Uncategorized

Labarina Season 4 Episode 12

 LABARINA.

MARUBUCI:  Nasir S Nasir Gwangwazo kat! Ne a duniyar rubutu. Tababas! Mun ga aikin ƙwaƙwalwa wajen jan zaren labarin ta hanyar ɓaddabami. Wato duk lokacin da lissafinmu ya yi Gabas, sai mu tsinci amsa ta bayyana a Yamma.

UMARNI: Shirin ya samu sanya hannun fasihin mai ba da umarni a duniyar finafinan Hausa. Malam Aminu Saura, gwani ne na yankan shakku.

KAMFANI: Saira Movies.

TAURARI:

Sarkin Waka

Lukman

Rukayya

Ummi

Baba Rabiu

Sa’a

Bello

Atete

Kabir

Talatuwa

Bintalo

Naja

Karanta:

✓ Sabbin Hotunan Momee Gombe, Maryam Booth da Hadiza Gano.

✓ An baiwa mawaƙi Umar M. Shareef jakada a gidan television.

✓  Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power

✓  Hukuncin Abincin Kirsimeti Ga Musulmi Fita ta farko 


JIGO: 

Tsaro da soyayya.

SALO DA SARRAFA HARSHE: An ƙawata shirin da kirari, kambamawa, da Karin magana. Hakan ya sake fito da gwanintar zaɓen kalmomin da aka yi amfani da su. Misali:

“Direba dangin kura, kana ganin gari ka kwana a daji. Hannu ya iya ƙafa ta saba, zuciya tana lissafi.

LUKMAN: Kina nufin nan gaba zan daina son Sumayya, na dawo soyayya da ke?

UMMI: Ko shakka babu

1. Kalaman Presido suna yin tsauri da yawa, ba ga suruka ba har da hukuma. Ya kamata a ce ya yi karatun ta-natsu.

2. Duk kalaman Kabir game da Sumayya gaskiya yake faɗi ma Lukman amma makanta ta hana shi ganin gaskiya.

3. Atete da Sa’a su ne mutane mafi bukatar zargin da bincike. Sam kalaman Atete babu gaskiya a ciki.

4. An sake danno wata matsalar da za ta fuzgi zuciyarmu. Matsalar Naja da buƙatarta na sanin asalin ta.

5. Role ɗin Ummi yana matuƙar burgeni, salon shigar da soyayyarta ga Lukman, akwai hikima.

Ƙorafi: Ma su kallo har da in, muna kuka da tallan da ke janye yawan lokutan kafin fara shirin da kuma a cikinsa. Musamman ma na e-naira ɗin nan da kuma na Kano. Ya kamata a duba gaskiya.

Akwai sauran kallo a labarin nan!                          Play video     Mubarak Abubakar Saulawa

                      

Back to top button