Uncategorized

Tubali Book 2 Page 2 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

A Jikinta ya manna kanshi da cikinta kana kuma ya cusa fuskarshi acikin jikin nata.

Tare dasa hannunshi na dama ya damƙe mararshi.

Gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi tamkar mazari, wani irin ciwo cikinnasa keyi masa, wanda har hakan yasa numfashinsa, ke kokarin kwacewa. 

Hannunshi na hagu yasa abayanta ya zagayeta, tare da riƙe ta gam-gam cikin gigitan ciwo da fitan hayyaci.

Hakan kuwa yayi masifar gigita Jannart,  wanda gaba daya jikinta ya d’auki rawa, kamar yadda nashi jikin ke rawa.

Kana ya kwakumeta ya kanainayeta ya hanata ƙwaƙƙwaran motsi.

Jannart kuwa Ganin hakan yasa cikin  firgici ta buɗe baki, murya na rawa ta fara cewa.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun Mamy! Mamy!! Mamy!!! Kalli yadda yakeyi fa!!!!”.

Yayinda ita kuwa Mamy cikin tsananin tashin hankali da kidima, ta fara juyawa tsakiyar falon cikin rashin sanin abinyi taketa rabkawa  Ramadan kira.

“Ramadan! Ramadan!!! Kazo!!! Rayyern ba lfy”.

Dr. Sulaiman ne wanda shi ya dawo da Rayyern din, ya turo ƙofar da hanzari, 

baishigo da wuri bane kuma, saboda ya tsaya fadawa Baba Mauɗo cewar ciwon Rayyern ne ya tashi.

A hanzarce ya faɗo cikin falon, 

Baba Mauɗo na biye dashi a baya.

Yayinda sukabar Hadi da Ari mai gadi kuwa tsaye a harabar gidan, sunyi jugum-jugum domin duk mai  imani, muddin yasan yadda ciwon Rayyern ke yi in ya tashi tamkar zai tafi da ransa to tabbas zai cika da fargaba.

Hakan ne ma yasa Hadi zaro wayarshi ya kira Abba, yana ɗagawa cikin yanayin tashin hankali yace.

“Alhaji jikin Rayyern fa ya tashi”.

Cikin kidima Abba ya kalli mutanen da yake tare dasu tare da miƙewa tsaye yace.

“Rayyern ba lfy”.

Yana faɗin haka ya fita daga falon da bisa alamu duk mgnar sirri yakeyi.

Yana katse kiran Hadi ya kira Ramadan yana ɗagawa yace.

“Kai Ramadan kana ina”.

Da sauri yace.

“Abba ina Minjibir ne. Lfy kuwa?”.

Cikin bada umarni da tashin hankali yace.

“Maza ka wuce kayi gida yau kuma cikin Rayyern ya tashi”.

Cikin tsananin tashin hankali Ramadan ya mike tare, da barin duk wani abu da yakeyi, hankalinsa amatukar tashe yace.

“innalillahi wa innailaihi rajiun! Jikin Hamma Rayyern ya tashi? Yanzu Abba Hamma Rayyern din yana ina?” 

Abba dake tsaye, cikin alhini da fargaba yace.

“Yana gida, kayi sauri kaje.” 

Yana gama fad’in haka ya katse kiran.

Kana yaci gaba da tuƙin da yakeyi.

Shi kuwa Ramadan a kidime  ya kalli Riyyam-nsra dake cewa.

“Hamma Ramadan meya faru”.

Ya ƙare .mgnar yana firfito da idanunsa.

Idanu Ramadan din ya rumtse da karfi, cike da alhinin abunda Abban ya gaya masa, ya kamo hannun  Riyyam-nsra tare da jansa, suka nufi parking lot, hankalinsa atashe yace. 

“Riyyam mu tafi gida yau kuma ciwon cikin Hamma Rayyern ya tashi, 

abunda yafi shekara biyu ya kusa shekara uku bai tashi ba, amma yau gashi ya sake tashi mishi.”

“Innalillahi!” 

shine abinda Riyyam-nsra ke ta maimaitawa.

Dai-dai lokacin da suka shiga mota.

A 360 Radaman ya figi motar yana cewa.

“Yah Rabbi, Yah Allah ka bawa Hamma na lfy, gaba ɗaya mun sakankance, da cewar ya worke tunda mukaga yayi shekaru bai tashiba”.

A nan gidan kuwa.

Cikin yanayi tashin hankali Mamy ta kamo hannun Dr Sulaiman, a gigice ta jawoshi zuwa gaban Jannart da Rayyern ke kwance kanta, irin kwanciyar nan ta rubda ciki.

Murya na rawa Mamy tace.

“Sulaiman duba min Rayyern yana raye kuwa duba minshi kaga fa baya motsi”.

Ta ƙare mgnar wasu irin masifaffun hawaye na kwaranyo mata.

Yayinda sai a lokacin kuma Jannart ta sunkuyo da kanta, ta zuba mishi ido tabbas kuwa ya daina motsi, duk rawa da karkarwar da jikinshi keyi ya bari.

Wani irin zaro ido tayi tana kallon Mamy dake cewa.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun Sulaiman ka duba min  Rayyern, kada ya tafi ya barmu akwai nauyinshi da bamu sauke a kanmu ba.”

Shi kuwa Dr Sulaiman kamo hannunta yakeyi, yana son zaunar da ita amman ina, gaba daya ta gama gigicewa, ga hawayen dake ta Kwarara acikin Idanunta.

Baba Mauɗo kuwa da sauri ya matso gaban Jannart ya tsuguna, cikin kuma tashin hankali yasa hannunshi, akan wuyan RAYYERN sabida a kife yake, murya na rawa dattijon ya fara kiran sunanshi.

“Rayyern! Rayyern!! RAYYANU!!! Muhammad Muhammadu tashi.

 Buɗe idanunka Mauɗona!!!”.

Ya ƙare mgnar hawaye na kwaranyo mishi.

Wanda ganinsu ne kuma yasa hawayen idanun Jannart tsinkowa.

Tausayin tsohon da Mamy ne sukayi masifar raunata mata  zuciya.

A fili zaka gano tsananin  tashin hankali da kidimar da suke ciki, kana da tsananin sonshi dake cikin kwayar idanunsu.

Shi kuwa Rayyern da yakejin kansa acikin wata duniya, mai dauke da tsananin azaba gami da radadi, sama-sama haka yake jiyo muryarsu.

Saidai kuma bazai taba iya amsawa ba, duk da yana jiyo kiran sunansa da  Baba Mauɗo keyi, saidai baya da hakikanin cewa, ko yan siraran labban bakinsa zai iya motsawa, saboda tsananin ciwon da yakeji.

Dr Sulaiman kuwa cikin samar da kwanciyar hankali wa Mamy, ya samu ya ajiyeta bisa kujera kana a hankali yace.

“Mamy Rayyern yana numfashi fa, babu abunda ya samesa, Dan Allah ki kwantar da hankalin ki, Insha Allah zai samu lfy, na mishi allura tun a asibiti, yanzu haka ciwon ya fara lafawa, Insha Allah gaba daya zai daina”.

Dr. Sulaiman din ya kare maganar cikin, kwantar da murya da kuma son samawa Mamyn nutsuwa.

Dai-dai lokacin ne kuma Abba ya shigo.

Da sauri ya iso tsakiyar falon.

Sai kuma ya iso gefen Baba Mauɗo a kidime ya fara kiransa.

“Rayyern”.

Sai kuma ya juyo da sauri jin Dr Sulaiman na cewa.

“Abba dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku barshi zuwa anjima kaɗan zai iya amsa muku, nayi masa allura Insha Allah zai samu sauki”.

Wani irin dogon numfashi Abba ya sauke, kana ya koma ya zauna bisa kujerar dake gefensa.

Yayinda Mamy kuwa har yanzu ta gaza tsaida hawayenta.

Gaba daya hankalinta yaki kwanciya, tsoro takeji kada wani abu ya samu Rayyern din, badon komai ba kuwa saidan sanin da tayi, cewar ciwon cikin baya tab’a yi masa da sauki idan ya tashi. 

Jannart kuwa da tayi k’asa da kanta, tana jin yadda Rayyern din ke kwakume da ita da masifar ƙarfi, yanayin rikon da yayi mata, dinne kuma yasa kugunta ya soma sarawa, saboda ba wai riko ne na wasa yayi mata ba riƙone na neman mafita.

Ramadan da Riyyam-nsra kuwa kusan a jere da sassarfa suka shigo cikin falon, kowannensu hankalinsa amatukar tashe.

More especially Ramadan da yasan irin yanda ciwon, keyiwa Hamman nasu idan ya tashi. 

Da sauri suka nufi kanshi, saidai basu k’arasa ba kuma suka tsaya, saboda ganin su Abba duk suna zaune.

Baba Mauɗo na zubda hawaye, Mamy ma haka kana Jannart da yake kwance lib a cinyarta kamar matacce, itama hawayen  take tsiyayarwa.

Abba kuwa habarsa ya tallafe, saidai kallo daya zakayi masa, ka karanto tsananin tashin hankalin dake kwance akan fuskarsa. 

Ganin hakanne kuma yasa, zuciyar  Ramadan wani irin harbawa, lokaci daya kuma  gaba ɗaya jikinsa ya fara tsuman tashin hankali, dan su a zatonsu Rayyern din ya rasu ne.

Cikin wani irin tashin hankali rauni gigita da kuma kidima.

