Hausa novels

NIHAAD Chapter 64 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

64

Bayan kwana biyu da tafiyar Khalil aka fara shirye shiryen biki a gidan, kai da ganin irin IV din da aka buga kadai kasan bikin na masu kasar ne, kusan kullum Mami sai ta fita for the wedding preparation, biki ne na gani na fada ake shirin yi, a kwana a tashi dae har bikin ya rage saura sati daya, tuni Noor ta koma gidansu Nadeeyah ta tare a can su ma suna nasu shirin da sauran kawayen Nadeeyah. Yau ma kamar kullum Mimi ta gama shirin tafiya school ta juya tana kallon Nihad da ba ta da wani aiki sai kwanciya all this days a daki, a ko da yaushe kuma zaka ganta babu walwala tare da ita, she look so dull, abincin ma wani lokacin sai Mimi tayi mata da gaske take dan tsakura, all this while kuma duk kiran da Khalil zai yi ma Mimi ta bata waya, sai dai ta amshi wayar amma baxata masa magana ba don Mimi na mika mata wayar take fita daga dakin ta bata space, har ya ma gaji da kiran ya daina, wayarta kuwa dama ta kashe ta ajiye kusan sati biyu kenan, a daddafe ya iya yin kwana sha biyu a Jamus don gaba daya hankalinsa yayi gida ba kuma wajen kowa ba wajen Nihad, rashin maganan da take masa via phone call ya damesa sosai…. Mimi ta ajiye handbag dinta ta zauna gefen gado tana kallonta tace “Nihad me yasa baki maganar makarantarki ne yanzu?” Nihad ta daga kai ta kalleta amma bata ce komai ba, Mimi tace “Soon za ki ji ance exams fa, for almost 2 month now baki shiga lectures ba, kuma naga ma kamar makarantar ne baki so ko??” Nihad dai bata ce mata komai ba, Mimi ta mike ta dau jakarta tace “Sai na dawo, zan bar maki breakfast dinki a parlon Mami ba sai kin je downstairs ba” A hankali Nihad tace “Allah ya tsare” Mimi na fita ɓangaren Mami ta tafi zata sallameta, Mami na kallonta tace “Breakfast din fa?” Tace “Ehh xan yi before leaving” Mami tace “Toh ita fa?” Mimi tace “Idan ta fito zata yi, she is still lying down, zan aiko Bilkisu ta kawo mata nata nan parlon” Kafin Mimi ta tafi ta sa mai aikin Mami ta kawo breakfast din Nihad nan parlon Mami ta ajiye, wajen karfe tara Mami ta fita zuwa wajen wata kawarta warce ita ce tayi assigning lafiyayyun chefs da za su yi girki na bikin, sae kusan karfe sha biyu ta dawo gida bayan an mata calculation din nawa kudin abincin zai kama gaba daya kuma ta tura masu, don tuni Janar ya tura mata a account dinta, Babu kowa gidan yanxu sae ita da su Mimi da Nihad sannan mai aikinta, Hanan kuwa na can gun uwarta, Janar ma yau kwanansa uku da tafiya India for checkup, the house is so empty duk da dama can gidan babu hayaniya, Mami na isa ɓangarenta taga breakfast din Nihad har sannan a ajiye bata shigo ba balle ta dauka, mamaki ne ya cikata ta fita zuwa dakin Mimi, sae da ta kwankwasa kofar dakin sannan ta bude, kwance ta sameta saman gado ba kuma bacci take ba, Nihad na ganin Mami ta mike zaune a hankali, Mami tace “Me yasa baki shigo kinyi breakfast ba?” ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Mami tace “Toh tashi ki fito kiyi….” Nihad tace “Toh” Juyawa Mami tayi ta fita, ta kira Bilkisu ta sa ta fita da Breakfast din tace “Make a new one immediately” Bilkisu ta amsa da ladabi sannan ta dau abincin ta fita… Ba a dau lokaci ba Nihad ta shigo parlon Mami tana jan kafa…, Hijab ne har kasa jikinta, Mami dake zaune parlon tana kallonta tace “Bari ta kawo maki wani yanzu” Nihad tace “Toh” Zata zauna kasa Mami tace “Zauna saman kujeran” Ba musu ta zauna kan