Hausa novels

Ruwan Zuma Page 27 Hausa Novel

(27) Haydar yaci gaba da bawa Laila labarinshi. “Bayan mun koma ne nake tambayan Ammi meyasa aka rusa mana gidanmu? Tace dama ba filinmu bane, kuma gwamnati ta sha aika mana notice kan cewa mu tashi amma bamu tashi ba. A wannan gurin Ammi ta had’a mana d’akin leda kamar tent muna kwana a ciki, sai dai in zamu fita dole mu d’auki duk valuable abunmu idan ba haka ba zamu zo mu samu an kwashe, kuma koda Ammi zata kwana tana tambayar wa ya d’auka baza a kulata ba. A hakan naci gaba da zuwa makaranta har na shiga nursery two Ammi na cigaba da sana’arta. Watarana headmaster yace in fad’awa Ammi yana son magana da ita, koda tazo d’aukana na fad’a mata tace sai gobe idan tazo ajiyeni sai ta shiga. Hakan kuwa akayi, washegari da safe suka had’u a office d’insa yake fad’a mata yana buk’atar mai aiki a gidansa idan tana so domin matarsa tana da ciki kuma an hanata aikin wahala. Ko da Ammi taji zai bata gurin zama sai ta yarda washegari muka tattara kayanmu muka isa gidansa. Ba wani tsararren gida bane kamar yanda nayi tsammani, asali shima talaka ne sai dai yafi k’arfin abinci da gurin kwana. Wani d’aki aka bamu d’an k’arami muka zauna a ciki, wannan shine karon farko dana fara kwana a cikin d’aki na gaskiya ba langa-langa ba.�? “Ammi ta daina sayar da plantain ta fara kula da matarsa da kuma yayansa uku wanda biyu daga cikinsu tare muke zuwa makarantarsa. Ban fad’a miki sunana da aka sanni dashi ba ko? Idan ana kiran sunan students a register kika ji sunan Chijioke Towolawi nine zan amsa, sai daga baya Ammi ta sanar dani dalilinta na bani wannan sunan yare biyun, wai saboda koda fad’a ya tashi na tsakanin k’abilu zan tsira saboda duk na tara sunan Yoruba da Igbo. Zamanmu a gidansa zama ne na jin dad’i domin bayan d’akin da muke kwana a ciki ita matar gidan bata tsangwamarmu ko da wasa. Ammi ce take yin komai na gidan har girki kuma ta kwasa ta bamu muci mu k’oshi. Bayan wata bakwai da komawarmu gidan matarsa ta haihu a asibiti. Washe gari zata dawo gida Ammi tana gyare-gyaren tar6anta Mr Eze ya shigo gidan ya sameni ni da yaransa muna wasa a tsakar gida, kudi ya bamu yace muje mu sayi minti sai mu zauna a waje muyi wasa kar mu shigo cikin gida. Da murna muka kar6i kud’in muka tafi shago mafi kusa damu, shi kuma a wannan lokacin ne ya samu damar yiwa Ammi fyad’e a d’akin matarsa. Muna tsaka da wasanmu naji ina son komawa gida domin Ammi bata ta6a bari nayi nisa ko na jima a waje, hakan yasa na koma da gudu na samu matar gidan ta dawo a cikin Taxi tare da ‘yan uwanta mata biyu. Ganina yasa ta bani wasu abubuwan na shiga dasu cikin gidan, sai dai jin kukan Ammina yasa na sake abun hannuna k’asa na ruga zuwa d’akinsa naga abunda yake yi. Ban san menene na d’auka na kwad’ayin mishi a kanshi ba amma dai na fasa masa kai wanda hakan yasa ya sauk’a daga jikinta yana ihu yana dafe kanshi.�? “Laila a ranar matar gidan da ‘yan uwanta ne suka mana duka ni da Ammi. Domin cewa yayi Ammi ce take seducing d’insa ni kuma na shigo na fasa masa kai don mu mishi sharri mu 6ata masa aure. Su suka watsar mana da kayanmu waje da warning d’in kar su sake ganin mun shigo unguwar balle gidansu. Shiyasa da naga kayana a watse a falo na tuno da wannan labarin.