Halysaah Page 155 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 155…Ajay ya bude idonsa slowly jin lips dinta a saman kansa, ji yayi she just turned him on, yaji kamar ya jawota jikinsa ya rungumeta, ya dan kalli Driver sai kuma ya kai hannunsa kan laps dinta a hankali in a romantic way yana shafa mata su, tana ganin haka ta buge hannunsa da sauri, dariya ta basa ya daga kai ya kalleta da lumsassun idonsa kamar me jin bacci, ta hade rai murya can kasa tace “Meye haka? Ni ka tashi kusa da ni Yaji dama ya dora kansa saman laps din nata banda driver dake gaban motar, kawai ya maida kansa saman shoulder dinta ya lumshe ido hoping she will continue kissing his hair amma taki yin hakan, daga karshe ita ma dai ta kasa resisting kawai ta dora habanta saman kan nasa…. Khaleesat tayi mamaki sosai ganin unguwan da suka zo after almost an hour ride, bayan driver yayi parking a kofar gidan Ajay ya kalleta sannan ya bude motar ya sauka, ita ma ta sauka ta daya bangaren, yaran Aunty Murja da yaran unguwan na hangota suka taho da gudu suna mata Oyoyo, Ajay dai idonsa na kansu kar su yadata ganin yanda suka dabaibayeta, daga karshe sai da ya hade rai yayi masu jan ido yace su saketa, duk suka tsorata suka koma baya suna kallonsa, Khaleesat na murmushi ta nufi cikin gidansu Aunty Murja, Ajay ya bi ta da kallo har ta shiga gidan, can ya juya yana kallon bishiyar mangwaro dake kofar gidan, lokaci daya wani memory yayi strucking kansa, ya dan yi murmushi ya jingina da motarsa ya rungume hannuwansa, Khaleesat na shiga cikin gidan Nenne dake zaune tsakar gida tace “Ikon Allah, zuwa babu sanarwa ke kuma?” Khaleesat ta zauna kusa da ita tana murmushi tace “Nima bai ce min za mu zo nan ba Nenne” Gaida matan gidan Khaleesat tayi ta maida dubanta kan Aunty Murja dake tayi mata sannu da zuwa ta amsa mata, Aunty Murja tage “Daxun nan Nenne ta gama maganar ki ashe kuna hanya” Khaleesat tayi murmushi tace “Ina Jiddah Aunty?” Aunty Murja tace “Kamar sun shiga makota da ita” Nenne ta mike tace “Sai keken nan ya zama kwandem hankalinku zai kwanta ku dena fafa da shi a unguwa, kika san nawa ake siyar da keken nan da za ki bari a maida shi abun wasan yara?” Dakin Aunty Murja Nenne ta shige tace “Sai dai ki nemi me siya maku wani amma ba Yarima ba” Khaleesat na murmushi ta mike ta bi bayan Nenne zuwa cikin dakin, ta zauna kusa da ita tace “Nenne Noor fa?” Nenne tace “Sun fita kasuwa da Abida, ina mijin naki?” Khaleesat tace “Yana waje” Nenne tace “Kai haba, shi ne baki fada ba ace ya shigo? maza tafi ki ce ya shigo ke dai baki da kai sai na daukan kaya wallahi, amma dai kafin nan ya za ayi da wannan magungunan da nake ta adanawa Khaleesah? Ni fa saboda maganin nan yasa ban koma Kano ba har yau, ina ta zuba idon ranan da zaki zo amma shiru, gashi ina ta zaune gidan nan kamar mara makabuli, ke baza ki iya ce masa za ki zo gaida ni ba Dreba ya kawoki ke kadai dole sai kun zo tare? Ta yaya za ayi ta zama babu aure? Yau naga abinda ya isheni ni dai” Khaleesat ta sauke ido tayi shiru, Nenne tace “Ba shiru zaki min ba don ubanki, ki bude baki ki gaya min abinda ke faruwa in kun zo kwanciya kar ki boye min komai don ance min asiri aka maki, baki ji yanda hankalina ya tashi ba da naji wannan magana, har yanxu kullum cikin xulumi nake idan maganin nan