Hausa novels

Kanwar Maza Page 72 Complete Novel By Ayshercool

Page 72

 

Matar da mamaki take kallon ruma, “I don’t get you, he is not available like how?”.

 

Maimakon rumaisa ta amsa, sai ta sake kashingiɗa ta ce “Elizabeth ma ta ci ubanta, haka ta gama turancin ta mutu”.

 

Cikin isa matar ta cire gilashin fuskarta ta ce “Kin san wacece ni kuwa?”.

 

“Ina ruwana da ke wacece? Ko da ban san ki ba, na san ba zai wuce kema a danginsu ki ke ba, masu zuwa su ci mini mutunci, ni kuwa dai-dai nake da kowa, wallahi duk wanda ya zageni ramawa zan yi ehe”.

 

“To yanzu zagin ki na yi?”

 

“Ai na san tatsuniyar gizo, ba ta wuce ƙoƙi, kun saba zuwa ku yi mini wulaƙanci, na sani ko kema abun da ya kawo ki kenan, daga shigowarki sai kallon banza ki ke yi mini, kuma dan raini ki ke tambayata wai ina matar gidan. To ban sani ba ko nayi kama da ƴar shara da wanke-wanke”

 

Matar ta riƙe haɓa, sannan ta jinjina kai ta ce “Anyway, na ji kece matar gida, kuma ban zo na ci mutuncin ki ba, i want see ma brother please”

 

Rumaisa ta ce “Ban iya turanci ba”

 

“Ohh ikon Allah, ina son zan ga ɗan uwana ne, wurinsa na zo”.

 

“To bacci yake yi, idan zaki jira shi to, bai daɗe da kwanciya ba, amma ina fatan ke ba ƴar uwar wannan samhan ba ce ba?”

 

Matar ta yi murmushi ta ce “No, am not” ta saka hannu a jakarta, ta ciro waya, cikin harshen Ingilishi take magana, da accent ɗin da rumaisa ba ta iya fahimta, ta ajiye wayar.

 

Bai fi mintuna takwas ba, sai ga takawa ya fito.

 

Da sauri matar ta miƙe, ta nufe shi, kamar zasu rungume juna, suka yi musabaha, ta sumbaci hannunsa ta ce “Takawarka lafiya ranka ya daɗe, gaba salamun baya salamun”

 

Adam yayi murmushi ya ce “Ke dan Allah yaushe ki ka sauka? Kuma da safen nan na je gidan mai girma turaki, na ji kasala nake ji, ban ƙarasa gidan ba, kuma jiya fa har 5pm muna gidan.

 

“Around 11 na ne gida, na cewa ammi kar ta gaya maka, yau na ce ammi ta saka a kawoni, na zo na ganka na ga amarya, and i met this little arrogant creature, screaming at me that why should I ask for you. She even claims that she’s your wife, but i doubt  she is the one in the pictures. She looks innocent and matured in picture”.

 

Takawa yayi dariya ya ce “She’s the one, rumaisa kenan maman sabir”.

 

Jiki a sanyaye ta ce “Adam, na ga yaron fulani, so cute, yaron kyakykyawa da shi”.

 

Rumaisa da ba ta kula su ba, ta ce “Tubarkallah”.

 

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ruma ya ce “Mimi, ga Anty Laila, cousin sister ɗina, da muka tashi tare, kuma uwar ɗakina. Tana aure a canada da mijinta da yaranta”.

 

“Au ai ban santa ba, kuma da ta zo ba ta gaya mini ita ce ba, na zata kawai ƴan uwanku ne masu zuwa gida, su yi mini wulaƙanci, shiyasa ban kulata ba”.

 

“To ai ba duka ƴan uwan mu ne, masu yi miki wulaƙancin ba, ku gaisa mana”.

 

“To ita kuma ya ake gaisheta, kar in yi ba dai-dai ba ta ƙi amsawa, ba zan sake gaisheta ba”

 

Yayi murmushi ya ce “Ita wannan baturiya ce ai, kowace irin gaisuwa ki ka yi mata zata amsa”.

 

Rumaia ta sake kallon laila sannan ta yi murmushi ta ce “Sannu da zuwa, ina wuni? Ya hanya ya iyali, sannu da zuwa”

 

Ta ce “Yauwwa thank you”

 

Ta tashi tsaye ta je ta kawowa laila ruwa da lemo, ta kawo mata kayan shayi ta ajiye, ta haɗo da cornflakes duk ta ajiye mata.