�? “I’m so sorry Haydar, I have no idea haka kayi fama da rayuwarka. Sannan ina baka hak’urin abunda Abul yake maka wanda nasan kaima ka sani baya cikin hayyacinsa ne. Kuma na kwashe kayan na adana maka, I’m sorry.�? Ta fad’i hakan tana ta6a gefen fuskarshi. Kwantar da kan nashi yayi a hannunta yana runtse ido kana ya d’ago yaci gaba, “Daga nan komawa k’ark’ashin gada muka yi, muka samu babu gurin zama mai kyau domin duk mutane sun cike. A hakan muka zamu gurin tsugunnawa muka fara jinyar jikinmu. Washe gari da safe bayan da yawa daga cikin mutanen gurin sun fita bara ko sana’arsu Ammi ta fito da kud’in data tara tana k’irgawa. A nan take fad’a mini zaman Lagos ya isheta zata koma arewa amma kud’inta ba zai kaimu inda take so ba. Bayan kwana d’aya mun samu k’arfin jikinmu muka je babban titi domin yin bara ko zamu samu cikon kud’in da muke buk’ata. Farko da muka fara nine na rufe idona Ammi kuma tana rik’e da sandana, sai dai dana ji tsayuwar mota sai in bud’e idona a ga cewa k’arya nake yi, hakan yasa wasu suka fasa bamu kud’i wasu ma suka bimu da zagi.�? Ya k’arisa maganan yana d’an dariya kad’an. Murmusawa Laila tayi tana share hawayen fuskarta yaci gaba. “Ganin zan 6ata mana plan ne yasa Ammi ta k’ar6i sandan ni kuma na rik’e ta rufe idanunta. A haka muka samu kud’i mai d’an dama domin da gaske nake kuka ina cewa a taimakeni Mamana bata gani bata da abincin bani. Ana hakan ne wata babbar mota ta tsaya aka mik’o mini kud’i na k’ar6a sai naji an kira sunan Ammi cikin k’araji ‘SUWAIBA�? hakan yasa ta bud’e idanunta cikin razana tayi arba da mutumin da yake ciki. Ina tunawa a guje Ammi ta jani muka bar gurin mutumin na binmu a baya. Sai dai da yake Ammi ta fishi sanin lungu da sak’on Lagos sai muka 6ace mishi. Daga nan tasha muka nufa cikin sauri domin a yanda naga Ammi ta razana da ganin mutumin nan nasan yana d’aya daga cikin mak’iyanmu masu son ganin bayanmu. Awa biyu da haka motarmu ta tashi zuwa Abuja, daga nan muka canja mota zuwa Kaduna muka fara neman gurin kwana. Da yake Kaduna ba kamar Lagos bane da ko’ina ka samu zaka kwanta sai gurin kwanciya ya gagaremu muka yi ta gagaramba a gari, da kyar muka samu wani dattajon arziki ya bamu shagonshi muka kwana washe gari yace mu san inda dare ya mana. Tasha muka k’ara zuwa muka hau motar Jos. A ranar farko da muka sauk’a a garin Ammi ta samu aikatau a gidan wata babbar ma’aikaciyar gwamnati. Motarta ce tazo wucewa muna bara dalilin kud’inmu ya k’are tasa aka tsaya tana kallona wai na mata kyau, hakan ne yasa ta d’aukemu ta kaimu gidanta tare da bawa Ammi aikin wanki da guga na masu gidan. Boys quarters muke dashi na ma’aikata a gidan wanda na mata daban haka na maza daban.�? “Albashin Ammi na farko ta sakani a makaranta naci gaba da zuwa lokacin ina da shekara takwas. Bayan mun dawo Jos ne Ammi ta fara koya mini addinina tace mini mu musulmai ne gaba da baya, kuma a nan ta daina 6uya idan zata yi sallah. Lokacin sanyi yana zuwa sauran ‘yan uwanta masu aiki suka matsa mata ta kira wanzami ya mini kaciya wanda daga ni har ita kuka muke yi an kasa samun mai rarrashin wani. Bayan na warke naci gaba da zuwa makaranta har na gama primary. A nan ne na fara matsawa Ammi da maganar ina Babana da dangina suke, dukan data mini ne yasa na daina tambayarta kwata-kwata har na shiga secondary school. A nan ne kuma Ammi ta fad’a mini sunana na gaskiya wai Aliyu Haydar ba Chijioke Towolawi ba. Ita kuma tace mini sunanta Suwaiba ba Mama junior da ake kiranta dashi ba.