Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 22 By Ayshercool

Kafin ta yi wani yinƙuri, ya janyeta daga jikin gate ɗin, sai dai kasancewar ba ƙwari ne da ita ba a kansa, sai da ta kai ƙasa.Ya buɗe ƙofar ya lelleƙa, bai ga kowa ba, tuni malam lawan ya ɓace.Ya dawo ya kalleta, ta sunkuyar da kai, sai murza yatsan ƙafarta take yi, da yake yi mata zafi, saboda faɗuwar da ta yi.Ƙwafa ya yi ya wuceta, ta lallaɓa ta tashi, ta shiga kitchen ta ɗora tea, ta ɗebi miyar nan da su Anty lubabatu suka kai mata, ta ƙara gyarata ta zuba ta kai masa falo.Ya wani maze yana basarwa, nan kuwa jira yake yi, tayi ta kawo masa ya ci.Sai dai yadda yake cin abinci ya goge mata a jikin kujera, ko carfet yana damunta, sai dai idan ya gama ya tashi ta goge.Dan haka ta sayo toilet paper, take haɗo masa da ita, amma ko kallonta ba ya yi, idan Allah ya taimaketa ne, wani lokacin sai ya goge a jikin kayansa kamar wani ƙaramin yaro.Da daddare kuwa kullum, sai ya cika gidan da warin sigari, wasu lokutan ba zai dawo ba, sai sha biyu na dare, ya shige ɗakinsa yayi ta shaye-shaye, da safe kuma idan ta ajiye abinci zai ci, idan ba ta ajiye ba ba zai tambaya ba, kuma ba zai sayo ya kawo ba.Idan za ta gyara masa ɗaki sau goma a rana kuwa, muddin ya shiga sai ya watsar da komai ya ɓata, yayi shaye-shayensa ya bar mata toka da sauran karan sigari duk a ɗakin.Wasu lokutan sai su shafe kwana biyu ba su haɗu ba, gashi zai kwana a gidan, amma ba zai shigo ba sai ta yi bacci, duk da wataran ba ta baccin sai ta ji shigowarsa, asubar fari kuma sai ya fice, ranar da ya ga dama kuma, sai ya bari gari yayi haske, ko za ta bashi abinci, dan sai yanzu ya fuskanci abincin waje wasu lokutan ga ƙaurin hayaƙi gashi ba sa jin sinadaran ɗanɗano, nata kuwa har cikin kansa yake jin su.Yau ma dawowa ya yi rana tsage-tsage, walid ya sayo musu abinci, yana fara ci ya ji babu daɗi, ya ajiye ya ce gida zai tafi.Walid ya ce “Da ranar nan tsaka zaka fi gida?””Eh” ya amsa a taƙaice.”Lallai, na fuskanci lamari yana ta daidaita to Allah ya sa mu ji alkhairi ya kawo zuriya ɗayyiba”Ya haɗe rai ya ce “Mai laya”Walid ya ce “Sorry maza, na kiyayi mai zamani” ya fice ya tafi gida.Jauhar tana ta lissafin kuɗin hannunta, sun kusa ƙarewa, girkin ma duk da dabaru take yin sa, ga gogan babu ruwansa sai dai ta dafa ya lashe.Da ‘yan dabaru take yin ɗan wake yau, ta aiki almajiri ya sayo mata kabeji da cucumber, tana jiran dawowarsa, Al’amin ya dawo, a duk lokacin da za ta ganshi sai ta razana, gashi ba sallama yake yi ba, ya hangota da tukunya a kan gas, ya yi ajiyar zuciya ya san zai ci abinci.Ya shiga ɗakinsa, ya tarar ta sake wanke masa kaya, ta gyara ɗakin tsaf.Tsaki yayi ya ce “Ita dai wannan an yi ‘yar wahala”Ya daidaici lokacin da ta gama girki, ya dawo falo ya zauna, aikuwa sai ga ta abinci bakinta ɗauke da sallama.Bai amsa na sai Alla-alla ta kawo