 

Laila ta ce “Ya zan yi da duk wannan kayan, kar ki takura kanki, na ƙoshi ni”.

 

“A’a kar ki je ki ce, kin zo gidana ba a baki abinci ba. Na san lokacin breakfast ya wuce, amma dai ki sha shayi, ko cornflakes, akwai fruit ma, yanzu zan je na ɗora girki”.

 

Laila ta ce “Girki kuma? Ba naga akwai maids ba, na ga baba uwani ma na nan, kar ki ciwo a kitchen fa”.

 

Rumaisa ta ce “Ai da yake a unguwar ɗorayi nake, na iya duk wani girki da yakamata, ni ba ƴar masu kuɗi ba ce, kar ki damu da yarinta ta, na iya abinci gidanmu ba ƴar aiki”.

 

Adam ya ƙunshe fuska yana dariya, rumaisa kuma ta nufi kitchen, tayi ƙasa da murya ta ce “Yenyenyen, ta wani shaƙe murya tana turanci, har da saka wando, babba da ita wai ita baturiya, Elizabeth ma ta gama saka wandon da mini skirt, aka haɗa da ita da turancin aka binneta”.

 

Laila kuwa ruma na barin falon ta ce “Bros yanzu da gaske this is your wife?”

 

“Yeah, ta canza miki ne, ita ce dai ki ka gani a hoto”.

 

Laila ta ce “Taɓɗijan, amma ba ta da kunya, a tsaye take, amma tayi ƙarama takawa”.

 

“Haba dai, yanzu ai ta ciko, ta yi ƙiba, rigima kam akwai ta har da ta sayarwa ma, sai dai duk da haka bamu fi wata ɗaya ba, na fara jin daɗin zama da ita. She’s very intelligent, fiye da yadda ki ke zato, wauta da ƙuruciya ne dai damuwarta”.

 

Nan ya bata labarin yadda rumaisa ta dawo da sabir, da yadda aka yi har ya aure ta, zuwa yanzu da suke tare, da abubuwan da take ta hasaka masa, a zamansu.

 

Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce “Well, amma ba ta da kunya gaskiya, a haka ku ke zaune?”.

 

Ya ce “Ya ki ke zagar mini mata ne, zaki shiga sahun Black list ɗin mu fa”.

 

“Am serious matarka ba ta da kunya takawa”

 

Sai ya tuna abun da ya faru jiya, ya ce “Kin san family ɗin mu sai a hankali, gida suka zo suke yi mata rashin mutunci, ta rama. Kin san ƙanwar maza ce ba tsoro. Haka nan muke lallaɓawa muke tare, ake rainonta kan Allah ya sa ta gama hankali, ko me za ta yi, ta cancanci ayi mata uzuri, kuma in kula da ita, abun da ta yi mini, ko duniya na bata ban biyata ba”

 

“Haka ne, amma ban gane ake lallaɓawa ake rainonta ba, haka ku ke zaune kana kallonta tana kallonka”

 

Yayi dariya ya ce “Ina ruwanki ne?”

 

“Babu, amma tun a hotonta nayi mamakin yadda ka auri ƙaramar yarinya haka, na sam baka da ra’ayin auren ƙaramar yarinya, na san plan ɗin ammi ne, ban da haka wannan guda nawa take? Me ta sani?”

 

“Ai fa, in dai ɓangaren zamantakewar aure ne, ba ta san komai ba, sai kaifin basirar sanya ido da gane mara gaskiya, shiyasa na yi mata registration na islamiyya matan aure, ta ce dai ba zata ba, ita yara zan sakata, ba zata shiga cikin matan aure su rainata ba, wannan kuma da ammi zan bar ta, dan sun fi kusa”

 

Laila ta ce “Well, tun da ba tare zaku tafi ba, ka bar ta a hannuna, zaka ga canjin kafin ka dawo in sha Allah”.

 

Ya dubi laila ya ce “Like how kenan?”.

 

“Kai ina ruwanka, tun da tafiya zaka yi, ta zo mu zauna a gidan ammi tare, she needs to learn so many things, ko kuma you are taking another wife ne, wannan tayi ƙwaila da yawa”.

