Karfe A Wuta Chapter 61 By Ayshercool
Gaban Nabila ya faɗi, cikin matsanancin tsoro da tashin hankali, ta din ga waige-waige tare da dubawa, idan akwai wanda ya ganshi, amma layin babu kowa, sai manyan security light da suka haska ko ina.Ta sake kallonshi, ta tabattar shi ne, ta ƙarasa in da yake da sauri ta ce “Viper, waye ya nuna maka gidanmu? Yau kuma ba office ba har gida?””Akwai matsala ne?” Yayi maganar yana ƙara ƙureta da ido.”Au tambayata ma ka ke yi? Amma dai ka san yayana nemanka yake yi ko meyasa zaka zo gidanmu, lallai sai ka tona mini asiri ne? Waye ma ya nuna maka gidanmu?””Shi yayan naki, ki shiga ki gaya masa gani ya zo ya kamani mana, shikenan ki daina wahalar da kanki da fargaba mana. Kina tunanin zan yi aiki da wadda ban san wacece ba?”Ta ce “Yanzu dai duk ba wannan ba, dan Allah mu je daga wancan lungun, mu yi magana”Ya sha kunu ya ce “Ban gane muje lungu ba””Eh mana, mu je can mu yi magana kar a ganka””A’a ni ba zan shiga lungu a daren nan ba””Innalillahi wa Innalillahi raji’un, to ai ba wani abun na ce ayi a lungun ba, magana kawai zamu yi kar a ganka nake tsoro””Kuma sai ki ce in shiga lungu””Na shiga uku, sai ka ce wata ‘yar iska, kar ka yi mini wata mummunar fassara mana”Viper ya ce “Ke da duk baki yi wannan tunanin ba, ki ka amince da aiki tare da ni, ki ke iƙrarin zaki taimake ni? Ki tsaya ki saurare ni” ya yi maganar fuskarsa ɗauke da matsananciyar damuwa. Duk da bai kasance mai fara’a ba, amma yau akwai damuwa sosai a tare da shi.”Amma dan Allah waye ya nuna maka gidanmu””Ba wannan ne ya kawo ni ba””To Allah ya baka haƙuri sir, me yake tafe da kai?””Nura” ya faɗa a taƙaice.”Waye hakan?””Ƙanina Nura guduma, bayan mutuwarsa ina duba mahaifiyarsa, sai dai bayan an tsare ni ban samu damar yin haka ba, amma su Walid sukan je amma ba ko yaushe ba, bayan fitowa ta kuma, bani da cikakkiyar nutsuwa, kuma ina matuƙar jin nauyinta ban je ba, ban kuma saka su walid sun je ba”Nabila ta nutsu tana sauraronsa, duk a tsorace take, kar wani ya ganshi, duk da akwai facemask a fuskar sa.”Mijin da ta aura bayan baban Nura ya rasu, shekaru biyu da suka wuce, tana ta fama da rayuwa, ga yaranta guda biyu, a taƙaice dai jiya da su Walid suka dawo daga garin, sun tabbatar mini da ‘yar ta aka yi wa fyaɗe ita kuma ba a san in da take ba” Nabila ta zabura ta ce “Kuma?””Yarinyar da ki ke bincike a kan case ɗin ta, Naja bunkure ta shiga case ɗin”Nabila ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, kalmar nan ko daɗin ji ba ta da shi, dama ita ce? To ba su gano in da maman take ba?””Ina gaya miki kina tambayata, na baki nan da sati biyu rak, tun da kin ce wanda ake zargi ba shi bane ba, ki fito da mai laifin, ko kuma ni na fito da shi ta ƙarfin tsiya”.Cikin rashin fahimta ta ce “In fito da mai laifi kuma ta ina? Nima bulayin nemansa nake ai saboda in wanke client ɗina””Sai fa kin nemo shi, ko kuma ki tabattar an yankewa mutumin nan hukunci dai-dai da abun da