�? “Bayan gama secondary school d’ina na lura Ammi na cikin damuwa, koda na tambayeta dalila sai cewa da tayi wai zama guri d’aya risk ne, mak’iyanmu zasu iya gane inda muke. Babu wanda ya sani muka tattara kayanmu zuwa tasha muka hau mota har zuwa nan Kanon Dabo. A nan Ammi ta saya mana d’an k’aramin gidan da muke ciki a hannun wata dattijiya wacce mijinta ya rasu ya barta babu d’a babu jika ta koma garinsu. Da kyar na samu shiga Jami’a bayan wahalan da muka sha na neman addmission Ammi na soya k’osai da doya a bakin titi har na gama makaranta. Kar kice na daina tambayan Ammi inda mahaifina yake, ban daina ba kullum idan abun ya ciyoni sai nayi maganar kuma sai ta mini fad’a ko kuma ta daina shiga harkata har sai na bata hak’uri. Na daina tambayanta su waye muke guduwa, domin nasan tana fad’in hakan ne don kawai in yarda cewa akwai masu son ganin bayanmu. Ranar dana dameta da maganar har na furta mata wata kalmar da bana fatan sake maimaitashi Ammi ta fad’i ta kamu da ciwon zuciya. Ikon Allah ne kad’ai ya tada kafad’unta Laila, tun daga ranar ban sake mata maganan mahaifina da dangina ba sai da kika shigo rayuwata na k’ara jin son sanin waye ni. Laila har yau har gobe ban san wanene ni ba, ban san daga ina nake ba, haka kuma bansan waye mahaifina ba. Kuma nayi alk’awarin har in bar duniya bazan sake tambayar Ammi akan hakan ba, domin dana rasata gwara na mutu a haka ba tare dana san komai a kaina ba. Wannan shine tak’aitaccen labarina dana sani.�? Ya sauk’e ajiyar zuciya yana kallon kyakkyawar matarsa Laila wacce ta aureshi ba tare da tasan komai a kanshi ba. Itama ajiyar zuciyar ta sauk’e kana ta jawoshi ya kwanta a kan cinyarta tana shafa gashin kanshi tana jin tsananin tausayinshi da k’aunarshi na ratsa dukkanin jikinta. “Bari nima in baka nawa labarin duk da nasan ko kad’an ba zai kai naka bak’in ciki ba.�? A nan ta bashi labarinta ta k’are da cewa, “Naga wasu jarabawar rayuwa amma a hakan Alhamdulillah ina cikin ‘yan uwa da dangina. Sannan na gane me kake son fahimtar dani, na gane Haydar.�? Juyo da kanshi yayi yana kallon fuskarta yace, “Shiyasa nake son auren matured mace wacce zata d’auki labarina ba abun kyama da gudu ba sai dai a matsayin jarabawar rayuwa. Ina son tara iyali Laila, tunda bani da kowa ina son ya kasance ni kad’ai na tara zuriyata sun yi yawan da baza suyi kewan danginsu ba.�? Wannan magana ta Haydar ba k’aramin tsoro ya bawa Laila ba, ina ita haihuwan yara da yawa a shekaruntan nan? Ko ba yau ba zasu yi wannan maganan domin zai yi wuya ta haihu ne gaba d’aya. “Baki ce komai ba.�? Yace da ita yana mintsinin tumbinta. “Lokacin sallar isha yayi.�? Ta fad’i hakan tana d’age kanshi daga kan cinyarta. Murmushi yayi ya tashi zaune yana cewa, “Zan yi alwala.�? “Kana nufin har ka karya alwalar magrib d’in?�? Tayi tambayar cikin mamaki. Gyad’a kanshi yayi yana murmusawa yace, “Ba kina kusa dani ba. Naki tana nan bata karye ba?