 

“Allah ya sa ta ji ki na ce mata ƙwaila, zaku yi faɗa da ita sosai, nikaɗai ne idan na faɗa take ƙyaleni, ni ɗin ma sai da tayi mini abun da na daɗe ina jin kunyar kallon ammi, ta gaya mata wai na ce zan ƙara aure saboda bata da nono”

 

Rufe baki laila ta yi tana dariya, ta ce “Lallai wannan yarinyar ɗanya ce sharaf, ka bar ta a hannuna kawai”.

 

Hira suka cigaba da yi, ya din ga bata labarin abubuwan da suka din ga faruwa, tun bayan komwarta canada daga hutun ƙarshe da ta zo.

 

Laila ta sha mamakin ganin yadda rumaisa ta kawo mata abinci da ta girka, komai nata tsaf, hatta falonta a gyare yake, dan har ƙamshin turaren wuta yake, a tunaninta ko masu aiki ne suka yi mata, sai da adam ya ce mata ita take abun ta.

 

“Mimi ina nawa abincin?” Adam yayi maganar yana kallon ta.

 

“Au, dama zaka ci? Ya ƙare saura ƙanzo, ko in dafa maka taliya da manja da yaji”

 

Yayi murmushi ya ce “zan kama ki ne, da ke da taliyar.

 

Rumaisa ta koma ɗakinta, ta bar musu falon, wanka ta yi, ta fito da nufin ta shirya, ta ga takawa a ɗakin nata. Ta ɗan tsuke fuska ta ce “Ya na ganka kuma, ina baƙuwar?”.

 

“Haka ake yi, kin yi baƙuwa kin tafi kin bar ta?”.

 

“To ba wurinka ta zo ba, ko zuwa zan yi na saka ku a gaba ina kallon bakin ku?”.

 

“To, yanzu dai ba wannan ba, dan ta tafi ma, taho mu yi magana”.

 

Rumaisa ta ce “Taɓ, kaya zan saka, ka je idan na kammala shiryawa, zan zo”

 

Ya janyo hannunta ya zaunar da ita a kan gadon, ya ce “Yanzu zamu yi, baki da isasshen lokacin cigaba da ganina. Idan na tafi gida zaki koma wurin ammi, zuwa lokacin da zan dawo, lokaci-lokaci kuma, zaki iya zuwa gida, shima sai kin nemi iznina tukuna”

 

Jiki a sanyaye ta ce “To meyasa ba zan koma gidanmu ba, ni fa ba zaman gidanku ne bana so ba, wannan ƴan rainin hankalin ƴan uwan naka ne ba zan juri wulaƙancinsu ba”

 

“Rumaisa kin iya cewa bani da haƙuri, ke haƙurin ne da ke? Babu ruwanki da su, gobe in Allah ya kaimu da azahar zamu tafi, idan na kammala wakilicin mai martaba, zan wuce in da zan yi course ɗina na watanni shida. Dan Allah ki nutsu ki zauna lafiya da kowa, ban da rigima, ga Anty Laila nan, zata kula da ke tana da kirki sosai”.

 

“Wannan ɗin ce mai kirki, bayan daga zuwan ta ta fara gaya mini magana, dan dai kawai ka ce yayarka ce”.

 

“Dai-dai take da ke ai, idan ki ka yi mata rashin kunya, ta san yadda za ta yi da ke”

 

“To yanzu idan ka tafi, wa zai cigaba da aikin binciken da kake yi?”.

 

Ya ce “Ga Bashir nan, akwai group ɗin mu da duk tare muke yin ayyukanmu, ki sanya ni a cikin addu’ar ki mimi, matsaloli sun yi mini yawa”.

 

Rumaisa ta ce “Allah yana tare da bayinsa masu tawwakali da haƙuri. Allah yana tare da mu papa, zan din ga yi maka in sha Allah”

“Thank you dear” yayi maganar tare da sumbatar hannunta.

Tayi dariya ta ce “Kai, sai ka ce abun indiyawa, kiss a hannu”

 

“To muyi a baki?” Da sauri ta saka hannu ta rufe bakinta, ta tashi. Murmushi yayi ya tashi ya bar ɗakin.

