Uncategorized

Tubali Book 1 Chapter 2 hausa Novel

 

“Jibi”. Ya bata amsa a taƙaice yana mai kallon Kyakkyawar fuskarta. 

Ita kuwa gyara zamanta tayi tare dasa hannu ta amshi cup ɗin ruwan sanyin, da Hajia Rabi’ah ke miƙa mata-ta ajiye shi bisa Stoll din baƙin glass dake gabanta.

“Nagode”. Ta faɗi cikin nitsuwa, sannan ta kalli Mahmoud dake bin fuskarta da ido.

Cikin yanayinta na nutsuwa da kuma bayyana zallan ajinta na y’a Mace tace.

“Akwai tabbacin jibi zai dawo? Sannan ta Abuja ko Lagos zasu sauƙa?”.

Wayarshi ya zaro a al’jihun rigarsa yana mai lallatsata kana yace.

“In sha Allah jibi zasu dawo.

Dan last night muna tare da Deen ƙanin Usman PA’nshi. 

Yayi magana da yayan nashi kan jikin mamansu ya tashi, yaushe zasu dawo.

Toh nan Usman ɗin ke cewa jibi zasu dawo.

Iya abinda na sani kenan, sauran bayani kuma sai dai in tuntuɓi Deen ɗin”.

Ya ƙare maganar yana sa wayar a amsakuwa yadda duk zasuji.

“Hello Deen ya Gida”.

Cewar Mahmoud.

Deen dake zaune gaban mamansu wanda yanzu ya gama magana da Usman ne yace.

“Lfy lau Alhamdulillah Mahmoud”.

“Yah jikin Mama”.

“Alhamdulillah jiki da sauƙi”.

Ya bashi amsa yana miƙa mata maganin.

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.

“Yah Usman ɗin yana dawowa ko?”.

Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.

“Eh to, zasu dawo, amman sai jibi fa kuma nan ma wata ƙil in sun iso su kwana a Abuja wata ƙil suda nan sai ranar jumma’a”.

ya ƙare mgnar da sanyi.

“Ayyah ba komai ai in dai jikin da sauƙi, jumma’a kamar yaune Allah dai ya dawo dashi lfy. Ka gaida min Mama da jiki Allah ƙara ƙarfin jiki”.

“Amin Amin”. yace kana sukayi sallama.

Katse kiran yayi tare da juyowa ya kalleta.

Numfashi suka sauƙe ita da Hajia Rabi’ah.

Sai kuma tace.

“Alhamdulillah, toh Mahmoud ko zaka bani number Deen”.

Da sauri yace.

“A a in fa yasan me kike bincika bazai saurareki ba”.

Hajia Rabi’ah ne ta amshi zancen da cewa.

“Kada ki damu Jannart in sha Allah komai zai tafi dai-dai.

Shi Mahmoud ɗin shi zai rinƙa samo mana bayani.

Tunda kuna da number’n juna zaike miki bayani, ba sai kin fito kinzo nan ba, tunda fitar naki aikine mai zaman kanshi.”

Cikin gamsuwa da hakan tace.

“Toh shike nan My Aunty, Ngd Matuƙa Allah ya saka da al’khairi”.

“Amin Amin.” tace

Tana mai gudun kada aikin ya bar hannun yarinyar tunda kowa ya ganta dai yasan bawai tana yin aikin dan neman kuɗi ko suna bane, tana yine dan ra’ayin tane gashi du-du watanni huɗu tayi da fara aikin kuma suna jin daɗin mu’amala da ita, so dama sanyin da shirin yayi shiyasa aka canza wanda ke yinsa a baya.

Kuma da alamun tana matuƙar jin daɗin aikin.

Kiran Salman ne ya shigo wayarta.

Da sauri ta amsa tare da karawa a kunne.

“Assalamu alaikum”.

Tace cikin sassayan sautin ta.

Daga b’angarensa kuwa murmushi yayi tare da cewa.

“Wa alaikissalam, Jannart kinbi diddigin Rayyern d’in? Kuma wane lbri kika samo mana a kanshi? “

Cikin yarda da kai tace.

“Duk motsinshi na cikin tafin hannuna!”.

Dariya mai sauti Salman yayi.

Hakama Hajia Rabi’ah da Mahmoud.

“Karsashi’nki da ƙarfin guiwarki akan aiki yana burgeni Jannart”.

Cewar Salman.

Cikin sauƙe numfashi tace.

“Toh ba doleba Salman, tunda naji ana shirin korata, ai sai inda ƙarfina da hikimata suka ƙare”.

Cikin wasa yace.

“Ke har wani ƙarfi a garreki da dai kin tsaya a hikimar na yarda”.

Murmushin daya sanya beauty point  ɗin ta lotsawa tayi. 

Haka dai suka ɗan tattauna batun bayan ta mishi bayanin abinda ta ji kan dawowarshi.

Saida tayi sallan azahar ne kuma ta fito suka nufi gida.

A kan hanyarsu ta komawa ne, Baba Ado driver’nta ya ɗan juyo ya kalleta cikin kulawa yace.

“Jannart yanzu dai ciwonki da sauƙi ko?”.

Numfashin ta ɗan fidda kana a hankali tace.

“Alhamdulillah da sauƙi dai zance, amman yana yawan motsa min a kwanan nan kamar yana son tashi.”

Cikin tausayawa yace.

“Toh amman har yanzu babu wani maganin da ake baki sai allurar da akeyi duk watan ne?”.

Kai ta gyaɗa mishi tare da cewa.

“Eh”.

Numfashi ya ɗan fesar kana yace.

“Allah ya sauƙaƙa yasa zakkan jikine al’farmar Annabi da al’ƙur’ani”.

Cikin jin daɗi tace.

“Amin Baba Ado nagode!”.

A can Ethiopia birnin Addis Ababa, kuwa.

Riyyam-nsra ne tsaye gaban wayarsa daya tsaida.

Rawa yakeyi da murmushi a fuskarsa.

Sai kuma ya kalli gefensa.

Wata kyakkyawar budurwa wacce a ƙalla suyi sa’anni.

Murmushi yakeyi cikin harshen Hausa yake cewa.

“Jibi iwar haka ina hanyar Nigeria, su Zayton kuma sai dai ayi ta aikin zumbura baki.

Fan’s ku gani, wai kishi takeyi dani”.

Da sauri ta kai mushi bugu tare da matso ƙwallar idanunta, tana faɗin 

“Mammy! Mammy!!”.

Wata kyakkyawar matace mai Kekkyawar sura da jiki da shiga ta kamala, wacce kyan surarta ya iya boye ainihin shekarunta, ta fito daga cikin wata ƙofar da fuskantar inda ya kafa wayar tashi.

Ɗan gudu-gudu da tsalle-tsalle yake yana zagaya parlon Zayton na biye dashi a baya.

Da sauri yayi tsalle tare da ɗan sakin ƙara yace.

“Ohh Mommy”.

Jin ta ɗan sa hannu ta bugi ƙeyarshi.

Tura baki yayi tare dasa hannunshi ya shafa ƙeyar yana mai zazzarewa Zayton ido.

Abin gwanin ban dariya da ka gani kasan akwai Kekkyawar shaƙuwa, ƙauna, tausayi, da son juna.

Ɗauke wayar tashi yayi ya sake video a shafinsa na TIKTOK.

