Karfe A Wuta Chapter 5 By Ayshercool
Wurin shiru, ba ka jin motsin komai, hantsi yayi, yana zaune a kan wani dutse, yana jin yadda ɗumin ranar ke ratsa shi, dan ba ta riga ta yi zafi ba, hannunsa ɗaya ɗauke da taba sigari, yana ta zuƙa yana busawa, idonsa yayi jawur.”Viper” matashin ya kira sunansa, yana ta sauke haki.”Ina jinka” yayi maganar ba tare da waiwayawa, ya kalli matashin ba.”An kama ɗan mama da kayanmu fa jiya da daddare, a chamber yamma da gari, yana tsaka da raba kayan ga mutane, kuma wadda aka kama da yawa”Ya saka yatsansa ya ɗan daki jikin sigarin, tokar jiki ta zube, ya ja numfashi ya ce “Wace hukumar ce?””Masu ƙwaya ne”Ya miƙe tsaye ya ce “Shikenan, kar ka damu, ku bar shi a hannunsu”Ya waro ido ya ce “A bar shi, Ka manta a halin da ake ciki? Idan wani abu ya faru fa?”Cikin takunsa na ƙaƙƙarfan namiji, ya ƙarasa gaban matashin, ya riƙe kwalarsa a hankali sannan ya ce “Ba na butulci walid, ɗan mama ni yake yi wa aiki, dole na fito da shi. Ni ba zan kamu ba, da zan kamu da basu bari na fito ba. Kuma ko a yanzu suna sane suka bar guzuma, suke harbin karsana. Ni na shirya a kama shi, sannan ina son ku je dabar Madaki, ko wurin da yaransa suke, ku tayar da hayaniya, ku zubar da jini, kar ku raga musu ko kaɗan, ko da kuwa hakan yana nufin jami’an tsaro su kama ku”Yayi shiru yana kallon viper.Ya shafi sumar walid, da tayi cibiri-cibiri ya ce “Ya ka ke kallona kamar kana tantama a kaina?”Ya risuna ya ce “Tuba nake mai gida, duk abun da ka ce dole ayi shi, umarninka muke yi wa biyayya””Good. Idan aka kama ku, ko da mutum ɗaya ne daga cikinku, ku ambaci sunana, ku ce ni ku ke yi wa aiki, ni ne na saka ku. Ina sake jaddada maka, kar ku ragawa kowa a cikin su. Amma ku kiyaye ƙa’idar aikina. Babu kisan kai, babu taɓa wanda babu ruwansa mata ko kuma ƙanan yara”Walid ya ce “An gama maigida”” Ɓace ” ya furta a hankali.Yau Nabila ko karyawa ba ta tsaya yi ba, haka zalika ko sumayya ba ta jira ba, ta tafi aiki.Daga office ɗin ta, tana hangen harabar chamber, ta ga isowar motar Barrister Bashir. Bayan mintuna talatin ta bishi office ɗin sa, suka gaisa ya dube ta ya ce “Ƴar ƙwalisa ya jiki?”Ta ce “Jiki kuma, ba ni da lafiya ne?”Ya ce “Ranar da muka dawo daga court, kina ta tari har ki ka tafi gida, ko kin manta?”Ta ce “A’a na tuna, na ji sauƙi ai””Wai meyafaru ne a kotun, bayan na je na ga abokina, da na dawo na tarar da ke gaba ɗaya ranki a ɓace, na tambayeki kin ce ba komai”Nabila ta ce “Da ma fa dan bana jin daɗi ne, ai ni ba zan manta da ranar ba, na ga masoyiyata kuma mudubina”Barrister ya ce “Wa kenan?””Barrister Naja’atu, ina son matar nan sosai “Yayi murmushi ya ce “Bunkure ki ke nufi?, mace mai hatsari kenan”Ta waro ido ta ce “Hatsari kamar yaya?””No, kin san ba ta da wasa da aiki, duk shari’ar da ta saka gaba, sai ta ga bayanta, ke kuma gashi ba haka ki ke ba, ba kya mayar da hankali a kan aikin”.”Ai in gaya maka ganinta kawai da na yi, na ji wata irin ƙwarin gwiwa, na ji sonake na nutsu na mayar da hankali sosai a kan aikina. Sonake na bi footsteps ɗin ta, nima na yi nasara kamar ita. Amma me ka sani a kanta da zaka iya gaya mini?”Yayi murmushi ya ce “Nothing much, ki tambayi barrister