Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 15 Complete Novel

๐Ÿ… MATAR DAMISA ๐Ÿ…

(The Wife Of Tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ

ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*

karfe 12am na dare Junaid yana zaune he didn’t fine anything about sarkin tsafi, bacci ne ya fara d’aukarsa a zaune ga kuma laptop a gabansa, kukan kuliya ne ya katsar dashi dasauri ya bud’e eyes d’in sa cike da mamaki yace “Whatt! what this cat are doing here?”

Shi a sanin sa babu kuliya a gidan nan..
kuliyar nan ba’ka ‘kirin ga jajayen idanuwa sai kuka taketa mishi tana fuskantarsa, zuciyar Junaid ne ya fara d’ard’ar shima kansa ya tsorita da ganin kuliyar nan…

abun mamaki mai zai gani?
Sai gani yayi kuliyar tana yun’kurin amai
ta amar da wata farar takarda a cikin leda fara,
tana amarwa kuwa ta 6ace 6att! sai sakon data ajiye masa, daman an turota ne ta kawo masa…

“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un” abunda Junaid ya furta kenam ganin 6acewar kuliyar…

tashi yayi a hankali ya nufi gurin da takardar take Ya karanci sunan Allah sannan yakai hannu ya d’auki ledar takardar ya yageta
wani rubutu ne a bayan takardar wanda aka rubuta da yaren fulatanci
ganin bai iya yaren ba yasa bai tsaya 6ata lokaci wajen karantawa ba kawai ya bud’e kai tsaye….

“Hahaha! Hahaha!! Hahahahaha!!! Junaidu! Junaidu!! Junaidu!!! Wato kana wasa da rayuwarka ko, kada kace zaka sha wahala wajen nema na, domin abune mai wahalan gaske,
ka zauna a iya matsayinka idan har kana son rayuwarka,
kasan dalilin dayasa na barka a raye? Hahahah saboda kai abun harin shalelen Damusa nane, kuma kaine jigon Damusa na,
Damusa na yana nishad’artuwa ne daga 6angarenka,
kaine lafiyar Damusa na, idan kaga ciwonka ya warke to Damusa ne ya mutu, zan iya juyar da tunaninka a duk sanda na ga dama, zan iya azabtar da kai a duk lokacin dana so,
kasani cewa 6ingel na itace farin cikina, ka kula mun da ita………

karshen sa’kon kenam!
‘Dagowa Junaid yayi sannan ya yayyaga letter yana fad’in “Nayi alkawari saina gama da rayuwarka, saina kamoka da hannayena…

yana huci ransa a matukar 6ace mutane biyu ya tsana a rayuwarsa,
daga wannan sarkin tsafi sai kuma Bara’atu wacce tayi sanadiyar mutuwar mahaifinsa……

“Toh amma wacece 6ingel kuma? aina take?
Itace farin cikin sa!!”
Haka yaketa wannan tunanin a ransa….

baisan 6ingel itace Ayush ba ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ

Idonsa ne yayi nauyi ga baccin da yaci idonsa ga takaicin wannan hatsabibin bokan,
da haka yaja ‘kafa yabar cikin d’akin nan ya rufe shi kamar yanda yake a rufe sai kofar ta shafe kamar ba d’aki a wajen,
toilet ya shiga ya watsa ruwa a kansa sannan ya d’auro alwala ya fito yayi lafulolinsa tareda addu’o’in neman tsari daga ubangiji,
daga nan yabi gadon kwanciyar sa,
already ya cire jallabiyan da yayi sallah da ita, daga shi sai short wando da singlet a jikinsa,
bacci ne yayi awon gaba da shi…..

Kwata-kwata Junaid ya mance da Ayush a gadon asibiti….

*****

Ta 6angaren Ayush kuwa Dr. Hasheem ne a wurinta har cikin daren nan bai koma gida ba, yana tsaron Ayush
yayi mamakin ganin ba wanda yazo duba Ayush tin tafiyar su Junaid, shi kuma bai nemesu ba,

shi yana kan kujera ya kasa yin bacci gani yake kamar za’a sace Ayush ya kasa motsawa ko ina…..

ita kuma tana kwance tanata sharar baccin ta, duk da kafin tayi baccin tayi tunanin su Junaid zasu dawo amma shuru….

______meyasa kike son shiga cikin rayuwar mu?

Nace miki ki tafi bama bukatar ki, amma kin ‘ki to yau zaki tafi kiyamar da bazaki ta6a dawowa ba…… ‘Daga wukar hannunsa ya yi zai caka mata!
Wani irin ihu Ayush ta kurma tana juye-ยฒ
Dr. Hasheem ne ya riketa yana fad’in
“Lfy kuwa Ayusha? wani irin mafarki ki kayi haka! Subhanallahi”

Tashi tayi tana huci tana waige ยฒ tare da fad’in “wayyo Allah na zai kasheni, zai kashe ni wallahi….. Gumi duk ya wanke mata ilahirin jikinta duk sanyin A.C dake cikin room d’in…

Addu’a Dr. yake tofa mata tare da sanyaya mata zuciya..
“kinga Ayushat ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai sameki kinji ko? kwanta ki cigaba da baccin ki”

“a’a inaso zanyi sallah ne, kafin lokacin sallar asuba ya gabato”
a cewar Ayush.
Allah sarki bawan Allah shi kuwa ko rintsawa baiyi ba duk yana zaman gadin Ayush!

