Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 8 Complete Novel

Matar Damisa Book 1 Complete Document

๐Ÿ… MATAR DAMISA๐Ÿ…

(The Wife Of Tiger)

MALLAKIN
ASMEETAH โœ๏ธโœ๏ธ

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu}}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ

ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ21 to 22

Ayush! Ayush!! Ayush!!! Cikin sassanyar murya ake kiran sunan nan, ita kuwa Ayush tana kwance akan carpet kuka yaci ranta taji ana kiran sunanta kamar daga sama, dakatar da kukan tayi tana sauraron kiran da ake mata, sautin zazza’kar murya ne yake dukan kunnenta a hankali take d’ago da kanta wani irin hajijiya ne yake d’iban ta a haka ta tashi zaune!

Download>>>ย Auren Karin Kasa Book 1 Complete Document

Da dara-daran idanuwanta wad’anda sukayi jawur ta d’agosu ta kalli yanda sautin sunanta yake fitowa, cikin firgici taja da baya ta zaro manya-manyan idanuwanta waje tsoro ne ya kuma bayyana akan fuskarta, baki na kakkarwa ta ambaci “Umaa” abunda ya fito daga bakinta kenam tana kallon gurin da wata zankad’edd’iyar mata take tsaye, tana sanye da fararen kaya daga sama har ‘kasa ta rufe doguwar suman kanta da farin mayafi, da murmushi a kan fuskarta…
Ayush ce ta sake motsa baki tana fad’in “Umaanah” tana kuka kuma tana had’awa da dariya tayi farin cikin ganin mahaifiyar ta a wannan Daren misalin karfe 2:00
Itama Uman da murmushi a fuskarta cikin sanyayyar murya tace “Yarinyata nazo gareki ne domin na tunasar da ke abunda kika manta a baya, ki kasance mai taimakon al’umma idan kika fuskanci suna cikin wani irin hali, kada ki dubi girman laifin da mutum yayi miki idan ya bu’kaci taimakon ki kawai ki taimake shi kema wata rana idan kika shiga wani hali Allah zai taimake ki, kada ki tsani bawa! kada ki cutar da bawa!! kada ki bari ata sanadiyarki a cutar da bawan Allah, Ayush d’iyata! ‘Dan uwanki yana bu’katar taimakon ki kije ki taimake shi kada ki damu Allah yana tare da mai hakuri, kije ki, ki je ki taimake shi……..!

Download>>>ย Kuskure Na Complete Document

Tana kaiwa karshen maganar ta 6ace 6attt.
A firgice Ayush ta tashi zaune tana fad’in “Umaa! Umaana!! Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, mafarki Ayush tayi kwanciyar da tayi tana kuka ashe bacci 6arawo yayi awun gaba da ita, zuwan da mahaifiyar ta tayi acikin mafarki ta zo mata.
Ta waiwaya ko Ina bata ga kowa ba ga hawayen da ya bushe mata akan fuskar “tabbas mafarki nayi, Uma tazo mun” a lokacin ta fara tariyo maganganun mahaifiyar tatan lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, Junaid ne ya fad’o mata a rai “Uma mutumin da ya rabaki da rayuwarki shi kike so na taimaka?” Kuka ne ya kwato mata sai wani tunani yazo mata a cikin zuciyarta take fad’in “Mahaifiyar shi ta taimake ni, ba don ita ba bansan Ina zan nufa ba, shin itama tana raye ne ko ta mutu? Tabbas suna bu’katar taimako a wannan halin” ta mi’ke tsaye cikin sauri lokaci guda kuma ta tsaya cakk
Alamar ta tsaya tunanin wani abu “amma meyasa naga shi wannan mutumin a manne da jikin gini ba tare da an d’aure shi ba, kuma jikinsa a faffashe kamar ma ya mutu”… ‘Kirjinta ne yayi wani irin bugawa ta zabura da gudu ta nufi hanyar d’akin takawa d’aya biyu taji kamar an ri’ke ‘kafarta ta doku a ‘kasi danma carpet ne mai gashi da tunin taji ciwo,
Tana shirin d’agowa kunnuwanta suka jiyo mata kukan mujiya ๐Ÿฆ‰๐Ÿฆ‰ mai firgitarwa a tsorace ta kalli saman cilling yanda ta jiyo kukan kenam, wutar nepa gidan ne ya d’age sai duhun daya biyo baya ko hannunta bata iya gani wani irin tsoro ne yabi jikinta, kamar daga sama tajiyo wata ‘katuwar murya ana cewa “AYUSHHHH KADA KI KUSKURA KI TAKA ‘DAKIN NAN, WANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA ZAKI TAIMAKA? TO LALLAI KEMA ZAI KASHE KI KAMAR YANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA, KIYI TUNANI SHI BA MASOYINKI BANE MAKIYINKI NE, YANA NEMAN AHALINKU NE DOMIN YA GAMA DA RAYUWAR KU GABA DAYA HAHAHAHA, HAHAHA, HAHAHAHA haka ta ringa jiyowa dariya marar dad’in ji,
Jikinta ne ya hau 6ari murya na kakkarwa tace “waye Kai?”