Kun san matsalar su kenan ƴan TIKTOK duk abinda zasuyi ko sukeyi sai sun nunawa duniya, More Especially irin Riyyam-nsra da yayi shuhura yayi zarra da dubban dubatan masoya mabiya, musamman a cikin kwanakin nan da yai mgn da Hausa ya janye mana hankalin matasan Nigeria, domin kuwa ayanzu followers d’insa harsun d’arawa two million. 

Gane abin da yayi dinne kuma yasa. Mammy matsoshi da kyau ta kama kunnenshi ta ɗan matse.

Ƙara ya kuma ɗan saki, wanda yasa Zayton tuntsirewa da dariyar jin daɗi tana ɗaga mishi gira.

Ita kuma Mammy cikin ɗan faɗa tace.

“Wato kai Riyyam baza ka taɓa canzawa bako, duk motsinmu sai ka bazamu a duniya? Kai kam inaga kana gab da nuna duniya yadda kake kashi ma ko”.

Hannunshi yake ɗan yayyarfawa tare da cewa.

“Afwan Yaah Mammy na tuba, wayyo Hamma Mammy zata tsinke min kunne”.

Dariya Zayton tayi tare da cewa.

“Zai aikata fiye da hakama Mammy ja kunnen da kyau”.

Hannunshi ya kai ya bugi hannunta tare da cewa.

“Yarinyar nan ki shiga hankalinki fa”.

Fuska ta haɗe tare da cewa.

“Waye yarinyar yaro in ka manta in tuna maka nice babba 15 minute nake baka, kaga kuwa dole ace da mijin iya baba, dan 15 minute ba 15 second bane”.

Sosai Mammy ta saki murmushi suna matuƙar sata nishaɗi da ɗebe mata kewa, da danne mata duk wani ƙuncin rayuwa, Especially in suna faɗa kan girma.

Zayton son girma kamar gyambo, 15 minute da take bashin nan ji takeyi kamar shekaru goma sha biyar take bashi.

Gefe ta zauna kana suka zo suka sata a tsakiya.

Cikin sakin fuska ta shafa kan Riyyam-nsra tare da cewa.

“Zoh nan autana”.

Gwalo yayiwa Zayton tare da ɗaura kanshi bisa cinyarta tuni kuma ya sake haɗa video.

Murmushi yakeyi yana yiwa Zaiton signal tare da cewa.

“Mammy asamin al’barka”.

Da sauri itama ta sako kanta tare da cewa.

“Mammy ai nice mace, dan haka ya riƙe girman ya matsa ni in kwanta”.

Cikin yin ƙasa da murya Mammy tace.

“Ya isa haka ku bari, Dida na bacci kada ku tada min ita”.

Toh sukace dan yadda tayi mgnar ba wasa.

Bayan ya saki wannan video ɗin ne kuma.

Ya gyara zamanshi ya fuskanci Mammy da kyau jin tana cewa.

“Riyyam sam hankali na. baya kwanciya da wannan rawan kan naka! Ina jin tsoron kayi nesa dani, gaba ɗaya ka juye ka zama ɗan nanaye, ka zama tamkar mazari duk inda kake sai rawa, sai waƙa, sai haɗa comedy duk inda kake waya na hannu, kai kaɗai a ganka kana dariya ko kana kuka ko kana haɗa fuska ko layi, kai gasu nan dai barkatai, ka zama ɗan Film a fili ka rubuta lbri ka tsara ka bawa kanka umarni kayi shirin. 

Ga ɗan karen yawo yau kace zaka tafi waccar ƙasar, gobe kace zakaje waccar gashi ka zama babu sirri duk inda kake an sani, shiyasa nake jin tsoron zuwanka Nigeria duk inda kaga mata sai ka bisu da ido”.

Da sauri ya gyara zamanshi cikin nitsuwa kamar ba shiba yace.

“Mammy babu komai sai al’khairi, ki yarda dani bana wani mugun abu, in ke bakya gani na ai Ubangijin talikai daya busan numfashin yana ganina”.

Uhum tsakanin uwa da ɗa kenan ya gane cewa tana zargin shi ne ko tana tsoron taɓarɓarewar tarbiyarshi.

Cikin sauƙe nannauyan numfashin tace.

“Wlh badon dole ba, bazaka jeba, amman ba komai Allah ya kaika lfy ya dawo da kai lfy. 

Sai dai dole ka nitsu ka dena wannan rawan kan”.

Hannunshi yasa ya kame kanshi kana yace.

“Toh Mammy na dena”.

Murmushi tayi hakama zaitun.

Washe gari ranar Laraba, Kano Nigeria.

Cikin bacci taji numfashin ta, na fita a cushe, kana tana shaƙan zazzafan ƙamshin turaren sa mai masifar ƙarfi da tafiya da numfashin ta.

Idonta ta buɗe cikin wahalar numfashi.

Da sauri ta ida buɗe su duka tare da fisgo numfashin ta a wahalce.

Sabida ganin Yah Junaid da tayi sunkuye a kanta hannunshi na kan ƙirjinta.

Wani irin tsuma da karkarwa jikinta ya farayi, da azaban ƙarfi.

Cikin tsananin tsoro da razanin ta yunƙuro zata tashi, tare da furta “innalillahi wa innalillahi raji’un.”

Wani irin azabebben tsoro firgita kaɗuwa da gigitane suka dirar mata lokacin ɗaya jin yadda yasa hannunshi ya matse ta  tare da murtuƙe fuskarshi.

Cikin tsananin rawan jiki take zaro ido murya da baki na rawa tace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un Y… Ya… Yah… Juna..Junaid,  me haka!!”

Wani irin masifeffen kallo ya watsa mata, tare da kai hannunshi duka biyu kan breast ɗinta, yayi musu wani irin masifeffen kamu wanda yasa ta saki wani irin gigitaccen ƙara, lokaci ɗaya kuma numfashin ta ya fara off and Dawn,  ciwonta na gab da tashi.

Shi kuwa Junaid wani irin sanyi yakeji a ransa tare da rumtse tafin hannunsa.

Mom kuwa dake ɗakinta, ita da Abdul cikin razanin jin sautin muryar Jannart ta miƙe tsaye jiki na rawa, ta fito falo.

Dai-dai lokacin kuma Jannart ɗin ta fara wani irin fiffizgewa sabida numfashin ta dake shirin barin gangan jikinta.

Wata iriyar fitinenneyar zufa mai cike da zafi,  ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta.

“Hahhhh! Uhhhhhhhh!! Fuhhhhhhhheeeeyyyy!!! M…Mom!” 

Ta fuzgo maganar da ƙarfi lokaci daya kuma numfashin ta ya dena shiga sai fifita.

Jiki na rawa Mom ta kutsa kanta cikin ɗakin nata.

Shi kuwa Junaid wani irin fitinenne abu yakeji yana tsirgar masa.

Hannunshi ya kirjinta. Tare da yiwa breast ɗin ta wani azabebben riƙon da saida yaji. 

Gamsuwa shaiɗan cinsa.

Kana ya juya ya nufi ƙofar fita.

A bakin ƙofar sukayi kiciɓis da Mom.

Wani irin mugun kallo ya watsa mata.

Ita kuwa Mom wani irin kallon  tuhuma take binshi dashi.

“Mchewww”. 

Taja wani dogon tsaki ganin bazai bata hanya bane yasa ta matsa gefe.

Wucewa yayi tare da cewa.

“Sai kiyi ai”.

Ita dai bata bi ta kanshi ba, ta wuce cikin ɗakin.

A gigice ta nufi kan gadon tana kiran ta.