ya aikata””Amma dai ka san ni lawyer ce ba ‘yar sanda ba ko? Jami’an tsaro sune za su yi maka wannan aikin, ni kuma na tsaya na tabattar kotu ta yi adalci”Ya tsare ta da idanunsa ya nuna ta da yatsansa ya ce “Ke zaki yi, ba wanda zai yi sai ke, ki nemo ainihin mai laifin, ko kuma ki bari a hukunta wannan mutumin””But he’s not guilty, he’s innocent, ka bari na bi komai a hankali”Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “No matter what it takes, ki binciko ainihin mai laifin nan, an cutar da matar nan fiye da yadda ki ke tunani”Nan ya warware mata ɓangaren labarin sa na Nura, da ba ta sani ba.Rawa ƙafafuwanta suka fara yi, jikinta yayi wani irin sanyi, ta kasa magana.”Ki din ga yi mini uzuri wasu lokutan, ni mutum ne mai tarin laifuka ga mutane, bana son in ga wani a cikin damuwa, ina tsoron ace matar nan guduwa tayi saboda baƙin ciki, ba haka ba ma, voice message ɗin da ki ka kunna mini, sai a yanzu na sake tabattar da muryarta ce, ta tabattar da har gida wanda yayi rape ɗin yaje ya ɗauke ‘yar, dan haka ramma tana tare da wanda ya yi mata fyaɗe, kuma Naja’atu Bunkure ta sanshi, ba dan ta tsayawa yarinyar ta shiga case ɗin ba, dan ta bawa mai laifin kariya ne”.”Yanzu ka yadda wanda nake karewa ba shi da laifi?””Na sani, amma dole ki yi wani abu, a nemo yarinyar nan da mahaifiyarta”Nabila zata yi magana, aka haske su da fitilar mota, ta saka hannu ta kare saboda hasken fitilar, shi kuwa yayi ƙuri yana kallon fitilar.Viper ya ce “Ko dai ki gaya masa ya kashe fitilar nan, ko na haɗa idonsa da na motar na ɗauke musu wuta gaba ɗaya” Fitowa yayi daga motar ya ƙaraso in da suke, ya kalli Viper, sai dai a wannan karon ma ya ji wannan faɗuwar gaban. Kallo ɗaya ya yi wa Viper, ya tuna a in da ya ganshi.Ya kalli Nabila ya ce “Arfa waye wannan? Irin wannan samarin kuma ki ka koma kulawa?”Ta kalli Viper sannan ta kalli Nasir ta ce “Yaya me yayi maka ne? Na gaya maka tun waccan ranar he’s my client””Client like how? Shi ne zai din ga biyoki har gida? Get inside kafin na kwaɗeki a wurin nan” Addu’a take Allah ya sa kar Viper ya hasala.Viper ya ciro wata fitila daga aljihunsa, ya haske idon Nasir, ya matsa daf da shi, Viper ya fishi tsawo sosai ya ce “Talk to me, like a man, baka din ga yi mata shouting ba”Ya ja da baya ya kalli Nabila ya yi mata alama da hannunsa na i will call you.Ta jinjina masa kai, shi kuma ya juya zai tafi.”Waye kai?” Nasir yayi maganar cikin dakewa, dan muryar Viper kawai a bar tsoro ce.Viper ya juyo, ya kalli Nabila, da ta bashi tausayi, ban da tana wurin, kuma bai san me abun da zai aikata ka iya haifarwa ba, da sai ya sakawa Nasir iraƙi sannan ya gaya masa waye shi, kamar yadda ya yi wa tijjani yayan yar madara.Ya kalli Nasir ya ce “A man” ya faɗa a taƙaice.Nasir ya waiwaya, ya kalli Nabila zai fara masifa, amma ta zura da gudu ta shige gida.Rufa mata baya yayi, yana masifa har ɗakinta ya bita, yana yi mata bala’i, ganin yana neman ya tozarta ta