Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 61 Complete Novel

*ASM Bk2061*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
…….bayan su Aunty Mareeya sun fito saida suka koma part d’in Hajiya suka k’ara yi mata Allah yasa Alkhairi sannan sukai mata sallama tana ta godiya duk aka fito harda su inna Zaliha da tun d’azu suka so tafiya Hajiya tace su bari za’a maida su gwaggo ta biyo su tace suje gida don Allah zata basu kayan biki, Motar Saleem Abbas yace su Aunty Mareeya da Feenah su shiga gwaggo ma ta shiga shi kuma ya d’auki su inna Zaliha da iyalan baba shehu sai wasu abokan aikin gwaggo da suka rage su biyu, a daidai kopar gidan su Fatuu suka tsaya gwaggon ta shiga ta d’ebo ma kowannensu su cin cin harda man shanu, bayan ta kawo masu suka yi sallama tana ta godiya tace ma Fauzy saura ta daina ganin ta tunda k’awar ta ta bar gidan tana yar dariya tace a’a zata rink’a zuwa har weekend ma zata rink’a zuwan mata, sosae gwaggo taji dad’i tace to Allah ya bada iko suka tafi tana ta k’ara godiya tare da d’aga masu hannu, saida sukai nisa sannan ta koma ta kullo gidan ta nufi gidan Hajiya don bata yi mata sallama ba ta taho, tana tafiya tana tunanin autar ta sai murmushi take wani lokacin ta d’an girgiza kai, har ta fara jin kewar ta tana son ta gan ta saidae ba dama don bazata iya zuwa part d’in ba a yanzu.
Feenah aka fara ajewa gida don tafi kusa tay ma Saleem d’in godiya sukai sallama dasu Aunty Mareeya har tana fad’in taga gida zasu rink’a zumunci in sha Allahu tace to shikenan ta gode, dama sun yi musayar lambar waya tun a gidan su Fatuu kafin akai ta, daga nan Goriba road suka nufa aka kai Aunty Mareeya, bayan ta nuna mashi gidan ya parker tay mashi godiya ya jinjina mata kai ba tare da ya ce komae ba ta bud’e kopar ta fita Fauzy dake a gaba ma ta fito bayan sun rufe mashi kopopin yaja ya tafi, tsaye Aunty Mareeya tay baki bud’e tabi bayan Motar da kallo kafin tace “da alama shima wannan lalurar gare shi” kallon bayan Motar da har tayi nisa Fauzy tay kafin ta juyo ta kalli Aunty Mareeya cikin rashin fahimta ta tambayi wace irin lalura gare shi, tace “irin ta mijin Zarah mana, daga gani shima miskili ne na gaske” yar dariya Fauzy tay “na lura da hakan don ko d’azun da za’a kai Zarah da muka hau Motar shi bai ce ma kowa uffan ba sai d’an Music da ya kunna sama sama” Aunty Mareeya dake kallon ta tace “da gani dai wani shege ne ko kuma d’an wani shegen shiyasa harda rufe lambar Mota, baice yana son ki ba?” ta kafe Fauzy da ido alamar jiran amsa, dariya Fauzy tay “taya zai ce yana sona na fad’i maki tunda muka hau Motar shi bai ce mana uffan ba, kema ba gashi kin gani ba har kin fad’a” k’wafa tay tace “Allah ya yabawa aya zak’in ta, ai da ya sake yace yana son ki har abun ya kai ga aure da an taimaka mashi an sashi ya rink’a magana shima yadda za’a sa abokin shi, Allah sarki Zarah….” Murmushi tay kawae bata ida abunda zata ce ba ta nufi gate Fauzy tabi bayanta acikin ranta tana tuna k’awarta Fatuu dama tunda suka baro ta ta tsaya mata a rai, a yanzu kuwa sai taji ta fara sha’awar yin aure itama.
