*ASM Bk2014*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
…….Tana komawa cikin gidan Falo ta nufa anan ta iske gwaggo zaune ta bud’e Akwatunan duka ta rafka uban tagumi tana ta kallon kayan sai kace lefe koda Akwatunan basu da yawa amma kud’in su dana kayan ciki zasuyi na wasu akwatinan lefen da suka fisu yawa itama Fatun tsaye tayi cike da Al’ajabin ganin uban kayan don ba abunda babu na buk’atar mace da ake sakawa a lefe kama daga d’inkakkun kaya da wanda ba’a d’inka ba,Cosmetics Undies takalma da dae sauransu, da alama dae bakin gwaggo ya mutu ta kasa cewa komae sai jinjina kai kawae take can ta kalli Fatun tace ta kama sukai d’akinta tace to ta matsa gwaggon ta tashi suka maida su d’akin nata, sai lokacin bayan gwaggo ta fita ta zauna ta fara dubawa nan take ta fara ayyana ina ma ace lefen aurensu ne a hankali siraran kwalla suka fara gangaro mata k’arshe ma sai ta kife kanta kan kayan ta shiga raira kuka ba mai sauti ba,
Washe gari da safe yazo d’aukarta don kaita Makaranta yana yin horn biyu ta fito cikin shiri ta zagaya ta bud’e kopar ta shiga bayan ta rufe kopar ta juya suka had’a ido ya jingina kanshi da headrest, da d’an Murmushi ta gaishe shi ya amsa fuska sake yace “How was ur nyt?” ta bashi amsa da “Alhamdulillah” ya jinjina kai daga haka yaja Motar suka tafi saida suka biya aka d’auki Haulat kaman kullum kafin suka wuce, ba laifi ta d’an saki jiki yau jefi jefi yake mata Magana tana bashi amsa Haulat dae nata bin su da ido acan k’asan ranta tana ayyana Fatuu ta warware ne ko ya akai ta saki jiki haka, bayan ya aje su ya basu kudin break tana Murmushi ta amsa tayi mashi godiya har zai ja Motar ya tsaya ya kirata bayan taje side d’in da yake ya tambayeta karfe nawa zasu tashi ne tace sai yamma yace to zaizo ya daukesu, akan hanyarsu ta zuwa Class ne Haulat ke tambayar Fatun game da warwarewar da taga tayi tace zata fadi mata in sunje aji, saida akai break ne ta bata labarin yadda sukae dashi sosae taji dadi da bata fad’i mashin ba ta kuma yaba da kirkin haisam d’in daya damu da damuwarta har haka ta tayata farincikin kayan data ce ya siya mata saidae bata ji dad’in jin Fatun bazata bikin ba tace mata “amman Fatuu miyasa zaki k’i zuwa bikin Ya Haisam ne fa ni kaina da za’a barni wllh ina son zuwa saidae nasan babanmu bazai barni ba amman ke tunda nasan su gwaggo ma zasu ai da kinje kawae tunda dae kin hakura dashi”
“Don na hakura ce maki akae na daina sonshi ne Haulat, har yanzu ba abunda ya canja kawae ba yadda zanyi ne shiyasa gwara ma kar naje naga abunda zai k’ara tarwatsa man Zuciya” ta k’arasa Maganar da damuwa kan fuskarta haulat tace ta fahimceta daga haka bata k’ara ce mata komae ba game da hakan bayan La’asar Haisam ya dawo ya d’aukesu, lokacin daya ajesu ya wuce gida yana zuwa bakin Gate Officer ya tsaidashi bayan ya tsaya ya nufo Motar lokacin ya sauke glass d’in,