�? “Kwarai ma kuwa.�? Ta bashi amsa in a duh tone d’in nan. “Then ya kamata mu zama d’aya.�? Yana fad’in ya kai hannu jikinta inda yasan dole ya karya mata alwalan. “Haydar, Haydar, Haydarr!!�? Mik’ewa yayi tsaye yana tafa hannayensa irin ya gama aikin nan yace, “Sai kije kiyi alwala Hajiya.�? Yana fad’in hakan ta rarumi pillow ta wurgeshi dashi tana harararsa. Kaucewa yayi pillow ya fad’i a k’asa shi kuma ya fita daga d’akin yana dariya. “Yaron nan ya rainani.�? Ta fad’i hakan tana tashi tsaye ta shige band’aki. Minti kad’an da haka ta fito zuciyarta na bugawa da taji Abul na bugun k’ofar d’akin Sabrin kamar zai 6allata. Falon ta fita tana kiran sunanshi amma yak’i amsawa yaci gaba da bugun k’ofar. Zama tayi a kan kujera hawaye na tsiyaya a idanunta tama rasa me zata yi. A haka Haydar yazo ya sameta yace zai bud’e k’ofar ya duba ta hanashi. “Karka shiga ya maka illah, ka bari yayi bacci giyar ta sakeshi sannan a bud’eshi gobe da safe.�? Jiki a mace ta tashi ta shige d’akinta tayi sallah ta zauna a gurin tana kwararo addu’o’i tana zubar da hawaye. Tana zaune a gurin Haydar ya shigo d’akin ya ajiye mata plate a gabanta tare da ruwa. “Jollof d’in taliya na miki ko kina so, sannan na kaiwa Abul ko zai ci na samu yayi bacci.�? Ajiyar zuciya Laila ta sauk’e kana tace, “Wallahi Haydar bana jin cin abinci, hasalima ko yunwar bana ji.�? “Kici ko loma goma ne karki kwana da yunwa don Allah. Bud’e bakinki in baki.�? Ya mik’a mata fork cike da taliyar. Tsayawa tayi tana kallonshi tana tausayin kanta da kanshi, a lokacin da kowanne ma’aurata suke more amarcinsu su kuma tashin hankali suke ciki. Sannan Haydar dattijo ne ba don ya tsufa ba, sai dai yasan abunda ya kamata yasan rayuwa da abunda ya dace. Yana da hak’uri da nitsuwa, she’s just lucky da Allah yake bata maza masu kyawun hali. “Tunanin me kike yi?�? Ya tambayeta yana mai tsura mata ido. “I was just thinking ba haka aurenka na fari ya kasance ba Haydar. Baka samu kulawa, jindad’i da farinciki irin wanda angwaye suke samu ba, k’arshenta ma sai na sakaka a cikin rayuwata mai k’unshe da new dramas kullum. I don’t deserve you Haydar, kafi buk’atar mace mai less tashin hankali a rayuwarta.�? “I’m glad I married you Laila, kuma ko gobe aka k’ara bani za6i ke zan za6a. Bana son kina fad’in hakan. Eat your food kafin yayi sanyi.�? Zata yi magana ya kwa6eta kamar yanda take yawan masa yace, “Laila!�? Shiru tayi tana jin hawaye na taruwa a idanunta ba don bak’in ciki ba sai don farin cikin samun mutum kamar Haydar a matsayin miji. “Thank you for being you.�? Dafa hannunshi yayi akan k’irjinshi ya d’an sunkuyar da kanshi kad’an yace, “My pleasure Your Majesty. Ina buk’atar her Majesty ta bud’e bakinta in bata abinci don kar ta kwana da yunwa a koreni a fadar zuciyarta.�? Yanda yayi maganar so serious yasa Laila ta kwashe da dariya tana goge hawayenta. “Wai dama ku mata haka kuke? Yanzu kuna kuka the next minute kuma kuna dariya? Confused creatures.�? Hakan ma dariya ya bata ta doki kafad’arsa kad’an tana cewa, “Kana da abun dariya.�? Murmusawa yayi kad’an yana mata kallon k’auna wanda yake jinshi har b’argon jikinshi, can kuma fuskarsa ta zama neutral yace, “Laila kici abinci, wasan ya k’are.