Ruwan Zuma Page 14 Hausa Novel
(14)“Kwaya kasha ko wiwin da yayi expire Haydar?! Me kake tunani har ka aikata hakan?�? Nasir ya k’arisa maganan yana rik’e kansa cikin mamaki da kuma tsoro. Haydar dake zaune akan benci a store d’in kantin yayi shiru bai yi magana ba. K’ank’arar ruwan dake hannunsa ya canjawa guri daga kumatunsa zuwa gefen bakinsa inda ya kumbura yana jini. “Kana ji ina tambayarka kana cikin hankalinka kuwa?�? Wannan lokacin Nasir cikin 6acin rai yayi maganar tamkar zai kife Haydar da mari. “I don’t know man, nima ban sani ba.�? “Waya dakeka?�? “K’aninta.�? “Sai aka yi yaya?�? “Kawai ta shiga ciki ta barni dasu, shine k’anin nata ya jawoni ta kwalar rigata har k’ofar gida ya hankad’ani na fad’i k’asa na fasa bakina.�? “Then..?�? “I came here.�? “Baka da hankali Haydar.�? “Nagode.�? Da haka ya tashi yana d’ingishi zai fita daga store d’in. “A hakan zaka fita? Ka duba wuyar rigarka a yage ga kumatunka da bakinka a kumbure fa. Ka zauna sai mutane sun watse kafin ka tafi don bazan iya musu k’arya ba in suka tambayeni.�? “A tunaninka zan damu ne? Kana zaton a duniyan nan akwai wani abu da zai faru a rayuwata ya girgizani? Wallahi babu wannan abun! Idan kana neman mutumin da rayuwarsa take cikin garari ka sameni domin har yau ban san ubana danginsa ko kuma wani daga cikin dangin mahaifiyata ba.�? “What?�? “Kwarai Nasir, na maka k’aryar cewa kurciya aka yiwa mahaifiyata don in 6oye sirrina, amma a zahirin gaskiya ni kaina ban san wanene ni ba. Don haka ban damu da duk wata magana ta mutane ba saboda ban d’aukeshi a bakin komai ba. Nagode da k’ank’ara.�? Da haka ya fita ya bar Nasir baki bud’e domin bai ta6a kawo hakan a ranshi ba. Shi da kanshi ya kan nemo maganin karya sihiri ya bawa Haydar wai Ammi tayi amfani dashi duk a cikin taimakon Allah yasa ta yarda su koma gida. Ashe shi kanshi bai san mutanen da yake kiran sunansu yana fad’a masa cewa danginsa bane? Haydar yana komawa gida ya samu Ammi a bakin murhu tana tuk’a tuwo. Ganin yanda ya shigo a hargitse yasa ta mik’e tsaye tana dafe k’irji cikin firgici. “Ali me nake gani haka? Wa ya maka d’anyen aikin nan?�? “Ammi ba wani abun tashin hankali bane.�? Ya shige d’akinsa amma Ammi ta bishi tana cigaba da tambayarsa ba’asi. “Fad’a kayi da wani?�? “Ammi nace miki babu komai.�? “Ya za’ayi kace mini babu komai? A tunaninka bana gani ne.�? Tayi maganar cikin 6acin rai. Shiru yayi ya tu6e rigarsa ya ajiye a gefe yana jin zafin da k’uncinsa ke masa. “Ali ka mini magana don Allah, wallahi ka sakani a damuwa hankalina ya tashi dana ganka haka.�? “Daa kin damu dani daa kin sanar dani waye ni.�? Ya k’ura mata ido yana kallonta. Hawaye ne ya gangaro daga kan fuskarta cikin takaici ta fara magana, “Nice danginka gaba da baya domin kuwa baka da kowa sai ni d’in, ka yarda dani ka kuma yi hak’urin rayuwa a haka kamar yadda nima nayi. Bamu da kowa sai junanmu.