“Barka da dawowa Yalla6ai” kai ya jinjina mashi yaci gaba “dama kana da bak’o ne” tambayarshi yay ina bakon yake ya nuna mashi can gefe da hannu ya d’an lek’o kanshi ya kalli direction d’in da Officer ke nunawa, wani dattijo ne ya manyanta sosae cikin shiga ta kamala yana tsugunne gaban mashin d’in shi Jincheng yana ganin fuskar Haisam ya mik’e yana kallonshi da d’an Murmushi, maida kan Haisam yay yace ace ya shigo daga haka yaja Motar ya shige, lokacin da Haisam ya fito daga cikin Motar dattijon ya shigo yay mashi alamar ya aje mashin d’in cikin wurin, da sauri ya nufo shi bayan ya parker mashi d’in nashi ya d’an rankwafa yana kokarin gaishe dashi ya mik’a masa hannu suka gaisa kafin yace su shiga ciki yace to saida ya koma ya d’aukko wata leda gari yayi zafi a jikin mashin d’in kafin ya bi bayanshi suka nufi part d’in Haisam, suna shiga ya bi parlon da kallo baki bud’e tunda yake bai ta6a shiga irin falon ba shi ko ganin irinshi ma a tv bai ta6a ba ga ni’imtaccen sanyi had’i da daddadan kamshi da ke kaima hancinshi da sauran sassan jikinshi ziyara, nuna mashi bangaren Armchairs yay alamar ya zauna ya nufi wurin ya zauna a takure, shiru suka yi Haisam bai mashi Magana ba shima haka sai dae faman murmushi yake can ya fara Magana yace “Yalla6ai baka gane ni ba ko?” Kai Haisam ya d’aga mashi alamar eh,
“Allah sarki ay dayake lokacin da tsawo sosae, Sunana Malam Garba kuma nine mutumin daka ta6a taimako ka biya masa kud’i a caji Office shekaru kusan ukku da suka shud’e tun lokacin naso nayi maka godiya sosae saidae ban samu halin hakan ba don baka d’aga waya dana rok’i Officer ya kiraka dama saida ya fad’a man bazaka d’aga ba karshe ya nuna man don Allah kai man in gode ma Allah kawae” d’an dakatawa yay Haisam dae nata kallonshi fuskarshi a sake don yanzu ya gane shi,
Malam Garban ya d’aura da fad’in “Wato Yalla6ai sanadiyyar taimakon da kayi man na samu bud’i sosae, da yar trader na bud’e ma yarona habu Allah yasa ma abun Albarka yanzu ta Zama k’aton shago Alhamdulillah yanzu ba matsalar Abinci a gidana sannan karatun yara ma ana kamantawa yadda ya dace shi kanshi wanda yay silar zuwana caji Office d’in Allah ya shiryar dashi ya daina d’aukar kayan Mutane yanzu ya natsu sosae suke Kula da shagon ni kuma naci gaba da sana’ata ta faci wadda dama injin d’inne ya lalace na daina sakamakon taimakon kudi da kayi man na canja wani wannan dalilin ne yasa na kasa hakuri don ban manta da abunda kayi man ba saboda ba abune da zan iya manta ba dama Officer ya fad’a man a wurin kakarka kake da zama tun wanccan lokacin hakan yasa ban sha wata wahala ba wurin nemo ka don ita d’in sanannace, a tak’aice dae Yalla6ai Nagode, Nagode Allah Ubangiji ya saka maka da mafificin Alkhairinsa ya dawwamar dakai cikin Farinciki kaman yadda kake saka bayinsa Farinciki, Allah ya jik’an Magabata ya raya maka zuria……” kasa karasawa yay sakamakon muryarshi da ta karye idanunshi suka cicciko da kwalla”,
Sigh Haisam yay Calmly yace “ai ba wani abu bane ka d’auka rabonka ne a hannuna ba sai ka damu ba” yar dariya yayi yana kokarin mayar da k’wallan yace “duk da hakan ai ance yaba kyauta tukuici, ko don dakon rabon da kayi ai na gode maka” d’an murmushi Haisam yay baidae cemashi komae ba can ya mik’e ya nufi Fridge ya d’aukko lemu da glass cup ya dawo saida ya d’aukko c-table bayan ya tsiyaya ya aje mashi yace bismilla ya sha yay godiya kafin ya daukka ya fara kur6a, bayan yasha kaman rabi ya ajiye ya kai hannu gefenshi ya d’ago da ledar daya zo da ita yace “yalla6ai wannan daga cikin kayan shagonne su Omo, Sabulu Tolen paper (toilet paper) da dae sauransu na kawo a ba iyali” still da murmushi kan face d’inshi yace “Ok angode sai dae a kaima Hajiya”