Gwaggo na isa part d’in Hajiya a parlor ta same su kaman yadda ta barsu ita da Saude sai dae ita Sauden tana kitchen tana yin girki musamman don su Fatuu kaman yadda Hajiya ta bata umarni, zama gwaggon tay Hajiya tace har ta sallame su tace mata eh suka d’an ci gaba da yin hira suna kallo, can gwaggo tace bari ta tafi sai Allah ya kaimu ta k’ara yi mata godiya da Addu’oi, tana k’ok’arin mik’ewa Hajiya tace ta tsaya zasu je wurin Zarah yanzu sai suje tare tasan dae bata rasa mararin son ganin ta, cike da Zolaya tay Maganar gwaggo dai d’an murmushi kawai tay ta sadda kai, bada jimawa ba Saude ta shigo cikin parlon hannunta ruk’e da wani had’add’an basket mai d’auke da k’awatattun Warmers, a gefen kujera ta tsaya cike da girmamawa tace ma Hajiya an gama, kokarin mik’ewa ta fara yi tace ma gwaggo suje itama ta mik’e, har zasu tafi tace ma Saude taje saman gadon ta towels na nan da aka manta ba’a saka mata a kaya ba ta d’aukko a kai mata tace to, bayan ta dawo ta d’auki basket d’in d’ayan hannun rungume da towels d’in da ta d’aukko suka tafi. Tun bayan da su Fauzy suka tafi ta kife fuska tana kuka sai da ta d’an d’auki lokaci a haka sannan ta d’ago idanunta duk kwalla tay zuru tana d’an kalle kallen d’akin, can ta kai hannu ta cikin ledan da Aunty Mareeya ta bata ta fiddo abun da ke ciki, bata gane ko miye ba saida tasa d’ayan hannun ta bud’e sannan ta ga ashe rigar bacci ce orange colour ta dai had’u ba karya yadin ta gwanin santsi irin mai bin jiki d’in nan kuma bazata wuce guiwa ba tana da d’an fingilallan pant mak’ale a jikinta, ajeta tay gefe ta zazzago sauran da ke ciki guda biyu, d’aya baby pink ce shara shara wannan da k’yar ta wuce mazaunan mutum irin wadda in aka sa a naked za’a ga mutum har saida Fatuu ta d’an bud’a ido ganin rigar, d’ayar ta karshe cream ce yadinta cotton ne mai dad’in tabawa gwanin taushi daga wurin wuyanta da k’arshen hannun ta da zai iya wuce guiwar hannu duk gashi gashi ne gazar gazar yana d’an walwali harda ribbom gareta, itama tana da pant sai dai gabanta a bud’e yake kawai yan igiyoyi gareta wuri ukku da zaka daure, har saida Fatuu ta d’an sauke ajiyar zuciya fuskarta a d’an kwa6e take bin rigunan da kallo ita kam bata jin zata iya amfani dasu a yanzu gani take zai iya mata kallon mara kunya, maida su tay cikin ledan ta d’an yi jimm can kuma ta mik’e ta nufi wardrobe don ta 6oye su a ciki, saidai duk yadda tay ta bud’e wardrobe d’in ta kasa ta rasa ta ya ake bud’eta don bata ga wani handle da zaka kama ka bud’e ba a jikinta, k’arshe d’aya daga cikin jakunkunan ta dake a gefen wardrobe d’in ta duk’a ta bud’e, a can k’asa ta tura ledan bayan ta rufe ta mik’e, a gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta, ita kan ta taga had’uwar da tayi don lace d’in ba k’aramin had’uwa yayi ba kuma ko ba’a fad’a ba da ka kalle shi zaka gane ba mai k’ananun kud’i bane, ga sark’a da yan hannun ta suma tamkar gold sun yi ma hannunta da ya sha k’unshi kyau ba kad’an ba, zuciyarta ce ta fara hasasho mata Haisam tsaye a bayanta har bata san lokacin da ta d’an yi murmushi ba, bayan ta gama kallon kan nata juyawa tay jiki a sanyaye ta koma bakin gadon ta zauna ta jingina da headboard, bada jimawa ba aka turo kopar ta kai idonta da sauri kan mai shigowar, Saude ce ta fara shigowa suka had’a ido tay ma Fatun murmushi itama tana niyyar mayar mata Gwaggo ta shigo aikuwa zumbur tay ta mik’e da sauri gudu gudu ta nufo kopar tana zuwa ta fad’a jikinta ta fashe da kuka lokacin Hajiya ma ta shigo tana dogara sandar ta idanun ta sanye da glasses har lokacin lifaya d’in ce nad’e a jikinta, sosae ta k’ank’ame gwaggon sai kace zata shige cikin jikinta sai faman kuka take har kallabinta ya fad’i haka gyalen ma ya zamo daga saman kan ta gashinta da ya sha gyara baki wuluk sai salk’i yake an yi parking d’in shi ya bayyana, har cikin ran gwaggo take jin kukan hakan ya karya mata zuciya daurewa kawai take tasa hannu guda ta d’an dafa bayan ta,