*****
Washe gari da safe around 10:00
Mom ce tazo d’akin Junaid tana ta knocking ganin shuru baizo ya bud’e ba yasa ta tura d’akin ya bud’u tana fad’in “My son baka tashi bane har yanzu ”

Shi kuwa yana kwance ya baje sai sharar baccinsa yake hankali kwance tin dawowarsa daga sallar asuba.

“Junaid wakeup mana, na gama had’a breakfast since, nasan kana jin yunwa”

“Please Mom leave me a lone, am really tired”.
Junaid ne mai maganar cikin gaga’ar bacci.

“Junaid kaje ka duba jikin yarinyar nan kuwa?”
A cewar Mommy.

“Wata yarinyar?…”
yana magana tare da yatsina fuska!

“ka manta da Ayush kenam? nayi tunanin jiya ka koma gurinta, Junaid marainiya ce fa kuma amana ce a garemu idan kuwa mukaci amana sai Allah ya tambaye mu.”

Junaid tashi yayi ya zauna ya ta6e fuska tare da turo karamin lips d’insa wanda suka ci maroon color sosai yana fad’in
“Mom ke fa kika d’orawa kanki wannan amanar fa, ba wai Allah ne ya d’ora miki ba, nine Allah ya baki amanata….โ€ฆ.”

“Junaiddd please ka zamo mai taimako mana,
Ba haka mahaifinka yake ba, shi mutum ne mai son taimako…….

Kafin ta ‘karisa maganar ya katseta da cewa “I known Mom, hakan yasa ya taimaki wacce tayi sanadiyar barinsa duniya ba, haka kike so nima ya faru da ni KO?…”

Ya juyo yana kallonta da shanyayyun idanuwansa wanda bacci ke shirin ya’kar su, daker yake lumshe idon sa domin jiya bai samu wadataccen bacci ba….

Ran mommy ya sosu da jin kalaman Junaid sai dai ba yanda ta iya dashi
“ka tashi muje muyi breakfast sai kaje ka dubo Ayush, idan kuma baza kaje ba ni zanje ni”
Tana kaiwa haka ta tashi tabar d’akin….

Bin bayan ta yayi da kallo yana wani tunani sai dai bae tsaya yin wani dogon tunanin ba ya tashi ya nufi toilet
Domin yasan halin Mom d’insa yanzu sai tace zata tafi kuma ba isasshen lafiya gareta ba…

After 1 hour
Mom tana zaune a gaban dinning table tana jiran fitowar Junaid amma shuru har yanzu.
Har ta gaji ga yunwa sai dai bazata iya cin komai ba batare da Junaid yaci ba….

sai jin takun sa tayi yana sau’kowa daga stairs a hankali kamar bazai taka ‘kasi ba…
Girman Kai, Isa, gadara, jiji da kai, kwalisa, iya wash duk sun tabbata akan Junaid!

Mom kawai binsa take da kallo itama kanta yayi mata kyau sosai..
yau wankan black janpa akayi
riga yazo masa iya cinyarsa baije gwiwa ba yasha hannun leaps, ga takalmi shima black cover shoe, ya gyara suman kayinsa ya kwanta lufยฒ sai she’ki yake har zuwa sajen sa zuwa short gemun daya bari sunyi ba’ki qirin sai sheqin da suke, hasken fatan sa ya ‘kara bayyana, ga wani siririn glass da ya d’ora akan dara ยฒ idanuwansa gwanin burgewa, kayan nan sun kama jikinsa sosai!!
Yana takowa a hankali but hankalinsa yana kan agogon hannunsa da yake d’aurawa….

A haka ya nufi dinning a nutse ya zauna yana fad’in “gud morning my Mom..”

‘Dan hararar sa tayi bata kula shi ba ta maida hankalinta kan kular da take zuba musu ferfesun kayan ciki a plate, ta had’a musu tea mai kauri da cake, sai kuma ta 6angare guda roll eggs ne with bread, sai kuma apple da banana da pineapple, watermelon, sweet melon, pawpaws and other things duk an yanyanka su a cikin dinner set…..

Cikin nutsuwa sukayi breakfast
Junaid ne ya fara cire hannu ya goge bakinsa da taisho sannan ya d’auki phone d’insa da key d’in motar sa,
Ya nufi hanyar da zai sadashi da waje yana fad’in “Mom ki daina fushi dani, sai na dawo.”