ma yaki yi ina za mu kama ni ‘ya su, to balle ma an rasa ta yanda maganin zai kai gare ki ba tare da wani yaji ko ya gani ko kuma ya sani ba” A hankali Khaleesat tace “Ni fa Nenne ba komai yanxu….” Nenne tace “Kamar ya ba komai yanxu?” Khaleesat ta turo baki tace “Ba sai nayi amfani da maganin ba kawai” A fusace Nenne tace “Kamar yaya ba sai kin yi amfani da maganin ba? Kun yi mu’amala da shi ne?” Shiru Khaleesat tayi, cikin fada Nenne tace “Na shiga uku da wannan yarinya kina ta bani wahala gashi duk hayakin iccen da ake girki da shi a gidan nan yasa nayi bakikirin na kode, ni da nake cikin AC a Kano banda lalura me zai sa in zo gidan nan in jabe? kayana fa banda warin hayaki babu abinda suke kamar warce taje karkara, ko mutum na gifta sai yaji kamar an turara kayan da icce, kuma ki ce min ke baza kiyi amfani da magani ba?” Khaleesat ta wani kalleta tace “Tunda nace ba sai nayi amfani da su ba ai ba sai nayi ba” Nenne tace “Shi ne nace ya san ki ne yanzu?” Dariya Nenne ta ba Khaleesat, can ta kwanta gefenta tace “Kila” Nenne ta kundumo mata wani zagi a fusace tace “Ni zaki mayar er iska ina maki magana?” Khaleesat ta turo baki tace To ai an riga an wuce wajen, me kuma zan yi da magani” Nenne tace “Da gaske kike ko kuma rainin wayo?” Khaleesat tace “To wai ba kun zo kun gan ni a bangaren Hajja ba” Nenne ta bude ido sosai tace “Me kika je yi bangaren nata?” Khaleesat ta kauda kai tace “Ai shikenan tunda ke baza ki gane ba sai mutum yayi ta magana Nenne tayi kasa da murya tace “Komai ya kankama tsakanin ku kenan?” Murguda mata baki Khaleesat tayi, Nenne ta daga hannu biyu sama tace “Alhamdulillah Allah Nagode maka, ai addu’a baya faduwa kasa banza, saboda wannan lamari kullum sai nayi tsayuwar dare in kai ma Allah kuka” Aunty Murja ce ta leko dakin tace “Nenne nace ma Yarima ya shigo, gashi nan ya shigo ki fito ku gaisa Da sauri Nenne ta jawo babban mayafinta tana yafawa tace “Gani nan zuwa Daga haka ta mike ta fita daga dakin zuwa tsakar gida, Ajay na zaune kan tabarman da Aunty Murja ta shimfida masa bayan ya gaisa da matan gidan, Khaleesat ta dinga kallonsa ta space din labulen Aunty Murja babu ko kiftawa, fararen kaya ne jikinsa, duk da gaisawan da yake yi da Nenne yaki daga kansa ya kalleta, Nenne tace “Mun ga abun arziki shekaranjiya, Allah ya saka da alkhairi ya sa afı haka Yarima” Aunty Murja na murmushi tace “Ameen” Ajay yace “Ina Noor da Jiddah?” Aunty Murja tace “Noor sun fita kasuwa da er mijina, Jiddah kuma suna makota wallahi” Kamar ance Ajay ya daga kai suka yi ido hudu da Khaleesat dake ta kallonsa daga cikin dakin Aunty Murja, murguda masa baki tayi bayan sun hada ido, shi dai ya sunkuyar da kansa yana dan murmushi, Nenne tace “Ya su Hajiya, fatan lafiya ku ka baro su?” Ajay yace “Lafiya Alhamdulillah” Aunty Murja tace “Nenne wai tafiya fa za su yi shi ne suka biyo su gaisheki” Hakan da Aunty Murja ta fada ba karamin taimaka ma Ajay yayi ba don ya kasa gaya ma Nenne akan hanya suke, gashi lokaci na wucewa, dama da Aunty Murja ta fita tace ya shigo ciki shi ne yake gaya mata za su yi tafiya ne suka biyo gaida Nenne, Nenne na jin haka tayi insisting su tashi su tafi ta leka daki da sauri tana kiran Khaleesat ta fito su tafi, har bakin mota yan gidan suka rakasu gaba daya, Ajay na kallon Aunty Murja