Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 27 Book 2 Complete Novel

  

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Abun da ya faru MARSHAL OMAR bai samu zuwa kaduna ba sakamakon Emmergency Call din daya samu daga wurin Abbansu cewa yana bukatar shi A headquater dinsu, a lokacin Motarsu har ta fita daga garin Abuja amma suka juyo da hanzari saboda Omar baya wasa da Omarnin mahaifinsa ko musu baya iyayi mashi, duk da yadda ya matsu akan son ganin su hosana da jahad amma haka ya haƙura😔 

Tun bayan da suka kammala shan corn flakes junaid ya wuce bedroom dinsa saboda dama agajiye yake, sehrish kuwa sai da ta tsaya a kitchen din har azmee tazo suka fara aiki, cikin kankanin lokaci suka kammala dinner,

sannan  ta wuce bedroom ɗinta ta kwanta tasha bacci har wurin magrib sannan ta tashi donyin sallah, bayan ta kammala jiki na rawa ta bude wardrobe dinta, tsayawa tayi saboda ruwan ido ta ma rasa me zata sanya acikin kayan, hannu tasanya ta janyo wata haɗaɗɗiyar Gown black colour mai kyalkyali masu daukar ido, jinjina kai tayi tare da cewa “Wannan zan sanya,” tayi maganar tare da hanging dinta asaman murfin wardrobe din, shaf shaf ta tube riga da wandon dake jikinta ta tura su, cikin laundry basket dinta, sannan ta dauki rigar ta shiga kiciniyar zira ta ajikinta, bayan ta kammala ta koma gaban mirror tana kallon kanta ta cikinsa, fuskarta dauke da murmushi tana tuna yaushe rabon da taji ta acikin kayan mata, kayan ma irin wannan sabbi masu kyau, rigar tabi shape din jikinta,hannunta mai dan tsayi ne wanda ya tsaya dai-dai elbow dinta,Jujjuyawa tayi tana ƙarewa kanta kallo, kafin tasa hannu cikin jerin Perfumes dinta ta dauko kwalbar turaren TOUCH ta feffesa ma jikinta har wani lumshe ido take yi saboda yarda fragrance dinsa ke dakar hancinta, bayan ta mayar da turaren ta koma cikin wardrobe din ta ɗauko mayafi white colour tayi rolling dinsa irin lagen da larabawa suke yi masha Allah 😍

Kama hanyar fita tayi tana bude kopan azmee na sanyo kai dama dakin nata ta nufo itama, ganin yarda azmee tasaki baki yasa sehrish sa hannu ta rufe fuska don tasan kallon na menene,

  “Nama rasa mai zance irin wannan kyau haka? Yarinya kamar ƴar larabawa ashe dama haka kike da Kyau ga ki dirarra,’? 

  Cikin jin kunya sehrish tace “Aunty azmee ko fa makeup banyi ba, i know u are just teasing me,

  Azmee tace “Reesh ae ko ba kiyi kwalliya ba kyau kike, ae ni ban ma so kiyi kwalliyar yanzu, don banson ki rikita samarin gidan nan, mu rasa wa zamu ba acikin su,’ 

  “BABBAN YAYA’ ta faɗi acikin zuciyarta a fili kuma tace “Mai rabo,” dariya azmee tayi tana cewa “Toh Allah yaba mai rabo sa’a time kawai zamu jira muga wanene wannan in da rai da lafiya,’ 

  Murmushi kawai sehrish ke saki, suna cikin wannan tsayuwar motocin su suka shigo atare mai ɗauke da jiniya, azmee tace “Alhamdulillah shikenan ma, tun da kin shirya in suka shigo ki tabbatar kin kaima Babban yayansu dinner dinsa tare da Omar, yanzu ma na kammala jera na dining din basu kai ga saukowa sunci ba, dama Twins ne da suka dawo bada jimawa ba sai Junaid da HAROON, just zanji da sauran kawai,’ 

  ta ƙare bayanin tare da kama hanyar fita daga ɗakin tana nanata mata,

  Sehrish ta amsa mata da “toh insha Allah,” 

    cikin sauri ta koma wurin window dinta ta janye labulan ta zuge glass din tana hangensu,