“To wannan kukan shagwa6a ne ko na me, sai kace wadda zaku rabu kwata kwata, duka yaushe kika baro gidan kuma gashi har kin gan ta to miye abun kuka Fateema” Hajiya dake tsaye gefe tay Maganar Saude nata kallon su gwanin ban tausayi, d’ago da ita Gwaggo tay suka had’a ido Fuskar ta duk tayi jage jage da hawaye a sanyaye tace mata ya isa hakanan ta kamata suka nufi gado ta zaunar da ita, Hajiya ta kalli Saude tace ta kai towels d’in saman jakunkunan dake gefen Wardrobe in ta tashi ta canza masu wuri tace to, tsaye gwaggo tay a gaban Fatun tana d’an murmushi Hajiya ma ta maido idon ta kan Fatun tace “Fuskar Amarya duk tayi jage jage haka, kar kija Angon naki yazo yay tunanin wani abun mukai maki ya d’auki mataki a kan mu” cike da zolaya tay Maganar Fatun ta sunkuyar da kan ta k’asa,
“Amman Dije ya akai aka bar mata kai haka ba’ai kitso ba” Hajiya dake kallon kan Fatun ta fad’a, gwaggon tace “Wllh naso ai mata shafa’a nayi gashi yau anata hidima ban ko tuna ba” jinjina kai tay tace “shikenan bari in Allah ya kaimu gobe sai a kira Balaraba tazo tay mata” gwaggo tace to cike da girmamawa, sake kallon Fatuu tay “Fateema ga Abinci can a saman Dining table in zaki ci in kuma zaki jira Angon naki ne sai ku ci tare dama can baya ke kike sa shi yaci da yawa yanzu ma sai ki dasa don har yanzu ba wani cin Abincin kirki yake ba” gaba d’aya d’an murmushi sukai banda Fatuu da ta sadda kai Hajiya ta kalli Saude tace suje, ganin gwaggo na niyyar bin su yasa tace in bata gama da ita ba ta tsaya zasu jirata a parlor cike da jin nauyi tace to, don dama bata samu yi ma Fatuu Nasiha ba, bayan fitar su Fatuu ta kalli gwaggon ta kamo hannunta cikin muryar kuka tace ta zauna sai ta girgiza mata kai alamar a’a, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta zauna tace bazata zauna a gadon suruki ba tay Maganar da yar dariya dole Fatuu ta k’yale ta sai kuma ta nuna mata bedside drawer tace to ta zauna saman ta, bata musa ba ta nufi inda take ta zauna Fatun taja jiki ta matsa kusa da ita ta k’ara kama hannunta tana yar ajiyar zuciya irin ta wanda yay kuka, bin juna sukai da ido Fuskar gwaggo da d’an murmushi ita kuma Fatun ta d’an kwa6e fuska idanunta sunyi raurau kaman zata cigaba da kukan, nannauyar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fara Magana a nutse,
“Ina matuk’ar godiya ga Allah daya nuna man wannan ranar gaki a cikin d’akin ki na aure hakan ba k’aramin abun farinciki bane, dad’in dad’awa kuma wanda ya kasance a matsayin mijin naki mutum ne da kowacce uwa zatay Alfahari in d’iyar ta ta samu irin shi a matsayin miji, bani haufi akan yadda zaki gudanar da rayuwar gidan auren ki don nasan wacece ke fiye da kowa, duk yadda ake son Mace ta kasance a gidan aurenta na tabbatar zaki kasance, saidai ina so in k’ara jan hankalin ki, a yanzu kin baro shek’ar da kika taso cikinta kika saba rayuwa kin dawo wata sabuwa da baki saba ba, dole zaki ga yanayin rayuwar ya bambanta sosae, kada kiga ai kinsan abokin rayuwar naki kun saba dole wasu abubuwan zasu canza, ki k’ara wasu ki kuma rage wasu don yadda kuke dashi a da da kuma a yanzu ba d’aya bane, yanzu shi Mijin ki ne wanda Aljannar ki na a tafin k’afar shi dole ki k’ara girmama shi kiyi mashi biyayya fiye da yadda kike mashi, ki bishi sau da k’afa sannan ki zama mai wadatuwa da duk abunda yay maki kada kiga yanzu kina da hakki akan