*ASM Book 2
Page 002*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……….Washe gari da suka tashi ta d’an ji sauk’in jikin nata kawae yanzu fargaba ce tafi damunta hakan yasa duk bata jin dad’in kirjinta bayan tayi sallar Asuba komawa tay tayi lamo kan gado sai sak’e sak’e take aranta, yanzu shikenan ta rasa ya Haisam, tana ji tana gani zai yi auranshi ya tafi ya barta, haka dai take ta tunane tunane tana matse k’wallan dake zubo mata ba tare da gwaggo ta ankare ba don ita duk tunaninta bacci Fatun ta koma, Wuraren k’arfe tara saura tazo ta tashe ta tayi karin kumallo, bayan taje tayo brush ta zauna don yin breakfast d’in saidai sam tama kasa cin komae don bata jin dad’in bakinta gwaggo dake zaune gabanta ta lura da hakan tace mata ta daure in taci sai tafi jin dad’in jikinta ta dai d’aga mata kai kawae, da k’yar ta d’an tuttura ta mik’e zata kwashe kayan gwaggon tace ta bassu taje ta kwanta in ta gama zata d’auke, bayan ta gaman ta kwashe komae ta kai Kitchen bata dawo d’akin ba saida ta had’a ma fatun ruwan wanka a toilet tace ta daure taje tayi ko ta ji k’arfi, d’akinta ta koma ta cire kayan jikinta ta d’aura towel ta yafa mayafi kafin ta fito ta nufi toilet walking slowly don duk jikinta ba k’arfi, bayan ta fito doguwar rigar material kawae ta zura ta haye gado taci gaba da tunane tunanenta,
Wuraren k’arfe 11 Fanan ta farka tun bayan sallan Asuba data koma tana saukko da k’afafunta k’asa idanunta suka sauka akan wata yar guntuwar farar takarda dake ajiye kan bedside drawer, hannu ta kai ta d’auki takardar tana duba rubutun dake jiki kamar haka,
_Went to work_
_Luv u_
Shine rubutun dake ajiki Murmushi ta saki sanin Haisam ne ya ajiyeta, baki ta kai paper d’in ta manna mata kiss had’i da furta Luv u too Babe,maidata tayi inda ta d’auketa ta ajiye ta wuce toilet don yin wanka bayan ta fito ta shirya cikin skinny jeans blue da farar top bayan ta gama shiryawa ta dauki wayarta ba tare data rufe kanta ba ta saki brown gashinta ya zuba gefe da gefen fuskarta ta nufi Parlor ganin ba Hajiya a falon yasa ta nufi d’akin Saude tana kwance kan katifa tana huta gajiyar aikin gidan data gama bada jimawa ba, zazzak’ar muryarta saude ta jiyo tana yi mata sallama hakan yasa ta tashi zaune da sauri suka had’a ido ta sakar mata Murmushi itama sauden Murmushin take mata don ba k’aramin burgeta take ba,
“Ina kwana” Saude ta gaidata ta nufo inda take ta zauna gefen katifar da Murmushi tace “kin tashi lpy ya aiki” tace “Alhamdulillah” shiru suka d’anyi kowa Murmushi ne akan fuskarshi can Fanan d’in tace “Hajiya ta fita?”