a gabam mutanen gidan ya sanya ta fara kiran sunam Abba da ƙarfi.Aikuwa Abba ya saukko daga kam benensa yana faɗin “Wai waye yake taɓa mini yarinyar nan, kai Nasir menene haka? Dukanta zaka yi? Shekara Ashirin da biyar sai ka kamata kana duka dan rashin mutunci?””Abba ba dukanta zan yi ba””To me ka yi mata take wannan kururwar haka?””Abba gaba ɗaya Arfa ta canza, ta tsiri wasu irin ɗabi’u na rashin gaskiya, rannan na je ofishin ta, na tarar da ita da wani mutum, gaba ɗaya bai yi kama da mutanen kirki ba, yauma still ta tsaya da wani a waje, maimakon cikin gida tana zance, kamar dai wancan mutumin ne, gaba ɗaya bai yi kama da mutanen ƙwarai ba”Abba ya kalli Nabila ya ce “Arfa, yayanki a kan gaskiya yake, ni kaina shige da ficen samarin nan naki, ya fara isata”.”Abba, wallahi ba mutumin banza bane ba, kuma ko mutumin banza ne, ba wata muguwar alaƙa ya gani tsakani na da shi ba, na gaya masa client ɗina ne kawai, amma yaƙi yadda kwanan nan komai nayi sai ya din ga zargina na rasa me nayi masa gaba ɗaya””A’a Arfa, Nasir yana cikin masu goyon bayanki a gidan nan, tun da har ya magantu, to ya fiki gaskiya, ki san irin mutanen da zaki din ga tsayawa, kuma ki din ga mu’amala da su, yanzu a cikin samarin nan naki, lallai ki duba mai nutsuwa ya zo in ganshi, nima zan fi samun kwanciyar hankali ace kina ɗakinki” Nabila ta yi shiru, Abba yayi ta yi mata nasiha, bayan ya gama ya fita, Nasir ya bi bayansa.Nasir ne ya bi bayan Abba, suka shiga ɗakinsa ya ce “Abba, yakamata ka ja wa arfa kunne, wasu abubuwan take yi kwanan nan, shishishigi a kan wasu abubuwa. Ta sako wannan barrister Naja’atu Bunkure a gaba, kar ta je ta janyo wa kanta wata matsalar”Abba ya ce “To ai ni kaga ban sani ba, ban san me take aikatawa ba wasu lokutan, amma babu komai, zan yi mata nasiha, ka san ba kowane lokaci faɗa yake tasiri ba”.Nasir ya ce “Haka na, sannan kuma Abba””Sannan kuma me, ina jinka”Ya ɗan muskuta ya ce “Abba dan Allah ka bani auren Arfa”Take annurin fuskar Abba ya ɗauke, ya ce “Auren arfa kuma?”Ya ɗan yi shiru yana wasa da yatsunsa.Abba ya numfasa ya ce “Kenan kishi ne ya saka ka shigo kana yi mata faɗa?” Ya girgiza kai ya ce “A’a Abba, ba haka bane ba””To, Nasir kai ɗa na ne, hakazalia arfa, babu wani banbanci a tsakaninku, dan haka ba zan so abun da zai cutar da ɗayanku ba. Ba zan manta abun da mahaifiyarka tayi mini a kan yarinyar nan ba, kuma haryanzu ina kallon irin ƙiyayyar da take nuna mata, na daɗe da gane kana sonta, amma ina fatan ta samu wanda hankalinta zai kwanta da shi. Muddin ka aureta mahaifiyarka ba zata taɓa barinta ta zauna lafiya ba.Ni bani da matsala da son da kake yi mata, amma ka nemi yardarta, da ta mahaifiyarka tukuna”Nasir ya ce “To Abba, na gode sosai” ya tashi ya bar ɗakin.Nabila banɗaki ta shige, ta rufe ƙofa ta kira Viper.”Yanzu fisabilillahi ka kyauta mini kenan? Ka saka an yi mini faɗa, Allah ne ya rufa mini asiri, dan Allah ka daina zuwa in da nake, gara ka kirani na zo da kaina””Ki je ki yi tunani a kan abun da na saka ki, ki san abun yi sati biyu kawai ki ke da shi””Ya kake bani umarni ne a haka, ka din ga lallaɓani mana, why are you always bossy ne? Sai da safe zan duba na ƙara effort, ina iya ƙoƙarina a kai, tauye ni ake yi, ka san ba ni da kowa sai Allah ni, amma ka yi mini addu’a in sha Allah ni zan kawo ƙarshen bunkure””Allah ya sa” ya kashe wayar.