Riyyam-nsra ya saki wani irin raunataccen kuka, tare da zamewa ya zauna aƙasa ya kife kansa bisa sawun Rayyern,  cikin rauni murya na rawa kuka na danne abinda yake faɗa yake cewa.

“Innallahi wa innailaihi rajiun Mammy mutuwa zata hanani cika miki burinki,

Wayyoooooooo Allah na Mammy na inama kina kusa kizo kiga halin da tsatsonki yake ciki, Mammy wlh shine wlh sune”.

Su Abba kuwa, tsananin tashin hankalin da suke ciki, yasa gaba ɗaya basa iya fahimtar kalaman Riyyam-nsra, asalima basa jin me yake faɗa da kyau.

Sai dai shi kuwa Rayyern da tunaninsa ke kokarin gushewa, a sama sama yake jiyo kukan yaron, da kuma abinda yake faɗi.

Duk da bawai yana fahimtar kalaman sosai bane, amma yaji wasu daga cikin maganganun, wanda ayanzu baya cikin Lfy da kuma hayyacin da zai iya nazari ko hasashen kalaman.

Dr Sulaiman ne ya matso kusa da Riyyam-nsra, ya jawoshi jikinsa ya zaunar dashi tare da cewa.

“Kai Riyyam-nsra kabar kuka bafa rasuwa yayi ba, ciwon ne ya fara lafawa kaga Abbanku ma yayi shiru”.

Sai alokacin Ramadan ya sauke wani irin numfashin daya,  sakar masa da wani nannauyan abu mai kama da dutse daya tsaya a ƙirjinsa.

Sabida gaba ɗaya ya fara rasa numfashin sa.

Shi kuwa Riyyam-nsra cikin kasa danne kukan sa yace.

“Yah Sulaiman, da gaske kake Hamma Rayyern dina, yana numfashi?”.

Kai Dr. Sulaiman ya jinjina, kana cikin sauri yace.

“Eh Riyyam-nsra bai rasuba gashi yana numfashi, nanda y’an mintuna zai tashi insha Allah.”

Ajiyan zuciya suka sauƙe baki ɗayansu.

Sai lokacinne kuma Mamy ta iya tsaida hawayenta.

Yayinda Baba Mauɗo Kuwa sam hawayen shi ya gaza tsayuwa.

Hakan kuwa shi yasa  Jannart ta gaza tsaida hawayenta, saboda acikin rayuwar ta akwai rauni sosai, matukar zata ga hawayen Babba, To Lallai zuciyarta saita karye, ba kuma zata iya lallashin kanta ba.

Ganin duk sun d’an nutsu ne kuma yasa, cikin sanyi Dr. Sulaiman ya samu ya zauna, tare da d’go kansa ahankali yayi gyaran murya kana anutse yace.

“Kwata kwata abun bai wuce 30mnt da fara mishi ba, domin tun da ya fara mishi na fahimta,  saboda naga yana ta haɗa zufa, kasancewar alokacin muna cikin meeting  ne da sauran Doctor’s din mu, 

Akan wani course da muke son wasu daga cikin Doctor’s ɗin namu suje suyi a Mascow, 

So dana fahimci cewa, ciwon cikin nasa nason tashi ne, sai na bukaci da mu tashi taron, amma sai yaki bani dama, to kafin mu gama ma abin har ya fara tsanan ta.”

Idanu duk suka tsurawa Dr. Sulaiman din, saboda Jin abunda yake fad’a.

Shikuwa Dr. Sulaeman gyara zamansa yayi, tare da fuskantarsu, cike da son sake samar musu nutsuwa yace.

“Insha Allah Rayyern zaiji sauk’i, domin muna fita a meeting din nayi masa allura, saidai kafun nan ma tuni abin ya gama tashi,  shiyasa ya ɗan wahal dashi amman Alhamdulillah, bayan 50mn idan alluran ta fara aiki zai dan ji sauƙi, wanda kuma zuwa yanzu inada yakinin, fara aikin allurar Dan shiyasa ma kukaga yayi shiru jikin ya daina bari.”

Cikin gamsuwa Ramadan da Abba suka gyaɗa kai, saboda wannan bayanine da likitocin suka saba yi musu, sudai fatansu shine samun saukin Rayyern din.

Baba Mauɗo dake zaune kuwa, ahankali yasa hannunshi ya shafa kan Rayyern din zuwa wuyansa.

Kana ya miƙe tsaye.

Tare da sharce hawayen sa.

Cikin tausayawa yace.

“Toh Alhamdulillah Allah ya bashi lfy yasa zakkan jikine, Allah ya daga kafadunsa.”

Ya ƙare mgnar yana nufar hanyar fita.

Cikin sauƙe numfashi Riyyam-nsra da Ramadan suka bishi da ido,  da kuma wani kallo mai cike da wani irin so na musamman.

Abba da Mamy kuwa.

Numfashi suka fesar tare da cewa.

“Amin ya Allah baba Mauɗo”.

Shi kuwa Baba Mauɗo yana fita

Hadi da Ari sukayi kanshi, cikin girmamawa da kwarjinin dattijon suka hada baki wurin cewa.

“Allah rene ya jikin nasa?”.

A hankali yace.

“Alhamdulillah jiki da sauƙi.”

“Allah ya kara sauki.”

suka had’a baki wajen fad’a.

Shikuwa Baba Maud’o.

“Amin ya Allah”.

Yace yana mai wucewa cikin ɗan side ɗinsu.

Kai tsaye Bathroom ya wuce al’wala yayi kana yazo.

Ya dauki Kur’ani ya fara karatu wai ko zaiji sanyin zuciyarshi, da wani nauyi daya danne mishi ƙahon zuciyarshi.

Amma ina hakan ya gagara,

Hawaye kuwa tamkar an bude bakin famfo.

Allah ya sani yana jin wani irin azabebben son yaran a zuciyarshi, 

Baya son gani ko jin duk wani abu da zai cutar dasu duk kankantarshi da yanada hali da ko kuda bazata sauka kan Rayyern ba.

Da ya dauka kawai dan kyautata mishi da sukeyi ne,  kuma dan kasan cewarsu yaran uban gidansa.

Toh amman zuwan Riyyam-nsra yasa ya fahimci, kawai yana son duk wani abinda ya shafesu ne.

Wasu lokutan yakanyi tunanin ko dan kamar da Riyyam-nsra din, yakeyi da Rayyern ne yasa yake masifar sonshi ma din.

Hannun shi ya daga sama yana mai yiwa yaran addu’a.

A nan cikin falon kuwa.

Shiru Jannart tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Yayinda hawayenta keta kwaranya ba ƙaƙƙautawa.

Tana ciwo amman bata taɓa ganin irin wannan tashin hankali a fuskar Daddy, kamar yadda ta gani a fuskar Baba Mauɗo da Abba ba.

Bata taɓa ganin makamancin gigitar da Mamy tayi a fuskar Mom ba.

Duk da tasan mom tana masifar sonta.

Wannan kawai ya isa shaidar son uwa da banne a duniya.

Mamy kuwa numfashi take ta saukewa kawai.

Riyyam-nsra kuwa miƙewa yayi ya haura sama.

Yana shiga kuwa ya kira Mammyn sa.

Abba kuwa cikin sauƙe numfashi ya tallabe haba.

Tare da cewa.

“Ramadan dagashi a kanta.

Sai ka gyara mishi kwanciyarsa”.

Cikin sauri Dr Sulaiman yace.

“A’a Abba barshi shida kanshi zai tashi in allurar ta gama ratsashi.”

Cikin sanyi Mamy tace.

“Ai kuma Jannart din zata gaji”.

Kai ya dan juya tare da cewa.

“Bazai dadeba zai tashi”.

Shiru sukayi.

Kana shi kuma Dr. Sulaiman miƙewa tsaye yayi tare da cewa.

“Toh Abba ni bari in wuce gida anjima zan dawo.”

“Toh mun gode Dakta”.

Abba ya faɗa yana mai gyara zamanshi.

Shi kuwa Dr Sulaiman Ramadan ya kalla tare da cewa.

“Kasan idan ya tashi zai tashi ba ƙarfi illar alurar kenan,  shiyasa ba’a cika son yawaita yiwa mutum itaba.

Zaijishi duk ba ƙarfi, so dole sai an taimaka mishi ka sani”.

Kai Ramadan ya jinjina tare da cewa.

“Eh na sani”.

Daga nan ya sallamesu ya tafi.

Su kuwa, shiru sukayi suka zauna jugum-jugum.

Ganin kuma yamma lokacin daura girki yayine, yasa Mamy miƙewa a hankali ta nufi Kitchen.

Bayan ta cire lallenta ne kuma  ta fara aiki.

Ita kuwa Jannart gaba ɗaya ta kasa kwakwaran motsi.

Sabida masifar kunya da nauyin Abba da takeji, kana ga kuma nauyin zaratan namiji dake kanta.

Wanda agaba daya rayuwarta bata taɓa fuskantar makamancin hakan ba ga wani irin masifeffen ƙamshin jikinsa dake narkar da jikinta, tattausan sumar kansa da sajensa ta zuwa idanu.

Yanzu kusan 50 minutes kenan suke a hakan.

Yayinda kuma har yanzu hawayenta ked’an disowa kadan-kadan.

Suna mannewa ajikin gashin idanunta.

Shi kuwa Rayyern dake kwance a hankali ya ɗan ja numfashin wahala tare da fesar dashi.

Kana ya rumtse idanunshi da ƙarfi tare da taune lips ɗinshi, duka biyu saboda so yake ya tashi, amman gaba ɗaya jikinshi daga kugunsa zuwa sawun takawarsa sunyi lakwas.

