Uncategorized

Macijine Shi Page 11-12 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 11/12

Ta ƙabbalallahu Minna waninkum.

Slm, ƴan uwa masoyan littafin MACIJINE, ina  miƙo gaisuwa tare da Barka da Sallah ,Allah ya maimaita mana,yasa munyi karɓaɓɓiyar

Ibada.

________________Kai tsaye su baffa suka nufi gurin lamiɗo,hannunsa riƙe da na fattu ,wacce ke tafiya ahankali cikin azabar raɗaɗin  da hannunta keyi,dakuma ciwon jiki.yayinda su arɗo ke mara musu baya burinsu kawai suga wane irin hukunci lamiɗo zai ɗauka akansu fattu ,cikin zuciyarsa arɗo yake fatan inama lamiɗo ya kori su fattu daga rugar ,inyaso su bisu hanya  suyiwa fattun fyaɗe,dan su kashe ƙishirwarta dake cin ransu.

Shikuwa mai gari tun daga nesa ya hango su fattu,gaba ɗaya nutsuwarsa ta bar jikinsa,ƙureta yayi da ido guri!!yana haɗiyar yawu da lasar leɓe kamar tsohon maye.

Kallonta yake yana ji kamar yaje ya kamota yayi ɗaka da ita.

haba malam ,yarinya bul-bul  da ita kamar nunannen tumatur,lallai yau zai sha shagali.lamiɗo ya faɗa cikin ransa yana mai kallon fattun.

Baffa kuwa suna ƙarasowa gaban mai gari ya nemi guri ya zauna tare da zaunar da fattu kusa dashi,wacce gaba ɗaya arikice take ,tsorone ƙarara shinfiɗe akan fuskarta.tayi luƙus ajikin baffanta jikinta sai rawa yake, ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa ,sai hawaye take sharewa.

Kowa yanemi guri ya zauna ,masu tsayuwa suka tsaya , da ƙyar lamiɗo ya iya saita kansa ya aro nutsuwa ya  yaɓa  akansa, tare da ɓata ransa ya kalli  baffa yace “malam bukar kana sane da irin abinda ƴarka take aikatawa awannan garin ?lamiɗo ya faɗa cikin kakkausar murya .

Ahankali baffa ya gyara zama kafin yace ,naji anata  wai wai  agari cewar ƴata tayiwa su jauro turen maciji ,amma sam ban yarda da wannan magana ba,dan kuwa ƴata ba mai kashe mutane bace ,sannan ba mayya bace kamar yadda ake faɗa”baffa ya faɗa cikin ɗaure fuska .

 Cike da ɓaci rai lamiɗo ya fara magana.

“To wllh malam bukar bazan ɗauki wannan abun agarina ba,yanzu ace abun nata ya wuce kan kowa sai kan ɗana  ?sannan kuma kace wai baka 

yarda da zancen ba ?kana nufin nayi maka ƙarya ne?to bari kaji dole ne saina ɗauki mataki mai ƙarfi akanka da ƴar taka ,dan ka nuna rashin ɗa’a a gaban fada.bayan kuma kowa yaga abinda ƴarka tayiwa yaranmu,

Dan haka  bazan yanke hukunci yanzuba sai zuwa gobe ,idan yaranmu  sun sami lafiya,dan haka yanzu za’a shiga da ita cikin gida anan zata zauna cikin wancan bukkar da ake ajiye masu laifi .

Dan haka kowa ya watse sai zuwa gobe da la’asar adawo nan dan jin hukuncin da zan yanke”mai gari yana gama faɗin haka ya jingina da jikin kujerar da yake zaune akai. 

gaba ɗayan mutanen dake  gurin sunyi na’am da wannan hukuncin nacewar fattu   ta zauna a gidan mai gari ,dan karta gudu.

Kuka sosai fattu ta sanya tana riƙe hannun baffa “wayyo Allah na baffa ka taimakeni,dan Allah karka bari akulleni adakin hukunci ,wllh bani nayi musu haka ba ,kuma sunzone da nufin keta min haddi baffa ka kalli Yadda ya famamin targaɗe na  wllh ba laifi na bane” fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka kamar zata shiɗe.