“Af,af d’ana ba dae ba iyalin ba?” ya tambaya da d’an mamaki shiru kaman bazai yi Magana ba sai kuma yace “Yea but Next week ne zanyi auren” ruke ha6a yay yace “iko sai Allah kace da sati mai zuwan nazu dana taras ana tsaka da hidima kenan”,
“Ba anan ne za’ai ba Abuja ne” idon Malam Garba a kanshi yace “Allah sarki Allah ubangiji ya kaimu ya nuna mana, aikuwa yakamata nima inje d’aurin auren nan”
“No, ba sai kayi hakan ba” ya bashi amsa a takaice yace “d’ana ba dae baka son naje d’aurin auren naka ba” da sauri yace mashi a’a kawae basai ya takura kanshi ba in yayi mashi Addu’a ya isa yay yar dariya yace” shikenan tunda kace hakan amma wllh ba wata takura ai Alhamdulillah Allah ya bud’a, Addu’a kuma kullum cikin yi ake wllh ba zancen ganin idonka ba aduk sallar da zanyi ta Farilla kota Nafila kana cikin Addu’oi na ko bama a salla ba” sosae Haisam yaji dad’in Maganar yace mashi ya gode,
Shiru suka d’anyi can Malam Garban yace “Yalla6ai bari in barka ka huta ka dawo aiki kuma na rik’e ka, saidae in ba damuwa ina son in gaisa da hajiyar taka,amsa mashi yay da Owk ya kai hannu gefenshi ya d’auki wayar shi yay Sending call, Tk ya kira saida ya tambayeshi yana gida yace mashi eh yace yazo part d’in nashi, bada jimawa ba sai gashi ya shigo da sallama ya gaida Haisam kafin ya juya ya gaida bak’on umarnin kaishi wurin Hajiya ya bashi yace to Malam Garban ya mik’e bayan ya dau ledan yace bari akai ma Hajiyan Haisam ya d’aga mashi kai, saida ya tsaya bakin kopa ya k’ara mashi godiya da Addu’oi sannan ya fita,suna fita Haisam din ya kira Hajiya tunkan tay mashi Maganar ya baizo yaci Abinci ba as usual ya rigata fad’in ga bak’o nan Tk zai kawo daga haka ya katse kiran ya mik’e ya nufi hanyar Bedroom.
Lokacin da suka shiga parlon Hajiyar na zaune kan 2 seater idanunta sanye cikin glasses ta juyo tana amsa masu sallamar da suka yi Tk ya nufeta yace ga bak’o nan inji Ya Haisam ta jinjina mashi kai ya juya ya fita ta maida idonta kan Malam Garba da yay tsaye tace “ka zauna mana kayi tsaye” fuskarshi d’auke da faffad’an murmushi ya amsa mata ya nufi one seater ya zauna Matar da yake gani a talabijin ko yajita a Radio yau gashi gata ba k’aramin dad’i ya ji ba,bayan ya zaunan ya d’an sunkuya yana gaishe da ita ta amsa fuskarta a sake shiru ya biyo baya can yaji tace “to bak’o daga ina don ban wayeka ba” tay Maganar tayi mashi k’uri ta cikin gilashin, gyara zama yay ya fara mata bayanin kanshi da abunda ya had’a shi da Haisam,
“Allah sarki da yake bamu ta6a ma yin Maganar dashi ba tunda ba fad’in abu yake ba in yayi” jinjina kai yay yace “Allah Akbar kaji mai yi don Allah, Allah ya saka da mafificin Alkhairinsa ya k’ara sutura” Hajiya ta amsa da Amin tana murmushi tace “ai Malam Garba da baka wahalar da kanka ba ma” da sauri yace “wllh Hajiya taimakon da yay man ne ya tsaya man a raina har mafarkinshi nike in ban zo nayi mashi godiyar ba bazan samu natsuwa ba” yar dariya hajiyar tayi ya fara bata labarin irin bud’in d’aya samu sanadiyyar taimakon da Haisam d’in yayi mashi tana ta fad’in Allah sarki an gode ma Allah, can ya mik’e ya kai ledar kayan