Wannan abun shiyasa baya son allurar.

Dan muddin akayi mishi ita sai yayi kusan mako guda karfinsa bai dawo dai-dai ba.

Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi.

Dai-dai lokacin kuma Riyyam-nsra shima ya sauko ƙasa.

A tare suka ɗan sunkuyo kanshi, ahankali ya buɗe idanunshi jin muryar Abba nakiran sunansa.

“Rayyern! Rayyern!!”.

Cikin wata iriyar sassanyar murya can ƙasan maƙoshi yace.

“Na’am Abba”.

Jin Rayyern din ya amsa ne kuma, yasa Abba cikin jin daɗi yace.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah!!”

Rayyern kuwa cikin ƙarfin hali da jarunta ya tattaro ragowar kuzarin sa baki ɗaya.

Ya yunƙura alamun zai tashi.

Da sauri Ramadan yasa hannunsa zai tallabeshi.

Cikin sanyin murya yace.

“Barni zan iya”.

Cike da rauni Ramadan yace.

“Hamma Rayyern bazaka iyaba”.

Kar-kar haka jikinsa ke rawa.

Lokacin da ya samu ya juyo ya ɗago kanshi.

Da sauri ya rumtse idanunshi ganin kamar kan Jannart yake.

Haka yasa ya miƙawa Ramadan hannunsa.

Da sauri ya kamoshi kana ya yunƙura ya zauna.

Lokacin Mamy ma ta iso cikin jin daɗi tace.

“Alhamdulillah sannu ko Babana”.

Kanshi ya gyada mata.

Ita kuwa Jannart a hankali ta miƙe tsaye.

Cikin son tsaida hawayenta ta nufi Kitchen.

Tashinta ne yasa Abba matsowa kusa dashi.

Hakama Mamy nanfa sukayi ta mishi sannu.

Ita kuwa Jannart tana shiga Kitchen aikin da Mamy ta fara taci gaba da yinsa.

Su kuwa A falon cikin ƙarfin hali ya maida kansa ya jingina da jikin kujera, kana a hankali ya fara yunƙurin tashi tsaye.

Da sauri Abba ya tallabeshi gefen damanshi.

Kana Riyyam-nsra ya tallabe gefen hagunshi.

Ramadan kuwa da Mamy ido suka zuba musu, sunaga yadda yake taka kafafunsa da suke karkarwa.

A hankali suka fara take steps din da taimakon su Abba ya samu.

Suka haura.

Kai tsaye Bedroom dinsa suka wuce dashi.

Suna shiga suka kwantar dashi.

Sanin kuma allurar zata sashi bacci ne yasa Abba juyawa ya fita.

Shi kuwa Riyyam-nsra gefensa ya zauna.

Yana gyara masa pillow.

Rayyern din kuwa yana kwanciya, lokacin ɗaya bacci ya fara fuzgarshi.

Ramadan ko ganin sun haura sama ne, ya sashi fita kaitsaye kuma  Mai-nasara pharmacy ya nufa, inda yaje ya d’auko magungunan da Rayyern din Kesha Idan ciwon ya tashi.

Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma nan sukaci gaba da aikinsu ita da Jannart. 

Bayan sallan isha’i.

A hankali Jannart ta dan juyo tana kallon kofar babban falon,

daga nan cikin falonta.

Da sauri kuma  ta miƙe jin muryar mutumin nan da taji ana kiransa da Baba Mauɗo yana sallama.

Da alamun kuma babu kowa a main falon.

Da sauri ta mike ta nufo falon.

Baba Mauɗo Kuma tsaye yake bakin ƙofar, ya ɗan turota yana sallama da ɗan buga kofar.

A hankali tace.

“Wa alaikassalam Baba ka shigo mana”.

Dai-dai lokacin kuma Mamy ta fito daga side ɗinsu.

Cikin girmamawa tace.

“A’a Baba Mauɗo ka shigo mana”.

Cikin kamala yace.

“Toh”.

Kana ya shigo.

A hankali Jannart ta dan rusuna tare da cewa.

“Barka da dare Baba”.

Juyawa yayi ya kalleta cikin wani irin mamaki da nazarin fuska da kammanin muryar yarinyar yace.

“Barka dai, Ya mai gidan naki da jikin?”.

Cike da girmamawa tace.

“Alhamdulillah jiki da sauƙi”.

“Masha Allah. Allah ya ƙara mana sauki”.

Ya faɗa yana mai juyowa yana kallon Mamy dake cewa.

“Bismillah mu isa yana sama, Abbansu ma yana can”.

Hakan ne yasa ya nufi saman.

Ita kuwa Mamy juyowa tayi ta kalli Jannart, da idanunta suka dan yi ja cikin kulawa tace.

“Kinyi salla ko?”.

Kai ta gyaɗa mata alaman eh.

Ita kuwa Mamy.

Ba tare da tace mata komaiba ta nufi Dinning area.

Foodflask ta ɗauko wanda tasa mata, 

Abincin da sukayi sakwara ce, da miyar agushi.

Miƙa mata tayi tare da plate da spoon tace.

“Gashi ki zauna kici abinci, ki kuma bar zubda hawayen nan haka kinji ko Mamana”.

Cikin sanyi tace to.

Kana ta amshi kular ta wuce ɗakinta.

Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma tazo ta shiryawa su Ramadan nasu ta kai musu falon sama.

Anan ta samesu.

Baba Mauɗo da Abba Kuma suna cikin dakin Rayyern ɗin.

Ganin har yanzu bacci yakeyi ne, yasa suka fito.

Ita kuwa Jannart ajiye kular tayi a falon.

Ba tare da tayi niyar ciba, ta kwanta a ƙasa bisa carpet din, tana rike da wayarta.

Sam ta rasa me take tunawa, 

saidai kawai ta fahimci cewa yau gidan babu daɗi dan ciwon Rayyern ɗin.

Sabida su Ramadan masu ɗebe mata kewa da Riyyam-nsra mai sata farin ciki duk yau basa da Gud Mood.

Tana nan kwance ahaka har tayi bacci.

A folon kuwa suna fitowa suka samu Dr Sulaiman ya iso.

Nan Abba ya koma dashi ya ɗan ƙara dudduba shi.

Kana ya sallamesu ya tafi.

Haka dai su Ramadan suka tafi dakinsu.

Mamy kuwa falon Jannart ta leƙa ganin tana bacci ne yasa ta wuce side ɗinsu.

Dan tasan yau Abba a dakin Rayyern zai kwana.

Haka 

Hakan kuwa akayi.

Rayyern kuwa baccin yayi mai zurfi sai karfe uku da rabi ya farka.

Abba da kanshi ya hada masa ruwa yayi wonka,

Kana yayi al’wala.

Yana fitowa yayi ramuwar sallan magriba da isha’i,  sannan ya dan sha tea ɗin da Abba ya hada masa da kansa.

Toh kuma daga nan sai idonsa ya ɗan bushe.

Sai da akayi sallan asuba.

Kafin ya koma wani baccin.

Koda Abba suka dawo masallacin sun sameshi yana bacci.

Nan suka fito.

Mamy da Jannart kuwa Kitchen suka shiga dan haɗa breakfast.

Kasan cewar yau ɗin asabar ce ba aiki.

Yasa Riyyam-nsra da Ramadan ma basu tashi da wuriba.

Sai karfe tara suka fito,

d’akin Rayyern suka shiga.

Zaune suka sameshi bisa carpet ya jingina jikinsa da gado.

Mamy da Abba ne zaune agabanshi.

Mamy na haɗa mishi tea.

Abba Kuma da kanshi yake zuba mishi ferfesun jan nama da Jannart tayi mishi yayi laushi tibis.

A hankali ya ɗan juyo ya kalli Radaman dake cewa.

“Hamma ya jikin naka?”.

Cikin sauƙe numfashi yace.

“Alhamdulillah”.

Riyyam-nsra kuwa matsoshi yayi da kyau tare da cewa.

“Hamma Rayyern Mammy ta gaishe ka da jiki.

Zaiton ma tace in gaisheka da jiki”.

Cikin sanyi yace.

“Ngd”.

Ganin kuma alamun bai son surutune.

Yasa suka sauƙo ƙasa.

Abba kuwa cikin kulawa yace.

“Rayyern kaci abincin tunda ɗuminsa kaji”.

Cikin sanyi yace.

“Abba na gaji bazan iya cin nama da sassafen nan ba”.

Da sauri Mamy tace.

“Rayyern yayi laushi sosai fa”.

Cikin narke fuska yace.

“Bani tea ɗin kawai is okay”.

Haka suka hakura suka barshi.

Tea ɗin yasha.

Kana Abba ya kuma hada masa ruwan wonka yayi.

 

Koda ya fito daga wankan, wasu tausassun riga da wondo yasa wanda Abban ya fito masa dasu.

Mamy kuwa tuni ta sauko k’asa,

aƙasan ta samu su Ramadan da Riyyam nsra a dining area suna zaune, Yayinda Jannart ke zuba musu abinci.

Da sauri Mamy tace.

“Kai kun kai abincin su Baba Mauɗo kuwa?”

Kai Riyyam-nsra ya gyaɗa tare da cewa.

“Eh Mamy nakai musu, yanzu ma na dawo”.

“To yayi.” 

Mamyn tace tare da zama gefensu, nan sukayi Karin kumallon.

Wunin ranar dai haka sukayi shi a gida gaba dayansu.

Alhamdulillah kuma  jikin Rayyern da sauki, sai dai rashin karfi da rashin cin abinci, dama kuma da rashin son mgn da bayayi, dama kuma  shi ba gwanin surutu bane, balle kuma yanzu ga halin ciwo.

