Halysaah Page 183 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 183…Mami ta jawo kujeran dake kusa da su ta sa Jay ya zauna kan kujeran ganin duk a birkice yake, ta kwantar da murya tana kallonsa tace “You will go to Makurdi Jawwad but not today” Da wani expression yace “Mami me yasa ba yau ba?” Mami tace “Saboda it’s already late today baka jin kiran Sallan Magrib? beside banki ai basa aiki da daddare Jawwad, don haka kayi hakuri ka bari gobe idan Allah ya kai mu da safe sai ka tafi, kuma kar ka yi ma Mai martaba wannan magana tukunna, i don’t want him to be worried too” A haka Mami ta samu ta lallabasa sanin sai ya iya bin hanya da magariban nan yace zai je Benue, shi dai kansa na kasa ya kasa ce mata komai amma ji yake kamar bazai iya jira har sai gobe ba, tamkar yayi tsuntsu yake ji, in dai ba ganinsa yayi a Makurdi ba his mind will never rest, he don’t mind waiting in front of the bank till in the morning, Mami tace to mu shiga ciki” Girgiza mata kai yayi cike da karfin hali yace “Ni zan tafi hotel Mami” Mami wasn’t convince with that barin da taga yanayinsa, bata ga alamar ya dau abinda ta gama gaya masa yanxu ba, tace “A’a baza ka je hotel ba, ga boys quarter kayi zaman ka nan har zuwa gobe da safe Jawwad, su Umar ma suna can” Dai dai nan sai ga Umar ya fito daga Boys quarter din da wasu frnds dinsa biyu za su tafi masallaci, Mami ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Jay tace “To gashi can ma ya fito, ka tashi ku tafi masallaci, amma promise me you are not leaving Jawwad, idan kayi hakan zaka daga min hankali sosai, kayi hakuri ka sa ma kan ka nutsuwa ka zama patient har zuwa gobe pls son, no one is stopping you from going to Benue but wait till tomorrow morning” Sauke idonsa yayi cike da karfin hali yace “Zan jira goben Mami” Umar dake ta kallon Jay da mamaki ya nufesa yace “Ikon Allah, Dakta idonka kenan yau” Jay ya mike trying his very best to compose himself, suka gaisa da Umar da frnds dinsa sannan fita zuwa masallaci tare, Mami ta juya ta koma cikin gidan jikinta a sanyaye da tunani iri iri a ranta akan debit din nan da aka yi ta account din Ajay, she is also confuse just like Jay, but ta ma rasa meaning din da zata ba incident din nan, ita kanta bata son saka hope at the end ta zama disappointed balle kuma Jay, shi yasa take tausayinsa, gani take kawai sharrin fraudster ne…. Ajay ya bude idonsa a hankali jin an bude kofar dakin hotel din da yake, wani mutumi ne da bazai wuce shekaru arba’in da biyu ba ya shigo dakin, ya karasa har kusa da gadon yana kallonsa yace “Are you feeling better now?” Duk da zazzabin da yake ji yace “Alhamdulillah” Mutumin yace “Sunana Bilyamin Muhammad…..” Ajay ya sauke idonsa yace “I am Ahmad Yusuf” Bilyamin yace “Ohk, hope you called home to ur relatives su san halin da kake ciki if possible su zo su tafi da kai, cause you don’t look okay” Ajay yace “Basa garin nan” Bilyamin ya saka hannu a aljihunsa ya ciro naira hamsin ya ajiye ma Ajay a kusa da shi yace “The hotel room cost 50k per night… Ga sauran kudaden” Ajay da duk ya kagu ya fita daga dakin don da kyar yake maganan yace “Nagode” Bilyamin yace “But me ya hana ka zuwa asibiti ka taho hotel instead?” Ajay ya girgiza masa kai don he is beginning to feel uncomfortable with the discussion yace “I am under medication” Bilyamin dai kallonsa yake baya ko