Mejo Najeeb Page 27 By Autar Alheri
“Wata mata takawowa mama bintu Isseta hargida inda tace tsintarta tayi tana kuka shine tamayarda ita gidan…faɗin farin cikinda mama bintu da mlm Musa suka shigama ɓata lokacine, sosai sukayi murna da bayyanar Isseta cikin farin ciki suke yiwa wannan matar godiya batareda suntsaya tunanin ina ta tsinci Isseta ba harta maidata gida sam idonsu yarufe da murnar dawowar ƴar amanar tasu..ahakan wannan matar tayimusu sallama tafi.Tofa jama’a wannan matar bakowa bace face gimbiya mardiya domin itace takarɓi Isseta agun hatsabiban aljannu da suka saceta abisa umurnin Haniya tabawa…ito gimbiya mardiya tagane yarinyar ne sakamakon suntaɓa zuwa ganinta a Niger itada umaima alokacinda gimbiya laweesat taturasu amadadinta domin tunda Hannah tahaifi yarinyar Allah yasakawa gimbiya laweesat son yarinyar sedai ba yadda zatayi tunda ba jinsinsu ɗaya ba amma lokaci zuwa lokaci tana sakawa umaima taɗauko mata ita taganta batareda Hajiya Hannah tasaniba domin ita Hajiya Hannah sam batasan da gimbiya laweesat ba balle tasan tasaka ana bibiyarta domin bata tsaro. To kunji yadda gimbiya mardiya tasan Isseta Hakan yasa dataganta taganeta kuma da takaita gun gimbiya laweesat setake gayamata abinda kefaruwa wanda yasa Maryama tadawo ƙasar Nigeria dazama hannun mama bintu.To daga wannan ranar kullun se gimbiya mardiya takawowa Isseta ziyara kuma tana ɗaukarta takaita gun gimbiya laweesat tajima acan inda gimbiya laweesat kezo mata afili taganta rabi mutun rabi kifi shiyasa sam Isseta bata tsoron Maah tun tana ƙaramarta domin sosai take wasa da jilar kifin maah idan tazo…sannu ahankali shaƙuwa meƙarfi tashiga tsakanin gimbiya laweesat da Maryama inda take kiranta da Maah tun tana ƙarama…..sannu ahankali tafiya tabi hanya har maryama tagirma tafara zama cikakkiyar budurwa kuma ahakan shaƙuwarsu da Maah naƙara ƙaruwa hartakai dakanta take zuwa domin taganta taɗauke ta uwa mahaifiya, Itama taɗauke ta amatsayin ƴa Hakan yasa duk wanda ketareda gimbiya laweesat yasanda zaman maryama kuma suke iyakacin bakin ƙoƙarin su wurin ganin sunbata kariya 💯 akan sharrin Hajiya tabawa.Daga gefe ɗaya kuwa sewani abin ya ɓullah acikin gidansu IssetaWannan abin kuwa bakomai bane face yadda mama bintu Takoma yiwa Isseta halin ko inkula sam babu ruwanta da sha’anin yarinyar kuma komi za’amata batacewa komai inkuwa yankata akayi agabanta ku kallonsu bazatayiba sedai idan angama tashige ɗalinta tayita kuka tarasa yazatayi Allah yasani tanason saka yarinyar ajikinta tazame mata uwa tagari me share hawayen ƴaƴanta amma tarasa miyasa kotaso tayi Hakan takejin kamar asaka mata takunkumi abakinta….inda kuwa matan gidan suka samu wannan damar suna musguna wa Isseta suka maidata baiwa acikin ƴaƴan su, har aka kawo wannan lokacin dazamanta gidan yaƙare tahanyar korarda Abba yayi mata….duk tsawon wannan shekarun da Isseta tayi ahannun mama bintu Hajiya Hannah takasa zuwa Taga halinda yarta keciki kuma Haka Alhaji Abdussalam dukkansu sun wofantarda rayuwar yarinyar har inda Alhaji Abdussalam yafara mulkin ƙasar Niger Basuyi tunanin karɓar ƴarsu ba sedai suka aikawa mlm Musa maƙodan kuɗaɗe domin kulada ita…amma fa wani lokacin dukkansu suka shiga damuwa marar misaltuwa akan rashin yarinyar sedai kosunso sayi wani yunƙurin akanta bazasu iyaba….kuma duk wannan abin dake faruwa dasu har su mama bintu sharrin Hajiya tabawa ne domin tasamu damar ɗauke maryama Takoma hannunta sabida tasamu nasarar samun saka hannunta akan takardun kadararta da Alhaji madu ya mallaka mata, kuma gashi haryanzu batayi nasara ba…..koyanzu da mama bintu ta’iya buɗa baki tayiwa mlm Musa magana akan zancen Isseta da wannan zuwan da Hajiya Hannah tayi duk yasamu asaline akan lalata wasu tsafukan Hajiya tabawa da gimbiya mardiya tayi har suka samu damar waiwayar rayuwar yarsu…..wannan shine asalin