yace “Zan tura sako ta account dinki za a ba Kaka” Nenne tace “A’a gaskiya Yarima wannan abun arzikin da ka hado Noor da shi ma ya isa wallahi, mun gode Allah ya sa afi haka” Shi dai bai ce komai ba ya bude ma Khaleesat back seat, ta daga manyan idanuwanta ta kallesa sannan ta shiga motar ya kulle, ya zaga ya shiga ta daya bangaren, Driver na reverse ya kalli Khaleesat dake waving ma su Aunty Murja hannu, ya jira har drivern ya gama reverse sannan ya kai bakinsa kusa da kunnenta yayi kasa da murya yace “Ko ince driver ya tsaya ki dan tsinka mana Mangoes? Naga you are good at that” Yana fadin haka ta tuno ranan da ya dawo da su Nenne da Aunty Farida ita kuma tana tsalle karkashin bishiyar mangwaro da dogon sanda a hannunta zata yi pluck din Mangoes ga yara sun bebayeta, kamar zata yi kuka ta rufe fuskarta tace “Bana son hakaa” Ya jingina da kujeran motar ya lumshe idonsa abubuwa da yawa na dawo masa zuciyarsa. Washegari karfe hudu na yamma suka sauka kasar Tanzania don a gidan Ammi suka kwana daren jiya bayan ya kai Khaleesat tayi mata gaisuwa, A airport din Dar es Salaam yayi booking Uber da zai kai su Hotel din da yayi masu reserving tun a Nigeria, suna shiga Uber din bayan sun bar Airport Ajay ya jawota kusa da shi yana kallonta ganin she is looking so tired and exhausted yace “Lazy gal, 6 hours flight din ne kika yi laushi? We still have another flight to Zanzibar tomorrow” Ta daga ido ta kallesa, yayi kasa da murya yace “How do you cope when going to Maryland?” a hankali tace “Ina ne Maryland? Ka san ni a can ne?” Murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba ya dauke idonsa daga kallonta, ita kuwa sai kallonsa take babu ko kiftawa, after a while ya kwantar da kanta a hankali kan shoulder dinsa to give her support, tayi lamo kan shoulder din nasa, a haka ta fara bacci, har suka isa hotel din da yayi masu reserving Khaleesat bacci take, bayan drivern yayi parking Ajay ya sauke idonsa yana kallonta, he couldn’t stop looking at her, ya kai hannu yana shafa gefen fuskarta gently, ta bude idonta a hankali tana kallonsa, ya hada goshinsa da nata yayi kasa da murya yace “Ko in dauke ki mu shiga ciki?” Turo baki tayi ta fara kalle kallen inda suke, ta dinga kallon 5 star hotel din da Uber ya kawo su, Ajay ya bude motar yana kallonta yana jira ta sauka, fita tayi sannan shi ma ya fita daga motar, drivern Uber din har ya sauke boxes din su ma’aikatan hotel din sun shigar masu da shi ciki, yana rike da hannunta suka nufi cikin babban hotel din, basu jima a reception ba wata ma’aikaciyar hotel din tayi masu rakiya har zuwa dakinsu ta bude da Access card din kofar sannan ta mika ma Ajay tana kara welcoming dinsu zuwa hotel din, workers din da suka taho da boxes dinsu suka shigar masu da shi dakin leaving it by the door side, Khaleesat ta karasa cikin babban dakin ta kwanta kan gado ta lumshe ido, bayan wa enda suka shigo da boxes dinsu sun fita Ajay ya karasa kusa da ita ya zauna ya kai fuskarsa kusa da nata leaning on her body yace “Sallah fa?” Ta bude ido a hankali, ya dagota ta mike zaune yace “Me zaki ci in amso maki kafın ki idar da sallah?” Ta girgiza kai tace “Bana jin yunwa” Dagota yayi ya nufi hanyar bandakin dake dakin tana biye da shi hannunsa a nata, ya bude mata bandakin ta shiga ciki, ko da