kujeran ta jinginar da kanta jiki, Mami dae sai kallonta take, can ta ci gaba da Chatting da sister dinta Hamida da zata taso jibi daga Yemen tare da mahaifiyarsu da kanninta mata biyu, tana sanar mata abinda zata taho mata da shi daga Yemen, Nihad na ta zaune har bacci ya ɗan fara daukarta Bilkisu ta shigo ta ajiye tray din hannunta a kusa da ita sannan ta fita, Mami tace “Shiga bedroom za ki ga carpet karami ki dauko sai ki zauna a kai, zuwa anjima za a kawo na parlon nan dazu aka fitar da wanda ke kasa” Nihad ta mike ta nufi bedroom din Mami, juya mata taga parlon ke yi, tayi baya zata fadi Mami dake kallonta ta mike da sauri, amma tuni har ta kai kasa, Mami ta nufeta da hanzari ta dagota zaune tana kallon ta da mamaki tace “Are you okay?” Kasa cewa komai Nihad tayi don har sanan kanta juya mata yake, Mami ta dagota tsaye tana rike da ita ta kai ta bedroom din dinta, ta taimaka mata ta zauna gefen gadonta tace “Sannu” Ita dai Nihad bata ce komai ba sai sauke numfashi take a hankali, Mami ta juya ta fito parlor, shayi me kauri ta hada mata a mug ruwan zafin ma ba da yawa ta zuba ba tayi diluting da Table water sannan ta koma dakinta, kwance ta gan Nihad gefen gadon idonta a rufe, Mami ta ajiye mug din shayin dake hannnunta ta dagota tace “Tashi ki sha shayin, it’s already noon” Nihad ta mike zaune a hankali, Mami ta dau mug din ta mika mata, amsa tayi ta kai baki ta fara shan shayin. Mami ta juya ta fita daga dakin, ko rabin shayin Nihad bata sha ba ta ajiye da sauri tana toshe bakinta, bata san sanda ta zabura ta mike tsaye ba har ta nufi kofa ganin aman ya riga ya taho mata kawai ta dawo ta shige bandakin Mami, nan ta dinga kwarara amai, Mami dake parlor ta mike da sauri ta koma dakin don a bude ta bar kofar shi yasa ta juyo kakarin amanta, bandakin ta shiga ta dafata tana kallonta tace “Sannu” Nihad ta kasa cewa komai, bayan ta wanke bakinta, Mami ta cire mata Hijab din jikinta sannan ta koma dakin da ita ta zaunar da ita gefen gado tana mata sannu, Nihad ta kasa ci gaba da zama kawai ta kwanta gefen gadon, Mami ta koma bandakinta don ta gyara, ko da ta fito bacci ta tadda Nihad take yi, ta fita parlor ta dau wayarta ta kira Dr Rukayya bayan sun gaisa tace mata ta zo gida zata duba mara lafiya. Mami na ta zaune parlonta bayan minti talatin da kiran Dr Rukayya aka bude kofar parlon, ta daga kai tana kallonsa, ya karaso ciki da sallama, ya zauna saman kujera ya cire face Cap dinsa sannan ya gaisheta, Mami ta amsa tace “Ya hanya?” Yace “Alhamdulillah, ya gida” Tace “Lafiya lau” Tace “Dama tafiyar ta sati biyu ce?” Ya ɗan shafa kansa yace “Eh” Mami tace “Ohk” Yace “Naga ba kowa a gidan Mami” Mami tace “Mimi ta tafi makaranta, Noor na gidansu Nadeeyah” a hankali Khalil yace “Ok….” Mami bata sake ce masa komai ba, bayan few seconds yace “What about Hanan?” Mami tace “Washegarin ranan da ka tafi ita ma ta tafi kaduna” Yace “Ohk” Suna ta zaune parlon for almost 5 minutes, bai ce mata komai ba ita ma haka, Wayarta ne ya fara ring tana dubawa taga Dr Rukayya ce, Mami na dagawa ta sanar mata tana compound, Mami tace “Ohk, bari Bilkisu ta karaso ciki da ke” Mami ta katse wayar ta kira Bilkisu, shi dai kallon Mami kawai yake, ya rasa ta ya zai ce mata ina Nihad, don yana shigowa gidan dakin Mimi ya fara nufa amma yaga ba kowa ciki, ya koma visitor room dake bangaren Mami nan ma yaga ba kowa ciki, har Mimin ya kira yaji inda suka je amma tace masa ai ita tana makaranta Nihad kuma na gida