Uncategorized

Tubabbiya Complete Novel Document

TUBABBIYA🏵





1



Official



By
AsmaBaffa
Copy by Zainab Butalawa





MARCYCOOL and FLOWER page dinku ne na farko.









Zamfara state Cikin kauyen Nahuce, Dattijuwa ce Kyakyawar gaske Fara tas da ita baza ta wuce 40yrs ba tana zaune cikin Dan sakarkarin gidansu cikin wata jemammiyar atamfarta, cikin lalatacciyar Hausarta wacce tayi Kama data Igbo can kudu ta Fara kiran suna da karfi tana Khadija...Khadija baza ki Bari ba,wannan wanne iskanshi ne wannan Abu naka,ke ko yaushe burinka ka tafi neman Kudi,Kwangilar banza kwangilar wofi, baka da ko sisi naka,Abinshi da kyar muke samu muci Instead of u muyi Sana'a mu samu kudin rufin Asiri Amma ke Sha Sha Sha kice kudi kika nema kiyi da yawa Haka,a kauyen Nan da muka dawo ga Yara suna zuwa gona suyi grass ko Firewood su siyar su Samu kudi Amma kinki,kece babba kece babbar banza,Ga Babanku ya rasu dangi Basu kula damu,Ki nutsu mu samu mu tsira da mutuncinmu kinki ke Dole kudi me yawa kike bukata ba Kya son motsa jikinki.

Wacce aka Kira da Khadija ta turo Dan kyawawan lips dinta jajaye dasu tace yanzu Mama duk kokarin da nake ba Kya gani kullum fa a Rana nake yini Dan kawai na samo Mana na abinci ya kike so nayi,Nace da ke mu koma birni kinki,idan a birni ne Dole zamu samu aikin yi,ke Mama kamar Baki waye ba,kamar bamu zauna a Kudu ba Anambra state fa cikin birni muka taso Amma Mama ke so kike ayi ta aikin Wahala,wani aiki ne a kauyen Arewa in Banda na gona etc,Yanzu ki kwantar da hankalinki Mama na hada Yara kartai manya Almajirai Wanda Zan dinga samun Kwangilar aikin Gona sai na tafi da yarana suyi aikin Noman a biya mu kudi na cire nawa na biyasu kudin aikinsu,kudi za a samu Mama daga Nan har birni sai mu koma ko ya kika ce? Mama ta kalleta kawai tace Khadija ba dai surutu ba,Yanzu Taya manyan kartai zasu saurareki kina Yar 16yrs jibeki fa ki Kuma ba wani jikin girma ne dake ba sai iyayi da giggiwa,Murmushin da Khadija tayi har Dimple dinta suka loba.

Tace Mama Mantawa kike da wace Ni,Dan kawai kina ganina kullum a araha,Baki San Nan wa Kika Haifa ba,maybe Matar shugaban kasa kike tare da ita,Baki sani ba ko Matar Gomna ce ma kawai kiyi Addua Mama.
Dariya Mama ta saki ba shiri tace to Allah ya taimaka Khadija,yanzu je kiyi sallah kizo Kiyi aikin gidan Nan.

Ba musu ta dauki buta tayi Alwala tare da gabatar da Sallar la'asar tana Gama Azkhar ta fito daga rubabben dakinsu ta Fara share share da sauran ayyuka,Wurin 5pm sai ga Maryam wacce suke ce Mata Merry tare da kannensu Ihsan da Ahmad sun dawo daga Islamiyya suna Hey Sister Hey Mama suka wuce ciki tare da Tube Uniform dinsu suka fito wurin Mama dake hada Jallof din Taliya,Khadija data fito daga wanka kenan tace Merry How far? a dey wooo sister,a done tired finished, Go and fresh up jooo cewar Mama wacce ta tsege gogoro irin na manyan Matan Kudu.