“Jannart! Jannart!! Jannart!!!”.

Ta Ƙarisa kiran sunanta a gigice tare da hawa kan gadon ta jawota jikinta tana cewa.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Abdul! Abdul kazo”.

Da gudu Abdul ya nufi ɗakin sabida dama yana falo Juinad ne ya hanashi shiga.

Cikin ruɗani tace.

“Abdul kira min Daddynku. Ka gaya mishi jikin Jannart ya tashi”.

Da sauri yace.

“Toh Mom amman bari in fara kiran Dr Lukman”.

Ya ƙare mgnar yana kara wayarshi a kunne.

Ita kuwa Mom sai jijjiga Jannart daketa kokuma da numfashin ta takeyi.

Cikin rauni Abdul yace.

“Assalamu alaikum. Daddy”.

“Na’am Abdul ya akayi ne?”.

Alhaji idi sele Dakata dake zaune a Office nashi Barrister Kabir Saleh Dakata na zaune a gabanshi.

Ya amsawa Abdul da kulawa.

“Daddy jikin Jannart ne ya tashi, na kira Dr Lukman kuma baya ɗagawa”.

Da sauri yace.

“Innalillahi Bari in kirashi yanzu-yanzu”.

Ya ƙare mgnar da katse kiran.

Cikin kula Barrister Kabir Dakata yace.

“Yaya lfy kuwa? Jikin Jannart ko?”.

Cikin damuwa yace.

“Eh”.

Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.

Bari inje mu tafi asibiti”.

Tuni kafin yayi wata magana ma ƙanin nashi ya fita.

Abdul ya kuma kira tare da cewa.

“Ga Abbanku na zuwa da likita”.

Toh yace kana ya katse kiran.

Shiru yayi yana nazartar irin son da Ƙanin nashi keyiwa yaranshi, Especially ma Jannart yana mata wani irin so  na musamman.

So na da ban a cikin yaranshi.

Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da meda kai ya jingina da kujera.

A hankali yake jujjuyawa, yana mai ƙoƙarin kauda tunanin da zuciyarsa ke kawo mishi.

Shi kuwa Barrister Kabir yana fita kai tsaye.

Asibitin Hamda

Ya wuce. Yana mai kiran babban  Dr.

Yana tafe cikin gudu kamar maiyin doguwar tafiya.

Yana isa kai tsaye Office ɗin Dr Sajo ya wuce.

Yana ganinshi ya miƙe tsaye tare da cewa.

“A a Ƙanina! Ka iso, ko ina mara lafiyar?”.

Cikin girmamawa da alamun tsohuwar amintaka yace.

“Barka dai Yaya Sajo,  dan Allah kayi haƙuri mara lafiyar tana gida.

Ni kuma daga Campany’n Yays Dakata nake, so kafin in koma gida in ɗaukota komai zai iya faruwa, kasan matsalar cutar athsman shiyasa nace bari in biya mu tafi tare. Dan Allah kayi haƙuri”.

Murmushi Dr. Sajo yayi tare da fara tattara abin buƙatarsa yana mai tuno amintaka da mutuntakar da ke tsakaninsa dasu a baya.

Cikin kuma kula da amintaka yace.

“Ba komai ƙanina muje, dama na gama yau bani da aiki”.

Cikin jin daɗi ya juya ya fita, shi kuwa yana biye dashi a baya.

Motarshi suka shiga, shiyasa yake taka motar da kyau.

Tsoro yakeji yasan yadda ciwon ke wahalar da ita.

A can gida kuwa, gaba ɗaya Mom da Abdul sun rikice.

Ita kuwa Jannart tuni ta gama gigicewa ta fita haiyacinta, fuskarta nan tayi jazir.

Sai fuzgo numfashin takeyi da ƙarfi.

Wayar Abdul ne tai ringing yana ɗagawa yace.

“Abba jikin fa ya tsananta”.

“Subahanallahi  Abdul gani nan zuwa yanzu”.

Toh  yace kana ya katse kiran.

Suna isa kai tsaye cikin gidan sukayi.

Abban na gaba Dr Sajo na biye dashi a baya.

Suna shiga Dr. Sajo ya fara aikinsa, allura yayi mata dan samun dai-dai-ta numfashin ta.

Allah cikin ikonsa kuma a take ta fara sauƙe ajiyan zuciya, lokaci ɗaya jikinta ya fara sakewa.

Sai ga wani irin bacci mai nauyi ya kwasheta…

Kusan a tare suka sauƙe ajiyar zuciya baki ɗayansu.

Cikin kuma sauƙe numfashi Abba yace.

“Alhamdulillah”.

Hakama Mom.

Abdul kuwa shiru yayi yana mai jin tausayin yar uwar tasa.

Dr. Sajo kuwa, harhaɗa kayan aikinshi yayi, kana ya kalli Barrister Kabir, gyaran murya yayi tare da cewa.

“Ciwonta yayi zurfi a jikinta, kuma  bata bin doka da ƙaidar maganin yadda ya kamata”.

Da sauri Mom tace.

“Ai ba’a bata magani Allura kawai akeyi mata duk wata”.

Cikin mamaki yace.

“Allura kuma? Toh wacce iriyar Allura ce duk wata kuma!?.”

Cikin sanyi Abdul yace.

“Gaskiya  bamu san wacce iriyar Allura bace”.

Da sauri Dr Sajo ya kalli Barrister tare da cewa.

“Wanne Dr ne yake duba ta?”.

Numfashi mai nauyi Barrister ya sauƙe kana a hankali yace.

“Dr. Lukman ne”.

Wani irin shiru Dr Sajo yayi tare da  alamun nisan nazari.

Kana yace.

“Ok muje ko Barrister”.

Toh yace kana suka nufi hanyar fita.

Sai kuma ya ɗan juyo ya kalli Mom dake gyarawa Jannart din kwanciyarta, cikin nitsuwa yace.

“Kada ki damu, zata samu lfy in sha Allah, sannan zamu canza mata Dr da zai na kulawa da ita da kyau”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Mun gode”.

A hankali Dr. Sajo ya juyo ya kalli Barrister Kabir dake jan mota, dan medashi asibitin sa.

“Ƙanina akwai buk’atar a canzawa Jannart likitan da zaina dubata.” 

Cikin nitsuwa Barrister Kabir ya ɗan juyo ya kalleshi tare da cewa.

“Yaya Sajo meyasa!?”.

Kafaɗarshi ya ɗan ɗaga tare da cewa.

“Noh ba komai, kawai dai ciwonta yanada buƙatar gamayyar likitocin zamani bawai a tsaya kan ɗaya ba, a samo wani shima ya gwada kwarewar sa”.

Uhum Dr.Sajo bai tuna cewa da  babban Lawyer yake mgna ba.

Cikin fahimtar wani abun  Barrister Kabir yace.

“Toh ba matsala in sha Allah za’ayi haka. Amman  ina zamu samu likitan?”.

Da sauri yace.

“A wannan mai sauƙine, akwai wani Babban Doctor yarone matashi mai ƙuruciya da sanaiyar ilimin likitanci na juya da yau, kana harna gobe yana bincika yasan aikinsa, mun gamsu dashi, Dr Rayyern Mai-nasara.”

Da sauri Barrister yace.

“Zakayi mana hanyar ganinshi kenan? Dan ance yana da wuyar gani”.

Ya ƙare maganar yana yin parking.

Kai ya ɗan juyo ya fuskanceshi tare da cewa.