 

A ranar takawa ya je ya yi wa mama sallama, ya sanar da ita batun zai bar ruma, a wurin ammi. Cikin kara mama ta nuna bakomai, tare da yi masa fatan alkhairi, sai dai bayan tafiyarsa ƴan mazan mama, duka din ga mitar, dan me ba zata dawo gida ba, za ta tafi gidan sirikai ta zauna, kamar mara gata.

 

Ruma ba ta ɗauki tafiyar takawa serious ba, sai da ta ga da gaske yana haɗa akwatinsa a daren yau.

 

Tana tsaye ya ce ta miƙo masa wannan, ta ɗaukko masa wancan.

 

“Papa, ya batun anty iman ne, ba wani abu da zaka yi a kai kan ka tafi? Kar wannan jabir ɗin ya aureta fa”.

 

“To ke ina ruwanki?” Yayi maganar yana duba wani turare.

 

“Da ruwana mana, ni fa na bana son jabir ɗin nan”.

 

“Ita ta ce miki ba ta son sa ne? Kin fiye damuwa, ko so ki ke in tayata mu bijirewa ammi?”

 

Rumaisa ta ce “Wallahi ba ta son sa, taɓ gaba ɗaya kalar munafukai ne jabir ɗin nan, da gani yana aikata wani laifi a ɓoye da Allah yake rufa masa asiri. Ko dan halin babarsa ma dole ya zama shaiɗani”.

 

Ƙurii yayi da ido, yana kallon rumaisa, zuwa yanzu ya daina mamakin abubuwan da take faɗa da aikatawa, dan idan ta faɗa, ko ɗari-bisa ɗari bai zama dai-dai ba, kashi saba’in dai-dai ne.

 

“To, haka ta ce miki, kin san ba zamu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba, mu cigaba da yi mata Addu’a, idan shi ne alkhairi……

 

“A’a ba alkhairi bane ba ma, kuma ba zata aure shi ba” ta katse shi.

 

“Tun da kece waliyyinta ko? Wai ke kin fi ni son ta ne? Kin ƙwace mini ɗa, kin ƙwace mini ammi, kuma ƙanwartawa ma da nake ji da ita, kin ƙwace ta, haka ake rayuwa ne?”

 

Rumaisa ta ce “Eh ɗin, tana da wanda take so yake son ta, amma ba wani jabir”

 

Takawa ya ce “To wa take so? Dan bani da labari”

 

“Ban gayawa kowa ba dai, saura ka faɗa kaima, mai sunan baba take so, kuma yana sonta shima”

 

Da sauri takawa ya ɗago ya ce “What?! Umar ɗin gidanku?”

 

“Eh mana”.

 

“Amma iman ba ta da da hankali, ina ita ina wannan yayan naki?”.

 

Rumaisa ta haɗe rai ta ce “Saboda talaka ne ko?”.

 

Shi ma ya ɗan tsuke fuska ya ce “Bana son bahaguwar fassara. Amma kin san halinsa dai sai dai ki gayawa wani, iman kuma is very simple and cool, ta yaya?”

 

Rumaisa ta ce”Ta yadda aka yi ka aureni, kai ba ruwanka, sai dai idan saboda talaka ne ba zaku ba shi ba, yaya umar bai taɓa damuwa da halin da wani yake ciki ba, ko zai shekara dubu bai ga mutum ba, in dai ba mama ba ce ko ni, ba ruwansa, amma zuwan da muka yi ya ce mini ina ƙanwar mijinki, to dan Allah ba soyayya ba ce haka? Ai kai dai ka san soyyaya ko, ka san ya ake ji?”.

 

Yayi ajiyar zuciya ya ce “Ke baki santa ba?”

 

“Ina na sani, ni fa sau ɗaya wani ya taɓa cewa yana sona, su yaya Aliyu suka ce, idan suka ƙara ganinsa, sai sun zane shi. To sam ban san ya soyayyar take ba, in ta so in ga ina zance”.

 

Ya kwashe da dariya, rumaisa ba ta rabo da wauta.

 

“Ni ba daga zuwa zance, ki ka haɗa kayan zancen ki ka cinye ba, ki ka faɗo jikina, ki ka sani neman kalaman kariya. To yanzu tun da baki taɓa saurayi ba, zan zama saurayinki, mu gani, idan na tafi sai mu din ga waya, irin na saurayi da budurwa”.