Khadija kuwa English wear dinta tasa Riga da wando pencil sabo da girman kudu ne Basu fiye sa kayan Hausawa ba sai na turawa Yan gwanjo sabo da rashin sabo.
Da dare bayan sunci Abinci Sunyi Sallar Isha Allo suka dauka har Khadija suka tafi makarantar Allon dare ta kauyen.
Malam liman yace Khadija biya muji karatun naki, Khadija ta Fara nuna rubutun da tsinke tana Alu, ambaki,wau,zal,ba,Alu Baki,lallan hakuri,minjaye nu'ara,Aya,Alu lallan da shadda,Khadija na zuwa Kan Lallan da shadda ta Dago da sauri tace Hey Malam a Qur'ani har da Shadda tazo? Shi yasa take da tsada da daraja,Liman ya kalleta kawai yayi Murmushi sabo da Khadija Sam Bata gane karatun Allo kawai Yi takeyi ta haddace.

Bata yi Shuru ba tace Hakuri hhhhh ta sheke da dariya tace wlh bazan sawa Dana Sunan Nan ba ai gwara Na Sa Masa Nu'ara,Liman ya daka Mata tsawa yace Nan karatu ake ba gurin shiririta bane,kalli kannenki su ba ruwansu,Merry ce ta matso kusa da Khadija itama Ana biya mata, Akace lunguda Merry tace Lungu kawai,Khadija da Bata iya rike dariya sai ta kwashe da dariya tace liman Dan Allah ka fada Mana wannan ba larabci bane? Liman yace larabcine ainihin rubutun Amma Malam bahaushe ne ya fassara da Hausa domin ayi Saurin ganewa,haba yanzu naji zance Dole shadda ta fito a ciki,Bulala liman ya shaudawa Khadija ta saki kara ba shiri suka ci gaba da karatunsu da karfi Khadija ta Ware Murya ba gidan da baa jinta a makwafta,gashi hausarsu Sam Bata fita irin ta Igbo ce bakinsu ya canja.

Washe gari akwai wata Igbo Madam Ngozi da Dennis mijinta a kauyen Wanda suka zo kauyen tare da bude katafaran Shago na siyar da kayan kanti,ganin Maman su Khadija sun dawo garin,gasu wayayyu,sannan daga kudu suka dawo kauyen Arewa,sannan Har yaren Igbo suke ji sosai,shike Nan Arnan Igbo Nan suka Kulla zumunci da gidan su Khadija,sosai suke taimakawa su Khadija da kayan Abinci, yau Ma Madam Ngozi tana gidan su Khadija Suna Hira da Maman Khadija cikin Harshen Igbo duk da cewar Suma Ngozi sanadin zamansu a kauyen Shekara da shekaru sun iya Hausa sosai sai dai da kaji Sautin kasan ba Asalin Hausawa bane, Madam Ngozi tace Maman Khadija akwai wani yarona Babba a Enugu yace Yana so Musulunci,Yana son ya musulunta,Ni bana son musulunci Amma yaron ya dage ban san ya Zan Masa ba,Babanshi yace a kyaleshi ya musulunta to Ni gaskiya na hakura na kyaleshi ya musulunta Amma bana so yayi Almajiri,Su Mama me zasuyi ba dariya ba,sabo da tunanin Ngozi Almajiranta tana daga cikin rukunan musulunci,Kuma sunga yanda Almajirai ke komawa a kasar Nan shi yasa,Mama ce ta ganar da ita Mene Almajiri Kuma ta gamsu.

Yau da Sassafe Mama ta Kora su Khadija makarantar Allo bayan an Gama Karatu Khadija tana zaune Almajiran da ake kawowa daga kauye ne suke Bata Tausayi,Yan Yara kanana sabo da rashin Imani,iyaye baza su iya daukan nauyinsu ba,yaro da iyayensa Amma a kawoshi Wata uwa duniya yayi ta garari Yana wahala karshe ya lalace ya koma Dan fashi, Kidnapping,Dan Shirka,Dan Ta'adda etc,zuciyar yaro ta bushe da rashin Imani sabo da ya taso a wahala.