“Eh to Gaskiya yana da wuyar samu, saboda yawan aiyuka, kuma a wani sashin bashi da wuyar gani, in har kaje Mai-nasara Hospital ɗinsa, muddin dai yana ƙasar, toh zaka ganshi sai dai ko in baya ƙasar, in kuma bakayi sa’a ba, sai a turaka wurin wani Dr ƙaninsa da kuma amininsa ɗin ba shiba, tunda yanzu aikin Company’s dinsa sun tasoshi gaba, dole ya samo wasu likitocin bayan shi. 

Saɓanin da da shi kaɗai ke jan ragamar asibitin.

Amman idan nasa hannu na baku takarda zuwa gareshi kuna zuwa shi ɗin zaku gani”.

Cikin gamsuwa Barrister yace.

“Alhamdulillah nagode matuƙa Yayana”.

“Haba ba komai Kabir yiwa kaine. Yauwa sai kuma batun allurar da akeyi matan nan, abar yi matashi akwai buƙatar in santa, sannan ina son sanin sunan allurar”.

Ya ƙare zancen yana fita daga cikin motar.

Cikin gamsuwa Barrister yace to.

Kana sukayi sallama.

Ganin lokacin sallan azahar yayine kuma yasa ya nufi masallaci.

Koda aka idar da sallah kuwa.

Gidan yayan nashi ya koma.

                 Ethiopia.

Dr Rayyern Mai-nasara ne. Tsaye cikin wasu tattausan Suit masu masifar kyau da taushi tare da sheƙi.

Inda Riga da wondon suit din suka kasance pink color masu dauke da zane-zanen fari, sai kuma neck tie ɗin shi daya kasance fari, yayinda long sleeve dinsa ma ta kasance white, takalmin dake kafansa kuwa pink color ne mai dauke da harafin R-M.

Sai kuma Diamond watch din dake hannunsa mai ɗan karen sheƙi da tsada.

Wayarshi kirar iphone 12pro max ne saƙale a kafaɗarshi yayinda ya mannata a kunne yana magana.

Kana kuma hannunshi ɗaya na riƙe da System ɗin shi. Daya hannunshi kuma na lallatsashi.

Bisa alamu aiki mai muhimmanci yakeyi.

Ga kuma wani irin masifeffen ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa da yake fitarwa.

Lallausan Sajenshi nan ya kwanta lib, yayiwa kyakkyawar fuskarsa kawanya sai sheƙi yakeyi.

Haka kuma Ɗan madaidaicin bakinsa mai jajayen lips na motsawa a hankali.

Yayinda siraran idanunshi suka fito ras, cikin ɗan siririn glass mai ruwan garai-garai, irin na Doctor’s daya liƙashi cas bisa karan hancinsa.

A hankali ya juyo ya kalli Usman daya shigo cikin alamun shiri.

“Sir gani”. Usaman ya fada anutse.

Da idanunshi yayi masa nuni da jakarsa, yana maici gaba da maganar da yakeyi a wayar.

“Uhumm”. Yace tare da lumshe idonshi.

A can ɗaya sashin kuwa ba tare da damuwa ba Sulaiman yaci gaba da magana.

Sabida sanin haka Allah ya halicce Rayyern mafi akasarin lokuta maganar Uhumm, ne ko eh ko hmm koko a’a

Bai cika yawan surutu ba, da fari gani suke miskilanci ne, sai daga baya suka fahimci abin da gaskene. Dan muddin za’ayi ta surutu ko hayaniya ko magana da ƙarfi a kanshi ko kukan yaro ko babba, a take idanunshi ke kaɗawa suyi jazir, lokaci ɗaya ciwon kai ke rufeshi larurarsa.

Ido ya ɗan juyo yana kallon Usman dake tsaye gefenshi.

Yayinda kuma yake jin Sulaiman na cewa.

“Wallahi Rayyern ni kamanninku ya daina bani mamaki yanzu sai dai tsoro, Allah ko da yayi magana da hausa ko muryarshi  iri ɗaya da Ramadan kuma”.

A hankali yace.

“Hmmm Sulaiman social media ka biyewa ko?”.

Da sauri yace.

“Dan Allah tsaya kaji, yaushe zaku dawo?”.

A taƙaice yace.

“Jibi!”.

Cikin fidda numfashi Sulaiman yace.

“Toh gashi kuma shi yaron yau zai taho Nigeria, ni nai zaton yau nema zaku dawo ince Allah yasa ku haɗu a jirgi kaga zahiri, abu kamar an dama kunu an raba har ɗan makolloto yake dashi irin naka fa”.

Ɗan gajeren numfashi mai d’auke da gajiya Rayyern ya fesar tare da cewa.

“Uhmm, it’s Okay a gaida Baby”.

Yana faɗin haka ya katse kiran.

Sai kuma ga wani kiran ya shigo.

Da sauri ya zauna bisa kujerar bayanshi kana ya amsa kiran.

Cikin tsananin girmamawa hade da ladabi da biyayya da kuma tarin mutuntaka yace.

“Assalamu alaikum”.

A can ɗaya sashin kuwa, wani kyakkyawan mutum ne mai cikar haiba kamala ne, zaune.

Alhaji Bashir Muhammad Mai-nasara kenan, sai Mami mai ɗakinshi dake gefenshi.

Kana ɗan matashin ƙaramin ɗansu Dr Ramadan Mai-nasara na zaune gaban Abba’n nasu.

Cikin tarin so kula bege da kuma ƙauna,

Alhaji Bashir ya gyara zamanshi tare da cewa.

“Wa alaikassalam”.

Cikin jin daɗin jin muryar mahaifin nashi yace.

“Abba Barka da safiya”.

“Barka dai Rayyanu”.

Ido ya lumshe cike da son mahaifin nashi yace.

“Abba kuna lafiya?”.

“Lafiya lau Alhamdulillah, ga Mamynku da Ramadan wai in tambaya musu yaushe zaka dawo, suna  kewarka”.

Murmushin gefen baki daya bayyana fararen kyawawan haƙoransa yayi, cikin kuma sauƙe numfashi yace.

“Nima ina kewarku Abba in Sha Allah yau ina hanya amman Abba kai kaɗai fa”.

Murmushi yayi fahimtar cewa.

“Shi kaɗai yasan yau zai dawo kenan.”

Ramadan kuwa murmushi yayi sabida jin abinda Hamman nashi ya faɗa.

Mamy kuwa Kekkyawar mace mai cikar haiba, murya ta ɗan ɗaga tare da cewa.

“Toh me zan dafa maka”.

Idonshi ya lumshe fahimtar sun jishi kenan.

Cikin sanyi yace.

“Mamy’na komai ma”.

Amsar wayar tayi tare da cewa.

“Cin zaƙi zai Barka kaci abinda zan dafa maka ko?”.

Cikin fuskar annuri yace.

“Yesssss! Mamy”.

“Toh shike nan Babana Allah ya kawo min kai lfy”.

“Amin Amin Mamy”.

Yace cikin lumshe ido

Daga nan sukayi sallama.

Kana ya juyo ya kalli Usman kana a taƙaice yace.

“Mu je”.

Da sauri Usman yace.

“Sir ina muka nufa?”.

Cike da mamaki Usman ya ɗago kanshi da sauri ya zuba mishi ido cikin al’ajabin jin yana cewa.

“Nigeria”.

Ya buɗe baki zaiyi magana ya ɗaga mishi hannu tare da nuna mishi ƙofar fita.