Washe gari ranar lahadi ma

Haka suka wuni.

Duk da surutun Riyyam-nsra ya rage,

saboda jikin Hamman nasa.

Da yamma kuma Nasir Ahmad yazo ya duba Rayyern din da jiki.

Bayan sun d’an taba hira shida Riyyam nsra ne kuma, yayi musu sallama daga nan kuma gidan Malam Mai-nasara ya wuce.

Nan yake sanar masa abinda ke faruwa…

Jannart kuwa tun ranar tun lokacin kuma bata sake ganinsa ba ko jin muryarsa.

Yayinda Mamy kuwa duk a zatonta Jannart din, duk safiya tana zuwa duba jikin Rayyern din.

Washe gari Ranar Monday Alhamdulillah jikin da sauki sosai, domin karfinsa ma ya ɗan fara dawowa.

Bayan sunyi breakfast ne kuma Ramadan ya tafi asibiti.

Hakan yasa Jannart da kuma Riyyam-nsra, sai kuma Mamy ne ke zaune afalon.

D’ago kai Riyyam nsra din yayi, tare da kallon Jannart dake riƙe da wayarsa, tana kallon comments ɗin followers ɗinsa akan wata wakar fullancin daya bibiya.

 

jin wayar tasa tana ringing ne kuma yasashi kallonta, tare da d’an gyara zamansa yace.

“Aunty Jannart Waye”.

“Mammy ce”.

Ta bashi amsa tana miƙo masa wayar.

Da sauri ya amshi wayar tare da amsa kiran

“Assalamu alaikum yah  Mammy”.

Jim ya ɗanyi na tsawon kusan daƙiƙu 2, kana a hankali ya miƙe tsaye tare da fara haurawa sama yana cewa.

“Afwan Mamma wlh shine baya son surutu, ko wayarsa bai amsa kira, tun ranar nake son hadaku toh ganin baida lfyarne yasa nai shiru”.

Ya ƙare mgnar yana ida hawa saman.

Kai tsaye dakin Rayyern ɗin ya nufa da sallama a bakinsa.

A falon kuwa cike da mamaki Mamy ta bishi da ido.

Zuwa yanzu ta fara tsoron wani al’amarin, to wai ma ya akayi bata taɓa tunanin Riyyam-nsra ya nuna mata hoton Mammansa ba?.

Tayi wannan tunanin.

Jannart kuwa da sauri ta juyo ta kalli wayarta dake gefenta, cikin mamaki ta zubawa wayar ido ganin number dake kiranta…

Shi kuwa Riyyam-nsra a hankali ya isa gaban Rayyern dake zaune bisa kujera.

Yasa system ɗin shi a gaba da alamun aiki zaiyi dan yanzu ya buɗe ta.

Idonshi ya ɗago ya zubawa Riyyam-nsra su.

Shi kuwa Riyyam-nsra cikin karya wuya.

Da rauni ya iso garesa, murya a raunace yace.

“Ayyah Hamma Rayyern, dan Allah ga waya kayi mgna da Mammy na, tun shekaran jiya take cemin in hadaku ta gaidaka da jiki taji muryarka”.

Ya ƙarashe mgnar yana karya wuya.

Ga mamakin Rayyern kuwa sai ga hawaye na zubowa a fuskar yaron.

Shi kuwa Riyyam-nsra cikin yin rau-rau da ido.

Ya miƙa masa wayar tare da cewa.

“Dan Allah Hamma Rayyern kada kace a’a”.

Ya rigada ya gama karya mishi zuciya da hawayensa.

Duk da ko mgnar yayi sai yaji ya gaji shiyasa baya son yawan mgn.

A hankali yasa hannunshin ya amshi wayar.

Cikin nitsuwa ya manna wayar a kunneshi tare dasa kafaɗarsa ya makale wayar.

Murya a sanyaye yace.

“Assalamu alaikum”.

A can ƙasar Ethiopia kuwa.

Wani irin lumshe ido Mamma tayi, tare da jan wani irin dogon numfashi, kana cikin tsananin harbawar da zuciyarta keyi tace.

“Wa alaikassalam Mauɗo am!!!”.

Wani irin rumtse idanu Rayyern yayi da azaban ƙarfi tare dasa hannunshi y…!

Ya dafe ƙahon zuciyarshi sabida wani irin masifeffen harbawa da yaji tayi  da azaban ƙarfi.

“Yah salam”.

Shine abinda ya iya fada cikin zuciyarsa.

Yayinda Riyyam-nsra kuwa ya zauna a  kasa, a gabanshi tare dasa hannunshi duka biyu ya tallabe Fuskarsa, kana ya zubawa Rayyern ɗin idanu kamar mai kallon madubi ko TV.

Shi kuwa Rayyern wani irin sakewa yaji jijiyoyin kanshi zuwa zuciyarsa sunayi.

Suna bada sautin

Ras-ras, yayinda duk kofofin gargasar jikinsa suka fara amsa amon muryar baiwar Allah nan.

Yayinda can wurin Mammy ma haka abin yake.

Dan Tuni ita wasu hawaye na ke tsiyayo mata, Yayinda takejin zuciyarta nayi mata ani irin duka.

Cikin rumtse idanunta tace.

“Maudo ya jikin naka?”.

Idanunsa ya dan lumshe, cikin kuma jin wani sabon bugun zuciya yace.

“Mammmmmy jiki da sauƙi Alhamdulillah.”

Riyyam nsra kuwa dake gefe, wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo, daga cikin idanunsa, wanda sukafi kama da hawayen farin ciki.

Yayinda shikuwa Rayyern meda kanshi yayi ya jingine,  jikin kujerar yana mai amsar saƙon da jijiyoyin jikinsa suke bashi.

Cikin kasala kuma ya motsa lips ɗinsa tare da cewa.

“Amin Mammy.”

Ya fad’i hakanne kuma saboda, addu’ar da Mammyn tayi masa. 

Mammy kuwa Idanunta ta lumshe, cikin kuma danne abunda takeji, yayi tsaye acikin zuciyarta, ta soma yi mishi addu’an samun lafiya, tare da sa mishi al’barka. 

Sai kuma ta daura da cewa.

“Ina Ramadan?”

Cikin sauƙe numfashi Rayyern din yace.

“Ya tafi wurin aiki”.

Daga can b’angaren Mammy kuwa Kai ta jinjina, tare da soma tambayan shi, akan sauran ahlin gidan nasu.

Shikuwa Rayyern duk yanda yakejin, mood d’insa na sanjawa, amma anutse yake amsa mata, kana kuma 

Cikin girmamawa.

Kamar da wasa kuwa, shida Mammyn saida sukayi mgnar mituna shida kana sukayi sallama.

Bayan ya zare wayar akan kunnensa ne kuma, ya mikawa Riyyam nsra.

Cikin sauri kuwa Riyyam ya karb’i wayan, tare da mikewa tsaye, direct ya koma dakin Ramadan.

Ganin fitan Riyyam dinne kuma yasa, Rayyern jingine kansa da jikin kujera, tare da rumtse idanunshi.

Asanyaye kuma cikin tausasshiyar muryarsa, yake fad’in. 

“Yah ilahi ya mujibadda’awati.

Ya salam”.

Sune abunda yake fad’a yana mejin

tamkar kanshi zai juye, abubuwa da yawa keyi masa yawo acikin tunanin sa.

“Maudona!!” 

Ya maimaita kalmar da yaji ya tsaya mai arai, dan sai yakejin tamkar ya tab’a jinta.

Idanunshi ya buɗe kana a hankali yace.

“Toh ko dai Baba Mauɗon da nake jine yasa naji kamar nasan kalmar ada can baya?”

Saurin girgiza kanshi yayi, tare dasa hakwaransa ya cije lips d’insa.

Take kuma ya fad’a dogon nazari, wanda hakan yasa ya gaza ci gaba da aikin da yake son yin.

A can falon kuwa, cike da mamaki Jannart ta zubawa wayarta ta ido 

Taki amsawa.

“Jannart ba kiranki akeyi ba ki amsa mana”.

Mamy ta fada tana kallonta cikin kulawa.

Jannart din kuwa cikin yanayin nazari tace.

“Mamy number’n ba suna, ban san waye bane”.

Ta ida mgnar tana jawo wayar jin da tayi sako ya shigo mata.

“Toh ki amsa mana ai zakiji waye ne”.

Cewar  Mamy.

Jannart din kuwa kai ta ɗago daga duba sakon tare da cewa.

“Lah ashe ma Aunty Dijat ce”.

Ganin kiran ya kuma shigowa ne yasa ta amsa kiran.

Tare da kara wayar a kunne.

Da sauri tace.

“Abba kaine”.

Gyara zama Barrister Kabir yayi tare da cewa.

“Eh nine dai Jannart, na fahimci.

Daddynki yana iya zargar wayata da bin diddiginta ne, yasa na kiraki da wayan Khadija.”

Cikin gamsuwa tace.

“Ayyah Daddy na”.

Miƙewa Mamy tayi ta bar wurin.

Sabida ta barta ta ɗan sake.

Ta sake din kuwa ganin Mamyn ta tafi cikin nitsuwa tace.

“Abba ya lbrin su Daddyn ya Mom tayi, ina Yah Azeez na?”.

Da sauri yace.

“Me ruwanki dasu”.

Shiru tayi cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi falon ta.

shi kuwa Barrister Kabir cikin kulawa yace.

“Kina lfy ko”.

“Lfy lau Alhamdulillah Abba”.