�? Gyad’a kai tayi ta kar6i abincin tana ci da kanta shima yana cin nashi ba tare da sunyi magana ba. Loma goman da yace tayi shi tayi ta ajiye plate d’in a k’asa ta d’auki ruwa tasha. “Ashe haka ka iya girki?�? Ta fad’i hakan da gaske domin ya iya girkin. “Wani lokaci ni nake mana tuwo da miya a gida idan Ammi tace baza tayi ba, komai ma na iya har shara da wanke-wanke.�? “Kace kawai in kori masu aikina duk zaka dinga mana.�? Ta fad’i hakan cikin zolaya. “In zaki dinga biyana zan yi.�? Ya fad’i hakan yana tattara kwanukan gurin ya fita dashi waje. Binshi kawai tayi da ido tana mamakin wace irin tarbiyya Ammi ta bashi daya taso haka a nitse sannan ga hankali da sanin ya kamata? Ko dai da gaske wuya na sa wani yaron yayi hankali? All her life bayan rasuwar mijinta k’ok’ari take yi ta bawa ‘yayanta rayuwa mai dad’i wanda baza suyi rashin uba ba, kullum burinta ta faranta musu rai ko da kuwa ba hakan ita take so ba. Shin anya bata yi laifi ba data kasa nuna musu cewa ita rayuwa ba dole aji dad’inta 100% ba? Tayi kuskure mai girma kuma tana addu’an Allah ya ji6anci lamuranta yasa Abul ya dawo kan hanya. Daga falo taji Haydar na kiranta ta amsa ta fita, a bakin d’akin Abul ta sameshi yana tsaye ya bud’e mata d’akin yace ta duba. Lek’awa tayi ta samu Abul ya kwanta har an lullu6eshi an cire mishi takalmansa ta jacket d’insa. A yanda yake kwance so peaceful zaka iya rantsewa ba giya yasha yazo ya kwanta ba. Kamanninsa da Babanshi kuwa kullum k’aruwa yake yi tana kuma jindad’in hakan a ranta. “Nagode Allah ya biyaka da alkhairi.�? Tace dashi yana jan k’ofar ya rufe. “Da yardar Allah komai zai zo ya wuce tamkar ba’ayi ba.�? “Allah yasa.�? “Ameen.�? Ya amsa mata suka koma kan kujera suka zauna tana tsakanin k’afafunshi ta kwantar da kanta kan k’irjinshi. “Laila.�? Ya kira sunanta ta amsa. “Meyasa kike son rufe kanki?�? “Ohh, ban cika yin kitso bane kuma babu dad’i inyita yawo babu d’ankwali.�? Cire kallabin kanta yayi kana ya fara sunce gashinta data tufke guri d’aya ta kuma d’aure da ribbon. “Meyasa bakya son kitso?�? Ya k’ara tambayarta yana cigaba da aikinshi. Shiru tayi na wasu sakanni sannan tace, “Tun bayan rasuwar baban su Abul har yau ban sake yin kitso ba, a ranar da zai dawo nayi kitso k’anana na tar6anshi sai Allah yasa ba zai gani ba.�? “Ina son mace mai gashi kuma mai yin kitso.�? Kawai ya fad’a wanda tasan me hakan yake nufi. “Zan yi Insha Allah.�? Ta fad’i hakan shi kuma ya k’arisa warware mata gashin gabad’aya. “Meyasa kike 6oye mini beauty nan?�? Ya fad’i hakan yana wasa da gashinta wanda ya sauk’o har gadon bayanta. Bata ce komai ba yaci gaba da wasa dashi wanda lokaci d’aya taji idanunta na rufewa ta gyara kwanciyarta a jikinshi tana lumshe ido. Washe gari da asuba ta tashi ta sameta a kan gado, waya dawo da ita d’aki kuma har kan gado? Bud’e k’ofar band’aki aka yi Haydar ya fito d’aure da towel a k’ugunshi yana goge kanshi da wani k’arami. “Kin tashi?�? Ya tambayeta yana takowa cikin d’akin. Gyad’a kai tayi kana ta kai hannunta kan k’irjinta inda taji an bud’e mata ma6allan gurin. “Meyasa kayi wanka da asuba?�? “Boys stuff.