wasu ma marayune suna da dangi amma sai su kasa rikesu su turosu Almajiranta,sanyi ya Kare musu,Rana,ga wahala malamai suna Basu aikin wahala suna zaluntar yaran sabo da ba yayansu bane,Wasu yaran Kuma sun Riga da sun kangare a gida basa Jin magana,maimakon a Basu tarbiya a kula dasu ayi musu Addua sai iyaye su jefosu duniya suce a kaishi Almajiranta karatu ko zai nutsu,karshe basa karatun kirki sai wahala su Kara lalacewa shike Nan su Zama bala'i a kasa.
Sannan mutane ma idan akace wannan Almajiri ne to bashi da daraja a idon Alumma sadaka ma sai abincin da aka rage,ko ya lalace za a Basu,ko a sasu aiki a ki biyansu hakkinsu,Idan yaro yayi magana ace ai Almajiran yanzu Basu da kunya Basu da mutunci baza a Basu Dan Allah ba,ya kamata iyaye musamman na kauye mu Gyara damu Alumma a taru a gyara.

Yaro Yana karami yake Fara koyon shirka,burinsa ya samu Hajiya Yana kawo Mata rubutu tana bashi abinci etc.
Khadija tana kallon wani Dan yaro karami Yana Bata Tausayi baifi 7yrs ba Yara suna ta tafiya makarantar boko har yaran Malam din duk sunyi Shirin makarantar boko Amma Almajiran su Babu dama Sai Malam ne ma yake hada kansu zai kaisu gonarsa suyi Masa aikin gona,wasu Kuma ya fito musu da manyan itace zasu fassakarawa matansa na girki,Haka wasu sun kwashi wankin matansa sun tafi Rafi,wasu Kuma sun tafi aikin karfi na gini zasu samo Masa kudin cefane sabo da me? Iyayen da Suka bashi yaransu ya koyar dasu Basu tallafawa malamin da kayan Abinci ba bare ya kula da yaransu.

Makarantar boko kudi ake tsugewa a biyawa Yara Amma na addini sai ace kyauta,Malam ya kashe lokacinsa na neman Kudi ya koyar da Yara Amma an Hana shi sisin da zai ciyar da iyalansa Dole yaranmu susha wahala a wajen Malaman ba a biyansu ko a taimakesu da abinci kawai Dan karatun Addini ne sai a ce kyauta.

Khadija tana mamaki Yaran da zasuyi faskaren Basu Fi 10yrs ba, da kyar suke daga gatarin,sun hada zufa,ko daya Basu faskara ba,Ado ne Dan gidan Malam zai tafi makarantar boko daya cikin Almajiran yace Dan Allah Ado jeka gida ka dakko Mana wani gatarin me kyau wannan Bai da kyau muyi sauri mu Gama Kar Malam ya zanemu,Kallon Banza Ado ya musu yace Baku Isa ba na makara a schl kuje Yan wahala ku dakko da kanku Mana ai Kuna shiga gidan,ya tuka kekensa ya bar wajen,Haka daya yaron yaje gidan ya karbo gatarin sukaci gaba da yi Amma sun kasa komai,Khadija tana gefe tana kallonsu cike da tausayinsu.

Malam ne ya fito daga dakinsa Wanda yake saukar mutane da suke Masa layi wajen karben rubutu da layoyi na maganin asirinsu,zagin yaran ya farayi Yana shafda musu bulala Basu faskara ko daya ba,Khadija tayi sauri ta Karasa wajen tare da fisge bulalar daga hannun Malam da lalatacciyar Hausarta Wanda watarana ma sai ta kasa fadar Abu da Hausa sai da turanci ko yaren Igbo,watarana Kuma sai tayi tunanin kalmar da Hausa kafin ta gano ta fada tace haba Liman, Imani Babu? Ina yaranka gasu can manya sun tafi schl boko shine zaka duka wannan yaron Mena suka maka? Kai wlh baka da Imani Malam,Foolish man ne kai,Liman yace Ke Dan ubanki ko ubanki Adamu Bai Isa ya fada min Haka ba bare ke Arnan banza.
Khadija da karfi tace ewoooo wonder shall never end so you call me Arna Dan burauba shege,Har ga Allah Khadija tunaninta bakar maganace tayi da Hausa ba zagi ba, liman yace sai Naga gatanku a garin Nan tunda Kika shiga safgata wlh ke da aure sai dai kiga anayi sai kin tsufa a gida,sai kinyi Shekara Arbain Baki auru ba Zaki san Ni Kika zaga,Ina liman guda me daraja a kasar Nan har ki iya dura min Ashariya Haka tunda nake ko kallon banza ba'a taba yi min ba sai ke.