ta bar ta, Mami na gama waya da Bilkisu ta ajiye wayar a gefenta, Jinginar da kansa yayi jikin kujera yana ta kallonta, Mami ganin kallon da yake mata tace “Toh sai ka tashi kaje kayi wanka ka nemi abinda zaka ci ka bani waje ko??” A hankali yace “I am okay” Mami tace “Toh ka bani waje za a shigo min da bakuwa yanzu” Cike da karfin hali yace “Mami tare suka fita da Mimi ne?” Mami tace “Wa?” Sai kuma ya kasa cewa komai, Mami tace “Baka da number Mimin ne?” Yayi shiru yana kallonta, bata sake kallon inda yake ba har Bilkisu ta shigo da Dr Rukayya, Khalil ya dinga kallonta, Ta gaida Mami da ladabi, Mami tace “Sannu da zuwa Dr” Dr Rukayya ta kalli Khalil murmushi kwance fuskarta tace “Barka da rana ranka shi dade” Yace “Longest time Dr” Tace “Ai kam ka buya” Mami ta mike tace “Mu je ciki Dr” Dr Rukayya ta bi bayanta zuwa bedroom dinta, Khalil ya bi su da kallo har suka shiga, kasa daurewa yayi ya mike ya bi bayansu, Tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallon Nihad dake bacci saman gadon Mami, Dr Rukayya dake duke dab da ita tana kallonta ta kai hannunta a hankali goshinta to feel her temperature, sosai taji jikinta yayi zafi, Dr Rukayya ta mike tana kallon Mami tace “Tun yaushe ne bata da lafiyan?” Mami tace “I just noticed today, da yake ba bangaren nan take ba tana dakin Mimi ne” Dr Rukayya ta gyada kai tana kallon Nihad da ta bude ido a hankali tana kallonsu, Mami na kallonta tace “Ya jikin?” Kai kawai ta iya gyada mata, Mami tace “Toh ki dubata Dr bari in baku waje” Tana fadin haka ta juya ta bar wajen, Khalil bai bari sun hada ido da Mami ba ya juya da sauri shi ma ya bar bakin kofar dakin, ko da ta shigo parlon bata gansa ba ya koma can first parlor, Dr Rukayya ta duka tana kallon idon Nihad da kyau, ta dago hannunta tana kallon fingers dinta, calmly tace “When last did u see ur period?” Nihad tayi shiru, sai kuma ta buda hannu alamar bata sani ba, Dr Rukayya tace “Akwai abu a bakin ki ne da baki son bude bakin kiyi magana Dear” Nihad ta girgiza kai cike da karfin hali tace “Aa” Dr Rukayya tace “Good, now tell me how you r feeling?” Nihad ta jingina da gadon cikin sanyin murya tace “Ina jin jiri idan na tashi, sannan in na ci abu sai in fara jin amai, i am feeling dizzy…” Shiru tayi daga haka, Dr Rukayya tace “Tun yaushe kika fara jin hakan?” Ta ɗan yi shiru sai kuma tace “Not too long” Dr Rukayya tace “Good, koma ki kwanta” Nihad ta kwanta a hankali, Dr Rukayya ta juya ta fita daga dakin zuwa parlor, zaune ta tadda Mami ita kadai a parlon, ta zauna saman kujeran dake kusa da Mami tace “Hajiya ina mijinta kuwa?” Mami tace “Shi kika tarar dazu ai da kika shigo” Ta ɗan buda ido da mamaki tace “Wai Dr Khalil?” Mami tace “Eh” Dr Rukayya tace “Maa sha Allah, ashe surkarki ce wallahi da na ganta fara na zata ko yarinyar er uwarki ce, maa sha Allah that’s nice, ashe Khalil yayi aure ba labari” Mami dai kawai ta ɗan yi murmushi, Dr Rukayya na dariya tace “Yana matsayin likita amma baxai duba matarsa ba sai an kira mata likita daga waje, ko rudewa yake… Kinsan haka wasu likitocin suke” Mami tace “Toh yanzu dai me ke damunta?” Dr Rukayya na murmushi sosai tace “Congratulations Hajiya, u are going to be a grandmum soon, duk da na so sai anyi test kafin in sanar maki but duk wani symptoms na ciki na gani a jikinta, ur in-law is pregnant” Mami ta dinga kallonta ko kiftawa babu, can ta sauke idonta a hankali tace “Toh Alhamdulillah” Dr Rukayya tace “Yanzu zan dauko Pt