Habib, ya santa sosai ” sai da ta ji wani dummm! Yadda suke faɗa da barrister Habib, amma hausawa su ka ce ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba, dan haka ta ce “To shikenan, na gode sosai ayi aiki lafiya”. Ta juya ta fita tana nanata “Dangerous woman, zamu gani ai”.Ba ta zame ko ina ba, sai ofishin barrister Habib, ta tarar da shi da wasu client suna tattaunawa, ya ɗago ya kalleta ya ce “Meye?” A ɗan hasale dan a ƙule yake da ita.Ba tare da ta yi fushi ba, ta yi masa murmushi sannan ta ce “Wurinka na zo, amma bari na jira ka gama”.”Idan na gama ina da abun yi” ya faɗa a taƙaice.”Dan Allah yaya habib ko mintuna goma ne””Na gaya miki ina da abun yi, fita ki bani wuri” tsayawa ta yi tana kallonsa, tare da tura baki, babu alamar ma za ta fita ɗin.”Ba magana nake yi ba?”A shagwaɓe ta ce “Dan Allah”Ɗaya daga client ɗin ya ce “Barrister a taimaka mana, kar ta yi kuka”Ya ce “Ta daɗe ba ta yi ba, ba zaki fita ba?”Nabila ta ce “Ya ka ke korata kamar wata kare ne? Na san ina yin laifi, ka yi haƙuri na shiryu ai”Tsaki yayi, ya cigaba da rubuce-rubuce.Ta tura baki ta fice, a zuciyarta ta ce “Ai ko da me ka ke yawo, sai na samu abun da nake son ji a wurinka”Ta je ta samu MD, suka gaisa, sannan ta ce “MD, ka ga Barrister Habib ko, na je na bashi haƙuri, amma ya kore ni a gaban mutane”. Ya yi murmushi ya gyara gilashin fuskarsa ya ce “Anya ba wani laifin ki ka yi masa ba?””Ba laifi na yi masa ba, haƙuri na je ba shi fa, amma ya kore ni a gaban mutane”MD yayi murmushi ya ce “Ai ke ɗin ce ba kya ji, ya so ya koya miki aiki yadda yakamata, mussman yadda ki ke da faran-faran da mutane, amma ki ka ƙi ba kya so, idan ya saka ki aiki ki ƙi yi, dole ku din ga faɗa ai”Nabila ta ce “Na daina fa, so nake na zama ƙwararriya a kan aikina, ko dan farincikin Abbana, ku yi haƙuri”Ya jinjina kai ya ce “Shikenan, Allah ya sa, ki je ki bashi haƙuri”Ya ce “Bayan ya kore ni, yauwwa sir dan Allah ka san barrister Naja’atu Bunkure?”Ya jinjina kai ya ce “Yes, she’s famous a tsakanin lauyoyi, har ma da jama’ar gari ma, ai sananniya ce sosai”Nabila ta yi murmushi ta ce “Wow ina yin matar nan sosai da sosai, yadda take gudanar da aikinta, ya ƙara jan hankalina a kan aiki, ai mun ganta kotu a lokacin da mu ka je kotu last, ni da barrister Bashir, ƴar gayu da ita””Nabila, ke dai ki na son harkar gayu, amma ba gayun ba, ki mayar da hankali sosai a kan aiki, ki yi ƙoƙari ki kamo ta, ko ma ki fi ta”.”In sha Allah, na yi maka wannan alƙawarin but i need your support”Ya murmusa ya ce “Kin samu, ɗari bisa ɗari, ƴar gidan major””Yauwwa to ka bawa barrister Habib haƙuri, zan koma team ɗin sa dan Allah kar ya sake korata, mussaman a gaban mutane””To za a bashi in sha Allah”Ta miƙe tsaye tare da faɗin “Godiya nake” ta fice ta bar office ɗin cikin nishaɗi.”Bunkure na ki zai zo mini da sauƙi, saura kuma Aminu Viper”***Major ya ɗan tsurawa Uwargidan sa mama da ta tattare kwanukan da ya kammala cin abinci.Ta ɗago su ka haɗa ido, ta ce “Ya dai?””Nasir””Me yayi?””Ki ja masa kunne, hawainiyarsa ta kiyayi ramata, na daɗe da gane in da ya dosa, amma tun da kin daƙile abun, to ya ƙara nesanta kansa da ƴa ta, kar ya kuskura in ji ko