   kowannansu agajiye ya fito daga cikin Motar, Abbansu ne tare da marshal Omar sai SGR, Abbansu na sanye cikin kaki, haka SGR army trouser ne ajikinsa sai shirt light green mai gajeran hannu sun ɗame jikinsa, Omar kuma Shigar dazu ce ajikinsa wadda yayi shirin Zuwa Kaduna dazu,

 tunda Armstrong ya buɗe masa mota ya fito yake faman lumshe ido hannunsa ɗaya na acikin sumar kanshi yana yamutsa ta, kallon shi Abban su yayi tare da cewa “Ko dae saina taimaka na goyaka ne? Naga alamar baka iya tafiya,” ɗago da eye balls dinsa yayi ya kalli Abban nasu sannan anatse yace “Dad kenan, ni da kai wa zai goya wani? kai ma ka sani,” 

   Yayi maganr tare da soma tafiya abban nasu kam dariya yayi yana cewa “Oh kana jin kanka Tamkar giwa ko? Ae ba abun mamaki bane kaga na sa6eka abayana, in banda ma yanzu daka zama jibgege haka ga tsayi nan nan nake ɗaukarka kana yaro har goya ka nake yi,” duk Omar na jinsu yana murmushi kawai saboda atare suka jera suka nufi cikin gidan,

  ɗan gyaran murya yayi tare da cewa “Abba yanzu ae sai dai ka goya grandchild dinka masu zuwa,” Omar ya faɗi,

  Abban su yace “hmmmm taya hakan zata faru bayan ƴan bukulu sun hana ruwa gudu, burina kenan kullum kamar yadda na haifa nima nawa su haifa amma abun takaici duka ya’yan nawa babu wanda ya ajiye ko budurwa bayan ni tun ina 20 years aka sanƙamamun aure muka sha soyayya gaba ɗaya,’ 

  Omar yace “Kada ka damu Abba, Insha Allah burin ka zai cika, in har hakan zaisa ka farin ciki, kawai acigaba da yi mana addu’a,’ 

   Jinjina kai abbansu yayi yana ɗan kallon SGR dake gefensa shiru tamkar baya jin me suke cewa,

   Ruko hannunsa yayi cikin nasa sannan yace “kai fa Son, Naji baka ce komai ba ? Ko baka son farin ciki na ne?

  yatsina fuska yayi tare da cewa “In dai yaron da zaka goya ne zan kawo maka shi,’

  “Uwar fa”? Abban ya tambaya adai dai lokacin da suke shiga babban falon SGR yace “Babu,” dariya omar kawai yake yi.abbansu kuwa baki sake yace “Shege zaka kawo min,’?

  “Ko baka so ne”? Sgr ya tambaya shima da zolaya,

  Abbansu yace “Ae da babu gwara ba daɗi, akawomin inaso,” 

   Omar yace “So funny wlh, abba son jikokin harya kai haka, to. Insha Allah ba shege acikinsu, Original zaka samu daga gurin kowan nan mun, ‘ cike da nishaɗi suke fira kamar bazasu iya rabu ba, wuce wa Abbansu yayi part dinsa, shima SGR tare da OMAR suka wuce Uptairs nasu parts din,

💪

   Tun da Omar ya shiga bedroom dinsa ya rage kayan jikinsa toilet yashiga ya yi wanka, yafito ya zura kayan baccinsa, har cikin ransa yaso ya kira Aunty babba don abasu Hosana yaji Muryarsu amma ransa yana bashi cewa yanzu sun isa suyi bacci, wannan dalilin ya hana shi calling ɗinsu,

Fitowa parlor dinsa yayi yasamu wuri saman sofa yazauna hannunsa ruƙe da wayarsa, sai lokacin yake dana sanin rashin daukar su hosana da jahad hoto ya ajiye acikin wayar shi koya samu na rage kewarsu, yana cikin wannan tunanin wayarsa ta soma ruri karatun kur’ani Ne ringin tone dinsa duba sunan daya bayyana a screen dinsa yayi nan take sunan*ABUSUFYAN*ya bayyana muraran,

  Cikin hanzari ya ɗaga ya kara a kunnansa “Assalamu Alaikum Uncle Sufyan yau an tuna dani ne”?