�? Tana jin hakan ta gane menene, kunya ce ta kamata ta fara gyara rigarta tana saka ma6allan ba tare data tambayeshi meyasa yayi hakan ba. Har zata tashi sai ta koma ta zauna dalilin jin da tayi kamar period d’inta ya dawo. “Baza ki tashi kiyi sallah ba ko?�? Ya tambayeta yana ajiye towel d’inshi a saman gadon kana ya d’auki fresh boxers ya saka. Bata kawar da kanta ba domin ta saba ganinshi a hakan sau ba adadi tunda ta lura baya kunyar bud’e jikinshi a gabanta ko kad’an. Har ya saka jallabiya ya feshe jikinshi da turare tana nan zaune bata ce komai ba. Har zai fita zuwa masallaci ya tsaya ya dubeta yace, “Lafiyanki kam?�? “Watana ne yazo k’arshe.�? Fuskarsa tayi alamar mamaki yace, “So?�? Don bai gane hakan me yake nufi ba. “In watan yayi k’arshe sai ki dinga kallon mutane or what? I’m sorry amma ban gane ba.�? “Kaje ka dawo zan fad’a maka karka rasa sallah.�? Kallonta yayi na wasu sakanni ya murmusa sannan ya kama hanya ya fita. Tana jin ya fita ta sauk’o da gudu tana duba inda ta 6ata taga bai ma bar jikinta ba. Sai dai Haydar ya 6ata gurinshi da yake coffee bedsheets ta shimfid’a musu. Kunya taji sosai ba kad’an ba ta yaye zanin gadon ta kai band’aki a kan zata wanke da kanta baza ta bawa kowa ba. Kafin ya dawo tayi wanka ta gyara jikinta tasa wata blue doguwar riga mai bin zubin jiki. Har zata d’aura d’ankwali sai kuma ta fasa ta gyara gashinta ya sauk’a a bayanta. “Hurul Ain.�? Shine abunda ya fara furtawa ya tako zuwa gurinta ya tura kanshi cikin wuyanta yana shinshinan gashin kanta. Dariya tayi ta tureshi kana ta fara shimfid’a sabon bedsheet a kan gadon nasu. “I’m sorry.�? Yace da ita yana kama kunneshi kamar k’aramin yaron da yayi laifi. Bata ce komai ba har ta gama domin ita kunya ma ya bata. Tana gamawa ya d’ale gadon ya kwanta yana mata signa, yace, “Kizo mu kwanta.�? Fita tayi daga d’akin tana cewa, “Hala ka manta kana zuwa aiki ko? Kayi bacci kad’an kafin in gama breakfast kaci ka tafi.�? “I love you.�? Ya bita dashi kana ya koma yayi kwanciyarshi yana murmushi. Sai da ta gama breakfast sannan ta shiga d’aki ta sameshi ya gama shiryawa zai fito, a tare suka fito suka nufi dinning yaci abinci ta bashi key d’in mota. “Yau bazan samu fita ba, zan jira Abul kar ya tashi ya fita ban sani ba.�? Ta fad’i hakan tana rakoshi bakin k’ofa. “Ki tanadi Panadol ki bashi, domin zai tashi da ciwon kai.�? “An gama Dr Aliyu Haydar.�? Ta fad’i hakan cikin zolaya. “Baki da kunya ko?�? Yace da ita yana matsowa kusa da ita ta fara ja da baya tana murmushi. “A bani goodbye kiss.�? Yayi caging d’inta da hannunsa. Kafin suyi wata magana suka ji ana bud’e d’akin Sabrin, hakan yasa da sauri Haydar ya saketa ya koma can gefe itama ta fara tufke gashin kanta. Abul ne ya fito a hargitse yana dafe da kanshi yayi hanyar kitchen ba tare daya lura dasu ba. Hakan yasa Haydar ya fita daga falon Laila kuma ta bi bayan Abul tana kiran sunanshi. A firgice ya juyo yana kallonta yana tuna meya kawoshi gidan, a take fuskarsa ta sauya ta koma ta 6acin rai matuk’a ya shige kitchen d’in ta bishi a baya. Inda suke ajiyan magani ya bud’e ya d’auki panadol yasha kana yayi hanyar fita ta rik’o hannunsa da k’arfi ta tsayar dashi. “Ba magana nake maka bane kayi shiru kana jina?�? “To me zan ce miki.