Sai kinyi bakin jini wurin Mata da maza,Babu inda za a so ki,sannan gaba daya zuriarku kun dinga shiga matsala kenan har abada,Khadija tace Kaine Allah? Baka Isa ba Malam tuni zanyi aurena kana Nan kauye,Kuma Wanda Zan aura sai kayi mamaki,sannan sai na kawo ma Mijin har Nan kauyen,Kuma kudi zamuyishi Animal fool an daina zuwa makarantar taka local man kawai,Malam yace ko kunzo ma bazan koya muku ba me kuka sani Yan iska masu yawo da tsangalallun kaya Kika sake cancer ce ajalinki shegiya me Jan kunne,Nasara bayahudiyar banza,Khadija tace gwara Ni kaifa kazami...kazami,see your face like Gost,kuma kasan in this whole village Babu me kyawunmu har city birni sai an duba anyi waca waca (sai an tona take nufi) za a samu kamata,kalleni like oyubo obodo kamar Baturiya Amma matanka fa Nono nasu Haka like slifas me kake tabawa,Babu Hips ko kadan Babu kalla nawa Katuna katuna Khairat ta juyawa Liman mazaunanta maka maka dasu,Liman ya hadiyi yawu,tace ka daina Hadiye saliver naka ba samun kamata zakayi ba.
Liman yace Zaki gani jeki,Khadija ta juyo tace sai na tona ma asiri kana Tara mataye a dakin can kana iskanci dasu kana Basu magani,wallayi (wlh)idan banyi aure ba sai na kawo police sun kamaka trust me stupid Khadija ta tafi gida da tsangalalliyar rigarta,Khadija sun koyi halayen yaren kudu na rashin Jin nauyin fadan ko wacce magana,sannan ga ba rufin Asiri,magana Kuma da karfi sukeyi musamman Khadija da Bata ji,gaba daya aladunsu na Yan kudu ne,Sam in ka gansu zaka ce ba musulmai bane sai dai shegen kyau kamar dama sun hada jini da labarawa domin Mama kwarori ne,Babansu Kuma Asalin bafulatani ne.

Liman kuwa wajen me gari ya wuce tare da fashewa da Kuka ya sanarwa me Gari abinda Khadija tayi Masa,Me Gari dake liman Yana Masa asiri iri iri sai yace Kar ka damu Liman dama Dangin nasu Mutum biyu ne fa ka manta ambaliyar ruwa duk ta Karar da danginsu kaf,korarsu a garin Nan ba komai bane kaje karka damu dama sun ishemu suna gurba ta Mana rayuwar yaran Gari da shigar banza Tubabbun banza wani musulunci sukeyi na kirki,ai indai akace maka ba bahaushe bane to ba wani musulunci sauran mutanen ke yi cewar Liman.

Khadija kuwa tana zuwa gida ta kwashe labari ta fadawa Mama abinda ya faru,Mama tace Allah ya fisu kyalesu,Washe gari Mama taje ta Saro manjan da take siyarwa,ita Kuma Khadija tana can cikin mazan data Tara duk zasu Kai 20 to 19yrs suka tafi gona tare tana inuwa su Kuma mazan suna cikin gonar suna noma Wanda Khadija ce ta Nemo aikin a hannun wani kansila na kauyen sannan kudin da za a biyasu ma Khadija ce ta fada.

Sai Magrib suka Gama aikin yayi Masifar kyau Khadija tana zaune a inuwa sabo da ita burinta komai ace itace shugaba,kudin aikinsu Kansila ya Bata, ta cire ba cuta ba cutarwa suka raba da samarin Nan Amma nasu duk yafi nata yawa sabo da su sukayi aikin,itace dai tayi kurda kurda ta samo aikin.

