Mejo Najeeb Page 38 By Autar Alheri
“Tana fitowa tanufi kitchen ɗin ganin duk anfitarda kayan abincin yasa tafito perlor karo sukayi itada mansura datafi to daga part ɗin Hajiya umma, zagawa isseta tayi zata wuce dudda taji mansura tabanketa amma tayi kamar batajiba, tako ɗaya tayi gana biyu taji antriƙo rigar ta tabaya, cak tatsaya tana mamaki miyasa zata riƙo mata riga bayan ita tabanketa amma kuma tariƙota.. “ke dabbar inace? Zakizo kibanke mutun kuma kiyi kamar bakiganiba bamanya agidankune?? Tatsinkayo Muryar mansura tana kora mata wannan bayanan…..lumshe kyawawan idanuwanta tayi ahanki tasake waresu akan mansurar dede lokacinda tajiyo gareta, ɗan gutun murmushi tayi kana tace “mutun kuma? Aina mutun yake anan? Domin nidai banga mutunba sedai karya matsananin haushi dakogajiyama batayi, taƙarasa zancen tana wani marmar da idonta.. ido mansura tazoro tana faɗar whatt?? Karya nice karyar?? Tafaɗa tana nuna kanta. “Of course gazahiri kingani wannan aikin ai se karnukan jeji, cewar isseta cikin dakiya da tabbatar da zancenta…wani irin ƙololon baƙin cikine yatadowa mansura cikin mugun fishi taɗaga hannu zata dokawa isseta mari,,,aicikin zafin nama isseta tariƙe hannun tareda sauke mata marinda seda taga taurari. Agigice mansura tadafe kumatunta tana duban isseta cikin mamaki da tsoro.. itako ƙarasowa tayi dab da,ita yadda zasu iya jiyo numfashin juna kana tace “kigaggauta janye makamanki akan Maryama domin kuwa bata taki takeyiba yanzu daman ƙwari zata kara bachakuri chichiba idan kuma ba hakaba wlh zakisha mamakina bari ganina hakan kice zaki tatamin iskanci nawuce duk yadda kike tunanina wlh idan kunne yaji tojiki yatsira taƙarasa zancen tana ɗalla yatsunta biyu dede fuskar mansura yadda suka bada sautin ɗass,ɗass kana tajuya zata bar wurin..”That’s very good Anty Maryam kinyimun dede wlh hakan yayi kyau karki bawa kowacce shegiya agidannan damar renaki duk wadda ta shiga gonarki ci ubanta babu abinda za’ayi wlh ko agarinnan balle agidannan domin matar mejo najeeb tawuce taki ga uban kowa, cewar sajad tacikin jin daɗin yadda isseta tayiwa mansura domin yana zaune a perlor tunfarko yana kallon abinda kefaruwa jiran yakeyi yaga yadda abin zekasance kafin yaɗauki mataki seyaga tadaukarwa kanta….jiyowa kawai isseta tayi tasakar masa murmushi kana tace “tabbas kuwa ƙanena kafaɗi da babbar murya uwar gidan najeebullah tawuce reni idon kowa domin kuwa matar soja ma ai soja ce, tana gama faɗar hakan tajuya zuwa pert ɗin Hajiya mama….wani irin murmushi jin daɗi sajad yayi afili yace wayyo Allah yah najeeb yaɗauko matarda zata gyarawa wata zama agidannan wlh domin inason mace takasance irin Anty Maryam wadda bata ɗaukar reni, harara ya ɓallawa mansura kana yace “aisekici ga daba da shigewa mijinta ko shiga lamarinta wlh kuwa kiɗanɗani kuɗarki agunta dakuma gun mijin nata banza marar class kana son wanda dakaida shara bakuda banbanci awurinshi, yana gama faɗar hakan yafice warshi.Tashi tayi cikin mugun ɗacin rai tanufi bedroom ɗinta domin yau