Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 18 Hausa Novel

Karo na babu iyaka kenana da ta dauki wayarta ta budo whatsapp ta duba; har yanzu bai amsa messages dinta ba kuma bai biyo whatsapp call din da ta yi masa ba. To me yake faruwa ne? Allah dai yasa lafiya Mustapha yake da shi da yaran. Da farko da taga tayi magana ta whatsapp bai kulata ba kuma ta kirawoshi ta whatsapp din bai daga ba sai ta zata ko fushi yayi, amma dai zuwa yau kwana uku abun ya fara bata tsoro kada taje ko wani abu ne ya sameshi.Ta riga ta san babuu credit a wyar don haka ko balance ma bata duba ba; shi din ba mutum ne mai son saka mata credita ba, idan ma tayi magana sai yace wa zata kirawo ko kuma me zata yi da data din. Idan aka yi albashi dai idan ta yi magana yana saka mata naira dari biyar, shine zata samu ta raba ta sa data sauran ta dan yi waya. Don haka yanzun ma babu na wayar sai dai data din da ta yi mata saura. Tayi tsaki sannan ta sauka daga kan gadon Nabila inda take kwance ta wuce dakin Mommy.A parlor ta sami Mommy tana zaune tana kallon tafsiri a tashar Sunnah TV, ta zauna a kusa da ita bayan tayi sallama ta amsa. Sai da suka dan yi jim kadan ta kula dai Mommy babu abinda zata ce mata sannan tace ‘Mommy don Allah ki dan saka min 1k a waya mana.’Ta kalleta tana dariya tace ‘1k kuma? Ina Mustaphan ko kuma yau ba nashi kike so ba tunda kina gidana nawa kike so?’Itama dariyar tayi ta kara langabe kai ‘A’a Mommy, don Allah dai ki taimaka, wallahi ya saka min kararwa nayi kuma dai kin san bani da kudi.’‘Ke kenan kullum baki da kudi?’‘Mommy bari dai na fara aiki.’‘Uhm, shi Mustaphan ko dan na kashewa baya yaga miki balle gaki ‘yar makaranta?’Ta dan marairaice ‘To ai kin ga yanzu anyi hutu Mommy, duk ‘yan sauran canjin ma na kashe.’‘Shi yasa kike maula kuma? To dauko min wayata a daki na saka miki a cikin wanda mijina ya bani.’Ta mike tana dariya tace ‘Mommy.’Baffanta ba wai millionaire bane amma dai ta san yana da kyauta; duk da Mommy tana sayar da ‘yan kunnaye da sarkoki amma duk wata sai ya tura mata kudin kashewa account dinta sai dai ko ya tura babu yawa amma fa sai ya tura. Kuma idan dai ta bukaci wani abu bayan wannan to yana iya bakin kokarinsa wajen ganin yayi mata sai dai ko idan babu hali.Tayi zaton haka zata je ta samu a wajen Mustapha, musamman da yake yana yawan yi mata kyaututtuka da saka credit a waya laokacin da yana neman aurenta. Sai dai bayan ta shiga gidan sai ta tarar ba haka bane; don wani lokacin a kan ya saka mata kati a waya ya gwammace ya bata aron wayarsa tayi waya. Ko da ta koma makaranta ma tayi zaton zai dan dinga bata kudin makaranta da kudin kashewa sai dai tun a ranar farko da gane ba zai jure ba. Domin da farko bayan ta gama shiryawa tayi zaton zai kaita ne, amma sai dai suna fitowa da aka zo inda zai dauke hanya ya wuce office dinsu sai yace ta sauka a nan ta hau motar haya. Da tayi maganar kudin mota kuma sai yace mata wai ya zata tana da kudi; ta dai samu ya bata naira dubu kamar ba da son ranshi ba. Tun daga ranar ma sai ya zama ta daina damuwa tayi saui ta shirya ta bishi, yawanci sai ta jira idan ya fita sai ta kama hanya a motar haya. Kudin motar ma tana shirin ta tambayi Baffa ya dinga bata aka shiga lockdown; kuma har yanzu tana da niyyar kafin ta koma gida ta sanar da Baffanta kawai ya dinga tura mata kudin mota. Tana ta wannan tunanin taje ta dauko wayar ta kawowa Momy; ba tare da bata lokaci ba ta tura mara katin naira dubu kamar yanda ta bukata.Nan da nan ta koma daki ta sake hayewa kan gadon Nabila sannan ta danna masa kira.Sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ya dauka, cike da isa yana magana da kyar ya amsa sallamarta, haka ma gaisuwarta kamar ba zai amsa ba. Wannan ya sa jikinta yayi sanyi kuzarin da ta fara wayar da shi duk ya gushe.Cikin sanyi murya tace ‘Babe, ya na jika haka? Ko baka da lafiya ne?’Sai da ya dan yi jinkiri sannan ya amsa ‘Umm, lafiyata kalau. Ke kin damu da lafiyata ne da kike wannan tambayar? Ba dole ki jini haka ba tunda kin zabi ki nesanta kanki da ni?’Nan ta fahimci inda zancen ya dosa, amma da yake so take ta waske sai tace ‘Haba Babe ya za ayi na gujeka? Tunda fa kuka tafi daga nan nake ta yi maka message ta whatsapp, baka gani bane? Kuma wallahi wayar ma ka san bani da credit, yanzun ma da kyar na samu Mommy ta saka min dari biyu shine nake kiranka fa. Haba Babe ya za ayi kace ban damu da kai ba?’