�? “Ammi muna da dangi muna da ‘yan uwa, babu yanda za’a yi ace haka kika taso kika ganki babu iyaye. Don girman Allah Ammi ki sanar dani abunda kike 6oyewa a rayuwata, wanene ni Ammi? Waye mahaifina?�? Shima hawayen ya fara yi yana takowa zuwa gurinta. K’asa tayi da kanta tana share hawaye amma bata ce dashi komai ba illa sheshshek’ar kukan da take yi. “Nice uwa kuma ubanka. Ka yarda baka da kowa sai ni.�? “Ammi ko dai ni shege ne?�? Yayi mata tambayar cikin karayar zuciya Tass! Ta watsa masa mari a k’uncin da Mas’ud ya masa d’azu.Nunashi tayi da yatsa amma bakinta ya kasa furta komai illa 6arin da jikinta ya fara yi. Ganin haka yasa Haydar ya tsorita domin irin hakan ya ta6a faruwa da ita lokacin yana secondary school. Nan ma ya dameta ne sai ta fad’a masa wanene mahaifinshi da kuma inda danginsu suke dalilin gorin uba da ake masa a makaranta. A ranar ya gwammace bai d’aga mata hankali ba, domin Allah ne yasa kwananta na gaba dalilin ciwon zuciya da take 6oye masa tana dashi ya tashi. Zaunar da ita yayi a k’asa yana kiran sunanta amma kamar bata jinshi illah runtse ido da tayi cikin ciwo. “Ammi don Allah kiyi hak’uri bazan sake tambayarki akan mahaifina ba. Ke kad’ai nake dashi kuma ke kad’ai kin isheni rayuwa. Ammi ki yafe mini bazan sake ba wallahi.�? Minti goma da haka ya tashi ya fita daga gidan a gigice domin jikin Ammi yayi tsanani bata ko bud’e ido. Napep ya taro a bakin titi suka dawo suka tsaya a bakin k’ofar gidan. Da gudu ya shiga ciki ya sakawa Ammi hijabi sannan ya fito da ita da taimakon mai napep suka sakata a ciki. Emergency aka shiga da ita shi kuma ya tsaya a bakin k’ofar yana kai kawo, a zuciyarsa kuma ji yake yi da mutuwa yayi da yafi masa wannan tashin hankalin da yake ciki. Ina zai sa ransa Idan wani abu ya faru da Amminsa? Matar da take danne buk’atarta don ta biya masa tasa. Matar da tsaya tsayin daka sai yayi karatu ya zama cikekken mutum. Matar da ta yi k’osan sayarwa a bakin hanya har ya gama Jami’a! Matar da burinta guda d’aya ce shine ya zama wani abu a rayuwa ya taimaki al’umma. Ina zai kai tarin laifinsa na sakata a wannan halin da yayi? Minti sha biyar da haka wani Nurse ya fito ya bashi takardan magani da zai sayo. “Ana buk’atarsu cikin gaggawa domin rayuwarta na cikin had’ari. Sannan akwai kud’in test da za’a mata na zuciya shima kud’inshi na jikin takardar. Kayi k’ok’arin kawosu akan lokaci don Allah.�? Ya bar Haydar a gurin ya shige d’akin da ya fito. Haydar jiri ne ya d’ebeshi ya zube a gurin bayan yayi lissafin kud’in gabad’aya. Ina zai samu mak’udan kud’i haka? Ba dai shi zai yi sanadin mutuwar Amminsa ba? Me yake shirin aikatawa? Mutanen da suke tsaye a gurin ne suka d’agashi suna tambayar lafiya amma bai iya furta komai ba illa d’aga musu hannu da yayi alamar ya gode da d’agashi da suka yi. Yana fita daga asibitin ya nufi gidan mai kantinsu domin shi kad’ai zai taimaka masa ya bashi koda aron kud’in ne sai ya dinga biyanshi a hankali tunda yanzu yana aiki. Sai dai bayan Haydar ya gama koro masa bayani Alhaji D’an liti ya murza yatsunsa yace, “Ikon Allah! To ai Haydar kazo a lokacin da bani da kud’i wallahi, domin jiya na sayi buhunan rid’i aka fita dashi waje. Sai dai ga dubu biyu ka rage hanya.