�? Yanda yayi maganar kamar bada mahaifiyarsa yake yi ba yasa Laila taji wani d’aci a ranta amma ta had’iye bata nuna mishi a fuskarta ba. “Kaje kayi sallah ina son magana da kai.�? Baice komai ba ya kwace hannunsa ya fita daga kitchen d’in ya barta cikin bak’in cikin wannan sabon halin nashi. Bin bayanshi tayi kana taga yayi hanyar fita ta kwala mishi kira ya tsaya bai juyo ba, “Idan har ka fita a gidan nan sai na maka abunda baka zato Abul. Ka dawo kayi sallah sannan ka kazo ka sameni a nan falon.�? Tana fad’in hakan ta juya ta samu guri ta zauna ta bashi k’eya yanda bata ganinshi. Ya kai minti d’aya tsaye a gurin sannan yazo ya wuce d’akinshi cikin fushi ya samu a rufe. Jijjiga k’ofar yayi tamkar zai 6allata Laila tayi kamar bata san me yake yi ba. Cikin fushi yace,“Ina key d’in d’akina?�? “Ka shiga inda ka kwana kayi sallah.�? Ta bashi amsa mai had’e da umurni. Kwafa yayi ya shige d’akin yana doko k’ofar da k’arfi sai da Laila ta tsorita. Runtse idanunta tayi da k’arfi hawaye na gangarowa a fuskarta amma tayi saurin sharewa. Bayan yayi sallah ya fito d’auke da jacket d’inshi yana kumbura fuska tamkar zai ci babu. Tsayawa yayi a can gefe yayi shiru bai ce komai ba. Itama bata tanka mishi ba taci gaba da duba wani littafin addu’o’i dake hannunta bakinta na motsi. “Gani ai ko.�? Yace da ita yana gyara tsayuwarshi ganin ta k’i kulashi. “Ka samu guri ka zauna.�? Tace dashi ba tare data d’ago ido ba. Zama yayi yana huci yana kallon ko’ina amma banda ita. Ajiyar zuciya ta sauk’e kana ta ajiye littafin tace, “Abul me yake damunka? Wani irin lalacewar rayuwa ce zai sa ka fara shaye-shaye?�? “Na tsani aurenki da yaron nan.�? “Shine dalilinka?�? Ta tambayeshi ba tare da taji mamakin hakan ba. Ko bai fad’a ba tasan menene matsalarsa. Bai ce komai ba ya kawar da kanshi gefe yana huci. “Abul nice na haifeka ba kai ka haifeni ba, sannan ya kamata ka sani ni zan za6awa kaina duk wanda ya dace dani ba tare da nabi ra’ayin d’aya daga cikinku ba. Nice na raineka tun baka san kanka ba har ka girma ka fara tunanin decisions d’in dana d’aukawa karan kaina bai dace ba. Menene ribarka idan kayi shaye-shaye ana zaginka a gari? Ko kana tunanin hakan zai sa nayi wani abu da kake so ne? Kai ba k’aramin yaro bane Abul, kasan mai kyau da mara kyau. Ya kamata ka gane cewa wannan d’abi’an daka d’auka baza ta ta6a 6ullewa da kai ba, zaka wahalar da kanka da kuma rayuwarka sannan ka jawowa kanka fushin Allah da kuma zagin mutane. Aurena da Haydar ba haramun bane asali ma koyi muka da da sunnar Manzo SAW wanda shima da bazawara wacce ta fishi shekaru yayi auren fari. Ka fad’a mini inda muka yi 6ata ko laifi.�? “Baki san aurenki mai ya jawo mini ba Mama, kin sa na zama abun dariya a cikin abokaina da wasu mutane da muke wata harka tare. Idan baza ki rabu dashi ba ni kuma bazan zauna a gidanki ba.�? Yana fad’in hakan ya tashi zai tafi. “Kenan kafi son kaga farincikinka data abokanka akan nawa ko? Kana nufin baka damu da ni me nake so ba? Kenan baza ka iya hak’uri a kan wata maganarsu mara tushe sai dai ni kake so inyi hak’uri in bi yanda kuke so? Abul kana sona kuwa? Ka ta6a ko sau d’aya kayi abunda zai faranta mini rai alhali kai baka so hakan ba? Abul me ka d’auki rayuwata ne?�? “Daa kinsan halin da nake ciki da baki fad’i haka ba.