labarin Isseta.Mukoma cikin labarinmu kaitsaye.Tunda Hajiya Hannah tafita daga gidansu Isseta ranta ke masifar yimata ƙuna sosai take jawa Hajiya tabawa Allah ya’isa babu adadi domin kuwa duk itace musabbin wannan al’amarin, kuka takeyi sosai azuciyarta wanda babu hawaye tanajin tausayin tillon ƴar tata kotana ina ahalin yanzu? Ko awanne hali take? Allah kaɗai yasani har suka isa masaukinsu batadena wannan kukan zucinba….iyya hassi kuwa sojojinnan nafita da ita Basu zarce ko ina da itaba se hidikwatar sojojin Nigeria dake cikin garin gwambe inda suka Nemi alfarman su ajiye musu ita tare da horo me tsani harsu tashi komawa Nigar kuma umurnine daga matar shugaban kasar Niger ɗin…aiko sunajin Hakan suka karɓi iyya hassi tare da turata wani ɗakin suka garƙame.LagosSeda suka gama duk abinda zasuyi agidansu general aliyu kana suka fito atare kamar yadda suka shiga, mufeedah naganin fitowarsu tataso cikin sauri domin ita tashirya dama fitowarsu take jira….bawanda yace da’ita komai harsukayiwa habbey sallama sukabar gidan…sunyi tafiya meɗan nisa inda suke cikin mota ɗaya su ukku mufeedah na agaba tare da diriver wato captain Ameer babban yaron general aliyu. Ɗagowa mejo yayi yabuɗe baki ahankali yacewa capital Ameen sunufi gidanshi dake cikin banana island ɗin… okay kawai captain Ameer yace inda general aliyu yabishi da kallon meɗaukeda tambaya tamizasuyi acan?? Basarwa yayi kamar beganshi ba har suka ƙarasa gidan…fitowa yayi yanufi cikin gidan kaitsaye bayan captain Ameer yayi Perking, da kallo suka bishi dukkansu amma ba wanda yace komai….ko minti 5 beyida shigaba segasu sunfito ajere kamar wasu taurari Isseta tayi shirinta cikin doguwar rigar less Marron color merashin baƙi kana taɗora baƙin mayafi akanta, haƙiƙa tayi kyau iya kyau duk sharrin mutum be Issa ya kusheba.Tunda suka fito daga cikin gidan general faruk yace “wow Masha allah wacece wannan beautiful baby ɗin friend? Yatambayi general aliyu….Ɗan murmushi general aliyu yayi kamun yace “ato gadai tanan ƙanwarmu ce amma wlh karufawa kanka asiri dazancenta indai mejo nakusa nadai nagayama, yaƙarasa zancen cikin tsokana…”tofa iKon Allah aa to nadena bazan ƙaraba koya kikace ƙanwata? Yayi maganar yana tambayar mufeedah datayi mutuwar zaune wurin kallon Isseta domin baƙarya tatafi da imaninta…ajiyar zuciya tasauke tana murmushi tace “wlh kuwa yanana haka zancen yake.Kafin waninsu yaƙara yin magana ne sukaga motar mejo ɗin yashigo gidan wadda captain Jameel keja,,ita yabuɗewa Isseta tashiga Shima yashiga kana suka Halba motocin akwalta…gabaki ɗaya general faruk da mufeedah suncika da mamakinshi amma general aliyu ko ajikinshi hasalima cewa yayi aiki yasameku indai mamakin najeeb zakuyi…..ahakan har sukazo wani mool, sukayi Perking motocinsu sukafito tare da nufar cikin wurin…babban wurine sosaina manyan mutane.Mufeedah ce tazo wurinsu tana bawa Isseta hannu tace good evening antynmu….da mamaki Isseta da mejo ɗin duk ke kallonta kafin Isseta ta amsa mata tayi saurin cewa “Sunana mufeedah ni ƙanwar yah najeeb ce inasonki ƙawa antynmu kema zakiyi ƙawance Dani? Tatambaya tana riƙo hannun Isseta ɗin…. murmushi Isseta tayi wanda yaƙara bayyanarda asalin kyawunta kafin tabuɗe baki cikin sexy voice ɗinta tace “Masha allah mufeedah nikuwa sunana maryama ba anty ba kamar yadda kike faɗa, Itama tayi zancen tana riƙo hannun mufeedah ɗin….murmushi su general aliyu suka yi sunabinsu da kallon birgewa yayinda mejo kuwa yadasƙare yana kallon zallar kyawun Isseta yanajin yadda sexy voice ɗinta kehuda kowanne saƙo najikinshi yakafeta da blue eyes ɗinshi ko kiftawa babu, suko su general faruk se kallonshi sukeyi suna murmushi cikin mamakin yanayin da yashiga lokaci ɗaya….kamar daga sama suka tsinkayo muryar dady Alhaji Khamis kenan, yana faman dokawa mejo najeeb kira amma sam bejishiba harya ƙaraso inda suke tsaye……!