kukanma yaƙi zuwa, ayau tayi nadamar zamanta gidannan domin tagano Hajiya umma bazata taɓa sawa yah najeeb ya auretaba dudda tana gani zata cilastashi aurenta ne amma tunda batada niyyar hakan garama ta tattara tabar musu gidansu domin bazata iya kallon wannan tozalcinba,,tana shiga tashiga haɗa kayanta komi seda taɗauke taɗauki car key ɗinta tafito kawai tayi tafiyarta ko hajiya umma batasan tabar gidanba..A perlor Hajiya mama kuwa Ummu ce zaune da Anty hawwa yayinda juwaira ke kwance ƙasa tana chat da yah balah inda yake gaya mata tazo yayi yayi missing ɗinta domin har jiyake kamar yabiyo bayanta… ɗan tsaki taja kamin takashe wayar kawai batareda tabashi amsaba, domin ita yanzu yadda zata samu soyayyar mejo najeeb ce damuwarta..”Wai Ummu waye wannan wanda aka kira video call ɗazu?? Anty hawwa ta tambayi Ummi domin ita sam batasan najeeb ba ko sunan mijinda aka aura mata itafa bata saniba amma tanason tasani ayanzu….”yah najeeb ne, Ummu tabata amsa ata kyaice…”waye kuma yah najeeb? Bantaɓa ganinshi agidannan ba. “Humm amarya kenan, to yah najeeb shine babban yayanmu agidan, cewar Ummu tana cigaba da kallonta……ido anty hawwa taɗan waro kana tace “to bacewa akayi babba yaron gidannan shine mijinaba?? Aina ɗauka wanda yakirashi awayar shine babba wlh. Taƙarasa maganar cikin mamaki.. wani irin kallo ummi kemata wanda yake bayyana asalin mamakinta akan furucin anty hawwa kafin tagirgiza kanta kawai tana faɗar “tab ɗijam wai kina nufin yah munir kikeyiwa kallon mijin naki? Hum to kemiyakaiki auren mijin dabakima saniba?? Ummu ta tambeta tana kafata da ido cikin tuhuma.. “Hum bazaki gane bane kedai kawai gayamin domin wannan auren biyayyar iyayene kawai tunda daga farko ai ƙanwata aka bashi wadda kika gani agidannan isseta daga baya ne data tafi yawonta auren yadawo kaina yanzu dai Please kinunamin waye mijin nawa domin wlh murmushi kawai danaji najiyakwanta min arai inaso naganshi please.. “hummm kawai Ummu tace tareda janyo wayarya tabuɗe wata folder meɗaukeda picture ɗin mejo najeeb sunfi 50 tamiƙa mata, kawai batareda tace mata komaiba.Karɓa tayi tana kallon picture ɗin, ido tazaro cikin mugun ruɗani murya na rawa take nuna picture ɗin inda yake sanye da kayan sojoji yana zaune akan mota waya maƙale akunnenshi tace “wan..wan..wannnan shine mijin nawa wannan ɗin?? Wayyoo Allah Abba ka kyauta mun daka aurar dani ga wannan haɗɗen guy ɗin wow he’s very handsome wlh. Tafaɗa cikin nuna zalamarta akanshi afili, tana kallon sauran picture ɗin…wani mugun tsaki juwaira taja kamin tace “iska nawahalarda me kayan kara anty hawwa domin wannan guy ɗin yamiki nisa kima Sena murnar mijinkine domin wlh baze zauna dakeba.