“Eh bata dad’e da fita ba taje wurin aiki ne” jinjina kai tayi sauden ta kuma cewa “ga breakfast can na shirya maki a kan table”,
” Owk thanks”,
“Babe ya shigo kuwa yayi breakfast?” ta tambaya tana kallon sauden,shiru ta d’anyi don bata gane babe d’in da take nufi ba gane hakan yasa fanan d’in cewa “I mean Ya Haisam” da sauri tace mata “eh ya shigo d’azun da shirin zuwa aiki ya shiga d’akin Hajiya kafin ya fito ya tafi,
“yayi breakfast?” kai ta girgiza mata “a’a ai bai yin breakfast yake tafiya gaskiya sai dai wani lokacin in hajiya ta matsa mashi yake dan yi shima dai kad’an” jinjina kai tayi tace “har yanzu baison cin abinci ko?” yar dariya Saude tayi kafin tace “eh to gaskiya yana ci amman fa ba sosae ba shima dai sai Hajiya ta matsa mashi yake d’an ci da d’an yawa” jinjina kai ta sake yi ta fara kokarin tashi Saude tace “Breakfast d’in zakiyi inzo in zuba maki?”,
“No don’t worry zanyi serving kaina”
“Don Allah ki bari kar aikin yayi maki yawa” d’an waro ido tayi alamar mamaki tace “miye ne aiki ciki just serving Myself ai kene mai yin aiki so just relax” tayi Maganar tana mata alamar ta kwanta da hannu ta juya ta nufi kopa Saude ta bita da ido tana Murmushi aranta take ayyana kirkin yarinyar yayi yawa sam ba halinsu d’aya da yar’uwarta ba, tana fitowa bata nufi dining don sai taji bata son yin breakfast d’in ita kad’ai, Bedroom d’in Hajiya ta koma ta d’aura boyfriend jacket bak’a mai d’an ratsin fari ta yafa d’an k’aramin bak’in gyale ta fito, gidansu Fatuu ta nufa wayarta ruk’e a hannunta tana zuwa bakin gate ta tsaya suka gaisa da su Officer tana ta Murmushi suma duk suka washe mata baki bayan ta wuce ne su kau yabonta, tana shiga gidan ta tsaya bakin kopa ta rafka sallama da zazzakar muryarta “Salamu Aleeikum” tana niyyar k’ara yin wata gwaggo ta fito daga cikin d’akinta tana amsa mata sallamar suna ganin juna suka saki Murmushi gwaggon ta nufeta tana Fad’in “Ah ya kika tsaya anan ki shigo mana y’ata” nufota tayi suka had’e a tsakar gidan d’an side hug tay ma gwaggo tace “ina kwana granny” da fara’a tace “lafiya lou y’ata ya gajiyar tafiya kuma”
“Babu shi” ta bata amsa gwaggon na niyyar ce mata su shiga falo tace “ina Sis Zarah ya jikinta fa” tace mata da sauki sosae tana cikin d’aki “owk bari in ganta” tare suka juya suka nufi d’akin gwaggo Fatuu da duk abunda suke tana jinsu tana jin sun nufo d’akin tayi saurin juyawa yadda baza’a ga fuskarta ba ta runtse idanunta sosae, suna shiga d’akin Fanan ta nufi gadon ta zauna a gefe ta kai hannu tace “Sis Zarah” shiru bata amsa ba hakan yasa ta kalli gwaggo tace ko tana bacci ne, ita kanta gwaggon ta d’anyi mamakin ganinta haka don lokacin da Fanan d’in tayi sallama tasan ba a haka take kwance ba idonta biyu har suna ma d’an Magana da ita, matsawa tayi gaban gadon ta kira sunanta da d’an karfi ba yadda ta iya dole ta amsa mata sanin gwaggon tasan ba bacci ta barta tana yi ba,
“Ki tashi ku gaisa da Auntynki da tazo nasan jiya ba lalle ma in kin gane wacece ba kina cikin ciwo” d’an jimm tayi kafin a hankali ta yunk’ura ta tashi zaune ta kalli Fanan dake ta faman yi mata Murmushi murya can ciki tace mata “ina kwana, anzo lafiya” hannu ta kai ta dafa shoulder d’inta tace “Lafiya, ya jikinki” amsa mata tayi da sauki tace Allah ya bata lpy, ganin yadda take ta faman yi mata Murmushi yasa itama da kyar ta d’anyi mata na yak’e,