Haka yasa ya gimtse maganar kana ya ɗauki kayyakin nasu

Suka fita.

 

Boke International Airport Addis Ababa Ethiopian.Suka nufa kai tsaye

Still Kai tsaye Airport parking suka nufa.

Bayan Driver’n’shi yayi parking.

Da sauri Usman ya fito ya buɗe mishi, marfin motar.

Cikin nitsuwa ya zuro ƙafarsa ta dama waje , tare da sauƙeta ƙasa ahankali, Saidai kuma da sauri ya rumtse idanunshi tare da dafe ƙahon zuciyarshi saboda wani irin m…!

Masifeffen harbawa da babbar jijiyar bayanshi tayi, tare da bugawan ƙirji a jere-a jere, har sau uku.

Rumtse idanunshi yayi da ƙarfi dan bai taɓa jin hakan ba,

Wani irin tsuma fatan saman idanunshi suka farayi, kamar shi yake juya su.

Kanshi ya jingina da marfin motar can ƙasan maƙoshin sa, ya fara mai-mai-ta.

“Hasbunallahu wani’imanwakil, innalillahi wa innailaihi rajiun. Subahanallahi Alhamdulillah”.

Shiru PA yayi tare da ratsa gefe, yana mai kallonshi.

Tsawon daƙiƙu 3 suka ɗauka a haka, kana ya yunƙura ya miƙe tsaye tare da ambaton sunan Allah.

Bayan ya fita ne kuma PA ya maida marfin motar ya rufe.

Kana Driver’n’shi da gwamnatin kasar ta bashi, da ƴan tsaron shi suka fito suka mara mishi baya.

Yayinda PA dinsa ke gefenshi.

Saida Suka shiga har cikin iya inda matafiya ne zasu shiga.

Kana sukayi musabaha duk suka juya suka tafi.

Shi kuwa da Usman PA Suka nufi cikin farfajiyar jirgin kasan cewar an fara cikiyan matafiya.

A can ɗaya sashin kuwa. Riyyam-nsra ne, tsaye gaban Mammynsu.

Yayinda Zayton ke manne da kanta bisa kafaɗarshi, tana rau-rau da idanu alamun zubda hawaye.

Cikin yanayi na rauni da taraddadi Mammy ta kalli Riyyam-nsra cike da jaddawa ta kamo hannunsa ta riƙe da ƙarfi ido cike da hawaye tace.

“Kasan manufar tafiyarka, itace burinmu da farin cikin rayuwata.

Ka kuma sani ina tsoron duk abinda zai rabani da kai.

Riyyam ka sani, kaine GARKUWAta nida ƴar uwarka.

 Lallai tabbas munada ciwo a zuciyarmu.

Ina tsoron kada garin gyaran gira in rasa ido.

Kada ban samu baɗiniba in rasa zahiri.”

Cikin ƙarfin hali da jarunta yace.

“Mammy babu abinda zaki rasa, in sha Allah ƙari zaki samu. Da izinin ubangiji.

Babu wani abu na duniya da zai miki hijabi da mallakinki”.

Cikin zubda hawaye Zayton tace.

“Mammy kin ganshi ko, shi baya tsoro, kada yaje yayi abinda zamu rasashi”.

Hannunshi yasa ya share mata hawaye tare da cewa.

“Koda zaku rasani sai kun samu madadina”.

Da sauri Mammy tace.

“Kamin al’khairi cewa, zaka kiyaye shiga hurumin da ba naka ba, kayi iya abinda  ya kaika ka dawo”.

Hannunshi ya ɗaura kan nata tare da cewa.

“Nayi al’ƙawari Mammy na”.

Rungumeshi tayi shida Zayton ɗin jin anata neman matafiya”.

Kanshi ta shafa tare da sa mishi al’barka.

Kana shi yayi ciki, su kuma sukayi baya.

Yana rataye da jakarsa bisa kafaɗa,

yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta matasan zamani.

Kamanninsa da Rayyern sun ƙara bayyana matuƙa, kasan cewar irin shigar Rayyern ɗin yayi.

Wayarshi ya zaro, ya fara ɗabi’ar tasu ta Tiktokers  viewing ya farayi, yana jujjuyawa ƙasan jirgin.

Tare da fara, mgn da Hausa.

“Assalamu alaikum Al’ummar Nigeria”.

Sai kuma ya haura ya ajiye wayar bisa steps din marfin jirgin, kana ya dawo baya, ya fara takowa a hankali yanayi yana ɗan rawa, da tsalle.

Mafi akasarin mutanen dake bayansa matasane, shiyasa suka tsaya suna murmushin calikancinsa.

Yana isa gab da wayan second ɗin daya saita na video na cika.

Dan haka yasa hannunshi ya ɗauki wayar kana ya kutsa kai cikin jirgin…

Zaune yake bisa kujera no 23 acan sama VIP, kusa da jikin windown  jirgin.

Yayinda Usman ke bayanshi.

Wasu files ya zaro cikin briefcase ɗinsa, tare da biro, a hankali ya sunkuya ya fara buɗe takardun, yana sa hannu a cikinsu ɗaya bayan ɗaya.

Shi kuwa Riyyam-nsra tafiya yakeyi yana ɗan dudduba no ɗin kujerun.

Yana isa kusa da Rayyern ya tsaya tare da cewa.

“Yesss! Kunga ga maƙocina, sarkin aiki har a jirgima aiki yakeyi”.

Bai ɗagoba kuma baici gaba da rubutun da yakeyi ba sai ƙirjinsa dake bugawa.

Jakarsa ya zare a kafaɗarsa ya sakata a mazaunin ta.

Wanda haka yasa saida ya matso kusa da Rayyern.

Yatsun sawun yaron ya zubawa ido cike da mamakin ganin yatsun iri ɗaya sak da nashi yatsun Har nails dinsu.

Da sauri ya ɗan ware idanunshi.

Ganin wani ɗan ɗigon tawadan Allah kan tsakiyar farcen babbar yatsar Riyyam-nsra.

A hankali ya ɗan motsa kafafunshi dan sai yaga kamar ƙafarsa ce.

Shi kuwa Riyyam-nsra zama yayi bisa kujerar dake manne data Rayyern, tare da sauƙe numfashi kana ya lumshe idanunshi saboda  wani irin masifeffen bugu da zuciyarsa keyi.

Yayinda gaba ɗaya cikin jirgin kuma kowa ya zauna mazauninsa.

Tsit kowa ya nitsu.

A hankali Riyyam-nsra ya buɗe kwayar idanunshi sabida,

Jin alamun an rufe marfin jirgin kana jirgin ya fara ƙugin tashi.

Shi kuwa Rayyern har yanzu idonshi na kan kyawawan sawun Riyyam-nsra.

A hankali Riyyam-nsra ɗin ya juyo ya kalli gefen da Rayyern ɗin yake.

Da sauri ya ɗan sunkuyo da kanshi ganin inda Rayyern ya fuskanta.

Janye sawunshi yayi tare da cewa.

“Salamu alaikum”.

Da sauri Rayyern ya juyo sabida muryar yaron sak muryar ƙaninsa Ramadan.

Yana juyowa shima Riyyam-nsra yana juyowa ya fuskanceshi.

Wani irin zabura Riyyam-nsra yayi tare da zazzaro idanunshi waje, kana ya yunƙuro zai tashi.

Da sauri ma’aikaciyar jirgin dake bayanshi ta nufoshi da sauri tana cewa.

“Hey Are you okay? please sit down!!”  