�? Da haka ya ciro rafar kud’i ‘yan d’ari biyar-biyar ya zaro dubu biyun a ciki ya mik’a mishi kana ya maida sauran a aljihunsa yana cewa, “Kasan bazan zauna babu kud’i ba ko don iyali, kullum suna bani-bani basa ko tausaya mini.�? Yayi dariya kad’an wacce Haydar yake jinta tamkar bugun guduma a zuciyarsa. “Nagode Alhaji.�? Kawai ya iya cewa ya tashi ya fita yana juya kud’in a hannunsa. Me dubu biyu zasu masa a cikin abunda ake nema? Kantinsu ya nufa gurin Nasir ya jawoshi gefe ya fad’a mishi halin da ake ciki. “Haydar kaima kasan banida kud’i amma wallahi daa sai inda k’arfin ya k’are akan Ammi. Amma muje gurin abokan aikinmu ayi taro-taro ko za’a samu wani abun.�? In ba don halin da Ammi ke ciki na gobe da nisa ba babu abunda zai sa Haydar yabi abokan aikinsa na daa yana rok’arsu kud’i. Wasu sun bayar da dar’i, d’ari biyu har masu naira hamsin amma wasu cewa suka yi basu dashi. K’arshe da suka k’irga kud’in dubu d’aya babu hamsin suka tashi dashi. “Nasir Ina zan je na samu kud’i a yiwa Ammi magani? Idan na rasata bazan ta6a yafewa kaina ba. Duk jajircewarta da kuma soyayyarta a gareni bata cancanci inyi sanadin mutuwarta ba. Ina zan je?�? Hawaye ne ya wanke masa fuska ba tare da ya damu ya goge ba. Tsayawa Nasir yayi a gefenshi yana tunani domin bai san kuma ina zasu je neman kud’i bayan nan ba. Ina zasu je? “Akwai inda zamu je watakila ka samu kud’in maganin Ammi, sai dai ba dole zuwa gurin ya maka dad’i ba.�? Fad’in Nasir yana takawa gaba. Haydar dake zaune a kan steps d’in mashigar kantin ya tashi tsaye yabi bayansa yana tambayar ina zasu je. “Me ya dawo da kai? An ce kar in k’ara bari ka shiga cikin gidan nan.�? Cewar maigadin gidan Laila. “Don Allah Habu ka yiwa Hajiya magana wallahi matsala ce na rayuwa ko mutuwa. Ka taimaka kace ta saurareni.�? Maigadin yayi jimm yana kallonsu, ganin da gaske Haydar na cikin matsala ce yasa yace, “Zan je na fad’a mata amma bazan bari ku shiga ba har sai ta bada izinin hakan.�? “Mun yarda, don Allah kaje da sauri.�? Fad’in Nasir shima yana rik’e tagar k’ofar gidan inda maigadin yake musu magana. Minti d’aya sai gashi ya dawo ranshi a 6ace ya kallesu yace, “Tace bata son k’ara ganin kazo gidan nan. Kuma idan ta sake ganinka a k’ofar gidanta sai tasa an maka abunda yafi na yau.�? Kana ya juya zai tafi. “Kace mata Amminsa ce bata da lafiya tana cikin matsanancin hali. Don Allah mallam Habu ka ceci rai, domin ita kad’ai yake dashi.�? Fad’in Nasir yana dafa kafad’ar Haydar daya sulale a k’asan gurin ya dafe kanshi. Lek’ansu maigadin yayi yaga halin da Haydar yake ciki. In bai manta ba dashi dasu duk talakawa ne, kuma idan masu kud’in basu taimaka musu ba to su zasu taimaki kansu. “Zan k’ara zuwa amma gaskiya Idan bata saurareka ba bazan k’ara komawa ba gudun kar na rasa aikina. ‘Yayana bakwai kuma da aikin nan nake ciyar dasu.