“How are u Feeling Now?” ta tambayeta k’asa k’asa tace mata “da sauki sosae kawae bana jin karfin jikinne” still hannunta na asaman kafad’arta tace mata ta kwanta, komawa tayi ta kwanta dama bata so tashin ba cike da kulawa take kallonta kafin ta maido kallon kan gwaggo dake zaune ta tambayeta tayi breakfast tace mata eh ta d’an ci kad’an, fira suka shiga yi da gwaggon kai kace dama can sun saba tace ko ta kawo mata wani abu taci bata kaiga d’aura abincin rana ba tace mata a’a ta barshi can gwaggon ta mik’e tace bari taje ta d’aura girki fanan d’in tace mata ba damuwa bayan ta fita wayarta ta shiga latsawa tana yi tana d’an d’agowa ta kalli Fatuu can ta kai hannu ta dafa kafafunta tace “Sis Zarah am really worried about ur condition, Allah ya baki lafiya kinji” a hankali ta ware idonta kan Fanan d’in dake kallonta cike da damuwa wani iri taji don ita kanta bata ta6a tunanin zasu kasance haka da Fanan ba yadda suka shak’u sosae har ta k’agara ta ganta a zahiri saboda yadda take nuna mata k’auna bata ta6a tunanin zuwanta zai jefata a matsala haka ba, a hankali wasu yan siraran hawaye suka zubo mata tana k’okarin gogewa fanan d’in ta matsa da sauri tana Fad’in ta daina kuka zata samu lafiya bada jimawa ba in sha Allah wai akace rashin sani yafi dare duhu, wayartace ta fara ringing takai idonta kan screen d’in ganin mai kiran nata yasa ta saki Murmushin da tun bata d’auka ba Fatuu ta yanke wanda ya kirata, cikin murya mai cike da tsantsar kauna bayan ta d’auka tace,
“Hlo Babe, how Work?” ta tambaya, on the other hand ya bata amsa da lafiya kafin ya tambayi tana ina tace mashi tazo ganin Zarah ne ya tambayi ya jikinta tace da sauki,
“am on my coming back now” ya fad’a, d’an ware ido tay ta cire wayan daga kunnanta ta duba time kafin ta maida tace mashi amman still Working hours ne ya akai zai dawo yace saboda bata yi breakfast ba yar dariya tayi tace waye ya fad’a mashi bata yi breakfast ba yace a jikinshi ya ji, cigaba da fira sukae cike da kauna har ta tambayeshi ya taho da gaske yace eh yana driving ma suke wayan, duk Maganganun da turanci suke wayar fatuu na saurarensu a hankali ta juya ta kalli d’ayan bangaren d’akin ta shiga yin kuka sosae ta rufe bakinta da hannunta guda don kar sautin ya fita, har ya kawo kopar gidansu Fatun suna waya ta mik’e ta d’an ta6a kafafun Fatun tace zata je ta dawo, kai kawae ta d’aga mata ta juya da sauri ta fice, tana fita kopar gida taga Motarshi ta nufi d’ayan side d’in ta bud’e ta shiga suna had’a ido suka sakar ma juna Murmushi ya kamo hannunta ya rike yaja Motar da d’ayan suka tafi, suna shiga Falon Hajiya Dining suka wuce da kanshi yay serving nasu don shima bai ci komae ba awurin aiki cike da tsantsar kauna suka shiga ciyar da juna koda ya tashi komawa wurin aikin bayan sun gama marairaice mashi tayi wai ya tafi da ita gidan is so boring yace ai Hajiya bazata dad’e ba zata dawo amman ta k’iya dole yace taje ta shirya su tafi, bada jimawa sosae ba ta fito sanye cikin bak’ak’en Suit na mata kafafunta sanye da ankle strap farare irin takalman nan masu tsini sosae masu rufe diddigen k’afa da igiya sama da ake d’aure k’afa kanta ta yafa k’aramin bak’in gyale hannunta ruke da farar clutch bag data hau da rigar cikin da kuma takalmanta yayinda kunnanta ke sanye da yan kunne fashion silver masu matsiyacin kyau hannunta na hagu d’aure da agogon diamond sai d’aukar ido take ba k’aramin kyau tayi ba, idanunshi akanta ya d’an lumshe su yana binta da wani kalan kallo ta nufo shi tana tafiya irin ta wayayyun yan boko tana zuwa gabanshi ta tsaya tana Facing d’inshi tana wani kashe mashi ido yay d’an Murmushi kafin ya kai hannu ya kama kunnanta yace dama tazo da shirin takura mashi kenan ko ta fad’a jikinshi tana dariya a lokacin idanunshi suka sauka kan gashinta dake kwance kan gadon bayanta hannu ya kai ya cire gyalen ya nad’e gashin yadda bazai fito ba kafin ya d’agota ya fara nad’a mata gyalen, Allah sarki ashe ga inda Haisam ya iya nad’a gyale da Fatuu ke tambayarshi ya akai shi da yake namiji ya iya lokacin daya ta6a nada mata har tace kumatunta sunyi kaman an tura biredi, kama hannunta yay a nutse suka tafi.