ta ajiye, saboda yadda ƙamshin manjan, ya cika masa hanci.Ta ajiye masa ya haɗa abun sa ya fara ci.Ta zauna a gefensa, cikin fargaba ta ce “Yaya” shiru ya yi mata, yana haɗiye ɗan wakensa da hurhuɗu biyar-biyar.Ta sake cewa “Yaya magana nake dan Allah abu zan tambayeka”.”Malama sunana Aminu, kar ki sake ce mini wani Yaya” a ranta ta ce ‘Ai na san a rina’A zahiri kuma ta ce “Ai ba zan iya faɗar sunanka ba, ya za ayi na faɗi sunan mijina kamar mara ɗa’a” sai ya ji abun wani banbarakwai wai mijinta.”To me zan din ga ce maka?” Ba ta jira amsar sa ba, dan ta san ba zai amsa ba, ita kuma zaman kuramen nan da suke yi ba son sa take yi ba, ace kana zaune a ƙarƙashin mutum, amma ba zai kulaka ba.”Na ji abokanka suna ce maka boss, ni kuma sai na ce maka master, idan na ce master zaka amsa, ko nima boss zan ce? Tun da ba ka son yaya?” Ta tambaye shi tana murmushi ba tare da ta kalli in da yake ba, saboda kwarjinin da yake yi mata, yanzu haka ma ƙarfin hali kawai take da take yi masa magana.Kallonta yayi, tana murmushi dimple ɗin ta na side ɗaya ya lotsa, ya gane dakiya kawai take yi, amma a tsorace take yi masa magana.Duk da bai bata amsa ba, amma matsern da ta ce zata din ga kiransa da shi, ya so yayi murmushi, amma yaƙi ya sha kunu, yana suɗe kwanon ɗan wakensa.Cikin hikima ta ce “Da da sauran garin ɗan waken nan, da na dafa maka wani, ko na ƙaro maka?””A’a” ya ajiye kwanon, cikin sauri ta miƙa masa wani tsumma mai kyau, ta ce “Gashi ka goge hannunka, manjan yana da kamu, sai mu je waje na zuba maka omo ka wanke sosai” ya karɓa ya goge, ya koma ya kashingiɗa yana duba wayarsa mai madannai.”Na ce, dan Allah sonake na shiga maƙwabta na yi musu sallama na tare, wai haka ake yi, ka ga mu bamu cewa kowa mun tare ba””Sauka lafiya” ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.”Yauwwa na gode sosai master, bari ayi la’asar, sai na je. Yauwwa mutumin ɗazu ya ce wai mai unguwa na nemank….. Ba ta ƙarasa ba ya tashi, dan surutunta ya fara isar sa.Bayansa ta bi da kallo, ‘Da sannu wataran zaka tanka mini ne, ni ba zan iya rayuwar zaman kurame ba’ tayi maganar a hankali.Huɗu da rabi, bayan ta yi la’asar, ta leƙa ɗakinsa ta ce masa za ta fita, ta tarar yana salla.Wata irin ajiyar zuciya ta yi, tare da hamdala a zuciyarta, ba ta taɓa tsammanin yana kai goshinsa ƙasa ba.Ta zauna a bakin ƙofar tana kallonsa, duk da shaf shaf yake yi, kuma azahar da la’asar ya haɗa a lokacin, amma ta ji dadin ganin yana salla.”Master bari na je, idan ka idar ka sani a addu’a, Allah ya sa ka daina jin haushina, ban san me nayi maka ba” dama ta san ba amsawa zai yi ba ta fita.Matasan ‘yan mata ne su biyu a gaban rahila suna cin abinci, da alama daga makaranta suka dawo, domin kuwa bayansu jibga jibgan akwatuna ne, na ‘yan makaranta.”Umma, nifa haryanzu na kasa daina mamaki, wai yaya ne yayi aure? Wai dan Allah ya aka yi