shi kice zaki rink’a rainuwa kan abunda yay maki, duk abunda yayi maki ki zama mai godiya had’i da Addu’ar k’arin budi a gare shi, sannan kada kice zaki rink’a yawan kai mashi buk’atu kiga ai yana da halin yi maki in dai abu ba ya zama dole ba to ki hak’ura don yawan tambayar abu na sa ka gundiri mutum koda bai fito ya nuna ba, na tabbatar zai tsare maki dukkan hakk’in ki don haka sai ki zama mai kauda kai, sannan 6angaren tsafta nasan baki da kyuwa ko ganda, ki k’ara dagewa wurin gyara jikin ki da Mahallin ku ki hana idon shi ganin abunda zai munana mashi haka ki hana hancin shi shak’ar abunda zai 6ata mashi….” D’an dakatawa tay idanun Fatuu akan ta sun yi rau rau, bayan ta d’an nisa taci gaba “a zaman farkon nan da zakuyi anan zaki k’ok’ari ki fahimci miye yake so da kuma miye bai so ma’ana miye in kinyi zai ji dad’i ya faranta mashi rai miye kuma in kinyi ba zai ji dad’i ba ko zai bakanta mashi, in kin fahimci hakan sai ki kiyaye sai kiga kun zauna lafiya har in kin ji wasu na korafin tsakanin su da mazajen su kita mamaki, a k’arshe inason in ja hankalin ki game da abokiyar zaman ki, ki sani ku biyu keda shi Saboda haka kada ki zamo mai son kai, duk abunda baza ki so ya faru dake ba to itama kada ki so mata haka duk abunda kika so ma kan ki itama ki so mata, ki zauna da ita tsakani da Allah, nasan in Maganar auren ku ta bayyana rai zai iya 6aci kiyi hakuri da duk abunda zai biyo baya ba kamar daga gareta don tabbas an mata ba daidai ba, in Allah ya daidaita tsakanin ku ki ci gaba da daukarta tamkar Yayarki uwa d’aya uba d’aya kar kiyi mata kallon kishiya balle har zuciyar ki ta samu damar sak’a maki wani abu ba daidai ba game da ita, in abun farinciki ya faru da ita ki taya ta murna in na jajantawa ne ki taya ta jajantawa kada ki sake ki bari shaidan yay galaba a kanki game da ita in ma zaki kishi da ita to akan kyautata ma mijin ku ne, haka dangin shi ma ki d’auke su tamkar naki ki zauna da kowa lafiya sannan ki dage da yin ibada don neman dacewa, a K’arshe ina Addu’ar Allah ubangiji ya sanya Alkhairi a zaman ku gaba d’aya Amin,(Wannan Nasiha ce ba ga Fatuu kadai ba ga duk wata Amarya da ke karanta Novel d’in nan, duk abun da kika ji mai muhimmanci ki aiki da shi zai maki amfani in sha Allah).
A tare suka fito parlon Hajiya da Saude na zaune suna kallo, tana ganin su ta fara k’ok’arin mik’ewa Saude ma haka, Hajiya tay ma Fatuu saida safe tace taje ta jira Mijinta yazo daga haka ta nufi k’opa, kallon juna sukai ita da gwaggo ganin idanunta sun ciko yasata girgiza mata kai alamar kada tay kukan had’i da yi mata d’an murmushi da k’yar itama ta d’an yi mata gwaggon ta nufi kopa har zata fita ta juya ta kalli Fatuu da tay tsaye tay mata alamar ta koma ciki a sanyaye ta d’aga hannu ta d’an yi mata bye bye ta jinjina mata kai daga haka ta fuce, bin parlon ta shiga yi da kallo har ta kai idanunta sama kan chandelier taga an canza wata da ta fi ta da k’awatuwa, d’an murmushi tay ta sauke idanunta ta juya har zata shiga corridor sai kuma ta juya ta nufi Dining Area tana tafiya kaman mai yin sand’a, tsaye tay tana bin wurin da kallo ya burgeta sosae can ta nufi wurin table d’in ta kai hannu ta fiddo Warmer guda ta bud’e farfesun yan ciki ne sai zuba uban k’amshi yake, fiddo d’ayar tayi wadda tafi girma itama ta bud’e taga Fried Spaghetti ce da tay brown tasha vegetables daga gefe manyan soyayyun tsokokin nama ne a jere, maida murfin tay ta rufe ta jera su kan table d’in kafin ta d’auki basket d’in ta wuce, Kitchen ta shiga don ta aje nan ma ba k’aramin burgeta yay ba fuskarta d’auke da d’an murmushi take k’are mashi kallo, daga baya ta juyo ta fito ta koma Bedroom.