kiftawa, can yace “Amma ai ya kamata dai ka kira gida ka sanar masu baka da lafiya su sani, By the way… why are you in Makurdi?” Ganin da yayi Ajay yayi shiru alamar bazai basa amsa ba Bilyamin ya rungume hannunsa yana ta kallonsa, after some seconds cikin nutsuwa yace “You are acting cunning, I suspect there is something you might be hiding, what is ur mission in Makurdi Ahmad?” Ajay ya daga kai ya kallesa jin abinda yace, Bilyamin yace “Answer my question now” kusan with authority Bilyamin yayi maganar, Ajay yaki cewa komai yana ta kallonsa kamar yanda Bilyamin din ma ke kallonsa, bayan Aj bar asibitin ya samu adaidaita sahu ya ce ya kai sa hotel me kyau, Mai adaidaita sahun ya samu hotel me shegen tsada kuma me nisa daga inda ya daukesa ya kai sa hotel din, Ajay na sauka ya zari yan duba daddaya bai ma san ko nawa ba ya ba dan sahun sannan ya shiga cikin hotel din da kusan last strength dinsa, yana shiga haraban hotel din yasan Receptionist din baza su sauraresa ba balle su basa daki duba da condition dinsa, haka nan yana ganin dishi dishi ya dinga layi ya tafi can wajajen parking space ya nemi waje ya zauna wajen flowers yana maida numfashi, if not that he look responsible da tun daga gate din hotel din za a ki barinsa ya shiga, dai dai sanda wata mota ta shigo hotel din, me motar ya sako kan motar zai yi parking a kusa da inda Ajay ya zauna, hakan yasa ya haska sa da fitilar motar, wanda ke cikin motar yayi ta kallonsa har ya gama parking sannan ya bude motarsa ya sauka, kamar zai tafi cikin hotel din sai kuma sai ya rufi Ajay ganin yanayinsa kamar na lafiya, yana kallonsa yace “Are you okay?” Ko ganinsa Ajay bai yi sosai sai muryarsa da yake ji, haka nan mutumin ya karasa har kusa da shi yana kallonsa da kyau yana kara yi masa tambayar if he is okay or need any help, Ajay ya gyara zamansa yayi karfin halin cewa “I think I’ve got a fever, I am far from home, so I came to pay for a hotel room and spend the night here” Mutumin kallon Ajay kawai yake as if trying to figure out something, Ajay ya ciro kudi bandir daya a aljihunsa ya mika ma mutumin yace “I don’t know the cost of a room per night, i will be glad if you could help pls” mutumin ya amshi kudin yace “Let me confirm” Daga haka ya juya ya nufi hanyar shiga reception din hotel din, not long after ya dawo yace “I’ve booked a room for you….” Ajay na jin haka yaji wani karfi ya zo masa, don kawai so yake ya ji sa saman gado cause sanyi yake ji sosai, ya mike tsaye yana dafa bango, a haka ya daure suka shiga hotel din tare da mutumin da ke tsaye kansa yan Endakin hotel dinsa, Calmly Ajay yace kama da mara gaskiya ne?” Bilyamin ya ciro ID card dinsa a aljihu yana nuna ma Ajay yace “DSP Bilyamin Muhammad, identify your self now” Ajay ya sauke idonsa, after some seconds a hankali yace “Nagode da taimakona da kayi Officer, but i am not a criminal, I have a record of none, I am just sick….” Bilyamin yace “Ina wayar ka?” Ajay ya girgiza kai yace “Bani da waya a yanxu” Bilyamin yace “Daga ina kake?” Ajay yace “I had an accident, I’ve been away from home for sometimes” Bilyamin yace “Ni zaka raina ma hankali kenan, identify your self or i get you arrested, where is ur national identity card?” Calmly Ajay yace “Dama ana arresting wanda bai yi wani laifi ba? I have no identity card with me….” Bilyamin ya ciro wayarsa yayi kira