Ta bashi amsa tana zama.

“Gaba ɗaya jiya ke nai ta tunawa da sanyin nan, ki kula da kanki sosai kin san irin wannan sanyin ƙarshen hunturun yafi miki illa da tada ciwonki, kiyaye shan ruwan sanyi da AC, sannan kike rufe Windows ɗinki duka sabida hazo kinji ko?”.

Cikin nitsuwa tace.

“Toh Abba”.

Juyowa yayi ya kalli Dijat dake ta son ya Bata wayar suyi magana da Jannart din, kauda kanshi yayi daga kallonta tare da cewa.

“Gidan naku duk lfy ko?”.

Gyara labulen window dake kusa da ita tayi kana a hankali tace.

“Uhumm shine dai baida lfy, tun ran jumma’a, wai ciwon cikinsa ya tashi, sai ka gani Abba kamar zai mutu fa”.

Ta k’are maganan cikin dan nuna tausayawa.

Abba Kabir kuwa da sauri yace.

“Subahanallah Rayyern din?”.

Kai ta gyaɗa kamar tana gabanshi.

Sai kuma ta daura da cewa.

“Eh Mamynsa nata kuka da Baba Mauɗo”.

“Innalillahi Jannart meyasa baki gaya min ba”.

Cikin sanyi tace.

“Abba na manta ne”.

Cikin faɗa yace.

“Jannart ki mance ciwo da lfyar mijinki? Kada ki sake yin haka kul kinji ko?”.

Cikin biyayya tace.

“Toh Abba”

Barrister Kabir din kuwa dan gyara zamansa yayi, tare da cewa.

“In sha Allah da yamma zan zo, akwai wani abu da kike buk’ata ne?”

Kai Jannart din ta jinjina, kana cikin sanyin murya tace.

“A’a Abba babu abunda nake buk’ata.”

“To shikenan sai nazo.”

Daga haka sukayi sallama.

Bayan ya katse wayarne kuma ta mik’e, tare da fitowa waje suka shiga Kitchen da Mamy.

Da yamma misalin ƙarfe biyar da da rabi na yamma.

Abba da Barrister Kabir din Suka shigo a jere.

Kasancewar shigowar Barrister’n ya samu Abban a wurin Baba Mauɗo ne.

Ganinsu ne kuma yasa, Mamy yin murmushi, fuska asake tace.

“Sannu da zuwa Barrister”.

Shidin ma Barrister Kabir din murmushi yayi, kana cikin mutuntaka yace.

“Yauwa sannu Hajiya, fatan na sameku lafiya ya mai jiki?”

“Lafiya k’alau Barrister, jiki kuma Alhamdulillah dan yana ta samun sauki, ya iyalai?”

“Masha Allah Iyalai Alhamdulillah.”

Ya fad’a adaidai lokacin da yake zama akan kujera.

Yayinda ita kuwa Mamy juyawa tayi kaitsaye ta nufi, d’akin Jannart tana cewa.

“Jannart ga Abbanki yazo”.

Jin abunda Mamyn ke fad’ane yasa Jannart dake zaune, saurin mikewa tsaye tare da nufo falon tana gyara mayafin doguwar rigar jikinta.

Murmushi Mamy tayi tare da juyowa.

Ta nufi falon ita kuwa ta rufa mata baya.

Suna fitowa ta nufi kusa da Abban tana murmushi.

“Abba sannu da zuwa”.

Tace tana zama agefenshi.

Yayinda ta hango Abban Rayyern kuma yana haurawa sama.

Mamy kuwa Dinning area ta nufa.

Goran Ruwan sanyi dana Nutri milk tasa a ɗan ma dai-dai-cin tray da cup, kana Akan santer table ɗin dake gabanshi, ta ajiye tray tare da zama bisa kujera.

“Sannu Barrister Bismillah ga ruwa”.

Ta faɗa cikin kulawa.

“To nagode.”

Barrister Kabir ya amsa.

Tare da daukan ruwan ya d’ansha kadan.

Jiyo alamun ana sauƙowa ne kuma, yasa Mamy maida kallonta ga stairs din.

Ganin kuma Rayyern ne yake takowa a hankali, yana sanye da wata tattausar jallabiya baƙa mai masifar sheƙi.

Irin mai guntun hannu ne jallabiyar,

gabanta kuma ta sama ank’awatasa da aninaye. 

Abba na biye dashi a baya.

Sosai ya ɗan rame duk da jallabiya ce a jikinsa, kuwa amma ramarsa ta ɗan fito, sai wani irin fari da yayi yayinda sajenshi yake ɗan hargitse.

Cikin jin daɗi Mamy tace.

“Alhamdullahi lallai yau kam jiki da sauƙi, tunda har Babana zai sauƙo ƙasa.”

Jin hakane yasa Barrister Kabir juyowa, ya kalli gefen damanshi ganin Rayyern ne, da yadda yake tafiya a kasalance alamun ba isashen ƙarfi ajikinsa ya sashi cewa.

“Ayyah Alhaji da ka barshi ai, Idan yaso ni saina haura in ganshi, gaskiya yaji jiki”.

Dai-dai lokacin kuma suka iso kan steps ɗin ƙarshe.

Cikin yanayin gajiya da maida nufashi ya zame, ya zauna kan step na biyu tare da jingina kansa, da jikin ƙarafunan gefe da gefen steps din, cikin lumshe ido yace.

“Abba na gaji.”

Ya ƙare mgnar yana kallon tsakiyar falon.

Ita kuwa Jannart jin muryarsa ne, da kuma abinda Mamy da Abbanta suka fadane, yasa ta ɗago kanta tare da ware manyan idanunta,ta kalli hanyar sauƙowan.

Wanda yanzu kusan satinta uku a gidan, amman bata taɓa zuwa ko kusa da wurinba.

Ido cikin ido sukayi dashi,

Wanda hakan yasa tayi maza tayi ƙasa da kanta.

Tare da lumshe idanunta tabbas ya rame sosai fuskarshi tayi wani irin haske.

Sajenshi ya hargitse kaɗan alamun babu isasshen ƙarfin jiki da nitsuwar lfya.

Dib-dab-dib-dab haka taji bugun zuciyarta na harbawa.

Shi kuwa Rayyern fuskarshi ya tsuke tare dayin mgnar zuci.

“Eh dole mana a Barka ka haura sama, tunda gaka ubana, kasan da ka gani ka karanta duk bai isheka ba ai, sai kaga makwancina”.

Mtswwww yaja ɗan gajeren tsaki cikin bakinsa.

Mamy kuwa cikin jin daɗi tace.

“Sannu ko Babana.”

Kai ya gyaɗa mata cikin sanyin jiki.

Abba kuwa gefenshi ya ɗan ratsa tare da cewa.

“Toh huta sai ka ƙaraso ko”.

Kai ya kuma gyaɗawa.

Barrister Kabir kuwa gyara zamansa yayi tare da cewa.

“Rayyern ya jikin naka?”.

Da sauri yace.

“Alhamdulillahi ni nama worke.”

Murmushi Barrister yayi domin ya gane cewar.

Har yanzu Dr.Rayyern bai yarda dashi ba, asalima zarginsa yakeyi.

Cikin kulawa yace.

“Masha Allah. Haka ake so.

Allah ya ƙara lfy da karfin jiki.”

A takaice yace.

“Amin.”

Shi kuwa Abban Rayyern da Mamy cikin jin daɗi sukace.

“Amin Amin Barrister mun gode matuƙa, Allah ya bar zumunci.”

Amin yace yana mai kallon Jannart data sunkuyar da kanta ƙasa, tana wasa da wayar hannun ta.

Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.

“Toh Alhaji bari in wuce gida, Allah ya ƙara sauƙi.”

Miƙewa shima Abban yayi tare da cewa.

“Amin Amin Barrister mun gode sosai”

Daga nan suka fita tare.

Suna fita itama Jannart ta miƙe ta nufi ɗakinta.

Da wani irin masifeffen kallo Rayyern ya bita dashi, kallon da yafi kama da harara.

Mamy kuwa shi ɗin ta zubawa ido, Jin ana kallonsa ne kuma, yasa ya ɗan juyo ya kalli Mamy ganin yadda ta tsareshi da ido ne, yasashi kwaɓe fuskarsa tare da miƙewa ya dawo kan doguwar kujera.

A hankali ya kwanta tare da ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya kana

Yace.

“Mamy Riyyim fa?”

 Numfashi ta sauke tare da cewa.

“Ya tafi yi mana cefene shida Hadi.”

Kai ya gyaɗa tare da fuskantar TV.

Ita kuwa Jannart tana shiga part dinta.

Wonka tayi tare da al’wala kana ta fito dan magriba ta gabato.

A falon kuma a tare Ramadan da Riyyam-nsra da Abba suka shigo.

Gaba ɗayansu riƙe da manyan ledodi.

Kitchen suka wuce.

Kasan cewar kayan miyane.

Yasa duk suka diresu nan.

Kana duk suka je sukayi al’wala.

Shi kuwa Rayyern dama ya koma ɗakinsa dan yin wonka.

Bazai iya zuwa masallaci ba, dan d’an haurowan da yayi duk jikinsa rawa yakeyi.

Haka yasa yayi salla a ɗakinsa.

Su kuma suka wuce masallacin.

Basu dawoba saida sukayi isha’i.

A haka dai Rayyern yayi jinyar ɗan motsawa kaɗan da ciwon cikinsa yayi.

Cikin ikon Allah cikin mako ɗaya ya samu lfy, sosai yanzu ƙarfin jikinsa ya dawo.