***** *****
Bayan Abbas ya aje su inna Zaliha direct G.r.a ya wuce, Haisam zaune acikin Bedroom d’in shi saman 3 seater ya d’an kishingid’a ya cire rigar shaddar jikin shi daga shi sai farar singlet da wandon shaddar, Video call yake da Fanan ta cikin computer d’in dake ajiye saman c-table sai faman zabga mashi shagwa6a take kan ya koma tana missing d’in shi sosae shi kuma yana rarrashin ta kan ta kwantar da hankalin ta ya kusa komowa, daga ita sai wasu yan fingilallun half vest da wandon ta wanda da kad’an ya d’ara ma pant sai faman yin abubuwan jan hankali take yanata d’an murmushi don ya gane mata sam bata da Sauk’i ta wannan 6angaren don in dai yana a kusa da ita hana mashi sakat take, suna cikin haka Abbas ya turo kopar Bedroom d’in ya d’an juya ya kalli wurin kafin ya juyo kan screen Fanan d’in ta tambaye shi waye can k’asan makoshi ya furta Abbas aikuwa da sauri ta tashi ta sauka daga saman gadon da take kwance tayi ruf da ciki ta nufi closet, Zama Abbas yay gefen shi yana sakin murmushi ya tambayi da wa yake Video call ne slowly ya furta mashi Fanan,
fad’ad’a murmushi Abbas yay yace “kace da uwar gida kake ganawa, to in ka gama ga Amaryar ka can mun kai maka tana jiran ka” wani kallo Haisam d’in yay mashi mai kaman harara, ba don Fanan d’in ta mik’e ba da tabbas sai taji abunda Abbas d’in yace, dariya sosae Abbas ke yi yana fad’in ya gama boye boyen shi dole asiri ya tonu, Haisam d’in bai tanka mashi ba saima ya maida idon shi kan Screen, lokacin Fanan d’in ta dawo ta zura doguwar riga kanta tasa hula sa6anin da babu hulan sai brown sumar ta da ta zuba gefe da gefen fuskarta duk da haka yanzun ma ta fito daga gefen wuyanta, tambayar ina Abbas d’in yake tay Haisam ya juya laptop d’in ta kalli Abbas dake dariya yace “gani nan uwar gida”,
itama yar dariya take tace “uwar gida and also Amarya” wata yar iskar dariya Abbas yasa har saida haisam yay mashi wani kallo suka had’a ido hakan ya k’ara bashi dariyar da k’yar ya tsagaita Fanan d’in tace mashi ko ta fad’i ba daidai bane da sauri yace “No, no daidai kika fad’a kawae yanayin yadda kikai Maganar ne naga kaman akwae son kai a ciki, da sai ki tsaya a uwargidan ita kuma Amaryar sai tazo” wani kallo ta watsa mashi ta had’e giran sama da ta k’asa tace ashe bai k’aunar ta har haka bata sani ba, da sauri ya d’aga hannu yana fad’in tuba yake, cikin d’an d’aure fuska tace to ya daina mata irin wannan mummunan fatan ita kad’ai ce ba k’ari wannan Alk’awari ne Until death do them part itama d’in tare zata d’auke su, jinjina kai Abbas ya hau yi yana k’ok’arin danne dariyar dake ciyo shi yace to ya bari Allah ya bada ikon ruk’e Alkawari tace Amin ai yasan waye mijinta tunda ya d’auka zai ruk’e da sauri Abbas yace gaskiya ne,
“To amman wai ya akai kika k’yale shi yay zaune anan ne naga ma kaman bai da niyyar dawowa nan” d’an 6ata fuska tay “nima na k’osa ya dawo bana jin dad’in rashin shi a kusa dani duk na takura, amman yace man wani aiki ne ya ruk’e shi ya kusa dawowa” d’an ta6e baki Abbas yay ya jinjina kai yace “Tabbas hakane na manta, ko yau ma ya k’ara samun wani babban aikin mai cike da Alkhairi don haka sai kin d’an k’ara hakuri kin d’aga mashi k’afa” d’an rausayar da kai tay tace shikenan ya zata yi tana yi mashi fatan nasara, da sauri Abbas yace “Yauwa, haka ake son matar kwarae duk in mijinta yazo mata da wani Al’amari ta fahimce shi ta yiwu Alkhairi