test strip a motata, don dake tabbatar da hakan” Mami tace “Toh” Daga haka ta nufi kofa ta fita, ba a wani dau lokaci ba sai ga ta da Urine specimen container da pt test stip, ta shiga dakin Mami ta gaya ma Nihad yanda zata yi amfani da shi sannan ta kama hannunta zuwa bandakin don ta kasa tsayawa sbda jiri, Dr Rukayya na ta jiranta a dakin bayan minti shidda ta bi ta zuwa cikin bandakin, murmushi tayi ganin test din was positive, bayan sun fito ta fita tayi discarding strip din da container, ta dawo parlor ta sake congratulating Mami da ke zaune looking speechless. Bayan fitar Dr Rukayya ta siyo drugs da alluran da zata ma Nihad, Mami dai na ta zaune parlor ta kasa ma shiga ciki ta duba Nihad din, can dai ta mike daga karshe ta shiga cikin dakin…. After Zuhur Khalil ya sake dawowa bangaren Mami, zuwa lokacin Dr Rukayya tayi ma Nihad duk abinda ya kamata ta wuce, Babu kowa cikin parlon amma ya kasa karasawa cikin bedroom din don bai san ko Mami na ciki ba, ya tsaya for almost 2 minutes contemplating kafin ya karasa ya tura kofar a hankali, Nihad ce kawai kwance dakin tana bacci restlessly, ya sauke wani ajiyar zuciya ganin Mami bata ciki ya karasa da sauri, ya zauna gefen gadon ya kai hannu forehead dinta yana kare mata kallo keenly, he sat there looking at her for almost 2 minutes, sai kuma yayi wani murmushi dai dai nan ta bude ido a hankali don baccin yin sa kawai take don dole, All her body is just weak, gashi ko tunanin abinci tayi sai taji zuciyarta na tashi amai na taho mata, Daure fuska tayi ganinsa, yayi kasa da murya yace “How are you feeling?” Ta kara hade rai zata juya masa baya ya dagota zaune, yayi kasa da murya cike da damuwa yace “To me na maki kike ignoring magana da ni for two weeks now?” A fusace tace “Ni ka kyaleni don Allah” Yace “Ki gaya min laifin me nayi?” Tace “Toh ai ba dole sai da ni kawai zaka yi waya ba tunda kana da warce ita ma zaka iya waya da ita” Kallonta yake yi da mamaki, ta fizge hannunta zata juya masa baya ya jawota ya rungumeta jikinsa yace “But ai ke kadai ce matata, ko da wacece zanyi waya ai ba matata bace tunda ba aure tsakaninmu” A hankali ta sakar masa kuka ya lumshe ido thinking of what to say to her don sarai ya gama gano ta, dai dai nan aka bude kofar dakin kafin yayi saurin saketa har Mami ta shigo, Nihad taji kamar kasa ya bude ta shige kawai ta huta, Ya mike da sauri ya kasa dago kai balle su hada ido da Mami, sai kuma ya nufi kofa, Mami ta bi sa da wani kalloz a takaice tace “Go back and take her to ur room” Tana fada masa haka ta juya ta bar dakin, sai a sannan ya dago kansa yana sosa keya, can kuma ya koma wajen Nihad yace “Tashi mu tafi” Wani kallo tayi masa tace “Wallahi baxan je ba ai ni ba fitsararriya bace” Ya wara ido yace “Ni ne fitsararre?” Komawa tayi ta kwanta ta juya masa baya, yayi murmushi ya juya ya fita daga dakin. Sanin Mami is watching his move ya sa ya shirya bayan la’asar ya tafi gidansu Nadeeyah… Yana ta zaune compound din gidan sai ga ta ta fito, shi dai ya ma rasa gane kanta for almost 3 weeks now, ta zauna saman kujera without looking at him tace “Ina wuni” yayi shiru yana kallonta, ta daga kai ta kallesa jin bai amsa gaisuwarta ba, yayi kasa da murya yace “Now tell me ur problem pls Nadeeyah, is it Nihad? In dai ita ce u need not to bother plss ba gida daya zaku zauna ba, sai ma ku yi wata da watanni baku ga juna ba i am assuring you, pls ina son ki kwantar da hankali ki daina duk wani kokwanto a