Gargadar So Chapter 117 By M Shakur
Cikin murya mai mugun mugun sosarai Khaleel yace “Hauwa’u Alhassan Na Sak………!” Dawani mahaukacin sauri Hawwa tashige jikinshi takai duka hannayenta biyu tadaura kan lips dinshi ta taushe bakinshi da duka karfin datake dashi aduniya tana kallon kwayar idanunshi lips dinta nawani irin bari kaman takama da shocking na electricity tana kallonshi hawaye na fita daga idanunta tace “w…….wa……wat……are….yh…u…..trying to tell me”? Daidai hawaye na gangarowa daga idanunta majina daya tsinke sosai nafitowa daga hancinta wani irin automatic gumi na ketowa daga goshinta tana kallon Khaleel dake mata wani irin kallo kawai ya kabar da hannuwanta saida Hawwa tai tangal tangal tai baya kaman zata fadi ta dafe mota, Khaleel yanunata da hannu kirjinshi nawani kalan beating yabude baki zaiyi magana azuciye saikuma idanunshi suka shiga juyawa dawani irin sauri Hawwa tace “Khale….!” Kafin tai kanshi yayi luuuuuuu zai zube Salman yayi wani jumping yatareshi yana jijjigashi, Hawwa tazo dagudu zata tabashi strictly Salman yace “you are not allowed to touch Yallabai! Babu relationship daya rage tsakanin ku kuma! I’m sure he made that crystal clear” kafin Hawwa tamayi wani abu Salman yadaga Khaleel chak yayi wajen mota dashi Hawwa jitayi kaman ana daddatse mata ruwan da naman jikinta da kyar da dafa mota ta tashi ta tahozatai wajen motan Khaleel but har Salman yaja mota sunbar wajen. Hannu Hawwa tadaura akai tafashe da kuka sosai sai kallonta ake daidai wasu yan sanda na shigowa plaza guda biyu sanye da uniform, da kyar ta iya tashi tamusu bayani yar sanda ce ita office number nata da ID number nata, tace fada sukayi daya ya suma an tafi dashi cus bataso Khaleel yashiga trouble tace daya kuma gashi amotanta, sannan tazo tabude musu baya suka tayata daukan Baban Yaseer suka sashi a motansu suka tafi dashi taciro kudi masu yawa tabasu tace “please take care of the payment, I know him he’s a family friend” ganin kudi da yawa suka karba suka wuce sannan tawuce da kyar tabude motanta tashiga takai kusan 2min azaune takasa driving sai tashiga addu’a sannan jikinta yarage bari ta kunna motan tana da gudu zuwa asibitinsu tun a parking space take kallon wajen but babu motansu daidai tafito saiga wani baturen Dr tareda Dr ta na ranan zasu shiga mota dasauri tace “is my husband here please”? Atare sukace “they’re taking him home we are going to your house now” faduwa gaban Hawwa yashigayi sosai tajuya tawuce motanta ta kunna su Dr na fita tana binsu abaya har gidansu.Scanning motan su Dr akayi aka barsu suka wuce direct ita take wucewa ciki ba’a duba nata motan tunda tai aure agidan, but sai taga bayan su Dr sun shiga an rufe gate, security gate yazo wajen motanta hakan yasa ta sauke glass kasa yace “Madam Salman yace Oga yabasa specific order not to let you into his house that aurenku yakare” Security yayi maganan casually no any emotions attach cus this is something dat always happens agidan nan, ana gamawa da mace bazata kara shigowa gidan nan ba kenan har abada, wani kalan faduwa gaban Hawwa yake tabude baki zatai magana taji kuka yazo mata kuma bataso taima security kuka, mutumin yace “I am sorry but I can’t let you go through unless I receive another fresh order, good bye Madam” yayi maganan yana komawa gate abinshi rike da bindigarsa.Wani kalan sanyi Hawwa keji tundaga tip na fingers nata na toes har zuwa the smallest tiny silin gashin kanta, kaman Organs nata are shutting down haka takeji, kaman ranta da zuciyanta na barin jikinta haka takeji, jikinta na shaking sosai, like is this happening? She has always wanted saki, ita takaishi court da kanta, ita keta demanding ya saketa, but now da kusan ai yama saketan ne toh maybe ya aiko mata da takardan agida, but just gidan nan dataji ance she’s not allowed to enter taji kawai organs nata na shaking cikinta na duri ruwa, wlh kawai taji cikinta na kuka gululuuu wani mahaukacin zawo taji yataso mata, da bala’in sauri ta tada mota tashiga zuba gudu a titi 30min yakaita unguwansu babu kowa a kofar gida kashe motan tayi ko wayanda da purse nata bata iya ta dauka ba da gudun gaske ta shigo gidan saida Umma dake tsakar gida tace “wayyooo waye haka” Hawwa ta sunkuci buta sai bayi Umma tace “Hawwa! Lafiya?” Dasauri Ammi da Baba suka fito daga dakin Hawwa jin ankira Hawwa daidai Hawwa na sakin wani wawan zawo mai karan gaske. “Paratatatttaaaa!” Umma tace “ayya ashe gudawa