gabanta yace ga irin kayan shagonne ayi amfani dasu ta kai idonta kan ledar tana fad’in harda hidima haka to an gode, komawa yay ya zauna yayi mata zancen bikin Haisam daya fad’i mashi tace eh in Allah ya kaimu juma’a mai zuwa ne da tun satin daya wuce ma zasu tafi to wai akwae uzurorin da bai kammala dasu bane saboda ba zai dawo nan ba to yanzu sai in Allah ya kaimu jibi zasu tafi yace ashe da rabon zai iskesu tace aikuwa, kokarin mik’ewa ya fara zai tafi da sauri Hajiyar tace “Malam Garba ya zaka tafi ko ruwa baka sha ba mun tsaya munata Magana bansa an kawo maka ba ka zauna sai ka sha ruwan zumunci tukunna, komawar yayi don bai iya yi mata gardama a ranshi kuwa yanata jinjina kirkinta yadda ta sake mashi sai kace dama sun san juna, Saude ta kwala ma kira tun kafin tazo cikin falon ta bata Umarnin kawo mashi ruwa da Abinci ta juya kitchen, bada jimawa ba ta kawo kayan Abincin cikin babban tray saida ta kinkimo sofa table ta kawo gabanshi sannan ta d’aura tray d’in tay Serving nashi bayan ta gaishe shi tace aci Lafiya yay mata godiya Hajiya ma ta mik’e tana fad’in bari ta bashi wuri ya samu sakewa ya tabbatar ya ci ya koshi ya amsa mata da to yana dariya, sosae yaji dad’in Abincin don Saude badae iya Abinci ba Musamman farfesunta in Mutum nasha kamar ya cinye da hannunshi don dad’i da wannan ta siye hajiya, bayan ya gama Saude taje ta sanar ma Hajiya ta fito don suyi sallama ta bashi kud’i tace ya sha mai yay mata godiya gami da Addu’oi ya tafi, Malam Garba bai tashi shan mamaki ba saida ya je parking space don d’aukar Mashin d’inshi nan ya iske Tk ya kawo mashi kwalin taliya da Macaroni harda yar galan d’in mai baki bud’e ya bi kayan da kallo kafin ya sauke idanun kan Tk dake ta washe mashi baki tun kafin yace wani abu ya riga shi fad’in Hajiya ce tace a kawo mashi kawae sai yasa ma Tk kuka yana fad’in wad’annan wane irin Mutane ne haka dama har yanzu ana samun Mutane masu tsananin kirki haka Tk yace “Wllh haka suke ni kaina nan daga Almajiri aka mayar dani d’an gida ba abunda ba’ai man wanda ake ma d’a Abinci,Sutura,Karatu da dai sauransu har iyayena ma ba’a barsu ba” waro ido Malam Garba yay jin wai shi Almajiri ne wanda ba kama ba alama ba don shi ya fad’a ba ma ba lalle ya yarda ba, cewa yay bari yaje ya k’ara yi mata godiya Tk yace ba sai yayi hakan ba ya tafi kawae su bama su cika son yawan godiya ba nan take ya tuna zancen SP acan baya hakan yasa ya hau mashin d’in Tk ya taimaka mashi ya d’aura komae har zai tafi ya dakata yace ma Tk don Allah in ba damuwa ya bashi lambar wayar Haisam yaji aurenshi ya kusa yana son in an dauran ya kira yay mashi fatan Alkhairi ya kasa tambayarshi ne d’azun yace Ok ya amshi yar wayarshi yay mashi saving lambar kafin ya mik’a mashi yanata shi mashi Albarka yaja mashin d’inshi ya tafi Farinciki fal cikin ranshi.(Allah ka had’a mu da Mutane irinsu Hajiyar Sanata ka bamu ikon sanya Farinciki a zukatan junanmu Amin)