 

Cikin tashin hankali baffa ya riƙe hannun Fattu ,ji yake kamar ya fasa ihu,aduniya ba abinda ya tsana irin  yaga Fattu cikin damuwa,”kiyi haƙuri fattu ba abinda zai sameki,in Sha Allahu Allah zai saka mana dan wannan mugunta ce ake son yi mana ,kuma Allah yana bayan mai gaskiya”yana gama faɗin haka ya juya gurin mai gari yace “lamiɗo ina neman alfarmar abarmin fattu mu tafi gida ,zamu dawo da ita zuwa goben,dan bata da lafiya kuma barinta ita kaɗai akwai matsala” ya faɗa cikin damuwa da alhinin wannan rashin adalci da ake ƙoƙarin aiwatar musu.

Cike da mugunta lamiɗo yace “kai bukar ina ganin girmanka karkasa in daina gani ka iya bakinka a faɗa kake,kasan idan na riga yanke hukunci ba mai ja dani ,dan haka ka tashi ka bani guri tun kafin raina ya gama ɓaci kuma yanzu zansa aje anemomin macijin duk inda ya shiga daga nan zuwa safiya ,”lamiɗo ya faɗa  yana mai kiran wasu matasa yace su shigar da fattu cikin bukkar.

Kuka fattu keyi tana faɗin”wayyo baffana wayyo Allah ka taimakamin zasu tafi dani wayyo Baffa na karka bari su nemo shi zasu kasheshi. “amma haka suka tura  ƙeyarta suka tafi da ita ɗakin hukunci.baffa yana ji yana gani ,hawayene masu zafi suka silalo daga idon bawan Allah ,zuciyarsa kamar ta faso ƙirjinsa yakeji, ashe ma ƙoƙarin keta masa haddin ƴa akayi?amma saboda rashin imani  da adalci aka ɗora mata sharri,ba komai Allah zai saka musu.

Juyawa yayi ya nufi gida ransa amatukar jagule,yanzu idan wani abun ya sami yarinyar fa?idan wasu suka ƙara yunƙurin cutar da rayuwarta fa?”ya Allah ka karemin yarinyar nan Allah ka duba matsalolin dake kanta da wanda suke shirin samunta.ya Allah ka sauƙaƙa mata ƙalubalen dake gabanta.haka  yayi ta mata addu’a harya ƙarasa gida kwata kwata hankalinsa baya jikinsa.

Yana shiga gidan  gwogwgo hansai ta sanya dariya cike da mugunta harda riƙe ciki tana nuna baffa da hannu.”wllh malam Gara ka cire wannan yarinyar daga zuciyarka,  inba haka ba kana tsaye zaka yanke jiki ka faɗi ka mutu.ba ruwa  na bani da asara, ai wllh banso lamiɗo ya kyaleta wai har sai gobe ba,daya sani yasa anyanke mata kai yau -yau ɗin nan ,da mun huta da nauyinta akanmu” ta faɗa tana turo wani baƙin ɗan kwalinta mai shegen datti zuwa gaban goshinta.

Kallon ta kawai baffa keyi ,cikin zuciyarsa yake kissima iri saɓawa gwogwgo da zaiyi dan yau zai nuna mata matsayin fattu azuciyarsa ,sai dai yana yunƙurowa da nufin maida mata martani,kawai yaji bakinsa yayi nauyi,wani irin shayinta da tsoro ya mamaye zuciyarsa.kai kawai ya girgiza ya wuce ɗakinsa ,wato itama gidan mai garin taje kenan?ba komai akwai Allah.

Fattu kuwa tunda aka turata cikin ɗakin nan banda kuka ba abinda takeyi, ita damuwarta ma yanzu bai wuce na rashin ganin macijinta ba,duk wannan abunda ke faruwa baizo ba.anya kuwa lafiya?kodai wani abu ya sameshi ne?

“Ya Allah ka kare wannan bawan naka ,ka bashi kariya daga sharrin mugayen mutane .

Shikuwa maciji adaidai wannan lokacin yana gidansu fattu yaje nemanta bai ganta ba yayi ta zagaye aɗakinta amma bata nan,tun lokacin datayi masa karatun nan daya fita yaje can jeji ya kwanta ,sam bayajin daɗin jikinsa sosai yake jin ciwo ta ko’ina ajikinsa,sai da lokaci yaja sannan ya nufi gidansu fattu ,ahankali yake tafiya cikin ciyawa da jikin katanga, harya ƙarasa gidansu fattu.