Also Downloadย FARRAH Hausa Novel Complete Document By Maman Shuraim

“NIIII MAI BAKI KARIYA NE, still ya ‘kara tintsirewa da razananniyar dariyar shi mai ban tsoro….
Lokaci guda kuwa haske ya bayyana ta daina jin kukan mujiyan.
“Innalillahi wa inna’ilaihi raju’unnn wannan wani irin bala’i ne a cikin gidan nan, Aljanu da mutane duk suna rayuwa a gidan nan” zuciyarta ne ta soma magana kamar haka “Ayush kar ki manta wannan Addu’ar da malamin nan ya koya muku ke da mahaifiyarki” anan ta tuno da Baba tsoho wanda yayi hijira zuwa dajin da suka zauna yayi tsawon shekara biyar atare da su, Babban malami ne na gaske shi ya koya musu karatun al’qur’ani mai girma tare da addu’oi ya koya musu alwala da yanda ake sallah su wankan janaba da haila ba abunda bai koya musu ba ta 6angaren addini, Ayush lokacin bata wuce 15yrs ba ita kuma mahaifiyarta tana ‘kara koyan karatun ne domin wad’annan karatuttukan mahaifin Junaid ya koyar mata su tin suna GHANA.
Damuwar dai Ayush ta samu ta koya duk da itama tana koya mata wasu abubuwan!!

Anan tayi firgitt ta soma jero manya-manyan addu’o’i….

๐Ÿ‘‰. “Allahumma laa sahla illaa maa ja’altahu sahlan wa anta taj’alul hazna izaa shi’ita sahlan”
(Yaa Allah! Babu wani abu mai sau’ki sai abin da ka sanya shi ya zama mai sau’ki, kuma Kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sau’ki)

Karanta>>>ย Yar Harka Romantic Hausa Novel โ€“ Aihausanovels

“‘Kadrul laahi wamaa shaa’a fa’ala”
(Kaddarar Allah ce, kuma abin da Allah ya so, shi ne yake aikatawa, domin da-na-sani tana bud’e ‘kofar aikin shaid’an).

“Laa ilaaha illallaahul aziimul haliimu,
Laa ilaaha illallahu rabbul arshil aziim,
Laa ilaaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kariim”….

Bayan ta kammala addu’o’in ta ta shafa ayatul kursiyu, duk wani tsoro da fargaba da ‘kuncin zuciya ya wuce mata ta ‘kwarin gwiwarta ta mi’ke tsaye ta nufi d’akin da ake bu’katar taimako!