Tana dawowa Mama ta ganta futu futu duk farar fatarta tayi furu furu,Zama tayi tare da mikawa Mama dubu biyu ta Bata labarin aikin,Mama tace ewooooo ashe dai Kwangilar Nan da gaske ake yinta ga harka ta Fara budewa,Af Danma ba a birni muke ba na fada Miki,Ina da Yara Kwangila kawai Zan na karba Ina wurin ayi aiki a biyani,Duk wani aiki Zan iya Mama matukar Zan faranta muku ke da kannai na.
Mama tace well-done my Daughter Allah Kara budawa,May God Continue to bless u my Daughter, Khadija tace Ameen Mama, Mama taci gaba Allah ya kawo min Miji na Gari na aura Wanda zai dauki nauyinmu Baki daya,Nan take annurin Khadija ya gushe cike da Shagwaba tace wlh baza kiyi aure ba,Dan Daddynmu ya rasu shine Zaki auri wani Dan Iskan,Allah idan Naga wani yazo zance to sai na zuba Masa ruwan zafi,Baki bude Mama take kallon Khadija,ta samu Miji da dama Amma Khadija ce ke hana auren,sai ta San yanda tayi ta Kori bazawarin,Mama tace wlh Bari kiji Khadija Ina samun miji aure zanyi ko mutuwa zakiyi,Baki Khadija ta turo gaba ta shige Bedroom tana kunkuni,Suma su Merry bayan Khadija suka bi suna kishin ubansu.


Gidane katafaren gaske estate gudane,Unguwa guda ne gidan part part ne Babu adadi a gidan,part din kowanne ya Hadu karshe yaji kayan Alatu,Babu abinda Babu a gidan irin na more rayuwa,gidan kamshi da kyalli kawai keyi maaikata na sintiri ta ko Ina,kowa da irin aikinsa,ga securities ko Ina Ana tsaro,garden da sweeming pool bangarensu daban a gidan.

Mami Pls kuyi sauri mu Isa Airport jirgin Ya ABDALLAH remain 5mnt yayi Landing Kuma kin San Ya Abdullah Bai son jira yau duk sai munci ubanmu a gidan Nan idan ya jira a Airport ba a zo daukansa ba,Mami tace ke karki yiwa Dana Sharri tuni securities sun Isa Airport Daddy ma Yana can tare dasu.
Cikin shiga ta Alfarma Dattijuwar daga ka ganta kaga marar mutunci tun a fuska tare da yaranta Afrah da Islam suka fito suna zuba kamshi,parking space suka Karasa inda iya kallonka motocine masu tsadar gaske iri iri ta ko Ina,Wasu Yan Mata ne da samari wasu suna shiga mota da Alamar fita zasuyi wasu Kuma sun dawo,wasu Kuma gasu Nan kowa da abinda yake, ganin su Afrah da Maminsu yasa aka fara gulmace gulmace Ana musu Habaici Ana Harare Harare,itama Mami da yaranta Basu fasa ramawa ba suna Maida martani da gani kasan ba a shiri da juna,itama Mamin da take Babba cewa tayi ki sharesu shegu yaran matsiyata,Alhaji shi ya jawo Daya kwaso iyayensu ya auresu,gida kamar kasuwa tsaki taja cike da Izza suka shige katafariyar mota Yar yayi Driver yaja su suka wuce airport.