aka samu aka bashi ‘ya a yadda yake? Kuma ba a bari mun dawo ba aka yi bikin?”Rahila ta ce “Ke dallacan, waye ya ce miki abun na shiri ne shahida? Neman mafita nake ba shiri faka-faka na saka aka samo wata yarinya ya je can ya ƙarata, ya ƙara sako mini yaro a gaba, irin kallon da yake yi mini, tsaf zai halakka ni, cikin ikon Allah tun da aka yi auren, ban sake ganinsa a gidan nan ba, ya samu mace yayi luf”Shahida ta ce ‘Ni wallahi mai tsautsayin da aka aurawa nake jin tausyai, yaya za ta yi da shi dan Allah dan Annabi?”Amira ta ce “Ke ina ruwanki ne shahida, ina ruwanki da ko ma wa ce ta aure shi, ba dai an samu ya tafi na, case close”.Shahida ta yi murmushi ta ce “Ina ne gidan nasa ne?””Yana can gidansa na ɗorayi, ba kuma cewa na yi ki je ba, kar abun da ya kai ki gidansa, balle ya lallaɓa ya dawo mana nan ya je can su ƙarke”.”Ahh haba umma, sai mu yanke alaƙa da shi duka kenan? Yayi aure muna school kuma mun dawo ba zamu ganshi ba?”Amira ta ce “Wallahi a garin shishshigin nan da ki ke masa, zai kassara rayuwar ki, ki yi ta shige masa yana yarfaki””Wallahi ki ka je gidansa ma sai na ci ubanki shahida, na gaya miki, ke baki san sai ku kasa auruwa ba saboda mugun halinsa da mummunan tabon da yake da shi ba a unguwar nan?”Shahida ta ajiye cokalin hannunta ta ce “Umma, shi fa jini ya fi ruwa kauri, the only male brother i have, sai ki ce sai na yanke alaƙa da shi?””Au jayayya zaki yi da ni? Shi Abban uban meye idan ba yayanki ba?”Ta tashi ta ce “Ai ba babanmu ɗaya ba, Yaya Al’amin kuma babanmu ɗaya, kowane ina son sa”Rahila ta ce “La ila ha illalahu Shahida “Amira ta ce “Dan Allah umma bar shashasha, za ta gane kurenta ne”Rahila ta cigaba da salallami, a kan yadda ke adawa da ita wasu lokutan a kan Al’amin.***Juahar gidan malam lawan ta fara shiga, wato gidansu halimatu da walida, yaran da suke zuwa tayata hira, suka gaggaisa da maman, sannan su halimatun, suka rakata sauran gidajen maƙwabta, tayi musu sallama. Har wurin masu kayan miya, da masu shaguna suka nunnuna mata da wurin makarɗe.A bayan gidan suka je har gidan wata tela, da har da yaranta, su na shigarwa jauhar, suka gaisa jauhar ta tarar da yaran suna stone work a jikin ɗinki, har ta karɓa tana taya su, saboda a rayuwarta tana son sana’oin hannu suna matuƙar burgeta.Take cewa matar, idan an samu stone work ta din ga aika mata da shi tana yi mata.Matar ta ce ‘To nawa zan din ga baki, dan kuwa ina samun aikin su sosai da sosai”Cikin tsananin murna, da jin cewa ta samu abun yi, ta cewa matar, ko nawa ne ta bata, tana son za ta din ga yi, nan hira ta ɓarke, take gaya wa matar, ta iya shirin dutse, har adon da ake yi da shi a jikin ɗinki, duk zata iya, suka yi yarjejeniyar matar zata din ga bata ta yi mata.Ganin hadari ya fara haɗowa, ya sanya ta yi mata sallama, ta koma gida, sai dai tana komawa, ya zura takalmansa zai fice, ta