Ta ƙare mgnar da ɗan sauti sabida lokacin jirgin, yake raba tayoyin shi na gaba da ƙasa, anfi buƙatar kowa a zaune.

Shi kuwa Riyyam-nsra wani irin masifeffen kaɗuwa al’ajabi mmki da tu’jjudine suka rufeshi, gaba ɗaya jikinshi rawayake.

Cikin buɗe baki ya nuna Rayyern da yatsarshi manuniya kana ya nuna kanshi.

Da sauri ma’aikaciyar ta sake cewa.

“Please I say sit down!.”

Jin hakanne da kuma ganin yanda yake baya baya.

Yasa ya koma bisa kujerar ya zauna.

Cikin kaɗuwa da wani irin fuska mai cike da mmki yace.

“Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, daya haliccemu da kamanni iri ɗaya.”

Shiru Rayyern yayi yana mai kallonshi da gefen ido.

Bai iya shiga sabgar da ba ta saba, a rayuwarsa baya taɓa sa kansa a lamarin da bai shafeshi ba.

Da sauri ya juyo jin Riyyam-nsra na cewa.

“Ina ma Mammy na ta ganka.

Allah mai iko.

Inama ace jirgin nan bai tashi ba, da na roƙeka da girman Allah da Manzonsa muje Mammy na taga mai tsananin kama dani.”

Sai kuma ya kalli sajen Rayyern cikin tsananin farin ciki, so, ƙauna, bege, yace.

“In sha Allah nima daga yau zan fara tara saje irin naka”.

Sai kuma ya matso kusa da Rayyern tare da dago wayarshi.

A hankali Rayyern ya ɗan juyo kwayar idanunshi kan fuskarshi ganin alamun zai manna kanshi bisa kafaɗarsa.

Fuskarshi ya tsuke tare da tsareshi da ido.

Da sauri ya kwaɓe fuska tare da karkata kai cikin turo baki yace.

“Na tuba”.

Sai ya ganshi lammanim ƙaninsa Ramadan sak da yayi haka, dan haka Ramadan kanyi mishi duk sanda ya tsareshi da ido.

Ido ya ɗan zubawa lips ɗin shi yana cewa.

“Please kayi haƙuri hoto zamuyi zan nunawa Mammyna ne, zata so ganinka”.

Ya juyo da nufin zaice a a.

Kawai sai yaji Riyyam-nsra ya ronƙofo kanshi da kyau.

Ya manna kansa bisa kafadarsa.

Yana  murmushi yayi musu selfie.

Sai ya zama suna kallon juna.

Kafaɗarshi ya ɗan manna da nashi dan jin bugun zuciyarsu ya dai-dai-ta yana harbawa a tare a tare, dib-dib.

Sai kuma ya zuba mishi ido ganin ya taso ya zauna ya juyo ya fuskanceshi da kyau.

Hannunshi ya miƙa mishi tare da sallama.

Dole ya bashi hannu ya kuma amsa sallama tunda horaswar Musulunci ne.

“Sunana Zakariyya amman Riyyam-nsra nakeso a kirani, ni ɗan ƙasar Ethiopia nanne, ban taɓa zuwa Nigeria’n ba sai yau.

Dalilin abokina Nasiru Ahmad zanje.

Kai kuma fa?”.

Fuska ya kuma kwaɓewa ganin ya janye hannunsa bai kuma ce mishi komai ba.

Cikin yanayin shagwaɓa yace.

“Please dan Allah gaya min”.

A nitse ya juyo ya kalli yaron da yakeji.

Sonshi da ƙaunarshi na ratsa mishi jinin jiki da zuciya, haka nan yaji wani aminci na musamman a kan yaron.

Cikin tattausan muryar da irinta yakewa Ramadan mgn yace.

“Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara”.

Ruggumeshi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.

“Nice name. Please Zan iya ce maka Yaya?”  

Kai ya jujjuya mishi alamun a a.

Da sauri yayi rau-rau da idanunshi tare da cewa.

“Dan Allah fa, to me zan ce maka”.

A taƙaice yace.

“Hamma Rayyern”.

Wani irin murmushin jin daɗi yayi tare da cewa.

“Hamma Rayyern”.

Sai kuma ya gyara riƙon da yayiwa wayarsa da tun tuni yake musu video.

Kusan a tare suka sauƙe ajiyan zuciya lokaci da jirgin ya gama ɗagawa, yayi sama ya rabu da ƙasar Ethiopia.

A hankali ya ɗan juyar da kanshi kana yaci gaba da  aikin da yakeyi.

Da sauri ya kuma kalli Riyyam-nsra da ma’aikaciyar jirgin nan tazo tana ce mishi lfy kuwa, ɗazu yake ta rawan jiki ta ƙare mgnar cikin yanayin saninsa da son suyi hoto tare.

Murmushi yayi tare da nuna mata Rayyern kana yayi ƙasa da murya yace.

“Yayana ne zai zaneni wai na cika surutu”.

Murmushi tayi tare da kallon fuskar Rayyern kana tace.

“Ka cika rawar kai, ba kamar yayanka ba.”

Sai kuma ta ɗan kalli Rayyern tare da cewa.

“Sir a rinƙa yi mishi faɗa yaron nan baya jin mgn a TIKTOK”.

Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya kalleta ba.

Hoto sukayi da Riyyam-nsra kana tayi gaba.

Usman PA kuwa yana can baya.

A hankali jirginsu yayi ta keta gajumare, yana ratsa sararin samaniya.

Tafiya ta nisa kowa sabgogin gabansa yakeyi.

Amman banda Riyyam-nsra gaba ɗaya ya shigewa Rayyern shigewa mai tarin yawa.

Ya kuma kasa yakice yaron.

Duk yadda yayi sai yake jin zuciyarsa mai raunice a kan yaron.

Wani irin son yaron yakeji har cikin ƙahon zuciyarshi.

Ga mamakinsa ko yanayin cimar da suka fiso iri ɗaya ne.

Domin tunda Riyyam-nsra ya shigo bakinsa bai zauna banza ba, sweet da chocolate ya cisu iri daban-daban.

Ya lura yaron bakinsa bai zama shiru.

Hoto kuwa yayi musu sunfi hamsin video kuwa sun kai goma.

Haka sukaci gaba da keta hazo…

A nan gida Nigeria kuwa gidan Alhaji Idi Saleh Dakata.

A hankali Jannart ta fara motsi, alamun farkawa daga baccin da allurar ya sa tayi na tsawon.

Awanni biyu da rabi.

A hankali ta fara motsa fatar idanunta da sukayi mata nauyi.

Dai-dai lokacin kuma Barrister ya turo ƙofar ɗakin tare da sallama.

A hankali Mom dake zaune gefenta ta amsa mishi.

“Wa alaikassalam, Barrister ka dawo”.

Cikin kula ya gyaɗa mata kai tare da ƙarasowa bakin gado.

Ido suka zuba mata cikin tausayawa, ganin hawayen dake bin gefen idanunta suna sauƙa har cikin kunnenta.

A hankali Mom tasa tafin hannunta ta fara share mata hawayen.

Ba tare kuma da ta buɗe kwayar idanun nata ba, ta fara sakin Shessheƙan kuka.

Zama Barrister yayi a bakin gadon, tare da kamo hannunta  ya riƙe, cike da tausasawa da kulawa yace.

“Sorry Jannart kiyi haƙuri ki dena, kuka dukkan abinda yayi tsananin zaiyi sauƙi”.