Mami kyakyawar gaske ce ka rantse balarabiya ce Haka ma yaranta suke wannan na wane wannan a kyau sai Rashi kyan hali.
Suna karasawa Airport wani azababben Guy ya sakko daga steps din jirgi Yana janye da karamar Trolley dinsa ta Yan gayun gaske,Sanye yake cikin wata tsadajjiyar t-shirt silver color,da wando jean fari Kal pencil, rigar ta wuce Masa zuwa cinya ta Dan Zobe daga baya kalar ta mawakan turawa,hannunsa wani zoben azurfa me azabar tsada,ga agogonsa Gucci,Haka takalminsa ma fari Kal kamar canvas me shegen tsada Haka yake sai dai an budeshi ba a daure zaren ba ya wani bude kamar wani Justin Bieber zaiyi Waka,Sumarsa irin ta Larabawa baka wuluk Tasha wani aski na iban albarka,an kwashe gefe gefe kadan tsakiya daga gaba an tarata da yawa sannan an yarfota saman goshi tayi wani gaba kamar zata rufe Masa Ido,kowa kallonsa akeyi Dan ka rantse wani mawakine daga kasar London ya sauka a kasar,Amma fa ya Hadu karshe ta ko Ina Babu Wanda ya Isa ya kalleshi Bai Kara ba sabo da Masifar kyansa,gashi fari wani jajir dashi,da Dan sajensa kadan da gemu kuyas, fuskarsa ba me Fadi ba, ba ku ma me tsayi ba,Hancinsa Wai zarkadi kyan hancinsa ya baci,idanuwansa madaidaita lumsassu farare Kar Kar,girarsa me yawa,Haka gashin idonsa,komai nasa me kyau ne,shi ba me tsayi ba ba Kuma gajere ba,ga jikinsa dai dai babu kiba ba Kuma ramamme ba.
Wani taku yake na zaratan matasa Yan gayu,lips din Nan nasa masu kyau jajir dasu yake wani tsotsa Yana tauna Chewgum a hankali idan ba kula kayi ba baza kace tauna yake ba.

Wani Masifar gadara da yake abin ba acewa komai ga bala'in iyayi da jiji da Kai da yakeyi abin sai Wanda ya gani,Afrah da gudu taje tare da fadawa jikinsa,kamshinsa ya cika wajen.
Da sauri ya janyeta a jikinsa Yana hararata Yana Dan Murmushi kamar Dole yace Ke Zaki Samin Dirty,Baki bude suke kallonsa har Mami Amma sun San halin kayansu zai aikata me Hali baya fasawa.

Mami ya mikawa hannu tare da rike Hannunta sai Kuma ya rungumeta Yana Dan Murmushinsa da Bai Kai cikin cokali ba a hankali yace Ina wuni Mami,ya gida? Lfy tace Son wannan wanka Haka wlh ban ganeka ba,Haka ka koma ka girma,ka ganka kuwa Abdallah, dariya kawai yayi Wanda mutane da dama maza da Mata sai da suka lalace wajen kallon wannan hadadden bawan Allah yafi uban kowa kyau duk gidansu albarka,ko a turai sai an tona samun kamarsa.
Islam wacce Bata Fi 10yrs ba ya dauka tare da dagata sama suna dariya yace cutie How u? I'm Good Bro,wurin Daddy ya nufa har kasa ya rusuna tare da gaidashi suna farin ciki gaba daya suka rankaya zuwa katafaren gidansu.

Tunda motoci suka tsaya a gidan Mutanen gidan bataliya guda kowa ya fito ganin gulma da tsegumi,har ta saman bene kowanne part Matan Yara da manyan tare da iyayensu Ana ta leke Ana tsegumin Abdallah.
Bayan Abdallah yaci abinci ya huta wanka yayi tare da fita ya shiga part part dake gidan Yana gaida matayen Babansa da yaransu suna amsawa,Yana fita za a fara gulma,Suma Su Mamin hakan take da yaranta Mata sai cewa suke wlh Dan Abdallah ne marar zuciya da mune ko part dinsu bazan kalla ba,Mami tace kyalesu Afrah a Haka zasu Kare na gaba yayi gaba,Can Kuma sauran suna cewa har ya fada Mana turai,muma yaranmu duk sunje can sukayi karatu me za a nuna Mana,ga yaron ma ya dawo a Dan iskansa,jibi askinsa wasu suce Wai su masu kyau shuwa Arab su fa Basu yarda ba Larabawa ne.