�? Yana fad’in hakan ya k’ara komawa falon Laila, Nasir ya bishi da godiya da kuma addu’a. Minti d’aya har biyu babu alamun maigadin ya dawo. Ganin haka yasa Haydar ya tashi tsaye duniyar na juya masa yace, “Mu tafi kar laifina ya shafeshi.�? Ya karkad’e jikinshi suka tafi. A bakin hanya suka tsaya taran acha6a da zai kaisu asibiti, domin Haydar yayi shawarar rok’an likitocin aron kud’i zai biyasu da zarar yayi albashin farko Idan har Laila bata sa aka koresa ba kenan. Wata mota ce ta tsaya a gefensu wanda Haydar yana gani ya gane ta Laila ce. Juyar da kansa yayi gefe kamar bai gani ba watak’ila Mas’ud ne yazo zai k’arasashi. Da yake shima Nasir yasan motar yana gani ya ganeta, ai kuwa ya dake ya tsaya domin bazai bar gurin ba sai ya ramawa abokinsa dukan da aka masa, duk da cewa shi ya jawo. Glass d’in motar aka sauk’e Nasir tuni ya dunk’ule hannunsa zai kaiwa mai tuk’awan duka a baki, amma ganin mace, macen ma kuma Laila yasa jikinshi yayi sanyi ya fara inda-inda yana gaisheta domin shima ba ita yayi tsammanin gani ba. “Ina Ammin take?�? Shine tambayar da ta fara musu fuskarta a had’e babu alamun wasa. Sai a lokacin Haydar ya juyo da yaji muryarta. Ai kuwa yana ido hud’u da ita yaji hawaye ya taru a idanunsa. “Asibitin Murtala ne Hajiya.�? Ya bata amsa yana mai takowa bakin motar har yana buge Nasir. “Ku shigo mu tafi kafin a ganni tare da kai a k’ara had’a wani labarin.�? A gurguje suka shiga suka rufe k’ofar. Haydar a gaba ya zauna yana maida numfashi sannan ya juyo da mamaki a fuskarsa yace, “Wani labari Hajiya?�? “Kafin ince komai wa ka ta6a fad’awa kana sona Haydar? A’a wait! Bana son k’arya domin har yanzu Ina jin kamar in mareka Haydar.�? Zai yi magana ta k’ara dakatar dashi. “Duk maganar da zata fito daga bakinka ka tabbata gaskiya ce Idan ba haka ba wallahi zan nuna maka bani da dad’i Haydar. Wa ka ta6a fad’awa kana sona?�? “Wallahi tallahi na rantse da Allah ban fad’awa kowa ba, ko Ammi bata sani ba, kuma wannan shine babban abokina amma ko shi bai sani ba sai da naje gurinshi bayan abunda ya faru yau. Ko ba haka ba Nasir?�? Ya k’arishe maganar yana juyawa ga Nasir. Nasir da yayi matuk’ar tsorita ya d’aga kai kamar k’adangare yace, “Wallahi Hajiya na masa fad’a sosai har nace bashi da hankali.�? Shiru Laila tayi tana cije le6enta wanda Haydar yabi da ido duk da halin da suke ciki. “Haydar baka san labarin rayuwata ba amma zuwanka cikinta ya jawo mini dana sani, domin duk wani had’uwa da nayi da kai yau an turo mini hotunan ana kirana fasik’a mai neman yara k’anana. Yau kuma da kazo mini da wannan banzan zancen nasan na tafka kuskure dana bari ka shiga jikina ba tare da nayi tunanin me hakan zai jawo mini ba. Ban yarda da zancenka ba, kuma watak’ila kaine kake son blackmailing d’ina, so I’m just doing this for Ammi, amma da zarar an kawar da wannan zan dawo kanka sai ka sanar dani uban da yasa ka fara shiga rayuwata har kake k’ok’arin rabani da masu sona na gaskiya.
Mum Fateey 👌