ne” murmushi tay kawai tace bari ta k’yale su suyi hira yace ok, juyo da Laptop d’in Haisam yay sukai sallama cike da nuna kauna kafin ya katse, maida idon shi yay kan Abbas dake dariya ya hau jinjina kai yace “Wato har na fara tausaya maka wllh, waya fad’a maka ana ma mata irin wannan Alk’awarin? Ai koda baka da ra’ayin k’ara Aure bai kamata kai mata Alk’awari ba don bamu ke da iko da kan mu ba komai na iya canza wa just like it happens now, yanzu in tazo ta san da zancen wane kallo kake tunanin zata maka in ma ta saurare ka kenan” bin shi da ido kawae Haisam d’in yay kaman ba zai ce komae ba, can yay sigh slowly ya furta “she was already my wife then” Abbas yace “amman ai ita bata sani ba ko” d’an d’age gira yay yace zai fahimtar da ita in buk’atan hakan ya ta so, d’age kafad’a Abbas yay yana murmushi yace Allah ya taimaka bai amsa mashi ba saima ya juyar da idon shi,
“Yanzu ka tashi muje in kai ka an bar yar mutane ita kad’ai kuma kasan ba sabawa tay ba” ba tare daya kalle shi ba yace yaje kawai, still dariya Abbas ke yi can ya mik’e ya nufi hanyar fita sai lokacin ya juyo ya kalle shi, bayan wani lokaci Abbas d’in ya dawo abunka da wanda yasan gidan hannun shi ruk’e da mug d’an tiriri na fitowa alamar abunda ke ciki mai zafi ne, wurin kujerun ya nufa ya koma inda ya tashi ya zauna ya kai hannu ya kama igiyan tea bag d’in data lek’o waje yana dan tsoma ta ciki yadda zai yi Sosae, bayan wani lokaci ya mik’a ma Haisam dake kallon shi yana murmushi yace ga shi ya sha, wani kallo ya bi shi da shi kafin ya maida kallon kan cup d’in baida niyyar amsa, k’ara kallon Abbas yay ganin irin murmushin da yake yi yasa ya fahimci ko na minene tunda ko da bikin su da Fanan ya bashi irin su, d’an girgiza mashi kai yay slowly ya furta “No need” Abbas d’in yace “kai dai ka amsa don kuwa kana buk’atar shi ko an gaya maka ita ma hakanan za’a kawo maka ita ba tare da an gyara taba ba kamar yadda kai mata aika aika” kallon shi kawai Haisam d’in ke yi baida niyyar amsa, duk yadda Abbas yay dashi kan ya amsa ya sha ya k’i k’arshe dole ya k’yale shi yace yayi ma kansa shi bari yasha Allah yaso zai mashi amfani, bayan ya shanye ya mik’e yace bari ya maida mug d’in daga can zai wuce, mik’ewa Haisam yay ya taka mashi suna zuwa bakin k’opa Abbas yace yaje ya shirya ya tafi gun yar mutane tana can ita kadae, tsaye yay yana kallon shi ya fita yana murmushi har zai rufe kopar sai kuma ya dakata yace “saura ka k’ara bari ka zama uncontrollable kazo kana fad’a man k’auli da ba’adin u feel like ur life depends on it” sai lokacin Haisam ya saki murmushin da har hak’oran shi suka d’an bayyana Abbas d’in ma dariya yake yi yace makullin Motan na nan a wurin da ya zauna ya d’aga mashi kai daga haka sukai sallama ya tafi,
Wurin kujerun ya koma ya zauna kan ta farko ya d’aura kafa d’aya akan d’aya ya zuba ma gaban shi ido da alama tunani yake yi, ya d’an d’auki lokaci a haka can ya mik’e ya fita daga wurin ya nufi hanyar corridor, saida ya d’auki kusan 30 minutes sannan ya fito da alama wanka ma yayi don ya canza kaya zuwa farar shadda Sol sai salk’i take da alama sabuwa ce bata ga ruwa ba, hannun shi d’aure da agogon diamond k’afafun shi na sanye da fararan half cover, kan shi ba hula sai nad’add’ar bak’ar sumar shi da gani an gyara ta don sai shining take yana janye da d’an madaidaicin trolley, saida yaje ya kauda laptop d’in dake saman c-table sannan ya dawo bakin dressing mirror ya d’auki Car Key ya kai hannu ya kama trolley d’in da ya aje, bayan ya latsa switch hasken d’akin ya d’auke ya bud’e kopar ya fita,