  On ther other hand ABUSUFYAN yace “Ko da yaushe cikin tunawa nake yi dakai Omar, nayi trying number dinka dazu baya shiga, kuma na jaraba ta RAFAYET tana ringing amma bai ɗaga ba,’ 

  Omar yace ” Kash ! rashin sani ɗazu ne na kashe wayar muna aiki ne shiyasa,” 

   Abusufyan yace “Dama inaso na maka magana ne About wannan yaran da goggon katsina ta ƙaƙabamun a matsayin ya’ya na”?

  Murmushi Omar yasaki kamar yana agabansa yace “Ae ko ɗazu da safe ta kira ni awaya, kusan kullum ne sai ta mun Complain akan ƴa’ƴan abusufyan ɗinta,’ 

   Abusufyan yace”Allah sarki, Nima tana kira na tana mun complain akan nasa ka mayar mata da ya’yana wuri ta, ynx ina yaran suke ne?  Ya tambaya yana jiran amsa 

Omar yace “A gidan general ishaq suke da zama, can na kaisu,” 

   “Ina iyayen su suke ne”? Ko yan uwan matar ishaq din ne? Ya tambaya

  Omar yace “A’a Uncle yaran fa basu da kowa kamar yadda suka sanar mun, na haɗu dasu ne a asibiti cikin mawuyacin hali tagwaye ne baza su wuce 17years ba Suna buƙatar taimako,

   Ajiyar zuciya abusufyan yasaki kafin yace “Meyasa ba zaka dawo dasu nan ba cikin abuja kusa da kai ba”?

  “Uncle kaima ka sani, zaman su anan bazaiyi yu ba, maza ne mu duka duk ba wannan ba AMMI bazata ta6a lamuntar wani bare ya zauna acikin jinin ta ba,especially su da suka kasance basu da asali,’ bayani yake masa tamkar yana agabansa

  ɗan gyaran murya abusufyan yayi kafin yace “Listenin to me OMAR! kana da kyakkyawar niyya akansu, inaso ka kaddara aranka cewa waɗannan yaran jinin ka ne, kasanya wa ranka cewa Ƴa’Ƴa na ne, ya’yan ƙanin mahaifin kane *ABUSUFYAN* ina so ka basu kulawa Omar ! Dan Allah kada ka bari su wulaƙanta kayi mun wannan alƙawarin…….

  Jikin Omar ne yayi mugun sanyi jin abun da Uncle Abusufyan ke faɗamasa, yanayin sautinsa da yadda yake yin kalamansa haƙiƙa ya ta6a  Zuciyar Omar sosai, tunani omar yashiga yi aransa har sai da Abusufyan yace”Naji kayi shiru OMAR,” 

  Cikin sauri yace “Insha Allah Uncle i wll take care of them more than u think, nima inajin su araina sosai Uncle, ina ƙaunar yaran har cikin raina,

  yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar Abusufyan alamar hankalinsa ya kwanta kuma yasamu natsuwa da bayanin Omar,

  ABUSUFYAN yaci gaba da cewa “OMAR!  INA SO KA DAWO DA YARAN NAN GIDA NA DAKE ANAN SU CI GABA DA RAYUWA, KA SANYA MUSU SECURITY TARE DA MAI AIKIN DA ZATA KULA DASU, INA SO SU RAYU ACIKIN GIDA NA, KAYI MUN WANNAN ALƘAWARIN!!!”

   runtse ido Omar ya ɗanyi yana jinjina kalaman Uncle din nasa daga bisa ni yace “Insha Allah Uncle zanyi komai kake so, zan dawo dasu nan acikin gidan ka kamar yarda kake so,” 

   Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama, ya ajiye wayar yana mai tunani iri-iri aransa, yana ji aransa in ya ɗauke su hosana daga gidan aunty babba tamkar baiyi mata adalci ba don ya Lura tana son yaran kuma sun saba dasu anya kuwa zai iya cika alƙawarin Uncle Abusufyan Na dawo dasu hosana cikin Abuja da zama!!? 😟

   Yana cikin wannan tunanin Sehrish ta shigo da sallama, batare da ya ɗago ya kalle ta ba ya amsa mata sallamar, sam ransa ajagule yake uncle dinsa ya ɗan ruɗa masa brain ɗinsa