Khaleesat ta fito bata gansa a dakin ba, tayi sallolinta sannan ta kara kwantawa kan gadon…. Ajay bai tasheta ba bayan da ya dawo dakin ya sameta tana bacci, ya rufa mata duvet don dakin da sanyi sosai, yayi kissing cheeks dinta sannan ya tafi ya zauna kan kujera yana duba wayarsa yaga kiran Mai martaba, he was expecting to see Jay’s call amma bai ga kiransa ba. Bayan Magrib Ajay ya sauka downstairs tare da Khaleesat hannunsa cikin nata suka tafi restaurant din dake hotel din, babu abinda babu na African Cuisine a restaurant din, duk ita ta zabi abinda zata ci da drinks, shi dai yana tsaye kusa da ita duk motsin da tayi idonsa na kanta, bayan ta gama zaba ta kallesa don ta tuna ba ko ina yake cin abinci ba, a hankali tace “To kai me zaka ci?” Da ido ya bi wajen da kallo, sai kuma ya matsa dab da ita har suna jiyo numfashin juna murya can kasa yace “Ke mana….” Unexpectedly amsarsa ya zo ma Khaleesat, taji wani irin kunya ya rufeta, tayi masa wani kallo tana tura baki zata matsa daga kusa da shi ya riko hannunta a hankali yace “Ko in kwana da yunwa?” tayi saurin kauda kai, kauda kan da tayi kawai ta hada ido da Abdul that was standing not too far away from them yana kallonsu, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa with surprise, exactly dressing din larabawan Dubai yayi na jallabiya ya daura Ghutrah a kansa, ya dan mata murmushi hakan yasa ta dauke kanta da sauri daga kallonsa, zuciyarta na bugawa ta kalli Ajay da shi ma ya dauke kai bayan ya hada ido da Abdul, Abdul ya karasa har inda suke har sannan murmushin fuskarsa bai yi fading ba ya mika ma Ajay hannu yana kallonsa Calmly yace “Assalamu alaikum” Ajay had no option than doing same to him suka gaisa casually, Ajay ya dauke kai, Abdul ya juya ya kalli Khaleesat yana murmushi yace “Hi Khaleesat, fatan kuna lafiya” Bata yarda ta kara kallonsa ba ta gyada kai da kyar tace “Alhamdulillah” Yace “Maa sha Allah” Daga haka ya amshi katin kudinsa da ake mika masa sannan yayi ma Ajay sallama ya juya ya bar wajen, Ajay zai biya kudin abincin da Khaleesat ta zaba aka mika masa Receipt aka ce ai Abdul ya biya kudin gaba daya, Ajay bai ce komai ba ya karbi receipt din ya mayar da card dinsa cikin aljihu ya amshi abincin da aka yi masu packaging ya bar wajen, Khaleesat ta bi sa da kallo sannan ta bi bayansa tana tafiya a hankali, har suka isa hotel room dinsu yana gaba tana biye da shi unlike yanda suka sauko downstairs yana rike da hannunta, bayan sun shiga dakin ya ajiye ledan abincin a kan table ya shiga bandaki without looking at her, Khaleesat ta zauna kan kujera, after a while ta jawo abincin da ya ajiye mata kan table ta bude, duk da yunwan da take ji bata wani ci abincin da yawa ba, don har ya fito wanka tana cin abincin little by little, sau daya ta kallesa ta sauke idonta don stature dinsa tsoro yake bata sosai, after a while ta dan saci kallonsa taga har ya sa jallabiya ya hau kan darduma zai tada sallah, har ya idar da sallah abincin na gabanta, can dai ta rufe abincin ta matsar daga gabanta don ta ma kasa ci, mikewa taga yayi daga kan darduman ya dau wayarsa ya zauna gefen gado, ta sunkuyar da kanta, shi kam ya hau duba wani hotel ta online, cikin few minutes yayi making reservation din wani hotel din sannan yayi order din Uber da zai kai su can….