in ga wani abu da zai sosa zuciyata, kuma kar ya kuskura ya saka ta fara son shi, tun da ba ki amince ba, balle a jefa ta cikin yanayi mara daɗi”.Cikin rashin fahimta ta ce “Amma major, wani abun ya yi ne?””Bai yi komai ba,gugar zana dai nake yi, idan ma yana shirin yin, to ya shiga hankalinsa” cikin mamaki take bin sa da kallo, tabbas idan aka ji major yana magana da kurman baƙi, akwai abun da ya gani, kuma ko me za ayi, ba zai fito yayi bayanin abun da yake nufi ɗin ba.****Kamar ɓarawo haka yake zagaye tilon matsakaicin gidan, wanda can nesa da gidan, kamfanunnunka ne, sai gonaki.Cikin ƙasaita yake tafiyar, yana yi yana duba ƙaramar wayarsa mai madannai.Kamar korarre, haka wani matashi ya ƙaraso in da yake tsaye.Ya ɗaga kai ya kalle shi ya ce “Menene labari, yaya aka yi ka fito?” Cak matashin ya tsaya, ya ce “Wai dama ba kai ne ka fito da ni ba?””Me zan tambaya idan na san komai?” Yayi maganar a ɗan hasale.”Wallahi master….Cikin wata irin razananiyar tsawa ya ce “Kar ka sake kirana da wannan sunan”Cikin tsuma ya ce “Tuba nake oga, suɓutar baki ce, ban san waye ya fito da ni ba, kawai cewa aka yi na tafi”Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Kuma ka tabattar da ka gaya musu sunana, cewar ni ne me kayan?””Wallahi na faɗa musu”Ya jinjina kai ya ce “Shikenan”Ya ɗaga rigarsa ya zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa, ya danƙa masa ya ce “Maza ka fasa cikin gari, unguwarmu, su walid sun tafi yaran Madaki zaku farwa babu sani babu sabo, idan an yi ram da wani daga cikin ku, ku ambaci sunana, ku ce ni ne jagoran aika-aikar, amma ku kiyaye ƙa’idar aikina”Ɗan mama ya risuna ya ce “Umarninka ne abun biyayya a gare ni, an gama za ayi yadda ka ce” ya soke wuƙar ya juya, ya tafi da sauri yana haɗa hanya..Cikin ƙaramin gidan ya shiga, ya nufi ɗakin kwanansa, ya kunna fitilar wayarsa, ya kunna ƙwan solar, haske ya gauraye ɗakin.Ya saka mukulli ya rufe ɗakin, sannan ya zauna yayi shiru tsawon mintuna, daga bisani kuma ya ɗaukko wiwi ya naɗa ta, ya kunna ya fara zuƙa.Madadin ya ji ƙunci, da zafin da zuciyarsa ke yi masa, yana raguwa, sai ma wani irin baƙin ciki da matsananciyar damuwa da suka kawo masa ziyara.Wani abu mai tsananin ɗaci yake ƙoƙarin haɗiyewa, amma abu ya gagara.Ya ɗaga wiwin yana kallonta cike da baƙin ciki da takaici, yayi watsi da ita yana sauke numfashi.Kamar mahaukaci ya zabura ya buɗe wata akwati, ya ɗaukko kwalaben allura, ya farfasa ya haɗa, ya yi wa kansa, ya nemi wuri ya kwanta.Bai fi mintuna goma ba, kansa ya fara barazanar tsagewa, ya fara kakari yana rirriƙe kansa.Duk yadda ya kai ga ƙara yawan doses ɗin abun da yake sha, ba sa ɗaukarsa, su mantar da shi damuwarsa, sai dai su wahalar da shi, shi a yanzu babban fatansa ya samu abun da zai yi amfani da shi, da zai goge masa komai na ƙwaƙwalwarsa ya yi bacci mai nisan gaske. ***Nabila ce tsaye a kitchen tana ta ciye-ciye, tana yi wa magajiya surutu.Baba magajiya ta ce “Dan Allah Arfa ki yi mini shiru na ji radiyona, wai ni ya aka yi, ki ka tashi da sassafen nan ma”Nabila ta yi murmushi ta ce “Baba magajiya kin gane mai muryar nan kuwa?”Baba magajiya ta yi dariya ta ce “Sumayya ce mana””Ashe za ki gane