takeyi haba nifa ince naga yarinya ta shigo a haukace tana gudu!” Hawwa zawo take mai kullewan ciki takai almost 10min abayin tagama komi amman ta tsaya abayin takasa fitowa bata tabaji arayuwanta tana shakkan Baba da Ammi ba kaman yau! Kawai taji Allah yasama zuciyanta wani mahaukacin tsoronsu da batama san ta yaya zatayi ba.Baba da Ammi na tsaye dan ganin Hawwa a gida sunsha jinin jikinsu barinma labaran komi da Ammi tagama gayamai dan bata boyemai komiba.Gajiya da tsayuwa Ammi tayi kusan 20mins tace “bacci kikayi abayin ne Hawwa bazaki fitoba”? Fashewa Hawwa tayi da kuka sosai duka jikinta rawa yake da kyar tabude kofa tafito daga Baba har Ammi kwayan idanunta kadai suka kalla sukasan wani abu yafaru Hawwa tai zuru zuru Ammi taga daga jiya data ganta zuwa yanzu har tadan fada,Baba kawai yajuya fuuu yakoma dakinta cus ayanda yakejin kanshi zai iya daga sandunan nan yama Hawwa dukan da saita suma ya rantse da Allah! Ammi ta tsaya tana kallonta tundaga kan yanda Hawwa bamata iya tafiya da kyau kaman kwan cikinta yafashe Umma ta ijiye shinkafan datake gyarawa takalli Hawwa sannan takalli Ammi dake mata wani kallo tasan wani abu yafaru, Ammi itama tawuce takoma daki Hawwa kawai saita taho wajen Umma tafashema Umma da kuka tace “Umma ki taimakeni Ammi da Baba na fushi dani Umma” wlh ba karamin tausayi Hawwa tabama Umma ba har zafi jikin yarinyar yayi dudda batasan meke faruwa ba amman tasa hannu ta gogemata fuska tace “ya isa daina kuka komi yayi zafi maganinsa Allah, suna jiranki wuce muje” Umma takama hannunta yanda Hawwa ke tafiya ko da wani zai shigo gidan da baisan meke faruwa ba dariya zaiyi kaman wacce ke shirin guduwa Umma tabude dakin tana rikeda hannun Hawwa tace “Assalamu Alaykum” tashiga shigo da Hawwa dataki shigowa Ammi cikin fushi tace “saketa Umma tagudu taje duk inda zata ai tasan metayi” dasauri Umma takalli Hawwa tace “ki shigo ki zauna anan ayi magana Hawwa asan me ake ciki baki da wayanda sukafi Babanki da Mamanki, koma menene dai kinsan bazasu kasheki ba shigo”Umma tashigo da ita yanda jikin Hawwa ke rawa Baba dake gaban kujeran kwalliyan Hawwa ke kallo, Ammi na zaune kan katıfa dukansu suna kada kafa, Hawwa tazo ta duka a tsakiyan dakin tai kneeling kanta akasa Umma tajuya zata fice Ammi tace “ki dawo Umma ki zauna diyarki ce rannan wanka ba’a boye cibiya she brought this upon herself kafin na sanar dake duka abubuwan da Hawwa ketayi tun bayan aure raina yariga yabani cewa wani abu yafaru dahar tazo gidan nan da safiyan Allahn nan” Ammi takalli Hawwa tace “Hawwa me kikayi? Meya kawoki gidan nan?” Har wani kalan ijiyan zuciya Hawwa ke saukewa tana kakkama riganta tana cin baki takasa magana kaganta kaman kamata kuka, Baba yawani buga karfenshi akasa da katuwan muryan nan kaman zai daga anguwan yace “badake ake magana ba” Wlh Hawwa jitayi kaman zuciyanta zai fito ta baki sabida ihun da Baba yamata, cikin muryan rudewa tace “yace yarabu dani karna sake dawowa gidansa, nakoma gidan security sun hanani shiga wai Oga yace kada akara barina nashigo!”Daga Baba har Ammi kallon Hawwa suke babu wanda ya iya magana cikinsu Umma ce tai dauriya tace “Hawwa me kikama Ibrahima dazai koreki? Meya hadaku!”? Tana rirrike riganta tana sosa cinya tace “da…..da gari yawaye nacemai zanzo wajen Ammi yace toh saina fito toh…uhmm” wlh Hawwa takasa contructing good sentence tsabagen tashin hankali and fear tadan kalli Ammi dataga tana kallonta, takalli Baba dataga yana kallonta shima sai kawai tayi rarrafe taje wajen Umma tarike Umma gam tace “shine nabiya KFC nasai abinci ina fitowa zan shiga mota sai naji anamin magana abaya najuyo naga Baban Yaseer ne!” Sosai suke kallonta arude tace “dama shekaran jiya danaje kotu naganshi………” Hawwa tafadi komi daya faru ba karya har zuwa wajen da ta taushe bakin Khaleel dasu bindiga matter, Baba kawai ya zabura yadaga karfenshi yayo kan Hawwa gadan gadan, Hawwa ta kwala ihu ta tashi ta rike Umma sosai tace “Umma ki taimakeni Umma wayyoo Allah na, Ammiii” Ammi tai maza ta tashi tashiga gaban Baba tace “Malam banda duka, nima kaman na kasheta nakeji amman dubi hannunka karfe ne idan akwai abu a jikinta kuma fa wani abu yasameta iyye? Idan rai yabaci kar hankali ya gushe Malam”Baba na kumfan rai yace “Zainabu ku banni na hallaka yarinyar nan nahuta! Anya y’ata ce Hawwa kuwa? Anya ba’a chanxamin yarinya a asibiti ba kuwa? Wlh bata dauko halina ba! Bata dauko halin mahaifiyarta ba!”.




