana tsosa, wani iri taji tayi nufin janye hannunta saidai ina ko motsi hannun beyiba, sai ma lashe duka yatsu goman daya farayi kamar wanda yaci danwake yake lashe hannunsa….

Sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, mutum kawai ya tsaya yana lashe hannun wani kamar wani maye, janye hannun ta sakeyi tana fadin;

“Saif sakemin hannu, meye haka wai!”…

Ko jinta beyiba dan ya riga yayi nisa a abinda ya sawa ransa….

Sake janye hannun tayi saboda yanda tsikar jikinta ke tashi kamar yana mata tafiyar tsutsa,  kawai ya janyota cikin jikinsa gabadaya sannan ya cigaba da lashe lashensa….

Suna cikin wannan hali taji anbude kofa, shi dama ya dade da barin duniyar mutane, juyowa tayi taga……..

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button