ta””Ka ji ƴa, yau na sanku da ke da ita, da zan kasa gane muryarta””Ai in gaya miki baba magajiya, wata mata ce ta takura wa aminiyata, a wurin aiki, da iskanci kala-kala ga sumayya da son aiki, amma matar nan tayi ta taɗiyeta, ni kuwa na ce ta daina saurara mata wallahi,shi ne ma fa ake ba ta karanta rahotanni wasu lokutan, da experience ɗin ta da komai, wata sokuwa ta cuceta, ta hana ta cigaba”Baba magajiya ta ce “Ohh Arfa, ai mahaƙurci mawadaci, yawan faɗa ba shi da amfani”Nabila ta ce “A’a fa baba magajiya, ni ma ba faɗa ne da ni ba, wulaƙanci ne ba na so, duk wanda ya wulaƙanta ni, sai mun yi fito na fito da shi”.Baba magajiya ta ce “A dai din ga haƙuri, tun da…. ba ta gama magana ba, Nabila ta yi wani irin tsalle ta ɗauki radiyon, tayi waje da gudu.Sashin mama ta faɗa, dan ta san tun da Nasir yana gari, lallai zai shiga sashen ta ya karya kafin ya fita.Aikuwa a sashen ta tarar da shi, yana karyawa, su na hira da mama, da kuma sauda.Ƙaro volume ɗin radiyon tayi, ta na yi masa nuni da ya saurara.Rahoto ne a kan rikicin faɗan daba, da ya gudana a cikin ɗaya daga manyan unguwannin kano, wanda tun goma na dare ake rikicin, har ƙarfe sha biyu ana rigimar, ƴan sandan sun yi nasarar cafke wasu daga cikin matasan, in da ɗaya daga wanda aka kama, ya ce Aminu Viper ne ya aka su Sai da suka kammala ji, Nabila cikin rawar jiki ta ce “Yaya Nasir, ba wannan ne wanda ka ke nema ba?”Ya jinjina mata kai ya ce “Shi ne””Ka yi sauri ka tashi, ka je division ɗin da aka tsare ƴan daban, a baka su ka zurafafa bincike, gidan radiyon su sumayya ne, sai na biya can na sake samo rahoto”.”Ke!” Mama ta daka mata tsawa, har sai da ta ɗan razana.”Tashi ki bani wuri, yaya ina magana da shi, ba sallama ba gaisuwa babu neman izini, kawai ki zauna ki na surutun banza” Nabila ta yi shiru ba ta ce komai ba.Sauda ta ce “Dama mama yaushe za ta gaishe ki, tana abu kamar mahaukaciya”Ta kalle su, ta kalli Nasir da yake wurin, ta haɗiye wani abu ta tashi, za ta fita.Nasir ya riƙo hannun ta ya tashi ya tsaya, ya ce “Sorry barrister, na gode sosai da wannan gudunmawa, zan je division ɗin, ki samo mini bayani a wurin sumayyan”.Ya kalli mama ya ce “Haba mama, kin san tana gaishe ki, tsananin zumuɗin ta kawo mini labari ne fa ya sa ta manta, thank you Arfa ki shirya ki tafi aiki kar ki makara”A ƙule mama ta ce “Wai kai har abada ba zaka yi hankali ba, dan ubanka ya zauna yana cewa in ja maka kunne, a kan shishshigin da ka ke yi mata, amma ina magana kana dizagani a gabanta” Nabila ta yi gaba ta fice a fusace, dan idan ta cigaba da tsayuwa, za ta iya aikata abun da zai hana kowa wuni cikin farin ciki.Ya ce “Ni ɗin kuma mama?””Kai ɗin fa, ko ka shiga hankalinka, ko kuma duk abun da ya biyo baya kai ka so”.Sam sai ya ji maganar kamar maman ce, ta shirya kayarta dan ta saba, dan haka ya yi musu sallama ya fice.A gurguje ta tsaya ta gaisa da Abba, ta fice cikin zumuɗi, gidan radiyon su sumayya ta fara tsayawa.Sumayya ta yi mamakin ganinta, ta ce “Hajiya lafiya ki ka zo mana wurin aiki da sassafe? Talla ki ka kawo ko cigaya?””