Jin muryar ƙanin mahaifin nata, mafi kulawa a gareta ne.

Yasa ta buɗe Idanunta, tare da yunƙurawa, zata tashi zaune.

Da sauri Mom ta tallabota, ta zauna tare da jingina bayanta jikin allon gadon.

Gyara zama Barrister yayi tare da kallon Mom yace.

“Mom Abdul a kawo mata wani abu ta ɗan ci”.

Da sauri Mom ta miƙe tare da cewa. “Toh”. Ta nufi hanyar fita cike da kekyawar niya da zuciya.

Shi kuwa Barrister ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Jannart data gaza tsaida hawayenta.

Murya can ƙasan maƙoshi ta fara mgn.

“Abba ƙirjina yana ciwo! Kaina yana bugawa, tunani ya hanani samun sauƙi, na gaza gano Yah Junaid wanne irin ɗan uwane a duniyar nan.

Anya kuwa Abba Yah Junaid yana da cikekken hankali da sanin haramcin babban fasadin da yake son ai katawa gareni.”

Sai kuma hawaye shar-shar, suka soma zubo mata ta kasa ƙara sa mgnar.

Shi kuwa Barrister cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa da firgici mai birkita tunanin iyaye na gari yace.

“Me kike nufi Jannart wanne irin fasadi kuma?”.

Murya na rawa ta kalleshi cikin rauni tace.

“Abba Yah Junaid fa fyaɗe yake son yamin, a lokuta ma banbanta, yana ƙudirin yi min Fyaɗe, idan na ƙi amince mishi ne, yake yunƙurin kasheni.

Abba cewa yakeyi fa zai kasheni in ban amince da shiba.

Ya kuma ce muddin na gayawa wani zai kasheni.

Wlh Abba zai kasheni.

Abba ya zanyi? Ina zan shiga a rayuwata in samu sauƙi, Ɗan Allah Abba ka rabani da gidan nan in ba haka ba Yah Junaid zai kasheni kuma Daddy ba zai hanashi ba”.

Ta ƙare mgnar cikin tashin hankali.

Da ya ta azzara nitsuwar Barrister Kabir saleh Dakata.

Wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai zafi ta soma tsastsafo mishi.

Cikin tuno abubuwa da dama na rayuwar duniya, ya kamo hannunta tare da fuskantar ta da kyau kana yace.

“Jannart! Jannart!! Jannart!!!”.

Ya kirata sau uku duk da amsa mishi da takeyi.

Cikin yin ƙasa da murya yace.

“In sha Allah, Junaid bazai kashe kiba, da izinin ubangiji sai kin rayu, rayuwa mai Al’barka domin ke ayace, kuma izinace sannan taƙin shaida mai ƙarfi”.

Hannunta ya kuma riƙewa cikin irin sona uba da ɗiyarsa yace.

“Jannart zaki rayu cikin aminci. 

Domin Ubangijin daya raya Annabi Musa acikin gidan Fir’auna cikin lfy da aminci.

Shiya rayaki a gidan nan cikin lafiya da aminci.

Ya rigada lokacin ya ƙurewa Magautan, bazasuyi nasaraba, dan sunyi nasararsu tun shekarun baya sun gama nasara, yanzu nasarar tamu ce. 

Gsky zatayi halinta, in sha Allah zanci gaba da zame miki jigo. Kuma zan nema miki GARKUWA, cikin gaggawa kafin su juyo garemu”.

Shiru tayi tana jin kalaman ƙanin mahaifin nata, sai dai ta kasa sama musu mizanin da zata aunasu ta ajiyesu ta fahimci manufarsu.

Gogewar hausarta batayi surfin ta Ƙanin mahaifin nataba.

Cikin ruɗanin da kalamanshi suka saka mata tace.

“Abba ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ka sake roƙon Daddy ya bakani ko zai yarda, in koma gidanka.”

Cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.

“Jannart sake roƙar tashi tamkar wasa da rayuwarki ne, kamar dai kusanto da a …”.

Da sauri ya haɗiye ragowar mgnar sanin ƙwaƙwalwarta bazata fahimci zancen nasa ba.

Ita kuwa cikin sanyi ta zuba mishi ido.

Dai-dai lokacin kuma Mom ta shigo da tray a hannunta, cup ɗin tea ne mai kauri, sai soyayyan irish da ƙwai.

Cikin nitsuwa tace.

“Abba to..”.

Hannu ya ɗan ɗaga mata tare da cewa.

“Ya isa da yamma zan dawo muyi mgn Jannart kada ki kuma yin kuka”.

Ya ƙare mgnar yana miƙewa tsaye.

Kai kawai ta gyaɗa mishi kana ta bishi da ido har ya fita.

Bayan ya fita Bathroom ta shiga, ruwa ta ɗan watsa, bayan tayi brosh kana ta fito.

Ba laifi ta ji sauƙin sosai numfashin ta ya dai-dai-ta.

Tea ɗin kawai ta iya sha.

Kana ta koma ta kwanta dan Alllurar bata ida saketa ba.

Can cikin bacci taji wayarta na suwa.

“Mahmoud”.

Tace tare da amsa kiran.

Nan yake shaida mata cewa.

Dr Rayyern Mai-nasara yana hanyar dawowa Nigeria tun safe jirginsu ya taso.

Zuwa azahar zasu sauƙa Abuja.

Kuma yau ɗin zasu shigo Kano cikin alamun bacci tace.

“Toh ya akayi kuma lbrin ya sauya Mahmoud ba sai jibi ba kace?”

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.

“Uhumm kin kuwa san waye Dr Rayyern, mutun yana nan tamkar Wahainiya gane shirinsa ko manufarsa fa wuyane dashi.

Ke dai in kin samu dama kiyi ƙoƙarin zuwa Airport da yamma wata ƙil a dace, zan turo miki hotuna Yah Usman PA Yayan Abokina Deen  wanda yayisu a bayan motocin Dr Rayyern ɗin so sai ki ɗauki number’s ɗin motocin ta wannan hanyar zaki iya samun damar bibiyarsa”.

Cikin sanyi tace.

“Toh Ngd matuƙa”.

Daga nan sukayi sallama.

Salman ta kira yana ɗagawa yace.

“Ya jikin namu?”.

Cikin sanyi tace.

“Da sauƙi waya gaya maka?”.

“A’isha Lawal ce ta gaya min tace ɗazu data kira Mom ce ta ɗaga wai jikinki ya tashi.”

Ayyah tace a taƙaice kana ta mishi bayanin da Mahmoud ya mata ta ƙara da cewa.

“Ka shirya da yamma muje Airport ɗin bari in turoma hotunan”.

Toh yace kana sukayi sallama.

Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya sauƙa cikin international Airport Abuja.

Bayan wasu ƴan daƙiƙu, aka fara fitowa.

Mutun kusan 21 suka fito.

Kana Rayyern ya sako ƙafarsa ta dama kan matakalan forko.

Wani irin sassanyan numfashi ya shaƙa a hankali tare da zuƙan iskar ƙasarshi abin sonshi da al’faharin shi.

A hankali ya fara takowa yana sauƙa cikin haiba.

Da sauri ya ratayo jakarsa a kafaɗa tare da biyoshi a baya da gudu.

Usman kuwa shima jakarsu ya ratoyo kana ya biyoshi a baya.

da sauri ya matsoshi.

Juyowa yayi jin an riƙe mishi hannun damanshi.