Mami Kuma da Afrah cewa suke yo mu da muke jinin arziki su kuwa duk matsiyata Daddy ya aurosu,ai wlh tukunnama sai sun ga matar da Abdallah zai aura,Ummi tace wlh kuwa Yar attajiri jinin sarauta Yar sarkin Ethiopia ga kyau ga Naira,Ai Mamanta ma ta Matsu ya Gama Masters Azo a Fara Maganar aure kwarya tabi kwarya,Dan Ma Abdallah banza ne Wai Humaira dince baya so to wlh sai ya aureta ko Zan tafi tsirara,Allah ya kawo Mana Dangin arziki zai watsa min kasa a Ido,Afrah tace karki yadda Mami Dole ya aureta,Mami tace kwarai ma kuwa yanzu ai ba a auren talauci,kana me kudi sai me kudi talaka sai talaka,Dana ya auri Yar Malam Shehu ai naji kunya,burina duniya tasan da zamana,so nake duniya tasan Dana ya auri Yar manya.

Mami Haka take ta kuri Babu ko sa Allah a ciki,duk abinda zaka dinga kuri ka Dora ranka Kai ba ruwanka da Allah to kuwa Allah zai iya kunyataka a idon duniya,Haka Kuma zai iya kyaleka ya baka abinda kake so ba ruwan Allah.

Garin Zamfara kauyen Nahuce Liman fa ya dukufa ya dage Dole sai yaga bayan su Khadija,tsafe tsafensa yake tayi akanta yarinya karama sabo da rashin Imani.
Khadija kuwa ta dage sai Kwangilarta take nemowa da yaranta suna aiki sosai,Haka Allah yake ko yaya kayi Abu idan yaso ya dafa ma sai asha mamaki,Khadija da kudin take ci dasu tufatarwa da kudin makaranta wa kannenta,Mama Sai mamaki takeyi kamar Wasa ga Khadija kuwa ta Zama 'yar Kwangilar harkar Noma, tayi katon asusu Ana Tara wasu kudin,ga samari yanda suke tururuwar sonta sabo da tsananin kyawun Khadija,indai kyau ne to a shafa Fatiha kawai a kanta,ga kyan sura da diri,skin dinta wata sumul sumul kasancewar babarsu Yar north Sundance farare ne kwal,Haka Babansu farin bafulatani ne,Khadija round face ne da ita,da hancinta madaidaici baiyi tsini da yawa ba,Idanunta Dara Dara,ga gashi har baya kusan tsakiya,hakoranta kanana kyawawa,ga dimple,girarta me yawa baka,Gata da uban Hips cinyoyi manya,gata da Da tsayi Amma ba can ba,kowa yaga Khadija yasan ta cika mace ta gaban kwatance,Haka su Merry ma kannanta kamar su sukayi kansu kyawawane sosai gwanin Sha'awa.

Khadija sabo da zaman kudu rawa wajenta kamar mazari Kuma na Yan kudu takeyi ayi ta girgiza mazaunai,a wani duka kasa tare da rike gefen Riga Babu kunya ko a gaban uban waye Haka suke rawa har Maryam Merry,A kauyen Khadija tana da kawa Abu,Abu yau tazo gidan ba Islamiyya ta samu Khadija da Merry har Ihsan tare da Ahmad sun kunna gidan radio an Sa wakar Wizkid suna ta tikar rawar suna ihu eh...eh...eh...sun cika gidan,yanda Khadija ke rawar zanku kamar kanwar Zlatan,Mama tana aikinta dake itama kudu ta ratsata sai cewa tayi Abu Bismillah ga rawa fa kiyi kema,kunya ta Kama Abu tace ban iya ba,Khairat ta wani duka tana eh....eh...chineke God ah...ah...we dey chill woooo let's dance Abu,Common eh...ehh Merry ma ta jawo hannun Abu Wai sai tayi rawa.
Mama tana kallonsu tana dariya harda gyarawa Ahmad rawar tana kalli yanda Khadija keyi maza ka koya kaima,Abu ta bude Baki Jin yanda Mama tace kunya ta rufe ta.

WRITTEN BY:    ASMA BAFFAH

NOVEL NAME:   TUBABBIYA COMPLETE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         463KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      16- MAY -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            ₦300

Proceed To Download Tubabbiya Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

KARANTA LITTAFIN: “TUBALI BOOK 1 CHAPTER 1”

KARANTA LITTAFIN: “TUBALI BOOK 1 CHAPTER 2”

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button