Ƙaniyarki na kawo” Nabila ta ba ta amsa.Sumayya ta ce “Ai na san ke ungulu ce, ba kya jewar banza, ya aka yi uwar makara”Nabila ta ce “Yau da safe kan na fito, na ji baba magajiya na jin program ɗin ku na labaran ƙarfe shida, bayan kin karanto naki, na ji wani rahoto na faɗan ƴan daba, jiya a kano”Sumayya ta ce “Eh meyafaru?””Kin je wurin ne?”Sumayya ta zaro ido ta ce “In je in yi me?””Na ji an ce wai yaran Aminu Viper ne”Sumayya ta ce “Eh to, ni ma haka na ji””Dan Allah ki tashi mu je asibiti, an ce an kama wasu, wasu kuma da aka yi musu miyagun raunuka suna asibitin koyarwa na cikin gari”Sumayya ta ce “To wai ke duk menene haɗinki da hakan?”Kamar Nabila za ta yi kuka ta ce “Sumy ban gaya miki ba? Yaya Nasir ne incharge ɗin bincike a kan mutumin nan, kusan kullum sai an faɗi mugun aikinsa, ya tabattar mini da in dai na gano masa in da yake, ko na taimakasa ya gano zan yi suna sosai”Cikin matsanancin takaici Sumayya ta ce “Tashi ki tafi ko na ɗura miki ashar, ƴar wahala, shi yaya Nasir ɗin ne ya gaya miki haka? Ƴar sanda ce ke? Su ma ya suka ƙarke da su balle ke ki na mace, wallahi ba zan kai kaina ga halaka ba””Sumy ki gane, this can all help our career ki zo mu je mana””Wallahi ba zan shiga shirgin ƴan daba su kashe ni ba, idan kin yi sunan uban me zai ƙara miki, za a binneki da shaharar ne idan kin mutu?”Cikin ƙoƙarin son fahimtar da sumayya ta ce “Ba za a binne ni da shahara ba, amma atleast zan samu chances da zan iya fuskantar Naja bunkure”Wata uwar ashar sumayya ta yi wa Nabila, ta tashi ta ce “Mahaukaciya, ai sai ki yi, ke da bunkuren ƴan wahala”Nabila ta tashi a fusace, ta ɗauki jakarta ba tare da ta sake cewa sumayya komai ba, ta tashi.Sumayya ta girgiza kai ta ce “Arfa Allah ya taro ki ya shirye ki, ya yaye miki baƙin taurin kai””Tun da kin ce ba zaki je ba, kar ki sake yi mini magana, kuma na gode””Eh ba zani ba, haka kurum a kashe ni a banza, mutanen da ba tsoron Allah ne da su ba, mutanen da suke shan ƙwaya tana gaya musu gaibu, su ɓantarani biyu a banza ba da ni ba”Nabila ta yi mata shiru ta fice.Nabila ba ta yi tunanin komai ba, ta garzaya asibitin koyarwa, na cikin gari.Ba ta wani sha wahala ba, saboda tana zuwa, ta tarar jami’an tsaro sun kewaye sashen emergency, ba wanda yake shiga ko ya fita.Zagaye harabar wurin ta fara yi,tana neman hanyar shiga, da son tabattar da abun da yake faruwa a wurin, ta samu wata cleaner, ko meyafaru a in da ƴan sandan suke.Nan ta sanar mata da cewa, yaran da aka illata a wurin faɗan daba a daren jiya, aka kawo an hana kowa shiga ko fita.Nabila ta yi mata godiya, ta yi mata alheri, ta nufi wurin da aka hana shigar da fita..Ta ƙarasa ta samu ɗaya daga cikin jami’an tsaro suka gaisa, sannan ta nemi shiga, suka ce ba za ta shiga ba.ID card ta nuna musu, amma ɗaya daga cikin su ya ce “Madam nan ba prison bane, kuma ba police station ba ne ba, nan Asibiti ne, ki bari idan aka kai su can, sai ki je ki yi aikin ki”.Ta kwantar da murya ta ce “Dan Allah yallaɓai, ku bar ni na shiga, Ma’aikaciya ce nima””Get out from here” yayi mata tsawa.Aikuwa ta hasala ta ce “A beg, don’t shout at me, aikinka ka ke yi, nima nawa nake son yi, a kan me za ka yi mini tsawa?” Hankalin mutane ya fara dawowa wurin.Sake hayayyaƙowa Nabila yayi, amma cikin dakiya da taurin kai, take mayar