  Tray na a hannunta ƙarasawa tayi tare da gaishe shi “ina yini ya Omar,”  ƙiris ya rage omar ya ɗago ya kalle ta saboda Voice dinta tayi mashi kama da ta JAHAD, amma yabar Abun a matsayin muryar mai aikinsu ne ya koma masa ta Jahad Saboda kewarsu da yayi sosai

Amsa mata yayi da cewa “Lafiya lou” 

   Ajiye masa tray din tayi mai dauke da food stuffs dinsa asaman table Din dake a front dinsa sannan ta juya takama hanyar fita tana jiyo shi yana furta “ngde,” 

   Sauƙin kan MARSHAL OMAR yana matuƙar burgeta, babu ruwan shi ba kamar SGR ba, yana da IZZA ta wani bangaren kamar abinci muddin takai masa sai tayi saving ɗinshi, amma Omar sam baya buƙatar wannan kawai daga an kaimasa shi yake zuba abunshi yaci,

  Saukowa tayi down a lokacin har su Twins da kanal yusuf Sun hallara suna cin dinner dinsu, tayi mamakin ganin babu Abbansu da junaid may be yana a part dinsa azmee takai masu acan

  Gaishe su tayi gaba ɗaya suka ɗan dago suna kallonta, Kanal yusif ya amsa mata da sakin fuska amma Ayaan da jahan kuwa sai dai suka bita da ido,😡

  Har bugun zuciya take ji in ta gansu cikin hanzari ta shige kitchen ta shirya ma SGR dinner ɗinsa ta fito ɗauke da tray ahannu ta nufi hanyar upstairs dinsa, 

   Da sallama ta shiga palor dinsa baya aciki, ƙarasawa tayi ta ajiye masa kayan abincin saman table dinsa, sannan ta ɗan dakata ko zai fito amma shiru babu alama, 

. yanke shawarar zuwa bedroom dinsa tayi a bakin ƙopar shiga ta tsaya sannan tayi sallama, daga ciki taji ya amsa mata ƙasa ƙasa kafin ya bata permission ɗin shiga ciki,

   A hankali ta zura ƙafa ta shiga ciki jikinta na ɗan kerma Hango shi tayi daga shi sai bathrobe ajikinsa kwance abaje saman gadonsa, alamu sun nuna cewa baiji ma da fitowa daga wanka ba, ya kwanta gajiya ce tayi masa yawa, idonsa na’a lumshe yace “Wanene ne,”

  sehrish tace “mai aiki ce dama dinner ne na kawo maka yana a palor naga baka fito ba,

   Jim yaɗanyi kafin yace “Tea kawai nake buƙata,akawo mun nan,’

   Amsa mashi tayi da toh, sannan ta fuce ta koma palor dinsa ta ɗauko kayan tea din dake acikin tray din da ta ajiye anan  sannan ta shigar masa dashi,

      har gab da gadonsa ta ajiye masa saman madai-dai cin table din dake a wurin ta matsa masa dashi jikin gadonsa,

      bin shi tayi da kallo saboda bai buɗe idonshi ba kuma baiyi yunƙurin tashi ba, yayi wani fresh dashi,

  Ganin alamun fa zai iya zarcewa da bacci yasa tace “Na kawo maka Tea ɗin,” 

  “I knew,” ya bata amsa, jinjina kai tayi ashe yasan ta kawo ɗin, wahalar tashin ce kawai yake ji,  kusan 15 mins sannan ya ƴunkura ya miƙe tare da sauko da ƙafafunsa ƙasa, rigar iya guiwar ƙafarsa ta tsaya, saukin yasa shorts daga ciki amma chest ɗin shi a buɗe yake fari kal,

    Zuba mishi ido tayi tana kallon ikon Allah wani irin bacci ne ke fusgar shi, ga uwar yunwa yana ji, ji take tamkar ta bashi tea ɗin abaki yasha, cikin sauri ta haɗa masa tea ɗin a cup ta ɗan tura masa agabansa tace “gashi nan,’ 

   buɗe blue eyes ɗinsa yayi a hankali sannan yakai hannu daker ya ɗauki cup ɗin yakai bakinsa yana ɗan kurba da zafinsa, ya sha ba laifi kusan sau biyu tana ƙara masa yana shanye wa,