ce masa kar ya fita, hadari ne a garin, amma ba ta gama rufe baki ba, ta ji ya buɗe ƙofa ya fice.Ta kawar da abun da zata kawar, ta rurrufe ko ina, ta laluba ta ɗauki mp a in da ta ajiye, ta tarar ya ɗauke kayarsa, ta ce “Da sauƙi, tun da ba ka yi mini faɗa ba”.Ruwan sama aka yi, kamar da bakin ƙwarya, ga wata irin iska da ta jefa jauhar, cikin razani da tashin hankali, yadda kwanon yake ƙara ji take tamkar zai kwashe ne, saboda ƙarfin iskar da ruwan.Ta takure wuri guda, tana ta addu’a, kasancewar lokacin da ake ruwan sama, lokaci ne na karɓar addu’a, mafi yawan addu’arta a kan Al’amin ne, da take masa fatan shiriya.Ko da ruwan ya tsagaita, ta fito falonta, ruwa ya shigo sosai, ya jiƙe ɗakin, ta buɗe ƙofar falon, rashin kyakykyawan magudanan ruwa, ya sanya kwatocin layin yin ambaliya, duk suka shigo mata gida, gashi ba ga da rariyar kirki, sai ta banɗkuna, dan haka babu wurin da ruwan zai fita, tsakar gidan ya shafe da ruwan kwatami, falonta ma duk ruwan ya shigo, gashi idan aka yi ruwan, tsigar jikinta tayi ta tashi.Haka ta samo kwano, ta din ga ɗibar ruwan tana zubarwa, ta naɗe carfet ɗin ta, ta jingine, sai zallar buhun da aka shimfiɗa a ƙasa, ta din ga kwarfe ruwa a falon nan.Ta je ta yi sallar magariba, Allah ya sa ruwa bai shigar mata bedrooms ba.Ana sallar isha’i sai gashi ya dawo, ya tarar da ita, fitilarta babu batirin kirki, duk tayi duhu, sai kwashe ruwa take a falo.A ransa ya ce “Iyayenki ne suka ja miki” tayi masa sannu da zuwa, ta cigaba da aikinta, har zai wuce ya dawo ya karɓi kwanon, ya haɗe mata kujerunta wuri guda, ya kunna fitilar ƙaramar wayarsa, ya ƙarasa kwashe ruwan.Shi kansa ya san gidan nan kango ne, yana buƙatar gyara sosai, bai ci ace har an saka mutum a ciki ba, amma da iyayensa da na ta, ya rasa wannene uban garajen da ya saka aka yi haka.Ya ɗaɗɗaga labulayen, saboda ɗakin ya sha iska, daga nan ya tafi makwancinsa, ta tafi nata.Da safe ruwan duk ya tsane, amma sai ƙanƙame jikinta take yi, ƙarnin ruwa da ya kwanta ya din ga damunta.Haka nan ta daure, ta gyara gidan, ta zuba miya ta yi jallof ɗin macaroni, kasancewar falon a jiƙe yake, da danshi, da sauran Lipton ɗin jiya, ta dafa shayi har da su citta ta yi sallama a ƙofar ɗakinsa, bai amsa ba dama labulen a ɗage yake ta shiga.Ta ajiye masa ta ce “Ina kwana?” Ba ta jira ya amsa ba, ta haɗa masa tea, ta tashi ta fita.Aka jima ta dawo, ta shiga banɗakinsa ta wanke, ta ɗauki bokiti ta dawo, ta haɗo ruwan zafi na wanka, ta kai masa banɗakin ta ce “Master ga ruwan wanka nan na kai maka, mai ɗumi ne” idan ta ce mastern nan, sai ya ɗaga kai ya kalleta.Ta ce “Yauwwa, master zan kafa ƙusa a toilet ɗin ka, idan ka gama wanka, ka dinga saƙale soson, idan ba haka ba sabulun narkewa yake yi, sai ka ga ya ƙare da wuri”Ta zagaye shi, ta fara tattare kayan duk da ya watsar a ɗakin kamar ƙaramin yaro.Ya gama cin abincin