 

“Eh ayi haka, Allah ya sa na ji ya soyayya take, in din ga yi maka waƙoƙin soyayya, irin na Indiya”

 

Dungure mata kai adam yayi yana dariya, ya ce you won’t kill me.

 

“Papa ni fa da, mai sunan baba wani tsoho zai aura mini a unguwar mu, malam ladan, mutumin nan ya taɓa zaneni da carbi, wai daga na tambayi mama wani abu, wai sai yayi mini aure, ya sai mini tabarma da buta. Wai ko a aura mini wani Ɗan ladi mai kan sirdi, kansa kamar plate, ka ga baƙinsa Astagfirullah, tsoro yake bani, gashi ɗan ƙarami, shi ba wada ba gashi nan dai, wata ƴar ajinmu ta ce wai saɓo yayi Allah ya mayar da shi biri, da ya tuba, sai ya koma haka”

 

Takawa zai iya cewa rabonsa da dariya irin ta yau, tun kan aisha ta tafi Saudiyya, dan ruma labarai ta din ga bashi irin na ta’asar da ta din ga tafkawa.

 

A haka ya gama haɗa kayan, kusan tun da ya aureta bai taɓa bata cikakken lokaci kamar wannan ba. Ita abun da yayi mata daɗi a ranta kawai shi take aiwatarwa a rayuwarta.

 

Ya kammala haɗa akwatinsa, ya ajiyeta.

 

Ya ce “To budurwata, na gode da gudunmawa, sai Allah ya kaimu da safe, zamu je na yi wa ammi sallama, daga nan mu je gidan mai girma turaki sai mu tafi”.

 

Ta ɗan yi shiru jiki babu ƙwari ta ce “Papa nan da wata shida, har ayi azumi da salla, kana can ko?”

 

Ya ce “In sha Allah”.

 

“To wa zai din ga baka abinci, da shayin dare?”.

 

“Saya zan din ga yi”.

 

Ta gyaɗa kai ta ce “To shikenan, sai da safe”.

 

“Allah ya tashe mu lafiya, ki kashe mini fitila” har ta kashe fitilar, ya ji kamar tana kuka.

 

“Mimi” ya kirata.

 

“Na’am” “Zo nan”.

 

Ta koma gaban gadon ta ce “Gani”.

 

Ya tashi zaune, ya zaunar da ita a kan cinyarsa ya taɓa fuskarta ya ji hawaye.

 

“Meyasa ki ke kuka?”.

 

Cike da rashin wayo ta ce “Dan Allah idan ka je, kar ka yi aure, bana son kishiya, kuma bana son ka tafi”.

 

Kawai ya kwashe da dariya ya ce “Ai fa dole nayi aure, tun da ni dai ba saƙago ne kamar ke ba. Ga rashin kunya da ki ke yi mini, daga taɓaki sai ihu da kururwa, ina sai dai ki yi haƙuri “.

 

“Amma dai ka san abun da ka yi mini bai dace ba ko? Ba kyau fa”

 

“To ai ba wanda zai gane, idan ba wannan maganannen bakin naki ne, zaki je ki faɗa ba”

 

Cikin damuwa ta ce “To idan ina yadda, ba zaka auri kowa ba, har da wannan samhar?”.

 

Ya ce “Eh mana”.

 

Ta ce “Taɓ! Wallahi na san Allah ya na kallona, kuma zai ƙonani, mama ta ce in din ga jin tsoron Allah a duk in da nake, idan ba ta ganina Allah yana kallona, kuma idan na lalace ban yi mata adalci ba. Ka yi auren ni dai ba zan iya ba, amma ban da samhar nan, dan na tsaneta” sosai hawaye yake kwarara a fuskar rumaisa, zai iya cewa tun da suka yi aure, duk bala’in da zai faru, sai dai tayi ta wulƙita ido, tana harare-harare, amma ƙarara weakness ɗim ta ya bayyana yau.

 

Kwantar da ita yayi a gefensa, sannan ya kwanta yana shafa kan ta ya ce “Let’s make a memorable day, mu kwana tare. Amma dai zan yi shawara tun da kin ce ba kya son kishiya, idan kin canza halinki kin daina rashin ji, sai a fasa idan baki canza ba, samha zan auro. Ita ba zata din ga yi mini ihu ba, tun da tana so na”.