***Ramma ce ta ƙurawa wayar Abdul ido, ta kalli ƙofar banɗaki, yana ciki yana wanka, ta miƙa hannu ta ɗauka ta bar ɗakin.Bai jima ba ya fito daga banɗakin, sai dai ya nemeta ya rasa a ɗakin, ya fita nemanta, ya tafi kitchen, ya tarar da ita a tsaye a kitchen, da wayarsa a kunnenta cike da rashin gaskiya.Babu tsammanni ta ji ya fizgota, ya kwaɗa mata mari, har sai da ta faɗi ƙasa.Ya duba call logs ɗin sa, ya ga ba a ɗaga kiran da ta yi ba, ya kalleta a matuƙar fusace ya ce “Saboda kin ga ina ɗaga miki ƙafa shi ne zaki tsallake gona da iri, zaki wuce makaɗi da rawa? Bari na koma miki ainihin Abdul ɗina, kuma wannan huakan da ki ka yi, dai-dai yake da sake nesanta kanki da iskar ‘yanci. Kuma bari na sake gaya miki, babu wani mahaluki da ya isa ya rabani da ke a duniyar nan ko waye shi, idan kin ga dama ki cigaba da ƙoƙarin lallai sai kin bar gidan nan, zaki ga yadda zan yi da ke”ya fice daga kitchen ɗin ya bar a zaune, hannunta riƙe da kuncinta, hancinta har ya fara zubar da jini, saboda azaba.Ta rasa me ma yakamata tayi, saboda zuwa yanzu zuciyarta ta ƙeƙashe, kukan ma ba iya yin sa take yi ba.Ta ja wuri ta zauna sosai saboda jirin da take ji.***Sallama take yi a tsakar gida, ta ce “Na shigo ko na koma?”Umma da take ƙofar kitchen ta ce “Idonki kenan arfa? Yaushe rabonki da gidan nan?””Tuba nake umma, ayyuka ne sun yi mini yawa sosai, amma ayi mini afuwa dan Allah”Umma ta ce “To Allah ya yi jagora””Amin umma, ina sumayya?””Tana ɗakinta”Nabila ta nufi ɗakin sumayya, ta sameta tana ta aiki a cikin computer, sallamarta kawai ta amsa, ta mayar da hankali ta cigaba da abun da take yi.”Sumy, dan Allah ki kalleni mana”Sumayya ta ɗago ta kalleta ta ce “Idan na kalleki mai zai amfana miki, ni da nake munafuka?”Jiki a sanyaye ta ce “Dan Allah ki yi haƙuri, nayi kuskure abun ne ya bani mamaki ya ɗaure mini kai”Tuni hawaye ya cika idon sumayya ta ce “A yadda muke da ke, ban taɓa tunanin wani zai kawo miki aibuna ki yadda ba, ba tare da kin yi bincike ba, amma kai tsaye ki ka danganta ni da kalmar munafunci, baki san wahalar da nake ta yi dan kare rayuwarki ba”Nabila ma sai ta saka kuka ta ce “Dan Allah masoyiyya kiyi haƙuri ki yafe mini, ɓacin rai ne, kin ga sam baki yi mini bayanin komai ba, na samu labarin an saka ki kina bibiyata, dole na shiga damuwa kuma ke baki gaya mini ba”Sumayya ta dubeta ta ce “Waye ya gaya miki ana bibiyarki ta hanyata?””Ba shi da amfani faɗar, amma dan Allah waye ya saka ki bibiyeni, ki din ga kai masa rahotona?”Sumayya ta kalli Nabila da take ta share