sa, ya fara shan tean, yana jin yadda ƙamshin da yajin citta yake ratsa shi yana yi masa daɗi.Yana zaune ta gyare ɗakin, ta kukkuna masa turaren wuta, sai dai kafin ta ƙarasa, ya kunna sigari a ɗakin.Sai da ranta ya sosu, akwai sauran warin ta jiya da daddare ma da ya sha, ta gama aikin ɗakin, ta kunna turaren wuta, ya kuma kunna wata sigarin.Ta maze ta ce masa “Ruwan wankanka, kar ya huce fa, na ga garin da sanyi haryanzu, idan ka yi wanka da na sanyi, zaka yi mura”A hasale ya ce “Ke, fita ki bar mini ɗaki, kin gama tsegumin ai, kin sakani a gaba kin ga abun da nake yi, to fita ki bar min ɗaki, ba zan wankan ba”Ba ta sake cewa komai ba, ta juya ta fice, ta cigaba da ayyukan ta, tana tsaka da wanke-wanke, ya fito da sauri, hannunsa riƙe da waya yana cewa “Kar ku raga musu, gani nan zuwa” ta miƙe tana kallonsa, amma ta kasa yi masa magana.A haka yana ƙaurin sigarinsa da komai, ga kayan da su ya wuni jiya, ya wayi gari da su, amma bai canza wasu ba, ya fice cikin matsanancin sauri.Ta koma ta cigaba da aikinta, tana addu’a Allah ya sa ba wani rashin jin zai je yayi ba.Baba yana gida, aka aiko ana sallama da shi.Yana fita ya tarar da ‘yan uwan Alhaji mu’azzam da suka kawo kuɗi.Suka gaggaisa, ƙanin mahaifin Alhaji mu’azzam ya ce “Gamu mun dawo, ɗanka ne ya dawo da mu, ya ce a bayar da haƙuri, kar a ji mu shiru, ayyka sun yi masa yawa, ba zai samu dawowa nan kusa ba, shi ne ya ce mu zo ayi magana, a ƙarasa shirye-shirye kawai, ayi auren a tura masa ita can”.Gaban Baba ya faɗi jikinsa a sanyaye ya ce “Alhaji dama ko da baku zo ba, zan neme ku ni na zo, an sami matsala ne, zan dawo muku da kuɗin aurenku”.Suka yi turus gaba ɗaya suka ce “Wace irin matsala ce haka?””Yarinyar nan, yau ta kusa sati biyu, ina mai baku haƙuri, a bashi haƙuri dan Allah. Zan kawo muku kuɗin aurenku””Amma wani abun yayi ne, ko wani laifin shi mu’azzam ɗin yayi?”.Baba ya ce “Ko ɗaya, ka san matar mutum kabarinsa, mu’azzam bai yi mini komai ba, dan Allah a bashi haƙuri”Suka ce “To shikenan, Allah ya tabattar mana da alkhairi”.Suka amsa da “Amin”Baba ya ce “Ku bani account number, na mayar muku da kuɗin auren”Ɗaya daga cikin su ya ce “A’a, a bar wannan maganar sai ya dawo tukuna, Allah ya basu zaman lafiya”Ya amsa da “Amin”.Bayan la’asar yara duk suna islamiyya, babu ‘yan aike, ta ce bari ta fita ta sayo maganin sauro, idan ya dawo sai ta gaya masa.A ƙofar gida suka haɗu da maman su halimatu a waje da wata maƙwabciyar su, suka gaisa ta ce “Maman halimatu, ba ku shigo mini mun gaisa ba haryanzu”.”Wallahi Amarya, ba ƙi muka yi ba, kin sa yanayin mijin naki sai a hankali, abun da tsoro, kar wani abu ya faru”.Ranta bai yi mata daɗi ba ta ce “Haba dai, ina ruwansa da ku? Kawai dai a shigo a gaisa, shikenan a gaida su halimatu” tayi gaba zuciyarta babu daɗi, a duk lokacin da ta ji an aibata shi, sai ranta ya sosu.Har dare ba