 

Shiru ta yi masa, tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, to ta din ga yadda saboda ba ta san ya ƙara aure. Amma da ta tuna, idan yayi aure haka zai din ga wasa da samha, ita ma ya din ga kaita makaranta, su din ga zuwa cin abinci tare, ita ma ya din ga rungumeta kamar haka yana yi mata dariya, su din ga ball tare wataran kamar yadda suke yi.

A ranta ta ce bana son kishiya, amma ba zan ci amanar mama ba.

 

Bacci ne yayi awon gaba da ita, ba tare da ta gama tunanin ba. Adam kuwa ya rungumeta sosai yana shafa gashin ta.

 

“Am going to miss you mimi, am feeling like am leaving my priceless asset in Nigeria. A lokacin da mutane suke yi miki kallon mara kunya, wadda ba ta ji. Ni a lokacin nake hangowa amfanin ki, a cikin al’umma, kin zo da babbar fitila mai haska hanya a cikin rayuwata, duk da kina bani wahala, am still owing you a debt” ya ƙarasa maganar a hankali tamkar tana jin sa, ya sumbaci goshin ta.

 

Addu’a ya cigaba da yi, na Allah ya bashi lafiya, kafin ya dawo, dan wannan wani babban sirri ne mai nauyin da yake jin, ba zai iya sanarwa da wani shi ba.

 

Ya sake ƙanƙameta, yana tuna farkon haɗuwarsu, da abubuwan da ta yi masa zuwa yanzu.

 

Da safe tare suka karya, sai dai ta ƙi sakin jiki ta ci, sai kallonsa da take yi, tayi masa zuruuu da ido.

“Kalli gabanki, zan ƙware”.

 

“Ni ba kallonka nake yi ba, gara ka tafi in huta, a daina takura mini”

 

“To mutumin da zai je yayi sabon aure fill, cikakkiyar mace ya rabu da ƙwaila, sai me dan ƙwaila ta ce ba ruwanta da shi?”

 

Ta haɗe rai ta ce “Ba ruwanka da ƙirjina, ka daina ce mini ƙwaila, kuma in sha Allah sai sun fito mini”

 

Ya sakata a gaba ya din ga dariya, ita kuma ta haɗe rai tana tura baki.

 

Bayan sun gama, da ita ta fito masa da akwatinsa, daga baya ta ce ba za ta ɗauka ba, tun da yake ce mata ƙwaila.

 

A ƙasa ya ce wa su baba uwani, idan ya tafi, zasu tattara su koma can gida gaba ɗaya, ba zai bar rumaisa a gida ita kaɗai ba.

 

Ƙarfe tara na safe, suka isa gidan ammi, ana ta yi wa takawa fatan alkhairi, abun mamaki sai ga Mummy ma a sashin Ammi, wai ta zo yi wa takawa Allah ya tsare, tun da bai je yi mata sallama ba.

 

Tana yi tana satar kallon ruma, ita kuwa ruma ba ta tata take yi ba, abun da ya dameta daban.

 

A gidan adam ya sauya kayansa zuwa shigar sarauta, ba kunya rumaisa ta ce “Masha Allah, saurayina ka yi kyau”

 

Yayi murmushi ya miƙa mata hannu ya ce “Ban mu kashe” ta bashi nata suka tafa.

 

Su Fauziyya da basu saba ganin taɓarar da rumaisa take yi, ko a gaban waye ba in dai suna tare da takawa, suka din ga ƙananan maganganu.

Laila kuwa kallon su kawai take yi, tana observing ɗin rumaisa.

 

Harabar gidan suka fito, hannunta na cikin na takawa, in da wasu za su raka adam gidan turaki.

 

Sai dai ya ga Mahmud riƙe da mukulli a tsaye a jikin motar da za a ja shi a ciki, nan aka tsaya kallon kallo.

 

Rumaisa a hankali ta ce “Papa” ya kalleta.