ranki, kuma ki sa a ranki i owe u a lot saboda halaccin da kika min” Nadeeyah tace “And this is the fifth time u are saying this to my ears, komai kace saboda halaccin da na maka ba, ko kuma kace baza ka karya alkawarin auren da ka min ba… so what i want u to make me understand now is that saboda abun da kake ganin na maka ne kake so ka aureni so that it wont be like baka min adalci ba, ko kuma saboda alkawarin da kake ikirarin ka min na aure shine zai sa ka aureni don ka zamo me cika alkawari or whatt?” Khalil yayi shiru yana kallonta babu ko kiftawa, tayi wani murmushi tce “No talk to me” Yace “Why are you complicating issues Nadeeyah? Me yasa zaki yi wannan tunanin?” Ta girgiza kai tace “You are the one complicating issues Kjay, bana mantawa kwanakin baya na tambayeka me ya kai ka gidansu Nihad driving, a ina kasan su har kaje gidansu, but u told me that should be a story for another day, kaga sai yanzu na fahimci cewar saboda ita kaje gidansu ka nemi driving don ka zauna a gidan har ka aureta” Khalil ya zaro ido yana kallonta yace “Billah ban taɓa ganinta ba sae da naje gidan, kin ji na rantse, kuma Nadeeyah na gaya maki times without number mahaifinta ne ya hada aurena da ita, wllh at first bata san ni aka aura mata ba mw” Nadeeyah ta mike tace “My frnds are waiting for me inside kuma wucewa suke son za su yi” yayi shiru yana kallonta, can yace “Ohk sae mun yi waya, ki gaida Mumy” Daga haka ya mike ya nufi motarsa ita kuma tayi wucewarta cikin gidan.

Inna ce zaune saman kujera a dakin Umma, ga Umman kwance saman gado ana kara mata ruwa sai nishi take Kamila da Nihal na zaune gefenta, Zaune a dakin Mumy ce da matan yayan Abba duk sun zo duba Umma, Hajiya Turai ma na zaune daga bakin kofar dakin, Inna tace “Toh ni dai bamu san kan ciwon Sumayya ba gaskiya, abu kamar wasa karamar magana ya zama babba, daga fasa goshi da targade a hannu, anya ba aljanu suka shafeta ba kuwa” Babu me cewa komai dai a dakin, sallama aka yi can parlor Inna tace “Kuma masu shigowa dubiyan nan ma ya kamata a hanasu haka don ba a san zuciyar wani ba, banda haka ciwo yaki ci yaki cinyewa, ta ina zamu kama hanyar kai akwati hankali ba a kwance ba, kila ma har sun gaji da jira a can Habujan kada ma suyi tunanin cinye kudin aka yi” Husnah ce ta makale jikin kofar dakin ganin mutane da yawa zaune ciki sai wuwwurga ido take, lokaci daya kuma tana sosa gabanta daga cikin Hijabin jikinta, gaba daya tayi wani zuru zuru da ita kamar ba Husnah ba, Hajiya Turai ta yamutsa fuska jin wani axababben doyi da ya bugi hancinta, Inna ta toshe hanci da gyalenta a gigice tace “Wacece wannan kuma? Ba haya tayi a wando ko me?” Husnah ta ɗan durkusa tana in ina tace “Aa wajen Umma na zo dama… Umma nake nema” Umma dake fama da kanta ta ɗan bude ido daya tana kallon Husnah, Inna na kara toshe hancinta a gigice tace “Wacece Umma, me zata maki?” Husnah ta fashe da kuka tace “Ni dai dama inda zan samu Nihad nake nema, ko ta waya ne don Allah” Inna ta mike da sauri ta koma can kofar bandaki tace “Wai wannan doyin meye haka yake gigita ni….” Mumy na kallon Husnah jin abinda tace, tace “Me Nihad din zata maki kike nemanta?” Umma ta mike zaune da sauri ba tare da ta shirya ba tace “Ke ya zaki fado ma mutane daki haka kai tsaye?? Daga ina haka?”

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Download NIHAAD Complete Novel Document By Khaleesat Haiydar

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

Back to top button