mata hawaye, Nabila cikin jin kunya da sanyin jiki, take ta ƙara bawa Sumayya haƙuri.Sumayya ta numfasa ta ce “Honorable indabo ne”Nabila ta waro ido ta ce “Indabo kuma? Meye alaƙata da shi? Me na yi masa?”Nan Sumayya ta warware wa Nabila yadda suka yi da Indabo, lokacin da ya ce taje gidansa su yi program.Hankali a tashe Nabila ta ce “Amma meyasa baki gaya mini ba Sumayya?””Ya za ayi na gaya miki? Ya ce muddin ki ka sani, zaki iya rasa ranki, kuma na san dole zaki iya aikata wani abu, da zai sanya su yi miki illa, babban abun da ya bani mamaki bai wuce lokacin da muka yi waya da ke ba, ki ka ce kin haɗu da Viper, ya ƙara rikicewa gaba ɗaya, amma na tabattar masa da ƙarya ki ke yi, baki haɗu da shi ba, ina tunanin akwai wani abu a tsakanin sa da Viper, dan cewa yayi, zai yi wa Viper tarko da ke, ya kama shi”Gaban Nabila ya faɗi, gaba ɗaya sai kanta ya kulle.”To tayaya zan zama tarkon da za a kama Viper? Meye alaƙata da shi?”Sumayya ta ce “Ban sani ba, amma dan Allah ki nutsu, kar ki aikata wani abu da zai saka ya cutar da ke, wallahi rashin imanin mutumin nan ya wuce tunaninki, ke hatta a wurin aikina akwai masu saka mana ido, da kin zo sai su kirani, su ce me muka tattauna, har wayar da nake yi da ke suke bibiya shiyasa nake kiranki da wasu lambobin””Na shiga uku, to ni uban me na yi masa? Sumayya da wace lambar suke kiranki?””Private number ce, ba sa kirana da lamba” zumbur Nabila ta tashi.Sumayya ta ce “Ina zaki je?”Tayi waje da sauri ta ce “Zamu yi qaya kawai” a tsakar gida ta yi wa Umman Sumayya sallama ta fice.Ƙaramar wayarta ta ɗauko, ta kira Viper, ya ɗaga a rikice ta ce “Kana nan ne, gani nan zuwa””Ke tsaya mana, ki zo ina?””In zo wurinka mana ina cikin ruɗani da rashin fahimta””Koma menene ki nutsu, ki yi mini bayani ina jinki””Ni ba wani bayani da zan yi maka, kawai zan zo gani nan”.Ya ce “Hanya babu kyau, na gaya miki kar ki zo fa””To a ina zamu haɗu? Rayuwata tana cikin hatsari, ni kawai kana ina, na shga uku”Viper da yake zaune ya tashi tsaye ya ce “Malama ki nutusu ki yi mini magana, kina cikin hatsari kamar yaya?”A fusace ya ce “Na gaya miki hanya babu kyau, ana bibiyarki ko kin manta? Za a fara tracking wuraren da ki ke zuwa yanzu haka. Ki tsaya ki saurare ni.”To ina jinka””Zan tura miki adress ɗin da zaki same ni, idan kuma ni in zo shikenan”Ta ce “A’a kar ka zo””Ki samu wuri ki ajiye motarki, zan turo miki adress ɗin in da zaki same ni”.”To ka yi sauri” ta cigaba da tafiya a motar, tana waige-waige ko zata ga wani yana bin ta.Ya turo mata adress ɗin da zata same shi, ta ajiye motarta, ta bi adress ɗin.Wurin kamar garden haka yake, ba kowa a wurin, sai manyan bishiyu, ga wurin sanyi mai daɗi.Tana tsaye tana waige-waige, ta ciro wayarta, tana ƙoƙarin kiransa, kawai ta ganshi unexpected a bayanta, sakin wayar tayi ta hau ihu.”Menene?””Ba tsorata ni ka yi ba, sai ka zo kana wani sanɗa da na zura da gudu fa, ka daina wannan sanɗar”.Ya kalleta ya ce “Idan