�? “Wani hali ne kake ciki? Ka kaini shiga tashin hankali ne ni da nake ganin d’ana yana shaye-shaye kuma yake son kashe mini aure? Abul kana da son kai, baka son kowa sai karan kanka ka sani.�? “Of course ina sonki, amma wannan karon abunda kika yi nima ya shafeni da inda bakya tsammani. Ina cikin tashin hankali Mama, amma baza ki ta6a ganewa ba.�? “Idan ka fad’a mini zan gane, ka zauna ka fad’a mini su waye mutanen da kuke harka dasu suke maka dariyan.�? Dariyan takaici yayi kana ya zauna ya dafe kanshi yace, “Ko ni ban sansu ba balle ke Mama. They are from the dark web, wanda mu muke yin duk wasu abubuwa da bazan iya fad’a miki ba. Don Allah ki rabu dashi wallahi nayi miki alk’awarin daina shan kayan maye har duniya ta nad’e.�? “Abul.�? Ta kira sunanshi cikin tsorita da maganarshi hawaye na tsiyaya a idanunta. “Idan kuma bata kashe aurenta ba fa?�? Duk suka jiyo suna kallon Mas’ud a bakin k’ofa wanda dama Haydar bai rufe ba. Shiru Abul yayi baiyi magana ba ya kawar da kanshi cikin jin haushin zuwanshi a wannan lokacin. “Kinga abunda nake nuna miki ko Kalti. Abul bai damu dake ba, babu ruwanshi da farincikinki. Idan har akan wata maganar banza ta tsakaninsa da abokansa zai so ya kashe miki aure to banga a rayuwa me zai iya baki don kiyi farin ciki ba.�? Ita dai Laila kuka kawai take yi domin abun ya wuce tunaninta, wai me suka d’auketa ne? Mutum-mutumin da bata da feelings na farin ciki ko akasinshi? Meyasa bazai iya tayata farin ciki ba a lokacin da take jin itama ta cancanci hakan? “Ka tashi mu tafi gidana a can zaka zauna.�? “You can’t force me.�? Ya fad’i hakan yana tashi tsaye zai fita daga gidan Mas’ud ya mishi rik’oshi. “You’ll do as i said Abul.�? Yanda yaga fuskarsa babu alamar wasa yasa yayi shuru yana huci yana k’unk’uni. Da haka ya jashi suka fita a gidan suka bar Laila na kuka tana jimamin halin Abul wanda bata san dama haka yake ba sai yanzu. Ta jima a gurin tana zaune har masu aikinta suka zo suka mata aiki suka tafi, komawa cikin d’akinta tayi ta d’auki laffayanta ta saka zata fita. Har taje bakin k’ofa sai ta tuno Haydar ya d’auki motarta ya tafi aiki, ta isa wajen maigadinta tace ya kira mata Adaidaita sahu zata je unguwa. Bayan ya tafi ita kuma ta koma ciki a nan take tunanin ya kamata ta fad’awa Haydar tunda zamanshi take yi. D’aukan wayarta tayi ta kirashi ta d’auka yana cewa, “Matar Haydar.�? “Ina so dama zan je gidan Ummii ne.�? Ta fad’i hakan kai tsaye domin tasan yana cikin office d’insu ne. “Ki jirani in zo in kaiki.�? “A’a ka bari ba jimawa zan yi ba, na aika a kira mini adaidaita sahu.�? “Shikenan, amma idan kin tashi dawowa ki kirani in zo in d’aukeki. Kuma karki fita da laffaya ki saka hijab.�? “Meyasa Haydar? Nafi son laffaya yafi mini dad’in sakawa.�? “Ni dai ga abunda nace Laila.�? Cikin fushi tace, “Naji.�? Kana ta kashe wayarta tana jin haushinsa a zuciyarta ba kad’an ba. Yanzu a gaban abokan aikin nashi yake fad’a mata haka yana bata doka? Kamar ta fasa zuwa gidan Ummii domin ya kamata ta zauna dashi ya daina kafa mata sharudd’a irin haka. A haka ya ganta yace yana so, sannan batun ya hanata saka laffaya bai taso ba, bazai yiwu ba kuma bazata d’auka ba.

Mum Fateey 👌

Back to top button