Yau Monday har asibiti yaje sai dai sam bakinsa ba daɗi shi yasa bai iya cin abinci.

Jannart kuma bata wani ganinsa bare wata mgn ta haɗa su.

A can sashin Alhaji idi Saleh Dakata kuwa.

Duk yadda Barrister Kabir ya zaci takun yayan nasa ya wuce zatonsa.

Hakan yasa ya tsananta matakan irin bi diddigi.

Da taimakon Baba Ado da Ashiru.

Duk yadda yaso gano ainihin zuciyar yayan nashi ya gaza ganewa.

Yah Azeez kuwa sosai ya shiga tashin hankali.

Wanda saida yayi jinyar ciwon da tashin hankalin yasakar masa.

Mom da Abdul kuwa gaba ɗaya gidan ya juye musu.

Domin abun ya musu yawa, ga Daddy da hawanjininsa ke yawan tashi, bini-bini ciwon kai an tafi asibiti.

A can tashar Arewa 24 TV kuwa.

Gaba ɗaya Aisha Lawal da Aunty Fauziyya D Sulaiman da Hajia Rabi’ah, dama sauran ma’aikatan hankalinsu yayi matuƙar tashi, da jin labarin ɓacewar Jannart.

Musamman Salman da gaba ɗaya ya gigice ya ɗimauce.

Dan abun ya daki zuciyarsa sosai, hakan yasa ko aiki yanzu ya dena zuwa, dan shi a zatonsa akan shirinsu aka sace ta sai yake gani shine next target din masatan.

Ganin tashin hankalin da yake cikine kuma yasa.

MD neman Barrister Kabir yayi mishi bayani.

Dole yazo har gidansu shida MD.

Nan sukayi mishi duk bayanin abinda ke faruwa.

Toh Alhamdulillah ya samu nitsuwa sai dai kuma ya shiga ruɗani.

Nan MD ya gyara zamanshi tare da cewa.

“Yanzu dai sai ka kwantar da hankalin ka.

Ka fara zuwa aiki”.

Da sauri yace.

“Toh Ni da waye zamuyi aikin?”.

Cikin sauƙe numfashi MD yace.

“Yanzu zamu bawa Asiya riƙon kwaryar shirin zuwa, lokacin da komai zai dai-dai-ta.”

Cikin tarin ruɗani yace.

“Toh ita Jannart fa?”

Da sauri Barrister Kabir yace.

“Kada ka damu da mgnar Jannart komai zai dai-dai-ta da izinin ubangiji.”

A hankali yace.

“Toh Allah ya yarda.”

Amin Amin sukace kana suka sallameshi suka tafi.

A gajiye ya dawo cikin gidan.

Ko yanzun fitowarsa kenan daga cikin mota, Yayinda  Usman PA ke riƙe da marfin motar.

Cikin kulawa yace.

“Sannu”.

Kanshi kawai ya gyaɗa kana ya raɓa ta gefen Usman ya wuce.

Shi kuwa Usman binshi a baya yayi, riƙe da jakar laptop dinsa da ɗaya wayarsa, sai wasu files dake hannunsa.

A hankali ya kalli Baba Mauɗo  dake yi masa ya jiki, fuska ya ɗan sake tare da cewa.

“Jiki da sauki Baba Mauɗo”.

“Masha Allah. Allah ya ƙara sauki”.

“Amin Amin.”

yace tare da wucewa.

PA na biye dashi a baya.

“Wa alaikassalam”.

Mamy tace lokacin da suka shigo tare da sallama a bakinsu.

“Masha Allah Babana sannu da dawowa ya Office”.

Mamyn ta Kuma faɗa.

Shikuwa Rayyern numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.

“ALHAMDULILLAH Mamy”.

Juyowa tayi ta kalli PA dake gaidata tare da, ajiye kayan uban gidan nasa agefenta.

“Lfy lau Usman ya Umma da jiki”.

Mamyn ta amsa masa tana d’an murmushi. 

“Jiki da sauƙi, tace ma in gaidaki”.

Ya faɗa yana kallon Rayyern ɗin daya nufi Dinning area.

Kai ya ɗan juyo tare da cewa.

“Riyyam fa, nasan Ramadan kam mun barshi a asibiti”.

“Riyyam yana sama yanayi musu gyare-gyare.”

Murmushi Usman yayi tare da cewa.

“Toh wai sai yaushe zai koma ne, yanzu fa yafi wata ɗaya da zuwa har ya shiga na biyu, kuma banga yana wani aikinba.”

Da sauri ya kalli Riyyam-nsra dake saukowa yana cewa.

“Toh P.A ko dai korata zakayi ne, wai dan Allah ma me na tare maka ne, nafa gane tun a jirgi ba sona kakeyi ba, to yawo nazo ko kana da mgna?”.

Ya ida mgnar yana turo baki.

Dariya sosai PA yayi domin dama akwai yar tsama tsakaninsu cikin dariya yace.

“A’a ni kuma in koreka, to a kaina kake ne?”

Cikin taɓe bakinsa da salon ƴan samarin TIKTOK da sukafi kama dana ƴan daudu yace.

“Toh waya sani”.

Murmushi Usman ya kumayi tare da cewa.

“Mamy ni bari in wuce gida”.

“Toh ka gaida Umma ko Usman”.

“In Sha Allah zataji”

Ya bata amsa.

Har yaje bakin ƙofar fita kuma ya juyo tare da cewa Riyyam-nsra.

“Nest week fa zamu wuce China, dan haka ka shirya mu sauƙeka a ƙasarku.”

Ya ƙare mgnar cikin tsokana.

Shi kuwa Riyyam-nsra murmushi yayi tare da cewa.

“Ayyah to dan Allah ka bari in zamewa Hamma Rayyern PA’nsa mu tafi tare”.

Dariya Usman yayi kana ya juya ya fita.

Shi dai Dr Rayyern bai kulasu bama,

Shi kuwa Riyyam-nsra System ɗin da wayar ya ɗauka ya koma sama dasu.

Mamy kuwa shiru tayi ta kasa kunneta can kitchine, dan tasan Jannart na ciki taga kuma Rayyern ya nufi can.

A hankali ya sako ƙafarsa ka step ɗin Dinning area.

Ƙamshin da yake jin ya ɗan shaƙa.

Ba tare da tunanin komai ba ya kutsa kai cikin Kitchen din.

Ita kuwa Jannart dake tsaye miyar taushe da man shanu take haɗawa, Yayinda tamaida gaba d’aya nutsuwarta, ga aikin da takeyi din, wanda hakan yasa ita sam bata ma lura da shiba.

Shi kuwa Rayyern yana shigowa cikin kitchine din, idanunsa suka sauk’a akan bayanta.

Wanda dogon gashin kanta ya sauk’o har tsakiyan gadon bayan ta, kasancewar kuma turkish gown ne ajikinta, shiyasa tayi kyau sosai yaudin, duk wani kuruciya da yarintar ta, I mean innocent dinta ya bayyana. 

Kallo d’aya yayi mata ya d’auke kansa, tare da tab’e bakinsa, batare kuma da ya aiwatar da abunda ya shigo dashi cikin kitchine dinba, ya juya  tare da ficewa, Kai tsaye ya nufi falon Abbansa.

Da sallama a bakinsa ya shiga.

Gefen Abban nasa ya zauna.

Bayan sun gaisane kuma ya ɗan gyara zamanshi, kana cikin nitsuwa yace.

“Abba batun tafiya ta China fa na gama komai, Insha Allah Ranar Monday mai zuwa zamu tafi.”

Cikin zuba mishi ido Abba yace.

“Rayyern baza’a bariba kuma, sai ka kara samun lfyar jikinka?”

Dan guntun murmushi Rayyern din yayi tare da gyara zamansa yace.

“Abba ba komai nayi sauki ai zan iya zuwa, kaga in mun je ɗin ma ba dadewa zamuyi ba, dududu bazan fi kwana ashirin ba zuwa da biyar zan dawo”.

D’an jim Abban yayi, kana cikin shakka yace.

“Kai gsky ni dai ban gamsuba.”

Da sauri yace.

“In sha Allah Abba ba komai fa, zanje lafiya nadawo lafiya.”

Kai Abban ya ɗan jinjina tare da cewa.

“Kayi shirin tafiyar ne?”

Da sauri yace.

“Ai na gama komai ma, nida Usman zamu je.”

Akaro na barkatai Abban ya sauke numfashi tare da cewa.

“Toh Allah ya kaimu, ya kuma bada sa’a.”

“Amin Amin.” yace.

Jin an fara kiran sallan magriba ne kuma, yasa duk suka mike sukayo al’wala suka wuce masallaci.

Yau jumma’a. Bayan an taso sallan jumma’a ne, kuma suna zazzaune a falon  suna cin abinci.

Dan duk basu ci abincin rana ba.

Sabida gudun kada su makara.

A nitse ya turo ƙofar falon ya shigo.

Tare da sallama a saman lips ɗinshi, yayinda Usman PA kuwa, ke biye dashi a baya.

Riyyam-nsra ne ya fara mgn ba tare da ya haɗiye danwaken da yasa a bakinshi ba yace.

“Hamma Rayyern Mammy tace in gaisheka da jiki.”

Cikin alamun gajiya da ɗan yunwa ya gyaɗa kai.

Yana mai kallon Mamy da Usman da suke gaisawa.

Kana Mamy na sawa Usman din danwaken a plate.

Shi kuwa Usman kanshi ya ɗan juyo ya kalli Jannart dake bare dafeffen kwai.