Sanye cikin gym outfit ya fito daga cikin d’ayan d’akin hannunshi guda rataye da k’atuwar Sport Bag d’inshi yana fitowa daga cikin Corridor ya d’an bud’a idanu alamar mamaki idonshi akan bakin kopar shigowa, Fatuu ce a tsaye jikinta sanye da Uniform d’in islamiyya ya nufi wurin da murmushi don yaji dad’in ganinta hakan ya tabbatar mashi da ta warware itama d’an Murmushin take mashi yace islamiyya zata ta d’aga mashi kai ya nuna mata kujera taje ta zauna, mikewa yay ya aje jakar a gefe kafin ya nufi Fridge ta bi shi da kallo babbar robar lemu Fanta ya d’aukko ya dawo ya zauna kan hannun Sofa inda ya tashi ya mik’a mata ta kalleshi ya d’an d’age gira ya furta “u’r my guest now” tana murmushi ta amsa tace ta gode shiru ta d’an biyo baya ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannun jakarta can ta d’ago taga ita yake kallo motsa baki ta fara a sanyaye tace “dama nazo in yi maka godiyar kaya tunda safe naso yi maka,Nagode sosae Allah ya saka maka da Alkhairi ya k’ara Arziki mai Amfani” d’an bud’a ido yay with a broad smile on his face da kaji yadda take Maganar cikin hankali zaka fahimci ta girma ba kaman da ba, cikin cool voice nashi yace “Ameen don kin cinye ma Amarya kud’in cin kayan dad’inta su kaza da kika ce ana ci” waro ido tay tana mashi wani kallo yasa dariya tana ganin hakan ta tura mashi baki sai kuma itama tayi yar dariyar, mik’ewa yay yace suje yayi dropping nata kar tay late tace to bayan ta saka lemun daya bata cikin jaka tabi bayan shi, lokacin da suka isa Parking space d’in duk a tunaninta Mota zasu hau amman sai taga ya fiddo bike bayan ya hau ya d’aura jakar a gabanshi yace mata ta hau amman sai tayi tsaye hakanan taji yanzu bata son hawan don tasan dole jikinsu ya hadu shi kanshi tasan ba so yake ba kawae don ya faranta mata ne, juyowa yay ya kalleta yace ta hau mana ta d’an yamutsa fuska tace ita tsoro take ji yace kada ta damu ba abunda zai faru ba gudu zai yi ba, ba yadda ta iya haka ta daddage ta hau tabi ta daddafe jikin mashin d’in yaja suka tafi, gaba d’aya a tsorace take don sai taga tayi sama sosae shi kanshi yaji a takure take hakan yasa yace ta rike shi da sauri ta kai hannu ta kama gefe da gefen rigarshi gadagam har saida ya d’anyi dariya don ya gama fahimtarta abunda bai kai ya kawo ba shike bata tsoro bata tsoron babban abu, a gefen gate d’in islamiyyar ya parker duk ba dalibai da alama duk an gama zuwa, kokarin sauka ta fara yi kwatsam ta tafi gaba d’aya zata kifa cikin zafin nama ya damkota ta dawo sama ta matuk’ar tsorata sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri lips d’inta na d’an motsi haka idanunta ta rufe su gam ga dogayen eyelashes d’inta sai rawa suke sakamakon idonta dake kyerma still yay yana k’are mata kallo tunda yake da ita bai ta6a samun closeness da ita ba haka da har zai kalleta tsaf ba, ba komae yafi d’auke mashi hankali ba irin gashin idonta dake rawa sai kace irin d’iyar roba da ake saka ma batir, jin ta d’an samu natsuwa yasa ta fara bud’e idanun a hankali kafin ta ware su sosae har saida ta d’an tsorata da ganin fuskarshi kusa ganin ya k’ura mata ido yasa duk taji wani iri a hankali tace zata sauka don har lokacin yana ruke da damtsenta sigh yay kafin yace “am so sorry for dat” kai kawae ta d’aga mashi ya taimaka mata ta sauka ta nufi cikin Makarantar, yana kokarin tashin bike d’in ya tafi kawae sai ganinta yay ta lek’o karaf suka had’a ido tasa dariya ta juya da sauri ta koma shima dariyar yake a fili ya furta “U’r too much Zaraah” daga haka yaja ya tafi.