Kayataccen murmushi tasau sannan tace “a dawo lafiya my son”

A harabar gidan ya nufa, ya shiga motar sa
Ya karya kwana a hankali sannan ya mi’ki hanyar get already kafin ya Isa mai gadi ya bud’e masa, a d’ari ya bar gidan kamar walkiya ko bayan motar ba’a gani…

Mommy tana zaune kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa,
Ita a duk sanda Junaid zai fita tana tararradi da fargaba domin ba wani cikakken mai hankali bane, ciwon sa zai iya zuwa mishi a kowani lokaci,
Kuma tsoronta kar ya hallaka mutanen dake waje…..

****

Junaid can Headquarter ya nufa wajen aikin su dake cikin Abuja,
Bayan ya gaggaisa da abokansa da kuma oganninsa direct office d’insa ya wuce domin gudanar da wasu ayyuka…

Duk da an dakatar dashi daga gurin aiki sakamakon cutar sa hakan baisa ya daina zuwa jifa ยฒ ba,
Ba korar sa akayi ba andai bashi hutu ne duk wasu ayyukan yana yinsu a gida……

Around 6pm yabar h-quarter ya nufi hanyar hospital, kafin kace Mae Junaid ya Isa domin shi baya tafiya da mota a hankali….

____________ da sallama a bakin sa ya shiga cikin room d’in da Ayush take,

Dr. Hasheem ne zaune a bakin gadon da Ayush take tana zaune itama yana bata abinci a baki
yana fad’in “idan baki samu kinci abinci ba taya zaki samu karfin jiki, kinga allurar tana nan zanyi miki idan baki ci ba….”
kamar wata Yarinya haka yake bi da ita akan taci abinci.

Shugowar Junaid ne yasa hankalinsu ya koma kansa!
Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, jikinsa ne ya soma za’kami, wani irin yawu ya had’iya kamar wanda ya had’iyi dutsi, ‘kololuwar ba’kin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa….

Da sauri Junaid ya nufi gurin da Dr. yake ya cakumi gaban rigar sa ya mi’kar dashi yana fad’in
“Dr. Hasheem what did you means about her? meye matsalarka da ita, ko akwai ala’ka ne a tsakanin ku?…”

Dr. ri’ke hannun Junaid yayi ya zamar da hannun daga kwalar daya ri’ke masa
Shima yana fad’in “captain Junaid kenam Kai meye na tada jijiyoyin wuya akan ta bayan ita ba komai bace a gurinka.”
Ya karasa maganar yana masa kallon tuhuma….

Murmushin takaici Junaid yayi sannan yace “she’s my life”

Junaid bai tsaya jiran abunda Dr. zaice ba ya finciko hannun Ayush wacce tana zaune ta zuba musu eyes ita bata San akan Mae suke wannan sambatun ba,
Sai ji tayi an jawota.
zai fita da ita Doctor Hasheem shima ya ri’ke d’aya hannun Ayush yana cewa “Ina kuma zaka kaita ai bamu sallameta ba”

“This’s our hospital bana bukatar sallamar ku…”
Junaid ne yayi maganar yana faman jan Ayush
Shima Doctor ya dage akan baza’a fita da ita ba yana ta janta ciki shima,
Haka suka sakata a tsakiya!
wannan yana jan ta tanan wancan yana janta ta can.

“wayyo Allah zaku cire mun hannu Ku sakeni, taimako jama’a, menayi muku ne haka…..”
Kuka ta fara rerawa.

Janaid fa ran maza ya 6aci wani irin wulli yayi da Ayush gefe Wanda shima Dr. bai san lokacin da ta zame masa a hannu ba,

Wani irin sha’ka Junaid yakai wa Dr. ya Kama wuyansa sosai ya d’aga shi sama da hannu d’aya,
Idonsa ne ya koma blue like tiger eyes,
Ransa ba karamin 6aci yayi ba kuma hakan yakan haifo da matsala irin haka…

Dr. ri’ke hannun Junaid yayi yana so ya ‘kwaci kansa amma ya kasa,
Numfashin sa ne yake fita sama ยฒ

Ganin haka yasa Ayush ta fice da gudun gaske ko waiwayowa bayan ta batayi, gaba d’aya ta gama tsorita!

Da gudun gaske tazo ta wuce security masu tsaron get d’in asibiti,
Suna tambayanta meya faru amma ko tsaya sauraronsu batayi ba, ita dai ta kanta takeyi, gani take kamar yana biyota a baya, hakan yasa ta ‘Kara bawa gudun nata wuta,
Ita kanta bata san Ina ta nufa ba…….

Security ganin Ayush ta fita da gudu yasa suka shiga ciki domin ganin abunda ke faruwa….

 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasaย ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Documentย 

(am nace ba na tausaya maka Doctor tinda ka shiga hannun tiger, bayan kasan halin sa mezesa kayi jayayya dashi? wato Kai lovayya ko ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ )..

*MASHA* *ALLAH*
๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™

 

Some of related Hausa Novels

*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*

*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

Back to top button