Wani irin tsoro ne ya fara kama Fatuu ganin dare yayi sosae don sha d’aya ta kusa, duk ta takure kanta a saman gadon sai wuwwurga ido take ga wata irin yunwa da take ji, lokaci bayan lokaci take duba time a jikin wayar ta dake a gabanta har ta fara fidda ran zuwan Haisam d’in ta shiga tunanin yadda zata kwana ita kadae a part d’in, can bayan wani lokaci taji ana k’ok’arin bud’e kopar aikuwa a tsorace ta tashi zaune jikinta har ya fara yar rawa kanta ba kallabi ta zaro idanu tana kallon kopar, a hankali ya turo k’opar ya shigo da yar sallamar da ko Fatun bata ma ji ba, yana shigowa idanun shi suka sauka cikin nata da ta zaro ya dakata suka bi juna da kallo, ya lura da a tsorace take hakan yasa shi k’ara yin sallama a hankali sai lokacin taji ta amsa tare da sauke nata idanun saman gadon shiru ta biyo baya, jin bai k’ara cewa komai ba yasa ta d’ago ta kalle shi, still yana tsayen suka k’ara had’a idanu cikin yar rawar murya tace “Sannu da zuwa” kai ya d’aga mata kawai ya juya ya nufi wardrobe yana janye da trolley d’in ta bishi da kallo, aje trolley d’in yay ya kai hannu gefenta ya latsa sai gashi ta fara zugewa da kanta sai lokacin Fatuu ta gane yadda ake bud’e ta, bayan ta gama bud’ewa ya kai hannu ya zuge trolley d’in ya fara k’ok’arin fiddo kayan ciki tana ta kallon shi, bayan ya saka na farko ta kai hannu ta d’auki kallabinta ta yafa saman kai ta sauka daga saman gadon a d’arare ta nufe shi, lokacin data isa ya saka na biyu yana juyowa ya ganta a gefen shi ya bita da ido, saida ta had’iyi abu sannan cikin yar in ina tace “b….bari in saka..” bai ce mata komai ba sai kawai ya juya ya tafi tabi bayan shi da kallo, Laundry room ya nufa ya tura kopar ya shige, a sanyaye ta kai hannu taci gaba da fiddo kayan tana jerawa har da su underwear d’in shi, har ta gama bai fito ba ta zuge trolley d’in ta maida shi gefe wurin jakunkunan ta ta aje, komawa tay wurin gado tana niyyar zama ya bud’e kopar ya fito fuskar shi da alamun ruwa haka k’asan hannun rigar shi mai links, tsaye tay ta kasa zaman tana kallon shi tana yi tana maida idon k’asa, tsayawa yay daga d’ayan bangaren gadon yana kallon ta kaman zai yi magana, sai da ya d’an d’auki lokaci sannan taji yayi Maganar saidae bata ji mi ya ce ba ta bishi da kallon rashin fahimta, ya gane bata ji mi yace ba ya d’an maida idon shi k’asa sai kuma ya d’ago slowly da turanci yace ta samu tsarki, kai ta d’aga mashi alamar eh tare da maida idon ta k’asa taji yace taje tayo Alwala tace to, ba tare da ta kalle shi ba ta nufi hanyar Laundry room d’in sumi sumi, lokacin data fito har ya shimfid’a prayer mat guda biyu a saman lallausan carpet d’in dake a gaban gadon yana zaune a bakin gado, wurin jakunkunan ta nufa ta bud’e ta curo Hijab ta fara k’ok’arin saka wa ya mik’e ya daidaita kan abun sallar gaba ita kuma ta hau kan ta baya ya kabbara salla, Nafila raka’a biyu sukai sam Fatuu batayi mamakin jin yadda yake sakin kira’a ba don ba yau ta fara jin shi yana karatun Qur’ani ba yana yawan yi ta cikin wayar shi, gaba d’aya Allah ya bashi ilimin boko dana Addini abun saidae ace ma sha Allah, zama sukai suna lazimi tana ta kallon sumar bayan kan shi ba zato sai gani tay ya juyo har saida gabanta ya fad’i