‘To idan kin damu dani ya za ayi nazo har gidanku ga azumi kin sani kuma gashi ana lockdown? amma kina kallonmu ni da yarana duk muna ta murna zaki dawo amma kika ce ba zaki dawo ba sai bayan sallah.’‘To ai na gaya maka wannan ba ni na tsara haka ba, Mommy ce. Kuma ka san dai idan mace ta haihu dai ana yin gyara da sauransu, sallar nana fa kuma saura bai fi kwana goma sha shida ba. Haba Babe to meye na fushin?’Shiru yayi ba tare da yace mata komai ba suna sauraren numfashin juna. Itace ta gaji da sauraro tace ‘Ya naji shiru ne? ina yara na?’‘Ai baki damu da su ba shi yasa sunata cewa ki biyosu kika ki.’Ta fara gajiya da wannan mitar tsa da duk abinda tace sai ya ce bata damu da su ba shi da ‘yayansa, to wai ita ba ta bukatar a damu da ita ne ko me yake nufi? Shi ba zai iya kula da ita ba kuma ya barta ma cikin natsuwa a inda za a kula da ita ta dan sami natsuwa yana nema ya hana? Ta dan yi murmushi mai sauti ta danne fushinta sannan ta saita muryarta tace ‘To don Allah kayi hakuri ka daina cewa ban damu da ku ba, kai ka san na damu daku. Kamar tau ne zaka ga lokacin yayi ai na dawo, ko ba shikenan ba.’‘Umm, amma dai da zaki dawo yanzu ai da ya fi ko? Haka kawai ni ba gwauro ba kin saka ni azumi babu mata. Kawai idan an bude gari na zo na dauke ki mu tafi, shine kawai zan san kin damu da ni.’Ta dan daga murya tace ‘Ah, Babe to me zan cewa Mommy, ni dadi miji zan bi mijina kenana ko me?’‘Ba wani dadi miji, ai aurene kuma itama ta sani.”‘To gaskiya dai ka bari sai bayan sallar kawai.’Haka dai suka dauki lokaci suna waya ba tare da ta amince zata dawo din ba, maimaita mas kawai take sai bayan sallar. Don haka kusan a fusace ya katse wayar ba tare da sun yi wata sallamar kirki ba.Ta jefa wayar a kan gadon kusa da ita ta ja tsaki, sai kuma ta kifa kanta a kan pillow sai hawaye. Ta godewa Allah nabila tana dakin Mommy tana bacci da sai ta gayawa Mommy tana kuka. Ta fara nadamar sakawa da tayi Mommy tace ta zauna a gida har bayan sallah, yanzu gashi yana fushi da ita. Ita bata zata wannan abun zai sa yayi fushi ba don da ta san zai yi fushi ma da ko gidan ba zata taho ba zata hakura yaje ya daukota. Bata sani ba ko zata iya jure jinsa a cikin damuwa har na tsawon sati biyu ko uku, amma dai zata gwada. Don da kunya tace a barta sai bayan sallah sannan yanzu kuma ta zo tace zata koma.Haka ta karasa wunin ranar cike da damuwa da nadamar zaman da ta zaba zata yi a gida.Haka ta cigaba da hakuri tana buga masa waya wanda kullum idan ta buga gaisawa kawai suke yi babu wata magana mai dadi, kamar ma shi dole take masa. Abun yana matukar damunta don haka ta fara rama wadda Mommy ta zata don ta cigaba da azumi ne tunda ta sami lafiya; idan tayi zuru-zuru aka yi magana sai tace azumin ne da wahala.____Tun da ya kaisu gidan Hajia bai sake zuwa ba tunda garin a rufe yake ba a fita, sai yau asabar a lokacin saura sati daya sallah.Yana fita ya tsaya a shagon telansa ya karbar musu dunkunan kayan sallansu wanda tun kafin a fara azumi ya kai; wanda harda na Khadeeja a ciki, ya tsaya aka bashi leda ya ware nata wadanda bashi da niyyar kai mata gidansu. Ya dai yarda zai ajiye mata a dakinta duk lokacin da ta dawo ta gani.Yana karba kai tsaye ya wuce gidan Hajia cike da kewar yaransa.Tun daga nesa ya hango Habib a zaune a kofar gida tare da wani yaro, ba wasa sukeyi ba a zaune suke kawai sun yi shiru kowa da abinda ya dameshi. Kafin ya karasa tsayar da motar ya taso da fara’arsa; ya gyara tsayuwar motar ya bude kofa yana sake karewa Habib din kallo wanda ya yi zuru-zuru kamar wanda ya kwana da yunwa.‘Abba sannu da zuwa.’ Muryar Habib ta katseshi.‘Yauwa Habib, ya naganka kamar kana jin yunwa ko azumi kake ya fara baka wahala tun da safe haka?’Idonsa ya dan yi rau-rau yace ‘Eh, azumi nakeyi.’‘To baka yi sahur bane?’‘Ba sosai ba, bakin tuwo ne kuma bana ci gashi kuma babu wani abincin a gidan sai shi, na dan ci kadan dai.’‘To ba sai ka fasa yin azumin ba? da safe kayi breakfast.’‘Hajia ma haka tace na fasa yin azumin amma ni nace zan yi, idan ma ban yi ba ba abinci zan samu ba sai an sha ruwa. Tunda muka zo ma sau daya na sha azumi.’Cike da tsananin mamaki yace ‘Ban gane ba abincin kake samu ba sai kace wani almajiri? Ba a baka abinci ne a gidan? Ina baito…

Back to top button