ta sake ganin Al’amin ba, gashi ita ba waya ba, wasa-wasa har dare yayi babu Al’amin babu dalilinsa har garin Allah ya waye, bai kwana a gida ba.Sai abin ya fara damunta, gashi ba ta san a ina za ta ganshi ba.Abu kamar wasa, aka sake shafe wuni, aka shiga kwana na biyu, babu shi babu labarinsa, nan fa hankalinta yayi mummunan tashi, gashi ba ta san wa za ta nufa ta gayawa ba.Maman halimatu ce tayi sallama, Jauhar ta saka hijjabi ta fito tana murmushin yaƙe ta ce “Maman halimatu, sannu da zuwa shigo””A’a ba shigowa zan yi ba, abbansu yana nan bai fita ba, bai san ma na shigo ba na ce kin kuwa san an kama mijinki?” Gaban Jauhar ya faɗi ta ce “Yaushe? A ina? Waye ya gaya miki?””A bakin Abban su halimatu na ji, cune suka yi masa aka kama shi, amma dan Allah kar ki gaya masa wanda suka saka aka kama shi ɗin dan Allah, na gaya miki ne na san baki sani ba”.Tuni idon Jauhar ya cika da hawaye ta ce “Eyya, meysa abban su halimatu yayi haka? Wallahi babu abun da zai yi wa wani, ba ruwan shi da kowa idan ba taɓa shi aka yi ba, ina aka kai shi? Dan Allah ki gaya mini, ina gidan ban san ina zan nufa ba ma”.Tayi ƙasa da murya ta ce “Yana anti daba can aka kai shi”.”Menene anti daba kuma? Ina ne?”.”Can in da ake kai ‘yan daba, ki shirya ki je ki duba shi”.Ta ce “To na gode” bayan tafiyar maman halimatu, take ta ji haushin malam lawan ya kamata.Tayi tunanin ko gidansu za ta je, ta faɗa, amma sai ta ga idan tayi hakan, kamar ta tozarta kanta ne, dan haka ta fasa ta ɗora girki, ta gama ta shirya, ta zuba a flask, ta bi kwatancen da maman halimatu tayi mata.Su kansu yanayin jami’an tsaron wurin, tsoro suka bata, ba ta taɓa zuwa police station ba, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta ce “Dan Allah wani nake nema””Wa kenan?” Wani ya tambayeta.”Al’amin sunansa”Ɗan sandan ya ce “Anya, babu wani mai irin wannan sunan da muka kama”.Ta ce “Dan Allah nan aka ce mini an kawo shi, dan Allah officer ka duba mini”Na kusa da shi ya ce “Ko viper take nufi?”Ta ce “Eh shi, mai dogon zamani””Ya aka yi me zaki yi masa?””Wurinsa na zo, maƙwabciyata ta ce mini cune aka yi masa aka kama shi, wallahi bai yi komai ba”.”Ke ya aka yi ki ka san bai yi komai ɗin ba? Wacece ɗin sa ke, ni tun da muke kama shi ma, ban taɓa ganin wani ya zo wurinsa ba, idan ba ire-iren sa ba ko yaran ubangidansa ba”Ta ce “Mijina ne”Saroro suka yi suna kallon jauhar, kyakywar yarinya ƙarama da ita.”Ke kuma auren soyayya ku ka yi? Jama’a kun ga matar Viper, yaushe ne kuwa zuwansa na ƙarshe aka fito da shi aka ce aure yayi” waiwayowa suka yi suna kallonta, ta sunkuyar da kai tana fatan Allah ya sa su bar ta ta ganshi.