Upstairs ta fara takawa a hankula har da iso bakin ‘kofar d’akin tasa hannu zata ture d’akin…
Aka daka tsawa “kada ki kuskura ki bud’e” amma kash duk wannan maganganun kunnen Ayush ya toshe bata jin maganar
Tana bud’e d’akin kuwa wani irin duhu ne a d’akin babu haske kwata-kwata tana shiga d’akin haske ya bayyana ta ko Ina, still yanda taga mutanen nan a kwance haka ta same su
Ta d’aga kanta ta kalli yanda Junaid yake a manne a jikin gini ganinsa yasa ta tsorita naman jikinsa duk ya farfashe ciwon yanzu yafi na d’azu hakan na nufin har yanzu basu daina azabtar da shi ba,
Girgiza Kai tayi tana maganar zuci “bazan iya kusantar ka ba, ka rigada ka mutu”. Toilet ta nufa ta d’auko bucket da ruwa a ciki duk bodyguard d’in da suke kwance ta bisu da ruwa tana kwakwkwara musu cikin sa’a kuwa suka tattashi a firgice suna ajiyar zuci, bayan sun dawo hayyacin su kowa rige-rigen fita yake daga cikin d’akin har mai gadin!
Ta dawo kan Mommy itama ruwa ta yayyafa mata, ajiyar zuciya tayi tana Jan numfashi sama-sama tana ambaton “Junaid! Junaid my son, ya mutu ko? Kamar wata zararriya haka take magana tana bin Ayush ta kallo, mommy bata san waye akan ta kawai dai tana sambatu ne,
Ayush ta tsaya tana tunanin aina ta ta6a jin sunan nan!

Karanta>>>ย Furar Kashi Chapter 1 By Billyn Abdul

Tana cikin wannan tunanin tajiyo kukan mommy ya tsananta sosai tana kuka tana nuna gurin da Junaid yake da yatsanta, kafin kace mai Mommy ta tashi da gudu tayi kan Junaid
Da karfin gaske aka hankad’o mommy baya da sauri Ayush ta tareta badon haka ba fad’uwa ‘kasi zatayi.
Lokaci guda idon Mommy ya ‘kakkafe ta dafe ‘kirjin ta tana shure-shure ciwon zuciyar ta ta tashi,
Ayush ta tsorita sosai da ganin haka da kyar ta iya d’ago Mommy suka fita daga d’akin
Falo ta nufa tana zuwa ta tarar da bodyguards duk sunyi cirko cirko kowa yaji jiki sai ajiyar zuciya suke sau’kewa
Da sauri sukayi kan mommy
‘Daya daga cikin bodyguard ne ya d’aga mommy cakk yayi waje duk sauran ma binsa sukayi a baya
Motor suka shiga gaba d’ayansu
Motor biyu suka d’auka
Biyu suka shiga d’ayan motor and order car shima mutum biyu a ciki,
Kafin one minute sunbar harabar gidan, iya Ayush da mai gadi kawai aka bari a gidan, da sauri Ayush ta nufi gurin mai gadi tana fad’in “Ina zasu Kai ta?”
In short amsa mai gadi ya bata “Asibity” yana fad’an hakan ya shige cikin d’akinsa zallar tsoro ne a tattare dashi…

“Anya kuwa ba Aljanu a cikin d’akin nan? Junaid kuma? Uma ta ta6a bani labarinta akan Junaid, a’a ba wannan Junaid bane, to aina Zan samu Junaid d’in da Uma take so na taimake shi??
Waye wannan Junaid d’in? Innalillahi wa ina’ilaihi raju’un shi na gani acikin mafarki na idon sa kamar na namun daji,
A’a sharrin mafarki ne bashi bane……
Haka ta rin’ka sa’ke-sa’ke a raanta!…

 

Click Here To Read Matar Damisa Book 1 Chapter 9 Complete Novel

(KASHH HABA AYUSH KIJE MANA KI TAIMAKI JUNAID MIJIN ASMEETAH ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ )

Yawwa dan Allah masoya kuyi hakuri a bisa jinkirin da ake samu waran yin posting, ba NEPA kullum chaji 100 naira, still i’am a student Ina bu’katar yin karatun exam, still I’m married not a single Ina wasu ayyukan gida da kuma Oga worker ๐Ÿ˜…๐Ÿ˜…๐Ÿ˜…๐Ÿ˜…. Hhhhhh amun uzuri please ๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™

*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*

*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

Back to top button