  Bayan ya kammala tace “kayan dinner ɗin fa na mayar dasu”? Ta tambaya cike da jin tsoran amsar da zai bata,

    “In akwai fruits ki haɗo mun,” ya faɗi tare da mayar da jikinsa ya kwantar akan pillow,

  Tattara kayan tea ɗin tayi sannan ta fuce dasu ta ajiye su a tray din dake ɗauke da warmers na abincin sannan ta ɗauke shi ta fita dashi kitchen ta shiga ta ajiye su, sannan ta ɗebo mashi fresh fruits acikin fridge, 

    A plate ta zuba mashi su sai da tafara yayyanka mashi su sannan, tana ƙoƙarin fita suka ci karo da Haroon tsaye abakin ƙopar kamar aljani, 

  Da ƙarfi ta furta “A’uzu billahi minashshaiɗanin rajim,’ 

   Haroon ya fashe da dariya tare da cewa “Ni ne shaiɗan ɗin, ko kin ga ƙaho akaina ne? 

  “Eh,” ta bashi amsa,

 Yatsina fuska yayi yana bin jikinta da kallon frm up to down kafin yace “Haɗaɗɗiyar Sura,”

  tace “Tubarkallah masha Allah,”

  Murmushi yaɗanyi kafin ya kuma cewa “ki dai bi ahankali naga kamar zakiyi rawar kai Kada kici ka zaƙewa mana domin kuwa har yanzu fa baki da wani matsayi acikin gidan nan, duk inda za’aje adawo bakya wuce ƴar aiki, sannan na lura kina shisshige ma wancan ifritun ko? to inaso ki sani wancan dashi da dutse duk ɗaya suke indai agame da feelings ne, mace bata gabansa koda zai kula matan ma bana tunanin irin ki, ae ma zaren ba kalar yadin bane iska ce kawai zata wahalar da mai kayan kara………

   tun da yasoma magana idon sehrish suka soma ciccikowa da kwalla amma bata bari hawayen sun zuba ba, ganin zai bata mata lokaci yasa ta bi ta gefensa ta fuce da sauri, tana jiyo dariyarsa sam tarasa gane ma haroon, batasan mai ta tsone masa ba,

    time ɗin da tashiga bedroom ɗin SGR samun shi tayi yana ta faman sharar baccinsa alamu sun nuna cewa ma tunda tasa ƙafa ta fuce ya fara baccin, tsayawa tayi akansa tana kallonshi hannunta na riƙe da fruits ɗinsa,

    Yayin da idonta Suke cike da hawaye saboda kalaman haroon ita kanta tasani tabbas SGR ba tsaran yinta bane kwata-kwata bama haɗi, jinjina kanta tayi aranta tace “nasani kafi ƙarfina nesa ba kusa ba, kuma nasan cewa kafin ni akwai wanda suka ruga ni faɗawa wannan tarkon bila adadin, Amma inaji araina babu wadda zata soka dan Allah kamar yadda nake sonka, tun bansan ya kamannin fukarka suke Ba, da sunanka kawai nakamu da tsananin ƙaunarka kuma zan cigaba da addu’a akan hakan koda bazan ci nasara ba aƙarshe…Ana ahabbuk kasiran BABBAN YAYA………❤💘

  Wani irin juyi SGR yayi har sai da Sehrish ta ɗan tsorata gudun karya farka ya ganta, gyara kwanciyar shi yayi, yadda yake sakin numfashi anatse yana bacci ba ƙaramin tafiya yayi da ita ba,

   Ajiye fruits ɗin tayi saman table sannan ta matsa a hankali cike da fargaba ta janyo lallausan blanket ɗinsa jikinta na ɗan kerma ta samu ta hayo dashi jikinsa ta lullu6a masa har zuwa neck ɗinsa,

  Murmushi ta ɗan saki ganin ta kammala batare da ya farka ba, juyawa tayi ta tattaka izuwa inda makunnin hasken ɗakin yake ta kashe mashi shi, nan take ɗakin ya soma kyalli yana bada wani irin haske har sai da ta ɗan razana, ashe furnitures ɗin dakine masu wannan sparkling light ɗin launi daban daban suke badawa, aduk time ɗin da aka kashe hasken ɗakin Yayi dark gaba ɗaya su kuma sai su soma bada nasu hasken mai launuka, fuska ɗauke da murmushi sehrish ke kallon wannan ikon Allan Bin su take yi da kallo tun daga Bed ɗinsa da bedside table ɗinsa, drawer ɗin da ke ɗauke da mirrow jerin wurin Closet ɗinsa gaba ɗaya sun ɗau hasken nan, sai taga ya ƙara yi mata kyau sosai,