don sun yi gab da juna, had’a ido sukai ta d’an waro nata yay mata alamar ta matso da kan shi, matsawa tay dab da shi ya kai hannu ya dafa kanta ta d’an sunkuyar da kan tana kallon k’asa gaba d’aya k’amshin shi ya gama cikata, Addu’ar da Manzo (S.A.W) ya koyar mutum yayi in yay Amarya ya shiga yi bayan ya gama ya sauke hannun nashi ta d’ago suka k’ara had’a ido, bai yi tunanin tambayar ta wani abu ba don duk abunda yake son sani game da ita ya sani, juyawa yay ya d’aga hannu ya fara jero Addu’oi da sauti kad’an itama ta d’aga nata hannuwan bayan ya gama a tare suka shafa ya yunk’ura ya mik’e tana dai ta bin shi da ido, har yayi taku d’aya zuwa biyu ya dakata ya juyo ya furta akwai abu akan dining table daga haka ya juya ya nufi kopar ya fita, zugudum tay ta bi k’opar da ido tama rasa tunanin da zata yi, gaba d’aya ta kasa gane mashi duk ya canza mata sai kace ba Ya Haisam d’in da ta sani bane, in don abun da tayi ne ai taje ta bashi hak’uri kuma ya nuna ya hak’ura to miyasa taci gaba da ganin shi haka wanda ada da ta bashi hak’uri yake hak’ura kuma bata ganin canji a tattare dashi kamar yanzu, gaba d’aya jikinta ne ya k’ara yin sanyi, tunowa da Abincin da su Hajiya suka kawo yasa ta yunk’ura ta mik’e, cire Hijab d’in tayi ta linke ta mayar ta dawo ta kwashe abubuwan sallan suma ta linke ta je ta ajiye ta d’auki kallabin ta dake a saman gadon ta yafa saman kan nata ta nufi hanyar fita, d’an jimm tay a bakin k’opar tana zullumin fita can dai ta kama handle d’in ta ja kopar ta bud’e a d’arare ta fita,
Tana zuwa bakin corridor d’in ta hango shi zaune akan L-shape ya d’an kishingid’a yana kallo, had’a ido sukai da sauri ta kawar da nata sum sum ta nufi hanyar dining d’in, tana zuwa taga manyan ledoji guda biyu ta fahimci sune yay mata magana akai ta kai hannu ta fara bubbud’a su taga miye a ciki, d’aya su ice cream da Youghort da kuma snacks d’ayar kuma fruit ne, shiru ta d’anyi tana tunanin yadda zata yi dasu can ta d’auki guda ta nufi freezer ta bud’e ta saka, dawowa tayi ta d’auki d’ayar ma taje ta kai ba tare data d’au komai ba don ta ci, bayan ta dawo tsaye tay gaban table d’in tana tunanin ko zai ci Abincin ma, wata zuciyar ta bata taje ta fara tambayar shi, kamar bazata je ba sai kuma ta tafi tana tafiya kamar wadda k’wai ya fashe mawa a ciki, bata zagaya cikin parlon ba sai ta bi ta bayan kujeru ta tsaya a d’an gefen bayan kujerar da yake zaune ta bi shi da ido ta kasa cewa komai, kamar yaji ajikin shi da mutum a wurin ya d’an juyo da kan shi suka had’a ido, d’an kikkafta idanu ta shiga yi da k’yar tace mashi dama Abinci ne aka kawo daga part d’in Hajiya, shiru ya d’anyi still idon shi na akan ta sai kuma ya d’an girgiza mata kai alamar bazai ci ba, maimakon ta tafi sai tay tsaye tana kallon shi ganin haka yasa shi cewa “Dare yayi” saida ta had’iyi abu kafin a sanyaye tace “ai Abincin ba mai nauyi bane” yanayin kallon da yake mata ne ya sauya da sauri ta maida nata idon k’asa tana haka taji ya mik’e ta d’ago tana kallon shi, saida taga ya zagayo sannan itama ta nufi Dining d’in ta d’ayan side d’in da ba ta nan ya bi ba………….
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
…
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :Â Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :Â @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:Â Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.