ban yi sanɗa ba, ban amsa sunan Viper ba, sai da aji hucina, ko bayan nayi ɓarna a ankare da na zo wuri, gani menene?”Ta ƙare masa kallo ta ce “Ɗan beauty”Ya tsuke fuska ya ce “Neman me ki ke yi mini?”Cikin damuwa ta ce “Mu zauna, na gaji da tsayuwa”Suka samu wuri suka zauna, ta ce “Dan Allah Viper meye haɗina da Indabo? Shi ya saka sumayya take bibiyata. Ta gaya masa yadda suka yi da sumayya.Ya numfasa ya ce “To me zan yi miki?””Ban gane ba, ka gaya mini meyasa Indabo yake bibiyata, me nayi masa?”Cikin ko in kula ya ce “Ya za ayi in sani?””Dan Allah ka gaya mini, kai ma fa ka tambayeni ko na haɗu da shi, me kake ɓoye mini ne? Dan Allah ka gaya mini mana””Meyasa liti ya rikice ranar farko da ya ganki, ya amince ya kawo ki maɓoyata?”Ta ce “To ya za ayi in sani, ina tambayarka kana tambayata? Ka gaya mini mana”Ya ɗago ya tsura mata ido.”Ka yi magana mana, dan Allah meyasa yake bibiyata, ta ce ya rikice lokacin da ya ji na ce na haɗu da kai” still bai yi magana ba.”Talk please”Zuciyarsa ya ji tana harbawa da sauri, ya girgiza kai ya ce “Kamar na ji kin ce mamanki ta rasu ko?”Turɓune fuska ta yi ta ce “wai ina ta rayuwata, kana tambayata wani abun daban”.”Nan gaba zaki so jin dalilin da ya sa na tambaye ki, bana surutun banza ni”Kamar za ta yi kuka ta ce “To ni yanzu ya zan yi da wannan indabon?”Viper ya ce “Ba ruwanki da shi, ni ne dai-dai shi, ki ji da bunkure karki manta, sati biyu kawai na baki ki yi mini aikina”Ta narke murya ta ce “Nawa zaka bani ne da ka sakani aikin, ka san dai ba lawyer gwamanti ce ni ba””Nawa ki ke so?””Kai nake so” gabansa ya faɗi, da ya tuna Jauhar sararta ce faɗar haka.”Kina wuce gona da iri” yayi maganar yana kallon in da yake facing.”Daga zuwanka, ka saka DSP ya haɗa ni da Abba, an ce sai na duba samarina na fito da miji, sai ka aureni, tun da duk kai ka janyo koma menene””Are you serious? Ɗan ta’addan zaki aura kina gidan masu kaki?”Ta ce “Eh mana, ka bani dama na zama yar suganka”Ya ɗora hannunsa a kan ƙirjinsa, ya ce “Ki daina wannan wasan ba na son sa ko kaɗan, haryanzu ina jin motsin jauhar a cikin zuciyata. Idan ki na irin wannan maganganun ji nake tamkar na aikata zunubi mai girman gaske, babu wani abu da zan iya haɗawa da soyayyar jauhar a zuciyata, ki kiyaye wannan ki daina wannan wasan, kar ya zama gaske”.”Ba ka son yar sugar kenan sai madara ko?””Ke ki ka san sugan, ni ba na ta’amalli da shi ma””To zuma fa ko mazarƙwaila” ya yi mata shiru.Ta tashi ta ce “Kar ka so ni ɗin, amma to ni ya zan yi da wannan indabon bashi da imani, kar ya kashe maka ni”Viper ya ce ‘Idan ya kashe ki ya hutar da ni”Murguɗa masa baki tayi, ta kama hanyar tafiya. Sai da tai nisa sannan ya waiwaya yana kallonta.Ita kanta murmushi ta yi, saboda yau ya sake, babu wannan alamar ƙuncin da damuwa a tare da shi.