 

Tayi ƙasa da murya ta ce “Dan Allah kar ka watsa mini ƙasa a ido, na yi iya ƙoƙari, kan a kawo wannan mataki, dan Allah kar ka watsa mini ƙasa a ido, ko dan ammi ta ji daɗi, sau ɗaya ta ganku tare, shi ya yarda ya ja ka a mota, dan Allah papa Please, kar ka yi wani abu da zaka sa maƙiya su ji daɗi”

 

Kallonta yake yadda take yi masa magiya, Mummy kuwa kanta yayi bala’in ɗaurewa, ta tsaya ta ga ikon Allah, kawai ta ga takawa ya ja rumaisa sun shiga motar, Mahmud ya karɓi sabir, ya saka shi a gaban motar, ya shiga ya kunna.

 

Motar da ammi suka hau ita da laila, kuka ammi take, tana “Laila, kin ga Mahmud da Adam tare a wuri ɗaya, Allah na gode maka, Allah ka ƙara haɗa mini kan iyalina”.

 

Laila ta ce “Is ok my dear ma, ai dama na sha gaya miki, addu’a da ki ke yi, Allah yana karɓa, lokaci ne kawai”.

 

Rumaisa a mota kuwa, sai aikin rarrashi takawa yake yi, ta kalleshi ta ce “Papa, na gode da baka watsa mini ƙasa a ido ba, daddy na gode sosai da sosai, da ka kasance cikin masu yi wa papa rakiya, ammi za ta ji daɗi sosai “

 

Mahmud ya ce “Daughter, ba abun da ba zan iya yi miki ba, ba sai kin gode ba”.

 

Ruma ta ce “To ba zaku yi magana ba? Ku gaisa”

 

Fuskar Adam ta kalla, yadda ya haɗe rai, ta ɗan girgiza kai ta ce “Papa, na ajiye maka saƙo a akwatinka, duk abun da ka gani, idan ka je, kar sake ka tambayeni komai a kai, kuma kar ka saka wani ya tambaye ni, har sai Allah ya dawo da kai lafiya”.

 

Ya ce “Menene abun?”

 

“Idan ka je zaka gani”

 

Shiru ya ɗan yi yana tunani, a dai-dai lokacin da suka shiga gidan turaki, ana ta bushe-bushe, turaki yana daf da fitowa.

 

Takawa ya saukko daga motar, bai iya tsayawa gaisawa da kowa ba, duk da ga su jabir da Jamil, da sauran manyan mutane, sai ƙoƙarin rarrashin rumaisa da yake yi a gaban mutane.

 

Kuka take yi sosai, yayi ƙasa da murya ya ce “Ki na so ni ma na yi kuka ne?”

 

Ta girgiza masa kai. “Haba budurwata, a haka zamu rabu? Saurayi da budurwa fa ba haka suke yi ba, ki daina kuka, zamu din ga waya, Allah ya tsare mini ku, ya kula da ku”.

 

Su Fauziyya tuni suka dira a gidan, suka wuce wurin Samha, suna bata labarin, abubuwan da suka faru a tsakanin ruma da takawa yau, wanda hakan ba ƙaramin jefata ya yi cikin matsanancin tashin hankali yayi ba, baba uwani ta yaudareta, da ba ta sanar da ita alaƙar da ke tsakanin takawa da ruma tayi ƙarfi haka ba.

 

Ta window ta hango takawa yana sharewa rumaisa hawaye, ya danƙa hannunta cikin na laila, ya nufi Mahmud da yake tsaye da Sabir a hannunsa, ya shafa kan sabir yayi masa kiss a goshi, ya nufi wata motar.

 

Da sauri Samha ta koma ɗakinta, ƙafarta har rawa take saboda tashin hankali, ta kira baba uwani a waya, ta rufe ta da bala’i.

 

Baaba uwani da ta rasa in da zata saka kanta, saboda ta ko ina, matsi da kyara take fuskanta ta ce “Ba laifina bane ba fa, Hajiya Jamila ce ta ce kar na sake sanar da ke komai, sai abun da ta yi mini izini”.

 

“What? Mummyn? Ni za ta ci amana!? Kuma ta rufe ni ba ta gaya mini ba?” Sakin wayar ta yi tare da yin ashar.

 

“Lallai matar nan baki san wuta ba, kuma kin takata a yanzu, zan yi maganinki, da ni ki ke zancen”.

 

Mummy ma na can ƙarshen kiɗima ta shigeta, ganin Mahmud da kansa, ya ja adam a mota, lallai tsuguno ba ta ƙare ba.

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 73 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button