   Lalla6awa tayi ta koma inda yake kwance tana kallon fukarshi yadda eye lashes dinsa suka fito radau zira zira dogaye kasancewar idon na’a rufe, sun kwanta luf,

   Addu’ar bacci tashiga yi mashi saboda tasan cewa bai samu damar yi ba ayarda ya kwanta ɗin nan agajiye ta jima sannan ta ɗan tattofa masa ajikin bargonsa, kamar karta bar ɗakin haka take ji

 (Nace ba mai zai hana kawai ki kwana anan Ehen 😂) 

   hannu tasa ta ɗauki Kayan marmarin dake acikin plate ɗin sannan ta fuce dashi bakowa a babban falon Dama tun fitowar farko da tayi duk sun kammala dinner ɗinsu sun shige cike aranta tace “Allah sarki su fawan hada rashin su yasa yanzu basu cika haɗuwa atare suna cin abinci ba ko zama a palor suna fira, ko yaushe zasu dawo? Duk da ina tsoran abunda zasu ce in suka ganni a 

Matsayin mace, Especially fawan nasan halinsa sosai baijin magana shine ya ta6a bani horo harna galabaita,” ta ƙarasa zancen zucin nata , bedroom ɗinta ta wuce da fruits ɗin saboda dama itama bata ci komai ba, asaman gadonta ta zauna tsakiyar gadon ta lankwashe ƙafa tana shan fruits ɗin tass ta shanye su sannan ta ajiye plate ɗin asaman side drawer ɗinta, dama empty yake tunda ta rotsa ma haroon fitilar saman shi akai, bata sake ajiye komai asaman wurin ba,

    sauko wa tayi tashiga toilet saboda bata yi sallar isha’e ba, alwala tayi sannan ta dauko hijab ta zura bayan ta shimfiɗa carpet ta gabatar da salla, 

    Tana gama wa ta naɗe carpet ɗin ko addu’a bata tsaya yi ba, ta tura su cikin wardrobe sannan ta haye saman gadonta taja bargo ta kwanta daker tayi addu’a kafin bacci 6arawo yayi awon gaba da ita……………..(Shin ko kun lura cewa Sehrish ta manta dasu hosana da jahad bakamar da ba? hmmmmm rayuwa kenan baka ta6a sanin asalin ya mutun yake sai yasamu wurin zama koya samu abun duniya nan zaka ga zahirinsa😥)

_____________________🌹🌹🌹____________________

In midnight Hosana tafarka da matsanancin Ciwo, wani sabon raɗaɗin ciwon ne ya taso mata agigice tafarka tana kuka tana zabga Uban ihu tana faɗin “Innalallahi wa’inna ilaihiraji’un , La’ila ha illallah muharammadur rasulillah Wayyo Allah na, mutuwa xanyi, gaba ɗayansu suka farka hankali atashe tun daga jahad har hafsat dake kwance saman Sofa sai da tafarka a tsorace,

  taruwa su kayi akanta jahad na faman yi mata addu’a tana tofa mata cikin kuka take faɗin “Hosana ki daina magana ciwon bakin ki zai ƙara raunata, dan Allah kiyi haƙuri innalallahi bansan ya zanyi ba,’tafaɗi tare da fashewa da wani sabon kukan itama, dama sai da ranta yabata cewa raɗaɗin ciwon hosana zai iya dawo wa sai gashi ya dawo, fuskar tayi suntum la66an sun kumburo hancinta ma yayi girma, idanunta ma sun kumbura duk kwantsa ko buɗe su bata iyayi saboda sun datse sosai, ita kaɗae tasan azabar da take sha ga haƙoranta suma nasu Zogin daban, ko’ina ciwo hakanne yasa ta haukace taita faman zabga salati tana kiran Sunan Allah da manzon sa 😭

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button