Nau’in Maza 4 Da Basu Dace Mace Ta Kula Su Ko Yin Soyayya Dasu Ba
Ba duk namiji bane ya dace da kulawarki ba. kuma ba duk namiji bane zaki bashi zuciyar ki ba. Ba duk namiji bane zaki amince masa da ya aureki ba duk zakuwarki da kina son aure.
Akwai wasu jerin maza guda 4 da duk son aurenki idan kika sake kika aure su sai kin gwammace da kin yi zama baki da aure. Wadannan mazan sune:
Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam
1: Namji Mara Ibada: shi rashin ibada ya kan iya jawo mutum ya zama baida da duk wani imani ko tausayin da ake bukata magidanci ya kasance da su ba. Muddin kika fahimci irin wannan namijin na sonki to kada ki kula shi.
Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata
2: Namiji Mai Ɗagawa: Kada ki sake ki kula namijin da yake da dagawa, ji da kai takama da gadara, muddin kuwa kika bashi dama ko da na rana daya ne sai ya nuna miki iyakar ki.
Sune mazan da suke iya duban cikin idanuwan mace su goran ta mata su kuma kaskantar da iyayenta.
Sune mazan da suke ganin auren mace tamkar alfarma suka mata da suka aure ta.
Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah
3: Namijin Da Bai Ganin Darajar Mata: Awaki mazan da suke ganin ita mace ba abakin komai take ba. Irin su basu ganin darajar mace suna iya yi mata wulakanci a duk inda ya kama kuma ko a gaban waye.
Irinsu suna ganin mace kawai abar jima’i ce aji dadi da ita daga nan bata da wani amfani sai kuma lokacin da wannan bukatar ta taso.
Muddin kika baiwa irin wadannan mazan damar a zuciyar ki zaki gwammace kida da karatu.
Karanta>>> Dalilin Daya Sa Matan Hausawa Ke Tsufa Da Wuri Da Zarar Sunyi Aure
4: Maza Makaryata: Duk inda ka samu makaryaci za kuma a sameshi da yaudara a bayan sa. Don haka makaryata maza suna da hadari da mace zata basu amincewarta saboda rashin sanin tabbacinsu. Yadda yake shinfida miki zance haka nan yake shinfidawa wata acan. Don haka mu’amala dashi yana tattare da matukar hadari.
Idan har kasan kana da wannan halayyar yi kokari ka canja domin baka makara ba/idan kin san kina da saurayi mai irin wannan hali yi kokari ki nusar da shi, in kuma yaki rabu da shi yar uwa dan ba abokin rayuwa bane.
Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.