zuwa nearest police station a aiko masa da yara da mota daya, Ajay was just looking at him, Bilyamin ya maida wayarsa aljihu yace “Ku ne manyan Bandit din da suka gallabi mutane a al’umma, you definitely look like one came you don’t even look Nigerian, bal identity card baka da waya amma kana da bandir din sababbin cash a jikin ka, you will explain better when we get to the station….” Ajay ya dan yi murmushi yace “Dama Bandit suna da kamanni? And how sure are you I am not a Nigerian, kawai daga ganina sai ka kira ni da Bandit? ohk.. yawo da cash yanxu ya zama offense ne a Nigeria? Or is there a new policy that i am missing” Bilyamin yace “Duk zaka samu amsar tambayoyin iskan nan naka idan muka tafi station yanxu” a hankali Ajay yace “Ohk” Strictly Bilyamin yace “For the last time, identify your self before we get out of this hotel in a way u never expect, and it’s not going to be funny when we get to the station, ban shigo hotel din nan yau da niyyar arresting criminal ba, i helped you out of pity but ur ways are suspicious, tell me who are you?” Ajay dake ta kallonsa ya mike zaune da kyar ya jingina da gadon dakin yace “So now tell me why you are getting me arrested? Na ce maka sunana Ahmad Yusuf, let me add I’m an Aboriginal of Bauchi state….” Bily of yace “Where in Bauchi state?” A hankali Ajay yace “I’ve been away from Bauchi for a long time, Ina nan wani riverine area before Makurdi, I don’t know the name of the village” Bilyamin yace “You said you are from Bauchi, where in Bauchi? Nima dan Bauchi ne” Ajay yayi shiru, can ya sauke Idonsa yace “Gidan Sarki” Bilyamin yace “Wani gidan Sarkin?” Ajay yace “Emirate din garin” Bilyamin yace “Kai wanene a gidan Sarkin?” Ajay yace “Ahmad Junaid” Bilyamin yace “Kal… Listen to my question carefully kar ka raina min hankall, I asked what is ur relationship with the Emirate?” Ajay yayi shiru kamar bazal ce komal ba, sal kuma ya sauke idonsa yace “Mahaifina ne ruler din Emirate din” Bilyamin was just staring at him, can yace “Mahaifin ka?” Ajay ya gyada masa kai, karasawa yayi ya zauna kan bedside drawer yace “Kana nufin Mai martaba ne babanka?” Nan ma dal Ajay ya gyada masa kal kawal, shiru Bilyamin yayi kamar me nazari, sal kuma ya mike masa wani kallo yace “Ko dal kai ne dan sarki that was missing few years ago?” Ajay bai ce masa komai ba, Bilyamin yace “But how will I believe you now? Idan da gaske you are the one that went missing few years ago ta yaya zan tabbatar da hakan, me yasa ka ki komawa gida for this long bayan da hankalin ka da bakin ka?” Ajay yace “Sai yau na fito cikin gari daga riverine area da na gaya maka, i don’t know for how long I have been there, take me to the hospital now, I need it the most, but before that I want to ask for a favor from you officer” Bilyamin was was speechless and surprise, yana ta kallon Ajay babu ko kiftawa, cikin sanyin murya Ajay yace “Pls bana son a samu labarina a gida for now, I want to recover and gain my strength first….” Bilyamin yace “Saboda me baka son a samu labarin ka a gida bayan wannan shekarun da aka dauka ana neman ka?” Ajay yayi shiru, Bilyamin ya koma gefensa ya zauna yace “I am still doubting ur story Ahmad, bani number wasi na gidan sarki yanxu” Ajay ya girgiza kal “Bani da number kowa a kai yanxu, i can’t remember any number, but to clear ur double you can search