“Hajia Barka da yamma.”

k’asa ta d’anyi da kanta, batare kuma da ta d’ago ta kalleshi ba, cikin mutumtawa tace.

“Barka dai PA ya gida.”

Tayi maganan tana bare kwan tana sawa a plate din da Mamyn ta turo mata.

Kana ta miƙa mishi.

Ramadan kuwa baki ya ɗan bude tare da ɗan yin shishitan yaji yace.

“Kai yajin nada zafi my Aunty ƙara min salat da tumatur  da kwai ɗin zai ɗan kashe yajin.”

Ya ƙare mgnar yana turo mata plate din,  murmurshi tayi tare da cewa.

“Toh sha ruwa kafin nan”.

Ba musu ya ɗauki cup din ruwa dan suna masifar tsoron yaji.

Riyyam-nsra kuwa sai ci yake yana tande baki kamar ɓera a gari.

Shi kuwa Rayyern a hankali ya ɗan muskuta tare da kwaɓe fuska.

Ido Mamy ta zuba mishi.

A hankali yasa hannunshin ya shafa cikinsa kana yace.

“Yunwa.”

Yayi mgnar can ƙasan makoshin sa.

Kai ta jinjina tare da jawo plate alamun zata zuba mishi.

Da sauri ya jujjuya kanshi tare da nuna mata Ramadan daketa shishitan.

“Abu sai kace cimar Mayu,mutun yanaci yana gigicewa.

Ai ni in nasa wannan a bakina suma zanyi Mamy.”

Yayi mgnar yana miƙewa tsaye.

Murmushi Mamy tayi.

Ita kuwa Jannart lips ɗinta duka biyu ta haɗe ta ciza.

Saboda yayi mgnar da ƙarfi kuma da gayya.

hakan yasa acikin ranta tace.

“Uhum ni dai ba mayya bace ato.”

Shi kuwa fara haurawa sama yayi tare da cewa Mamy.

“Please Mamy abu mai ɗan ruwa-ruwa.”

Ba tare da ta kulashi ba.

Ta kalli Jannart tare da cewa.

“Kici mana Jannart.”

Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.

“Na koshi Mamy sai anjima.”

Juyowa sukayi suka kalli ƙofar ɗakin.

Jin ana bubbugawa.

Da sauri Riyyam-nsra dake ta hanyar kofar ya mike tare da zuwa ya buɗe.

Fahad ne telan Mamy da ta bawa kayan Jannart.

Cikin sauri Riyyam-nsra yasa hannunsa ya amsar masa jaka ɗaya tare da cewa.

“Bismilla shigo ciki, Mamy Fahad ne.”

Yayi mgnar yana shigowa Fahad na biye dashi a baya, yana dariya tare da rufe ido.

Da sauri Mamy ta juyo tana kallon Fahad tare da cewa.

“A Allah mai iko al’ƙawarin tela bai zuwa masallaci, nanfa ace min mako, biyu, har zance yayi yawa ma, amma nai shiru sai gashi kuma sai yau ka bullo.”

Dariya mai sauti Fahad din yayi tare da ajiye jakar hannunshi.

Kusa da inda Riyyam-nsra ya aje na hannunsa.

Kanshi ya ɗan shafa tare da zama gabanta kana anutse yace.

“Wlh akasi aka samu zazzaɓi ne ya…”

Da sauri Ramadan ya katseshi da cewa.

“Dan Allah kada ka daurawa kanka ciwo Fahad kai dai kawai kayi shiru.”

Dariya yayi tare da cewa.

“Toh Hajia buɗesu ki ganima zaki sha, mamakin kyansu da tsarinsu.”

Murmushi Mamyn tayi tare da cewa.

“Toh Jannart tattare plates din nan.”

Murmushi Jannart din tayi tare da fara tattare wurin.

Ita kuwa Mamy Fahad din ta zu bawa danwaken tare da sa mishi duk kayan haɗi.

Gyaran zamanshi yayi tare da fara ci.

Yayinda Jannart kuwa  ta gyara wurin.

Riyyam-nsra kuwa kayan ya fara jawowa da sauri Fahad yace.

“A kai malam dakata ya kake figosu haka? a dinke a goge suke da ko wanne yana haɗe da ɗan uwansa cikin leda.”

Ya ƙare mgnar yana matsar da plate din gabanshi ya matso.

Kana ya fara fito dasu daya bayan daya saida ya fiddasu kab, kala ashirin da biyar.

Shadda biyar lace biyar atampa biyar material biyar shadda lace biyar.

A hankali ya fara ware ɗinkin wata shadda pink color, wacce akayiwa ɗinkin fent wok mai masifar kyau dan doguwar rigace.

“Masha Allah gsky ɗinki yayi kyau”.

mamy ta faɗa tana kallon rigar atamfar da ya kuma warewa.

Irin ɗin kin nanne na duwatsun shuwariski masu masifar kyau da akabi da kelleyen kolliyar.

Kasan cewar atampar koriyace sosai take daukar ido.

Medata yayi ya ninke tare da jawo wani shadda lace, mai azabar kyau pink and purple mai ɗan karen tsada.

Sai wani lace ya kuma fiddasa kalan yellow and orange, anyi masa ɗinkin gariyar mata mai masifar kyau.

Ita kanta Jannart kai ta jinjina dan ta gamsu da kalar kayyakin, da zafafan ɗinkuna na zamanin da suka samu.

Cikin jin daɗi Mamy tace.

“Kai sannu da aiki Fahad na huce, dan gaskiya kamana dinki mai kyau, ninkesu kawai medasu leda, dama 

nasan ɗinkinka ai babu haifi”.

Murmushi yayi cikin jin daɗi kana ya medasu cikin leda.

Tare da ci gaba da cin danwaken.

Cikin jin daɗi Jannart tace.

“Gsky ɗinkuna sunyi kyau.

Allah ya saka da al’khairi Mamy.”

Amin Amin tace tare da kallon Riyyam-nsra tace.

“Yauwa ɗauki kayan kai matasu Bedroom in ta shigo sai ta kimtsasu.”

Da sauri yace.

“To.”

Kana ya fara jidansu.

Ita kuwa Mamy cikin kula tace.

“Nawane sauran kuɗinka Fahad?”

Gyara zama Fahad din yayi, tare da jinjina kansa yace.

“Ba ranan Hadi ya kai min 70k ba da fari kuma kin bani 50k 

Yanzu saura 30k kenan Hajjajo.”

Cikin dariya Mamy tace.

“A’a fa Fahad kuke jin tausayin mutane mana kana nufin dubu dari da hamsin kenan a ɗinki kala ashirin da biyar.”

Da sauri yace.

“Allah ko Hajjajo ɗan ma kece kuma nasan ba adawo dasu da wuriba.”

Kai ta jinjina tare da cewa.

“Toh ba matsala Ramadan yi mishi transfer.”

Cikin sauran ɗan shishitan yace to.

Kana shi kuma Fahad ya fara gaya mishi ac no dinsa.

Haka dai yayi mishi send 30k din kana yaci yayi haniƙan kafin ya sallamesu ya tafi.

Usman ma tare suka fita.

Shi kuwa Ramadan anan ya miƙa sai bacci.

Mamy kuwa cikin alamun baccin itama tace.

“Yauwa Jannart jeki kimtsa kayanki.

Sai kizo ki samawa mijinki wani ɗan abu mai sauƙi.” 

Kai ta jinnina kana ta miƙe.

Riyyam-nsra na cewa.

“Yauwa kiyi ki fito my Aunty zan tayaki.”

To tace kana ta wuce daki.

Itama Mamy dakin ta wuce.

Shi kuwa Riyyam-nsra nan ya zauna tare da fara sana’ar tasa.

Bayan ta gama kimtsa kayan nata kab da shiryasu cin drawer ne.

Ta fito a falon ta samu Riyyam-nsra.

Cikin alamun gajiya itama tace.

“Muje mu dama masa kunu.”

Tayi mgnar tana gaba.

A ranta kuwa tana cewa.

“Mutumin da ba’ayin masa gwaninta, zanyi mgninka ne kunu zan dama maka, idan kaga dama kasha in kaga dama ka bari cikinka ko nawa.”

Shi kuwa Riyyam-nsra yana biye da ita, har cikin store.

Shinkafa danya ta ɗiba gongoni biyu.

Ta miƙa mishi tare da cewa.

“Yauwa wonke wannan ka jiƙa min shi”.

Toh yace tare da amsa.

Manyan Robobin dake jere a wurin ta ɗan fara budewa.

Tana buɗe na forko ta samu tankadedden garin kunune, da alama ya dade ɗan har ya fara yin zare-zare.

Tana buɗe na biyu kuma ta samu markadedden gyada ne mai kyau, sai nason mai yakeyi.

Cikin jin daɗi tace.

“Lah markadedden gyaɗa ai ban saniba,In sha Allah kwannan zan mana miyar kase zan matse man inyi tunkuza.”

A roba ta ukune kuma ta samu barerren ɗanyen gyaɗa, ɗan ƙasa irin jajayen nan.

Ɗan ɗago kanta tayi ta ɗauki roba, gyad’an a diba gongoni huɗu.

Kana ta fito cikin Kitchen din, inda ta samu Riyyam-nsra tsaye ya wonke shinkafar ya jiƙata.

Sa gyadan tayi a tray’n roba ta bushesa tare da tsince duk wani ɗan daɗi.

Kana tasa ruwa ta wonkesu.

Sannan ta haɗesa da shinka fan.

Kujerar ɗan table ɗin dake tsakiyar Kitchen din Riyyam-nsra yaja ya zauna.