Koda yaje yaga bata nan saiya yi ta zagaye ɗakin yana nemanta ,amma bata nan. Kwanciya yayi akan ɗaurin kayanta yayi lamo kamar ya mutu.saidai hawayene ke zuba cikin idanunsa .

Can kuwa gidan mai gari ,da misalin ƙarfe bakwai na dare sosai hadari ya haɗu agarin, dan haka kowa ya shige cikin gida dan gudun zubowar ruwan,da akowane lokaci yana iya sauƙa.

Daidai wannan lokacin kuma fattu na duƙunƙune cikin ɗakin  hukunci sai kuka take zuciyarta tayi mata ƙunci ga yunwa dake addabar ta rabo ta da abinci tun madarar da baffa ya bata da safe.hannunta sai zagi yake mata.

Ahankali taji ana turo kofar ɗakin hukuncin,da alama shigowa za’ayi,ga duhu aɗakin.

Zabura tayi cikin sauri ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa,kar dai ace su jaurone suka dawo ?wayyo  Allah na ” ta faɗa tana dafe ƙirjinta ,zuciyarta kamar zata fito dan tsoro da firgici.

Cikin rawar murya tace “wa…w….ayee.”

Ahankali cikin murya mai kama da raɗa,yace “ke kwantar da hankalinki,nine nan lamiɗo”

Ya faɗa yana mai haska tocilan ɗinsa  .

Cikin zubar da hawaye tace “dan Allah lamiɗo ka fitar dani daga gurin nan ,wllh ban aikata komai ba,bani na kashe jauro ba”ta faɗa cikin kuka.

“Kinga ki nutsu jauro bai mutu ba yana raye ,kuma idan kika bani haɗin kai muka yi komai  cikin sirri ,to zan kyale ki ki tafi gida abinki”lamiɗo ya faɗa yana matsowa gareta.

Ja tayi da baya cikin sauri tace “me kake so nayi maka ?dan Allah ka gyaleni na tafi gida ,an fara ruwa”ta faɗa cikin kuka,dan ta gano manufarsa ,irin tasu jauro ce ,wato fyaɗe yake son yi mata.

Matsowa lamiɗo yayi tare da ruƙo hannunta yana mai cewa”Ayya fattu yarinya mai kyau da kyan jiki ki yarda dani mana duka -duka minti nawa ne ba dayawa zanyi ba kinji ki taimaka min”ya faɗa yana mai janyota jikinsa sosai .

“Wayyo Allah na baffa kazo ka taimakeni,dan Allah lamiɗo kayi haƙuri wllh ba kyau kaji tsoron Allah ka tausaya min na roƙeka”fattu ta faɗa cikin rawar jiki da matsanancin kuka,tana mai tureshi daga jikinta,banda warin tsufa ba abinda yake yi.

“Ke dan ubanki ki tsaya ko saina miki ta ƙarfine?Shegiyar yarinya haka zamu zuba miki ido muna kallonki kin cika kinyi tunjum dake amma ba mai morarki,ki tsaya dan ubanki”lamiɗo ya faɗa yana mai ɗauke fattu da wani gigitaccen mari Wanda saida ji da ganinta suka tsaya na wucin gadi.kusan minti biyu kafin kwakwalwar ta ta dawo aiki,kuka ta sake fashewa dashi mai tsananin gaske lokacin da lamiɗon ya Kaita ƙasa yana ƙoƙarin dage yar ficiciyar rigar dake jikinta ,wacce jiƙaƙƙiyar ƙasar nan ta gama bushewa .

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un wayyo Allah na baffa wayyo mai taimako kana ina?kazo gareni,ina buƙatar taimako ka ahhhhhhhh “fattu ta kwalla wani irin ƙara mai ƙarfi lokacin da lamiɗo yayi………

Tofa masu karatu me lamiɗo yayiwa fattu ne ?

Muje zuwa kuci gaba  da bin alƙalamin anty mammy.

Mrs babi 💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment 

More typing.

Back to top button