masa da martani.Da ƙyar aka rarrashi police ɗin, dan cewa yayi sai sun tafi da ita station, wataƙila ma ƴar ƙunar baƙin wake ce, ko ta na da alaƙa da masu laifin.Nabila ta ce “Ni za ka yi wa sharri, ki in ƙunar baƙin waken zan kai, zan tsaya saurarku ne, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba”.Ana ta ƙoƙarin sasanta magana, amma Nabila ta ƙi yin shiru.Ta ciro wayarta, ta kira Nasir sai huci take yi.Yana ɗagawa ta ce “Yaya, ya ake ciki ne? Akwai wani labari ne?”Ya ce “No, wallahi arfa kin ganni, na zagaya station uku a yankin, duk ba a kai su ba, amma wata majiya ta tabattar mini da sakinsu aka yi, just recently””Sakin su kuma? Saboda me?” “Ban sani ba, a kan abun da nake ƙoƙarin yin bincike kenan””Ka hanzarta ka taho asibitin cikin gari, akwai waɗanda aka kwantar, police sun hana shiga sun hana fita, an hana kowa shiga, ko da kuwa kusa da ɗakin. Har da ƴan jarida ma an hana su”Cikin sauri ya ce “Ok shikenan, gani nan in sha Allah, hankalina bai kai kan in zo asibiti ba ma na duba ko akwai abun da zai taimaka mini, amma gani nan stay safe”Ta amsa da “Ok”Ta ajiye Wayar a jakarta, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ƴan sandan suka saka mata ido, dan kar ta yi wani mummunan yinƙuri, dan ba su san manufarta na dagewa a kan son shiga wurin ba.Babu tsammanni aka fito da matasan, wasu ɗauke da raunuka, wanda ba za su iya tafiya ba, an turo su a kan gado, an nufi hanyar barin emergency da su.Nabila ta nufe su cikin sauri, amma ƴan sanda suka tare ta.Ta kalli ɗaya ta ce “Yallaɓai ina za a kai su? Na ga wasu a mugun yanayi, ya za a bar asibiti da su?”Babu wanda ya kula Nabila, aka saka matasan a cikin ambulance, har da iyayen wasu daga cikin matasan jami’an tsaron suka hana su bin su, suka rufe ambulance ɗin, su kuma su ka hau ta su motar ta ƴan sanda, suka bar harabar asibitin.Ƴan jaridar da suka yi ƙoƙarin bin su ma, aka dakatar da su, aka hana su ƙarasawa ma in da motar take har suka tafi.Tsayawa ta yi kamar wata shashasha, tana mamakin yadda abubuwa suke tafiya, kamar a film.Motar DSP Nasir ce ta shigo cikin harabar asibitin, yayi parking ya fito, yana ƙoƙarin kiran Nabila a waya,ya tambayi tana ina.Da sauri ta ƙarasa in da yake, tana kallonsa, amma ta kasa magana.Ya ce “Yaya dai? A wane ɓangaren suke, kin samu ganin na su kuwa?”Nan ta kwashe duk abun da ya faru, ta gaya masa.Cikin asibitin ya shiga, tana biye da shi, ya tambayi office ɗin incharge na A&E ɗin, ya gabatar masa da kansa, tare da yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, aka sallami mutane da raunuka a jikinsu. Amma ya tabbattar masa da cewa, babu wanda yayi musu wani cikakken bayani, kawai ƴan sanda sun kawo musu yaran jina-jina tun a daren jiya, sun ba su kulawar da ta dace, daga bisani ƴan sandan suka ce asibiti za su canza musu, aka tafi da su.Nabila ta yi shiru, sannan ta ce “Akwai wata a ƙasa yaya Nasir, ko waye wannan Aminun, ya na da wanda su ke sponsiring ɗin sa. Shi an kasa kama shi, amma ya na saka yaran mutane ta’addanci, you need to put more effort, and i will hundred percent support you, everyone is equal before the law, dole a nemo shi a hukunta shi”
Ayshercool
08081012143
