Novel Document

Mejo Najeeb Romantic Complete Hausa Novel Document

Description/Story:

Menjo Najeeb Book 1! Complete Hausa Novel Document Written By Autar Alheri

 

Description

“Tafiya sukeyi cikin nutsuwa acikin wani Dan jeji daga dukkan alamu Rafi suka nufa konace gulbi inkagansu kamar wasu tagwaye Amma kallo Daya zakamusu kasan cewar batagwaye bane sedai k’awayene na Amana, Sund’anyi tafiya menisa kamun d’ayar tad’ago tana fad’ar Isseta Allah nagaji wai haryanzu bamukaiba Allah nafara gajiya nidai ko mukoma gida kawai na hak’ura da ganin maman taki…..ahankali wadda akakirada Isseta tad’ago da Dara daran idanuwanta tazubawa k’awar tata kana tabude Baki cikin wani Dan iskan sexy voice me masifar ratsa jiki tace “ayya yi hak’uri halima ai munkusa k’arasawa kecefa kikace nagaya mata zakizo kiganta yanzu idan bamuje tareba bazataji dad’iba. Takarasa zancen tana matse hannun halima sosai. Da kallo nabisu dukkansu Jin yadda Isseta ke maganar hausarta Bata bita da kyau sosai dajin yadda bakinta yake baseka tambayaba kasan bafulatanace ta’asali, shiyasa nake kallonsu. Ayadda idona sukayi tozalida Isseta seda nayi jinjinaga uban gijin talikai Daya halicci wannan kyakkyawar budurwar me cikar haiba da Kamala cikakkiyar mace Ako Ina son kowa kin wanda yarasa komai yaji ajikin Isseta abun ba’amagana babban abunda yafi birgeni atareda ita shine Dara daran idanuwanta dakuma sexy voice d’inda Allah yabata domin bawai namijiba macema idan taji voice d’inta se yabirgeta….tobawai Isseta ba halima ma ba’abaya takeba wurin kyau da d’aukar hankali abundai sewanda yagani mekaratu ka misilta kyawun way’annan y’anmatan dakanka musamman Isseta domin duk yadda zanmisilta bezama lallai kufahimtaba asalima semucinye page d’in bamu k’areba…….sunyi tafiya menisa kamun suzo bakin wani gab’ar ruwa masu yawan gaske daga dukkan alamu yankin wani tekune acikin rugar tasu idan anshigo wannan jejin.

Tsayawa sukayi awurin halima na karewa ruwan kallo cikin tsoron ganin yawansu yayinda Isseta keta famar doka murmushinda yak’ara fitoda asalin kyauta na fulanin asali…..tsayuwa Isseta tagyara kamun tabud’e Baki cikin sweet voice d’inta tace maaaahhhh. Tafad’a dakarfi yadda duk seda wurin ya amsa, atakeko ruwannan suka d’auki rugugi suna torok’o ijiyar ruwan nayi sama tana dawowa alamar wani abun nason bayyana acikinsu…..arazane halima tarik’e hannun k’awar tata tana fad’ar nashiga ukku Isseta minene kikayi Hakan ? Miyasa wannan ruwan keyin Hakan dubafa kigani tafad’a duk a tsorace…kamun Isseta tabud’e Baki Tayi maga sekawai gawani katon jelar kifi Irin shape dinnan me had’iye mutane Tayo Saman ruwan kamun suyi wani k’wak’k’waran motsi sekawai ga mamallakin jelar ta bayyana wato hajo ruwa Rabi mutin Rabi kifi(🧜‍♀️) wani Irin waro Ido halima Tayi tana Munata da yatsa tanaja dabaya Tama kasayin magana gabaki d’aya jikinta ko a’ina rawa yakeyi kamar mazari, cikin wani Irin tsoro da rud’ani take fad’ar innalillahi Isseta munshiga ukku haj…kafin tak’arasa Isseta Tayi saurin rufe mata Baki tana girgiza mata kanta cikin damuwar ganin k’awar tata atsorace tace “Dan Allah halima kinutsu wannan fa mamata ce bawai wadda kike tinaniba Kuma babu abunda zata mana hasalima idan Taga wanda zecutamana bazata bariba Dan Allah kinutsu.

Se yanzu halima tadanji sanyi aranta Jin kalaman k’awar tata ahankali tad’an sassauta rik’on datayiwa Isseta d’in Amma Bata saketa dukaba…….itako wannan kifanyar kallonsu kawai takeyi fuskarta d’aukeda kyakkyawan murmushi gata kamanninta yafito Sak balarabiya.

Ahankali tabud’e Baki tace *MARYAMA* Baki bawa k’awarki labarin mamarki ba bil’adama bace ne? Aidakinga gaya mata bazata tsorataba….murmushi Isseta Tayi ahankali tace “bangaya mataba maahh nasha’afane wlh inata d’aukin zuwa ganinki yau kwana biyufa bangankiba. Tafad’a tana turo Dan k’aramun bakinta gaba.

“Ikon Allah kwana biyu shine abun rigimar maryama? “To ai yayi yawane maah… murmushi maah tak’arayi kana tace shikenan naji yanzu ya kuke keda aminiyarki yakuma gidan naku dasauk’iko? Ta tambayeta cikin kulawa kamar batasan abunda ke faruwaba….ajiyar zuciya Isseta tasauke kana tace “babu sauki maah komai nanan yadda yake Sema abunda yak’aru Allah nafara gajiya da wannan rayuwar maah…tak’arasa fad’a idonta na cikowa da k’wallah.

“Humm kiyi hakuri maryama komai nada lokacinshi Ina gaya Miki akwai ranar da za’ayi walk’iya agidanku ranarda kwaizefashe me masifar wari ranarda Zaki banbace tsakanin Dede da ba dedeba abunda zan gayamiki ayanzu shinedai wanda nasaba gaya Miki shine kiyi hakuri Kuma ban yadda kiyiwa kowa rashin kunyaba agidanku kinjiko Amma bance kibari atakakiba.

Nisawa Isseta Tayi kana tace to maah kid’auki mataki akansu mana…Humm maryama kenan zan d’auka Amma kamar yadda nake gaya Miki komai nada lokacinshi kijira lokaci Yana zuwa dazan dauki matakin kinji y’ar albarka…..to shikenan maah. Tafad’a tana murmushi…itama wannan kifanyar murmushi Tayi ganin Isseta tasaki ranta kana takarabo tamannawa Isseta kiss agoshi Kuma tayiwa halima datayi mutuwar tsaye ganin Rabi mutin Rabi kifi na magana agabanta. Amma wannan kiss da maah tayimata yadawo da ita duniyarmu…sedai ta makara domin lokacinda tadawo hayyacinta tuni maah ta nutsa cikin ruwa har sund’auki rugugi kamar yadda sukayi daga farko. Hakan yasa tak’ara k’ank’ame Isseta sosai domin ita kam haryanzu a tsorace take……

 

File Name   Mejo Najeeb 1… Hausa Novel Doc.
Title    Mejo Najeeb 1
Author    Autar Alheri
Group     Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    05/05/2024
File Size     70Kb
Format Size    TXT
Phone No   07037092176
Download Mejo Najeeb Book 1 Complete Novel Document By Autar Alheri

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button