Ɗan shiru anty hawwa tayi tana kallon ƙanwar Tata kamin tace “mikike nufi juwaira muguwar fata zakimun baƙin ciki kikemun kome? Wannan wacce irin banzar maganace hakan? To tunda baze zauna daniba aike sekije ya zauna dake wai ko sonshi kikeyine bansaniba?? “Au seyanzu kikasani? Cewar juwaira kafin tayi guntun murmushi taci gaba da faɗar”idan nasoshi laifine? Tunkafin kisanshi nasanshi kuma nake dakon soyayyar shi, shiyasa nace baze zauna dakeba domin kuwa bazan bari kurasamin farin cikinaba sabida babu yadda za’ayi yazauna damu duka ukku ita isseta ubanmu ɗaya kekuwa uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya sabida hakan doline ɗaya ce zayi nasara kuma wlh komizefaru sedai yafaru amma srkunbarmin mijina domin yah najeeb nawane dan ki kaɗai akayi shi kuma zan nuna muku nawane ɗin da gaske.. “tasss kikaji anty hawwa taɗauke ta da kyakkyawan mari tana watsa mata mugun kallo cikin takaici take faɗar”yoshe kikazama marar hankali juwaira?? Mijin nawa? Kuma agabana? Yoshe reni yashiga tsakanina dake hakan?? “Tun ranar da kika kulla alaqa da muradin raina tun lokacin reni yashiga tsakaninmu bakuma mari ba kokasheni zakiyi wlh sedai kikasheni amma bazan barmiki yah najeeb ba, cewar juwaira cikin tafasar zuciya da baƙin kishinda kecinta.”Tofa 🤔yau inaganin ikon Allah wai miye hakan kukeyine? Duk akan namuji ɗaya wanda bemasanda ku ba a duniya kuke wannan tashin hankali? Ummi tafaɗa cikin mamakin wannan lamarin nasu….wani mugun kallo anty hawwa tawatsawa Ummu kana tace “besanda niba amma yasanda aurena akanshi kuma yasan inada hakki akanshi sabida doline zesan dani wlh daya dawo gidannan zakuga asalin wacece hawwa…..wani mugun kallo juwaira tawatsa mata zatayi magana kenan isseta tashigo perlor dauke da sallama abakinta.Dukkansu da kallo suka bita…itama kallonsu tayi sheƙeƙe kafin tayi magana ummi tace “anty Maryam harkin fito?? “Eh nafito Ummi ina mama? Tana ɗaki inaga sallah takeyi…”okay dama zan tambetane miza’agirka agidan yau?? Idan tafito kitambeta seki sameni a perlor.. “okay to amma ai yau Hajiya umma ce dagirki domin yau girkin mama yafita baranazo na tambeta. “No yizamanki barana tambeta dakaina cewar isseta tana barin perlor…..wani mugun tsaki anty hawwa taja afili tace “wai neman gidin zama aiko duk wannan bata fiddake wlh isseta dama bansan wannan ne mijinba amma yanzu za’abuga asalin wasan..tana rufe bakinta Ummu ta ƙyalƙyale da dariya cikin shaƙiyanci tace “aiko indai gindin zama ne anty Maryam tasamu kedai kemanshi ayanzu domin gindin zama duk bewuce soyayyar wanda ake yaƙin akanshiba kuma ita tarigada tasamu kekuwa bemafasan dazamankiba, taƙarasa maganar tana koma sakin dariya…gabaki ɗaya ta ƙukardasu hakan yasa bawanda yace da ita komai a cikinsu amma tabbas da ba’a gidansu suke zauneba wlh dasesun lakaɗamata shegen duka gobe bazata ƙara kawo musu renin hankaliba..Isseta nafitowa taga anashigiwa da kayan abinci ana kaiwa kitchen wasu daga cikin sojojin gidanne keshigowa dasu yah munir nahiye dasu abaya,,,,suna haɗa ido tasakar mishi murmushi, shikuwa yace “anty Maryam Barka da fitowa, “yawwa barka yah munir tafaɗa cikin sakin fuska..”ido yaɗan waro tareda rike baki yace “Please dan Allah kidena ce mun yaya karisa babban yaya yakarairayani abanza wlh bazan iya daukar dukan sojaba, yaƙarasa faɗa yana ƴar dariya…itama dariyar tayi tana faɗar aikuwa bazan