“Hamma Rayyern daga nan wanne state ɗin zaka tafi”.

Ya rasa gane meyasa zuciyarsa ke bawa yaron amanna ko dan kamar da sukeyi ne.

Sam bai shiryawa amsa mishi ba kawai yaji lips ɗinshi sun furta.

“Kano”.

Wani irin tsalle yayi tare da cewa.

“Yesssss! Nima Kano zan tafi ai”.

Cike da mamaki Usman ya nufosu har yana tuntube tare da cewa.

“Sir wannan fa?”.

Juyowa yayi ya kalli Usman da salon.

Baya son shisshigi.

Shi kuwa Riyyam-nsra da sauri ya dawo kusa da Usman hannu ya bashi tare da cewa.

“Ni ƙaninsa ne”.

Baki buɗe Usman ya bishi da ido.

Daga nan masallacin cikin Airport ɗin suka wuce, ganin azahar tayi har lokacin yaso zarcewa.

Suna idar da salla Usman  ya miƙe da nufin fita ya samo abinci.

Dan yasan ubangidan nasan bazai buƙaci abinci yanzuba.

Juyowa yayi ya ɗan kalli  Riyyam-nsra tare da cewa.

“Bishi kuje Restaurant”.

Kai ya jujjuya tare da cewa.

“Bana jin yunwa”.

Kai kawai ya gyaɗa mishi.

Nan suka zauna har la’asar tayi.

Bayan an idar da sallane kuma, suka koma ciki.

Domin shiga jirgin da zai wuce Kano.

Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai jirginsu ya tashi daga birnin tarayyar Nigeria zuwa Kano ta dabo tumbin giwa.

A nan cikin Kano kuwa.

Jannart ce zaune cikin motar, Salman kana shi kuma yana gaba  gefe.

Baba Ado dake  jansu.

Yayinda sauran garadan dake tsaronta, suke hangame da baƙi a zatonsu tana can cikin ma’aikatar nasu, dan sam basu lura da lokacin da ta fitoba, koda yake Salman ne ya bawa Baba Ado key kana ya jawo motar har zuwa bakin mashigansu ya kawo mishi.

Shiyasa suka fita, basu ganeba.

Kai tsaye filin jirgin sama na malam Aminu Kano suka nufa.

Sosai kuwa Jannart tayi kyau acikin shigar pallazo da kuma tight shirt din dake jikinta, wanda ya bayyana lafaffen cikinta, kasancewar kuma rigar nata na d’an bayyana nipples dinta ne, yasa ta daura wata Navy blue fashion top akan shigar ta ta, wanda tsawonsa ya kawo har guiwanta, Yayinda ak’afanta take sanye da wani navy blue hill shoe, na company’n gucci mai kyau da tsada da uban tsini, akanta kuwa wani had’add’en medium vail ne wanda ya sauko harkan kirjinta.

Sam akan fuskarta babu wani kwalliya sosai, saidai kuma hakan bai hana zallar kyawun fuskarta bayyana ba, Yayinda small lips dinta suka sha peach lipstick, acikin jikinta kuwa wani sassanyan k’amshi ne yake tashi.

Suna shiga cikin Airport ɗin sukayi paking a Airport parking.

Kana suka wuce suka nufi cikin.

Bayan isarsu da kamar 5 minute, jirginsu Rayyern yayi sauƙar angulu.

Bayan yan daƙiƙu ne kuma matafinyan suka fara fitowa.

Da sauri Usman ya matso kusa da uban gidan nashi, cikin yin ƙasa da murya yace.

“Sir in kira driver?” 

Shiru yayi ganin ya ɗan kaɗa mishi yatsarshi manuniya.

Shi kuwa Riyyam-nsra da sassarfa yake biye da Usman a baya.

A haka har suka fito asalin filin da matafiya kan zauna su jira masu tarbarsu.

Kanshi ya ɗan ɗago ya kalli taron mutanen, yatsarshi yasa ya ɗan gyara zaman farin glass ɗin dake idonshi.

Gefen lips ɗinshi na ƙasa ya ɗan kamo ya ɗan tauna a hankali.

Da sauri kuma ya ɗan juyo ya kalli bayanshi.

Inda ya hango Riyyam-nsra can baya yana ɗan tahowa yana waige waige a alamun shi yake nema.

Gabanshi ya nunawa Usman tare da yin mgna can ƙasa.

“Ƴan jarida ne, zanbi nan, in sun tsareka kaji dasu.”

Yana faɗin haka, ya ratsa yabi yar siririyar hanyar dake gefen damanshi.

Shi kuwa Usman ya nufi hanyar fitan.

 

Jannart kuwa da sauri cikin tsananin razana ta koma bayan Salman tare da yin ƙasa da kanta murya can ƙasa tace.

“Innalillahi Salman gacan Hakim abokin Yah Junaid idan ya ganni zai gaya mishi.”

Sai kuma ta zaro ido jikin tashin hankali ta dafe kirjinta  tare da cewa.

“Na shiga ukuna tare suke da Yah Junaidu ma gashi can bayanshi”.

Da sauri Salman ya ɗan kalli gabanshi kana ya juyo.

Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi sabida hango Hakim Da Junaidu sun nufosu gadan-gadan.

Jujjuyawa tayi.

Ganin wata ƴar siririyar hanyar ne gefen hagunta, wacce nan Rayyern yabiyo.

Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ratsa cikin ƴar hanyar ta ɓacewa ganin su.

Nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe, tare da ci gaba da tafiya cikin yar siriyar kusurwar.

Tana tafiya tana wai-waye da juyawa tana kallon bayanta.

Shi kuwa Rayyern, cikin  ɗan sassarfa yake tafiya.

Saboda so yake kafinma Usman da Riyyam-nsra su fito, ya shiga taxi ya tafi.

Tafiya yake yana dai-dai-ta kan files da takardun da yayi ta aikin rattaɓa musu hannu a cikin jirgi.

Haka yasa  bai lura da gabansa.

Ita kuwa Jannart tafiya take tana wai-waye shiyasa bata ganin gabanta.

Jin kamar takun wani a bayanta ne kamar ana boyota, kuma yasa ta ƙara saurinta.

Dai-dai lokacin kuwa  Rayyern ya iso gab da ita.

Jin ana ce. Ke! Ke!! Yasa ta juya da nufin zata arta da gudu.

Sai kawai ta jita jikin mutum sunyi karo.

Goshinta ya bugi gemunshi da azaban ƙarfi.

Take files da Takardun hannunshi suka watse.

 Yayinda ita kuma tayi tangal-tangal ta koma baya zata faɗi ƙasa, da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin sauti mai cike da tsoro, hade kuma dasa hannunta da nufin dafe ginin dake wajen, dan kare kanta daga faɗuwa ƙasa. 

Kawai sai ta kamo kwalan rigarshi ta gefe ta cikin da kuma Suit ɗin dake saman da ƙarfi.

Pet-pet haka boturan jikin rigar duk suka ɓalle,  kab suka watso ƙasa, hakan yasa gaba ɗaya rigunan jikinshi suka buɗe.

Cikin wani irin masifeffen takaici yasa hannunshi ya fisge hannunta dake shaƙe da gefen kwalar rigarshi.

Ya yarfa hannun tare da zuba mata wani irin masifeffen….!

Kuyi hakuri rashin jina da wuri.

Rayyern da ban Riyyam-nsra da ban ai sunayenma ba iri ɗaya bako.

Karanta√√√  Tubali Book 1 Chapter 1

Back to top button