Washe gari Alhamis bayan ya aje su Makaranta tana kokarin fita ya tsaidata ya tambayeta yau ma sai yamma zasu koma tace eh, ganin ya d’an yi Jim yasa ta tambayi ko akwae wani abu yace da yana son zasu fita ne da rana,itama shirun tayi sai kuma tace to sai ta koma da an tashi ba sai ta tsaya lesson ba yace ba matsala tace eh ai dama past question papers ne ake fidda masu kuma duk ta iya yace Ok zai dawo lokacin tashin ya dauketa tace to, gaba d’aya sukuku take koda taje aji sam hankalinta bai a tare da ita sanin gobe ne Haisam d’in zai tafi ji take kaman ta bishi amman tasan tabbas hakan matsala zai k’ara zame mata gwara ta hak’ura kawae, ana tashi k’arfe biyu saura sai gashi ya zo d’aukartata Haulat ma tace binsu zatai ta tafi gida aka tafi da ita, bayan ya sauke Fatun tana shirin fita taji yace kada taci Abinci sosae yasan ita acici ce zasu ci in sun fita tayi yar dariya kawae ta fice shima murmushi yake ya nufi gida, tana shiga d’akin gwaggo ta nufa lokacin gwaggon na kwance tana bacci bata dad’e da ta kwanta ba bayan tayi sallar Azahar hakan yasa Fatun na shiga ta bud’e ido tace mata har sun dawo da wuri haka saida ta gaidata sannan ta sanar mata da zancen fitar da zasu yi tace to tay sauri taje ta shirya ta amsa da to ta fita, ko Abincin ma bata ci ba ta hau shiri ba tare da 6ata lokaci ba ta gama shiryawa cikin k’ananan kaya riga da skirt kayan roba ne hakan yasa suka kamata sosae shape d’inta ya fita sai ta d’aura After dress tay rolling veil d’in ta fiddo takalma masu tudu ta sa ba k’aramin kyau tay ba don ma kumatunta sun d’an fad’a, tana gamawa bada jimawa ba ta jiyo horn d’in shi saida ta lek’a don yima gwaggo sallama ta iske tay nisa a baccinta hakan yasa ta tafi kawae, zagayawa tay d’ayan side d’in Motar ta bud’e kopar ta shiga wani fitinannan kamshi mai tsuma zuciya ne ya bugi hancinta har saida ta d’an lumshe ido tana kokarin rufe kopar, juyawa tay suka had’a ido ta gaishe shi yay nodding kai tana shirin juya fuskarta ta kalli gaban Motar kaman daga sama taji ya furta “Kinyi kyau sosae” da sauri ta kalleshi with surprise ol over her face don bata tsammaci jin hakan ba saboda tunda suke da ita bai ta6a ce mata hakan ba ko a da saidae in ita ta tambayeshi tayi kyau in tayi gayu sannan yace eh ko in tasa kayan daya siya mata ta nuna mashi sai yace sun mata kyau, ganin ta k’ura mashi ido yasashi d’age mata gira yace “What?” da sauri ta girgiza mashi kai ta juyar da kanta yaja Motar suka tafi acikin ranta ta fara tunanin yadda yake mata abubuwa wanda bai saba yi mata ba can zuciyarta ta ayyana mata don ya sakata Farinciki ne kawae, ta juyar da fuskarta gefe tana kyakkyafta idanu don ta mayar da kwallan dake kokarin taruwa……….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.