denaba tanufi part ɗin Hajiya umma…shikam kitchen ɗin yashiga bayan yakira siyana suka shiga jera kayan abincin.Koda tashiga perlor hajima umma bakowa hakan yasa tanufi bedroom ɗinta nanma bataga kowaba juyiwa tayi zata fito tariƙa jiyo sautin magana kamar bana mutaneba kamar kuma Muryar Hajiya umma cikin mamaki taƙarabin ɗakin da kallo amma ba kowa juyawa tayi kawai zata ficewarta idonta yasauka akan wata kofa agefen widroup ɗinta, ƙarasawa bakin ƙofar tamirɗa seta jita kulle, gaya kuma tana jiyo Muryar Hajiya umma aciki.. gimbiya mardeeya dake biyeda ita tunɗazu batareda tasaniba itace tashiga ya mirɗa key ɗin ƙofar tabuɗe isseta na ƙara mirɗawa seta buɗe,,,shiga tayi tukunnah tarufe setaga hanyace me nisa tafiya tashigayi hartazo dede ƙofar wani bedroom dake cikin wurin..adede anan taji maganar Hajiya umma raɗau tana faɗar “Nima bansan misuke nufiba amma wlh bazan basu wannan damarba doline ayi komai aƙare domin aikina ya kammala,,bataji me akace mataba sedai kawai taji tace “a’a ba gimbiya laweesat bace amma tabbas akwai ko wacece tashigo gidannan, shirutayi tana sauraren maganar da’ake mata kafin takoma cewa “shikenan aida yadawo zansan abinyi za’ayita taƙare kawai domin tabbas sunason mayarminda hannun agogo baya..isseta nacikin sauraren ta setaji kamar motsi za’sfito hakan yasa tayi saurin ficewa daga wurin tafoto zuciyarta fall tunani anya Hajiya umma nada gaskiya kuwa mitake aikatawa ne datake zancen za’amaida mata baya? Wanene zekawo ayita taƙare? Ya’akayi Hajiya umma yasanda maah ɗinta? Min mike faruwa agidanan? Wacece matarda ta iskota ɗakin mejo?? Wake zuba aiyukkan sihiri acikin duka abincin mutanen gidan? Gaskiya zuciyarta takasa yadda da Hajiya umma domin itadai tunda tashigo gidannan hankalinta be kwanta da matarba sedai ba yadda zatayi da ita tunda mahaifiyar mijintace? To amma anya wai itace mahaifiyar shi ba Hajiya mama ba domin Hajiya mama tafi nuna kawaici akanshi maybe itace tahaifi najeeb kauda idone takeyiwa Hajiya umma, kai gaskiya ƙwaƙwalwarta tashiga ruɗani amma doline tasakawa Hajiya umma ido domin dai wlh baya yadda da ita ba…da wannan tunanin ta isa kitchen ɗin koda taje a gama jera komai har yah munir tafice…kayan abincin tashiga dubawa tagansu lafiya qalau murmushi tayi kawai kana tashiga neman abinda zata dafa, ɗora sanwar tuwon simo tayi cikin ƙanƙanin lokaci tatuƙa tuwon tasakashi sulala,,,tana cikin haɗa kayan miyar agusi Ummu tashigo kitchen ɗin cikin farin ciki tace “anty Maryam harkin fara ke kaɗai?? “Eh Ummu gashi kuwa inayi.. “to shikenan kawo natayaki tafaɗa tareda fara gyara mata kayan miyar…sosai Ummu tazage tataya isseta aikin sukayi towo damiyar su wadda tasha bisashen kifi da naman kaza, bayan sun gama suka haɗa fruit salad kawai tareda dafa coffee ko akwai masu buƙatar shi,,,nantake gidan yaɗauke da ƙamshi matada tsohuwar yunwa🤣seda suka gama komai suka jera a dining suna cikin gyara kitchen ɗin ne Hajiya umma tashigo tanabin kitchen ɗin da kallo kamin tamayarda idonta kansu tace…!