***Da daddare Nabila tana kan social media, taga wani dogon rubutu, da aka yi, na jinjinawa Naja bunkure, a kan ayyukan ta na jin ƙai. Sumayya na ganin posting ɗin, tayi tagging ɗin Nabila.A take Nabila tayi reposting ɗin post ɗin, tare da caption kamar haka *Lokaci yayi da yakamata mu san haƙiƙanin ayyukan da Bunkure foundation ke gabatarwa, shin da gaske dan talaka take yi, ko kuwa dan rufe ɓarnar masu ido da kwalli kawai take yi?.Mu duba case ɗin yarinya zulaiha, da ya faru shekarun baya, wadda ta fuskanci cin zarafi, daga wani ɗan mai kuɗi, bunkure foundation sun shiga case ɗin domin su tsaya mata, a hukunta shi, amma ƙarshe sai labarin mutuwar zulaiha muka ji, ta kashe kanta ta hanyar shan fiya-fiya, shi kuma wanda ya aikata, yana shekarar ƙarshe na kammala karatun degree a ƙasar Amurika.Bana ƙwaina sai da zakara, akwai tarin hujjoji da nake da su a kan maganata.Jikinta na tsuma, ta yi posting ɗin, ta rufe data.Tayi addu’oin kwanciya bacci, ta kashe wayarta, har ta rufe ido maganganun ta da Viper suka faɗo mata.Lumshe idanunta ta yi, amma maganar sa ta din ga kai komo a zuciyarta.*Ba zan iya haɗa soyayyar jauhar da komai ba, dan haka ki ma daina wannan wasan*Dafe ƙirjinta ta yi, ta ce “Na shiga uku, tausayin sa kawai nake ji, da wasa nake yi, me nake ji a raina ne?’ ta tambayi kanta.Wasi-wasi ne kawai, ta bawa kanta amsa tare da kwanciya.Washegari da safe bayan sallar asuba, ta kwanta ta sha bacci, kasancewar lahadi ce, babu aiki.Sai wajen ƙarfe goma ta tashi, ta yi wanka ta fito ta shirya ta ɗauki wayarta ta kunna.Jerin saƙonni ne suka din ga rige-rigen shigowa wayarta, bayan ta kunna data.Messages kuwa, ga na barrister Habib, ga na summaya.Ƙarƙashin post ɗin ta kuwa, comment ya kusa dubu, da masu kare Bunkure da masu zagin Nabila, kasancewar alherin bunkure galibi mutane suka sani.Ta ɗaga kiran wayar sumayya da yake shigowa, ta ce “Ya ne?””Nabila daga tagging ɗin ki a post, kin rikita media”Nabila ta ce “Ai makaho ba ya sanin ana kallonshi sai an taɓa shi, bar su su gama haukan da kare ta, ina nan zan saki maganar ramma bayan an kuma zaman kotu”.”Amma Arfa kar fa ta yi miki wani abu””Ba abun da ta isa ta yi, ai ina da hujjoji “”Allah ya ƙara tsare ki, zan cigaba da nemo miki sahihan bayanai a kan ta”Naja ta kalli posting ɗin ta yi murmushi ta ce “Bari na nuna wa yarinyar nan ainihin kalata da take son gani.Kira Nabila ta gani da private number, babu tsoro ko fargaba ta ɗaga.”Wane irin move ne haka, kin san mutanen nan ba za su barki ba ko?”Nabila ta ce “Kai ka bani aiki ka ce nan da sati biyu, aka yi sara a kan gaɓa, sumayya ta yi tagging ɗina a kan post ɗin, na ga ya dace na tofa wani abu”.Viper ya ce “Shikenan, amma ki shirya matakin da za su ɗauka a kanki”Nabila ta ce “Ina da kai ai, idan na je aiki zan kiraka”Nasir ne ya faɗo ɗakin ta ya ce “Nabila, wai meyasa baki da hankali ne”Ta kalleshi ta ce “Me nayi kuma?””Ban ja miki kunne a kan Naja’atu Bunkure ba? Kin je kin tsokanota, gashi an fitar da sanarwa hukumar DSS suna nemanki, an shigar da ƙararki for defomation of character”.
Ayshercool 08081012143