Ɗaya daga cikin su ya ce “Ku fito da shi, ta ganshi, amma dai Viper yayi asara, daga aurensa ya saka ‘yar mutane fara sintiri saboda shi”.Saroro yayi da ya hangota cikin hijjabi, ‘yan sandan suna yi mata tambayoyi.Tana ganinsa tayi ajiyar zuciya, ya ƙaraso gaban kantar ya kalleta ya ce “Me ya fito da ke?””Kwana biyu baka nan, ban san in da ka ke ba, sai yau ban san kama ka aka yi ba”Ya sake kallonta ya ce “To ware ki koma”Jauhar ta ce “To in koma, kai fa ba sakinka za su yi mu koma ba?”Al’amin ya ce “Ki tafi na ce, kuma kar ki sake zuwa wurin nan kina mace, ware” haushi ne ya kamata, yadda yake korarta, shi ba ayi masa abun arziki sai hantara.Ta ɗora leda ɗuake da flask ɗin Abinci ta ce “Gashi abinci ne na kawo maka” sai da ya ɗan yi shiru yana kallonta.Tun da ya fara rashin jin sa, babu mai tunawa da shi, ya kawo masa ziyara ko abinci, idan ba su walid ba, sai kuma ita yanzu.”Ahh yau zamu ci girkin amarya, amma hajiya sai kin fara ci kafin ya ci”Bai saurari ɗan sandan ba, ya ɗauki abincinsa ya koma gefe.Ya buɗe, ta yi sauri ta zagaya, ta huda ruwa pure water, ta ce masa “Ka fara wanke hannunka”Kamar ya shareta, sai kuma ta zuba masa ya wanke, ya saka hannu ya fara cin abincin.”Akwai sauro ne wurin? Na ga kamar ya cijeka, jikinka duk cizon sauro?””Mmm” ya amsa yana cigaba da cin abincin.”To yaushe zasu sake ka, kar ka yi rashin lafiya, saboda cizon sauro” shi dai yayi shiru yana cin abun sa.Ya gama ci ta bashi ruwa, ya karɓa ya zuƙe, ta ƙara masa wani ya shanye.Ta ce “Officer, to zaku sake shi? Bai yi komai ba””Ke, da wiwi muka kama shi da ƙwayoyi, sai kuma ki ce bai yi komai ba? NDLEA zamu kai shi”.Jauhar ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba in sha Allah, Master ka basu haƙuri su ƙyaleka mu tafi” miƙewa yayi tsaye, ya nufi hanyar komawa cikin ceil.”Officer to, idan na sayo maganin sauro da ashana, zaku bar shi ya kunna?”Gaba ɗaya sai ta basu tausayi, ya ce “Sayo”Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya ya waiwayo ya bi bayanta da kallo.”Viper, wai dan Allah ka bamu labari, wurin wani bokan ka kai ‘yar mutane da iyayenta, suka aura maka ‘yar su?”Shi dai ya ƙarasa ya koma cikin ceil, yayi zamansa, ba a jima ba, sai gata da maganin sauro, da ashana.Suka karɓa a nan kan kanta, suka ce ta tafi.”Dan Allah ku bari na sake ganinsa””Ke wuce ki bar nan, da ki ka samu ma aka bari ki ganshi?”Ba ta karaya ba ta sske cewa “To ana bashi abinci? Ko ina kawo masa na dare ma””Au uban wa ki ka ajiye da zai bashi abinci a nan? Ware ki tafi”Jiki a sanyaye ta ce “To, zan tafi ga wannan dan Allah officer ko buredi ku bashi” ta ajiye musu ɗari biyar sannan ta ce “Dan Allah kuma ku yi haƙuri, kar ku kai shi NDLEA, dan girman Allah in sha Allah zai daina, ba zai ƙara ba ma dan Allah””Ki je ki kawo dubu hamsin, sai mu sakar miki shi” Tayi shiru, har ga Allah ba ta da ita, ba ta da dalilinta amma ta ce “To zan kawo, amma dan Allah kar ku kai shi, zan kawo muku in sha Allah”Ta fito daga wurin, tana tunanin ina zata nufa ta samo dubu hamsin a sake shi. Ayshercool 08081012143

Back to top button