Ita kuma store ta koma, ta ɗan dudduba tsamiya, saidai kuma bata samuba.

Da sauri ta fito kitchine ɗin.

Fridge ta bude ɗan tuno akwai lemun tsami.

Guda biyar ta dauko manya, ta miƙawa Riyyam-nsra tare da cewa.

“Yauwa ga wannan matse min ruwansu.”

Aje wayarsa yayi tare da cewa.

“Toh bani cup.”

Miƙa mishi cup da wukawa tayi,

kana ta koma gaban Fridge din.

Kwakwa kwaya biyu da dabino ta ɗebo, mai ɗan yawa sai citta kwaya biyu rak, sai kanamfari cokali ɗaya,

tazo ta baresu tare da cire kwallayen dabinon da bawan kwakwan.

Kana ta watsasu cikin shinkafar da gyaɗan data jika.

Blender ta ɗauko tare da lallatsashi.

Kana tazo ta zuba kayan haɗin duka da yake kofin blender’n, babbane ruwa ta ɗan tarfa ciki,

rufewa tayi tare da kunnawa, ta markadeshi  lukui.

Bayan tagama ne kuma ta ɗauko tukunya number uku.

Ta lallaye sannan ta dauki rariyar tatan koko.

Shina ta lalleyeshi.

Kana ta juye cikin tare dasa ruwa ta lallaye kofin blendern mai dan yawa ta lallaye ta meda shi wurin zamanshi.

Ta tace markaden.

Yayi wani irin fari tas tamkar madaran shanu.

Gas din ta kunna kana ta ɗan rage ruwan kunun a kofi, sannan ta ɗaura kan wuta, tare da dauko ɗan ƙaramin muciyarsu.

Ta matso kusa tasa cikin tukunyar, tana ɗan motsashi a hankali wutan naci, tana nan tsaye tana gaurayashi kuwa har ya fara kauri.

Tana motsashi tana tarfa wannan ruwan data diba tare da ruwan lemun tsamin.

Lokaci ɗaya ya fara wani irin masifeffen ƙamshi yayi kauri yayi fari tas, in ka gani zakace kinɗirmo ne aka burge.

Kashe wutan tayi tare da sauƙe tukunyar.

Riyyam-nsra kuwa aje wayarsa yayi tare da cewa.

“Har kin gama.”

Sai kuma ya matso ganin yadda kunun yake da sauri yace.

“Kai my Aunty wannan ko nono ne kikayi?”

Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.

“Kunun Gombawa kenan.”

Kai ya jinjina tare da miƙo ƙaramin cup yace.

“Samin in mana dandanel”.

Murmushi tayi tare da sa mishi.

Kana  ta ɗauko wani roba mai kyau ta juyeshi ciki.

Kana ta rage kaɗan tasa a ƙaramin flaks.

Tasa bisa tray’n tasa mug da spoon kana sai madarar gari a roba mai haɗe da set din flaks din.

Ɗayan kuma tasa zumar a ciki.

Kana ta mikawa Riyyam-nsra.

“Ajiye kam table a Dinning.”

To yace ya amsa.

Ita kuma ta jawo nashi kofin kunun, madarar ta saka mishi tare da zuma ta motsa da kyau.

Kana ta miƙo mishi tana cewa.

“Biri in sa wannan kuma a Fridge don in yayi sanyi yafi daɗin sha.”

Kai ya jinjina tare da amsa ya fita.

Ita kuwa ta buɗe Fridge ta sashi ciki.

Kana ta wonke komai ta fito.

(Gareku masu karatu.

Kunun yana sauko da ni’ima a jikin mace sosai kana da ruwan nono ga mai shayarwa, ga maza kuma yana sasu feelings yana kuma mgnin ciwon ciki in kin yawaita zuma da dabinon yana kuma gyara fatan jiki.)

Da sauri ta fito falon jin Riyyam-nsra na cewa.

“Wow masha ALLAH kai my Aunty wannan kunun duniya ne, yaseen yayi masifar daɗi.”

Yadda yayi mgnar da ƙarfine yasa Ramadan buɗe idonshi tare da yin tsaki.

Cikin murmushi Jannart tace.

“Kadama ka sake rufe ido la’asar tayi.

Tashi kawai.”

Miƙa yayi tare da cewa.

“Wallahi yajin nanne ya sani bacci.”

Juyowa sukayi jiyo takun.

Rayyern yana sauƙowa.

Kanta ta kauda daga kallonshi tare da nufar ɗakinta.

Shi kuwa Riyyam-nsra ya kalla tare da cewa.

“ku tashi kuyi al’wala mu tafi masallaci.”

“To.” Sukace kana duk suka miƙe sukayi al’wala suka mara mishi baya.

Ita kuwa  Jannart tana shiga bathroom ta faɗa wanka.

Wonka tayi da ruwan sanyi dan cikin kwana biyun nan.

Duk zafi ake ɗanyi, alamun sanyi na tattara kayansa zai tafi ya bawa zafi wuri.

Al’wala tayi kana ta fito.

Bayan ta idar da salla ne, ta mike ta isa gaban dreesing mirror’nta, mai ta ɗan shafawa jikinta.

Kana ta ɗan murza yar fauda tare dasa kwalli sai man baki, da ta ɗan goga akan lips dinta, tare kuma da gyara gashin giranta.

Takowa tayi zuwa gaban durowar ta, Ido ta zubawa jerin kayan bayan ta buɗe durowar, ahankali tasa hannunta ta jawo ledar da taga wata tattausar atamfa, Black and green color sai ratsin red, wanda akayiwa dinkin riga da zani.

Underwear ta zaro fari ƙal da pant shima fari.

Bayan ta rufe drawern ne kuma, ta dawo bakin gadon ta tsaya, kana anutse ta zura kayan.

Cas kuwa suka zauna mata a jikinta, Musamman rigar da tayi cib-cib da jikinta, breast cup din da aka yiwa rigar tamkar an gwada mamanta ne.

“Kai tela maye ne.”

Ta faɗa lokacin da ta dawo gaban dreesing mirror’nta, ganin yadda ƙirjinta yayi cib-cib a cikin rigar.

Ɗaurin ɗan kwali ta murza tare da fito da jelan gashinta gefe.

Turare mai sanyin ƙamshi ta fesa ajikinta, kana ta zaro gyale red color ta yafa a kafad’anta kana ta fito.

Kitchine ta nufa, sabida jiyo motsin Mamy da tayi.

“Kai Masha Allah diya kinyi kyau”.

Mamy tace lokacin da tayi arba da ita.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Ngd Mamy”.

Ta ida mgnar tana shigowa ciki tare da cewa.

“Mamy ga kunu a fridge.”

Kai Mamy ta gyaɗa tare da cewa.

“Au kunu ne ni ai nayi zaton kimdirmo ne.”

miƙowa Mamy hannu tayi alamun ta bata aikin, suyan kayan miyan da takeyi tace.

“Haka Riyyam-nsra ma yace.”

Kai Mamyn ta jinjina tare da cewa.

“Ato bari in na gama zan sha,yanzu bar wannan ɗauko semolina kizo ki tuƙa mana tuwo, yau miyar kuɓewa da bandan kifi zamuyi da tuwo bayanshi bazamu ƙara komai ba mun gaji”.

Toh tace kana ta ɗauki garin tazo ta fara tukawa.

Ita kuwa Mamy ruwan nama tasa a suyan kayan miyar nata, kana tasa tafasheshshen nama da kifi banda, da ɗan dakakken daddawa da citta da kanamfari.

Ita kuwa Jannart bayan ta gama tuka tuwon ta rufeshi yana turara.

Tace.

“Mamy kubewar fa.”

“A gata can na gogata.”

Dai-dai lokacin Rayyern ya shigo cikin falon, da sallama a bakinshi tare da daurawa da kira 

 “Mamy! Mamy!!.”

“Na’am Rayyern gani nan fa”.

Tace tana juyowa tana kallon ƙofar Kitchine ɗin.

Shi kuwa cikin alamun gajiya ya shigo.

Kauda kanshi yayi daga kallon inda take.

Kujera yaja ya zauna tare da cewa.

“Kai Mamy daddawa yayi yawa a miyar nan, ji yadda duk Kitchine din ya dibke.”

Rufe tukunyar Mamy tayi tare da cewa.

“In ta tafasa zai ragu.”

“Mamy yunwa.”

Yace yana mai ajiye wayarsa gefensa.

“Jannart bashi abinda zaici.”

“Toh”.

Tace tare da juyawa ta fita.

A hankali ya ɗan juyo kwayar idanunsa.

Jin motsin ta ajiye tray’n gefensa.

Yatsunta ya ɗan kalla kana ya kauda kanshi.

Ita kuwa bud’e flaks din tayi ta zuba mishi kunun a cikin mug mai dan girma.

Saida ta kusan cikashi, kana a hankali ta ajiye tare da sa spoon ta debi garin madara, cokali uku ta saka mishi, kana ta ɗaga robar zuma ta sulala mishi, tare da motsashi kana ta ajiye mishi a gabanshi.

Da sauri ya ɗan sunkuyo ido ya zubawa kunun ba tare daya fahimci menene ba.

Cikin kwaɓe fuska yace.

“Mamy me wannan kuma?”

Tana mai fita Kitchen din tace.

“Taɓa kaji.”

Sai kuma ta kalli Jannart tare da cewa.

“Kwashe abin cinnan haka.”

“Toh Mamy.”

Jannart din tace tana mai juyawa ta nufi wurin tukunyar.

Back to top button