Jawwad Ahmad Yusuf on IG, nasan baza ka rasa ganin hotunan mu tare da shi ba, he is my brother” Bilyamin ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga IG yayi yanda Ajay yace masa, al kuwa nan yaga hotunansa da Jawwad kana ganin wasu shigarsu kaga yan gidan sarauta, sai kuma hotunan Mai martaba da ya gani masu yawa, Ajay was just staring at his father’s picture babu ko kiftawa, Bilyamin ya kallesa yace “Ahmad, me yasa kace baka son a samu labarin ka a gida?” Ajay ya daga idanuwansa ya kallesa a hankali yace “Reason because i am afraid i can’t stand the new changes that might have occurred during my absence, kilan zuciyata bazata iya dauka ba…” Da mamaki Bilyamin yace “Wasu irin canji kenan kake nufi?” Ajay ya kasa ce masa komai, Wayarsa ce ta fara ringing ya duba sannan ya daga, yan sandan da ya kira station yace a turo masa ne suka iso suna outside of the hotel, ya nufi kofar fita ya kullo kofar, Ajay ya sauke kansa he felt in dai abinda yake tunani a zuciyarsa haka ne to dama barin duniyar kawai yayi cause he can’t stand to witness it too, ya dafe kansa da hannu biyu don tunanin hakan yasa fever dinsa ya karu, zuciyarsa bazai iya daukan abun da yake tunani ba, dalilin ma da yasa ya ba Officer din Handle din Jay na IG yasan ko zai shekara yana masa magana bazai bude message din ba, amma yana da number both Jay da Mai martaba a kansa, ya ma fara regretting gaya ma DSP Bilyamin wanene shi don yasan definitely zai nemi hanyar contacting Emirate, da ya bari kawai an tafi da shi police station din, bai san Bilyamin na fita daga dakin har ya aika ma Jay DM immediately ta Instagram…. Bilyamin ya sallami yan sanda da suka zo ya dau Ajay zuwa asibiti wajen karfe tara na dare. Washegari ganin har karfe takwas saura Jay bai kira Mami ba yace mata zai tafi Benue yasa ta fito to check if he is even alright, Umar kawai ta samu a Boys quarter din bayan ya gaisheta ta amsa da fa tace “Jawwad bai tashi back ko?” Umar yace “Ai Mami tun hudu saura na asuba Jawwad ya bar gidan nan, yace min zai yi tafiya ne” Da mamaki Mami tace “Hudu saura na asuba?” Umar yace “Wallahi lokacin da ya fita kenan Mami” Mami bata sake cewa komai ba, after some seconds tace “To shikenan Umar Juyawa tayi ta bar bakin kofar ta koma cikin gida jiki a sanyaye, ta tafi dakin da aka saukesu ta dau wayarta tayi dialing number Jay, Khaleesat na zaune dakin da breakfast a gabanta taki shiga cikinsu Inteesar tun jiya don hayaniyar kawayen Inteesar na damunta a brain dinta, duk da ita ma dai Inteesar din isn’t lively kamar ba aurenta ake yi ba, duk a sanyaye take tun da suka zo, Khaleesat ta kalli Mami ganin yanayinta tace “Mami wani abu ya faru ne?” Mami ta sakar mata murmushin da bata yi niyya ba tace “A’a babu abinda ya faru Halysaah, har kin gama breakfast din?” Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, Mami ta nufi kofa ta fita bayan Jay ya daga wayar, da damuwa tace “Jawwad tun asuba Enbai vi ba dama ka bar gidan nan? Kan yanxu?” A hankali yace “Mami i just arrive Makurdi 15 mins ago, Ina bakin bank d yanxu haka amma basu fara aiki ba tukun, ba a bude bank din ba, but workers din suna ciki…..” Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ma rasa abinda zata ce masa, har cikin ranta taji tausayinsa, tasan da kyar in ya runtsa daren jiya, after some seconds ta kwantar da murya tace “Plsss i want you to calm down Jawwad, ko ma me zaka tarar a bank din nan you have to accept it with good faith, Kar ka saka hope din komai a ranka, babu ta hanyar da masu cuta basa cire kudi a account din mutum idan sun yi niyya….” Jay yaki ce mata komai don baya son tana basa less hope, it’s making him weak and frustrated, jin yayi shiru tace “Duk yanda ake ciki ka kirani” Ya gyada mata kai kamar tana ganinsa don ya ma kasa bude baki, ta katse wayar sanin bazai ce komai ba, Jay ya jinginar da kansa jikin bango don yana zaune ne a dai dai kan dakalin da Ajay ya zauna jiya bayan un fito, bank da Ozhi…. Nenne na kwance a parlor duk ta hada uban zufa, ga su Mama Zubaida da Mama Shatu da ta saka kwaleman dole su ma sai aiki suke ransu bai so ba don sai cika suke suna batsewa, da bakin cikin labarin da suka samu na auren Faridah da Sarki za su ji ko da na kwaleman dole da aka saka su, wato duk uban kudaden da suka kashe kar Faridah ta auru ya tashi a banza a iska lokaci daya sai jin aurenta suka yi da Sarki sukutum da guda, daga Mama Zubaida har Mama Shatu babu wanda yayi baccin kirki daren jiya saboda bakin ciki, ko auren Khaleesat da dan sarki basu yi bakin ciki ba kamar na Faridah warce da ita ma suke kishi a gidan ba Umma ba tunda ita ke biyesu, har Sha’awa sai da Nenne ta kira daga Mariri ta zo ta taya su aiki, ko ina na Parlon gida ya dawo sai sheki yake ga uban turaren wuta da aka kunna, Hajiyah Zaliha ce ta shigo Parlon tana murmushi tace “Maa sha Allah, Sannun ku da aiki Nenne ashe har dake a aikin, da na sani ai da na zo tun daxu na kama maku nima” Nenne tace da zai zauna da Zaliha, ai bamu ga ta zama ba, in an sauko sallan juma’a ne daurin auren fa, muka san adadin bakin da za mu yi daga gidan sarauta yau, ai yau gidan nan sai Allah….” Hajiya Zaliha na dariya tace “Gaskiya ne Nenne, ina sarauniya faridar tamu take? Ina ta zuba ido in ga ta shigo min bata shigo ba, duk na kira kawayena na sanar masu suna hanya yanxu haka, wannan aure ai namu ne, wallahi baki ji yanda nake farin ciki ba Farida zata shiga babban gida, Allah mun gode maka da wannan ni’ima” Su Mama Zubaida suka wani harari Hajiya Zaliha cike da takaici, Nenne tace “Zaliha kinsan mutum fa bai iya samun waje ba, wai ita sam bazata iya da gidan sarauta ba, bata kuma sha’awar zama gidan, tana can ta daga hankalinta….” Hajiya Zaliha ta bude ido sosai tace “Wa yace mata dama ana iyawa da gidan sarauta? Ai sai kaje zaka koyi iyawa a can? Tana ina?” Nenne tace “Atoh dai, ni ko bin ta kanta ma ban yi ba don ba ita bace gabana fatana ayi ayi a daura auren anjima, tana can dakin yayarta babu walwala, ni ko gaisheni yau ma bata yi ba wallahi, wato kana neman er bakin ciki ka samu Faridah ai an gama, idan ba tsantsan bakin ciki ba meye wannan take yi Zaliha, ita din banza zata ja da maganar sarki da zai aiko a aura masa ita, har tana cewa ita al bai mata magana ba kuma yana da numberta, Ni ko nace ita din wa za ayi ma magana fisabilillahi? Al zubar da girmansa ma zai yi idan ya tunkareta da maganar, tsakaninsa da ita ai sai in an kai ta masarautar….” Hajiya Zaliha ta nufi dakin Umma tana murmushi, Nenne tayi kasa da murya tana goge kayan kallo tace “Ke ba er kowan kowa ba ki ce kina gudun auren sarkin gari guda, de Enda dan talaka bai iya samun wa wallahi, tayi ma kanta bakin ciki mu ma ta mana, to Allah ya fita wallahi….