Bayan Azahar Amadu ya shigo cikin gida daga Makaranta don yanzu a Poly yake Karatu don tuni ya kammala Secondary d’inshi kuma Haisam ne ke d’aukar nauyin karatun nashi shi da Tk don shima ya dasa HND bayan ya gama ND din da yake, d’akinshi ya bud’e don yanzu koparshi na a cikin gidan aka maidota lokacin da Haisam yasa aka gyara masu gidan sai aka k’ara ma zauren girma, yana shiga d’akin gwaggo ta fito daga cikin Kitchen ganin kopar d’akin nashi a bud’e ne yasa ta kwala mashi kira tace ya dawo ne don bata ji shigowarshi ba, fitowa yay ya nufo inda take tsaye yace “Eh na dawo in ci abinci in d’an huta don sai k’arfe hud’u nike da lecture” kai ta d’aga yace “ba yau zaki fara aikin rana bane naga baki shirya ba kuma lokaci yayi” da yar damuwa tace “to na tafi aiki Fatuu ba lafiya, har yanzu fa jikinta bai mata dadi wllh ina lura da ita har kuka take tayi” ajiyar zuciya ya sauke yace “amma ba kince jiya har Allura an mata ba?’
“Eh anyi mata amman ai kasan ciwo ke shiga lokaci d’aya sauki sai a hankali ko, kuma ni wllh damuwata kar ace ciwon da nike tunani ne” sanin ko wane ciwo take nufi yasa Amadun cewa “in sha Allahu ba shi bane ma, amman ina ganin ki tafi aikin ni bari sai in fasa komawar kawae” tace “ayi haka bazaka samu Matsala ba?”
“A’a ba wata matsala dama komawar k’ila wa k’ala ce don ba lalle ma lecturer d’in yazo ba haka yake sai anata jiranshi ya kira waya yace bazai zo ba” jinjina kai tay tace “k’ilan uzuri ne ke masa yawa kasan hidindimun rayuwa, bari to in mik’o maka Abincin sai inje in shirya don ya kamata inje tunda yau Monday akwae tsare tsaren da zamuyi” tana k’arasa Maganar ta juya ta shige kicin,bayan ta mik’o mashi abincin ta zuba ma Fatuu ta kaimata saida ta matsa mata ta d’an tsakura tace mata ta k’oshi bata jin dad’in bakinta dole ta kyaleta ta hau shirin tafiya aiki bayan itama taci Abincin.
Lokacin da suka isa wurin aikin tun da suka fito daga cikin Mota ake ta faman binsu da ido dan duk wanda ya kallesu sai ya k’ara wasu da suka kafesu da idanu ko kyaftawa basa yi, da suka shiga cikin wurin wad’anda suka san Haisam da basu iya hakuri bayan sun gaisa dashi sai suce wai sabuwar Ma’aikaciya suka yi ne anan ya gabatar masu da ita a matsayin wife to be d’inshi, fatan alkhairi aka shiga yi mashi yayin da wasu ke fad’in perfect match har kiran Mutane aka rink’a yi suzo ga Fiancee d’in Zakee tanata fara’a take gaisawa da mutane, bayan sun gama gaisuwar Office d’in su Nana ya wuce da ita wanda babban Office ne don su hud’u ne aciki duk mata biyu matan aure ne sai su Nanar da wata sune marasa aure, Nana zaune tana lallatsa Computer jikinta sanye da doguwar rigar atampa gyalenta akan kafad’a taji an d’anyi knocking kopar kafin aka turota hakan yasa ta kai idanunta wurin, Fanan ce ta fara shigowa ai suna yin ido biyu da Nana zumbur ta mik’e ta dafe k’irji tace “innalillahi, wa innahu min sulaimanu wa inna hu bismillah…” tana rufe baki Haisam ya shigo tana ganinshi ta sauke nannauyar ajiyar zuciya don ta fahimci tare suke tace “Haba Zakee irin wannan ai sai ka fara shigowa kai da muka sani, ni wllh nayi zaton gamo nai yo kawae ana bud’e kopa sai inga Mutum irin wannan ta shigo tana man dariya” sauran yan Office d’inne suka sa dariya taci gaba da cewa “kad’an ya rage ban saki fitsari ba” ita dai Fanan Murmushi kawae take haka ma Haisam,
“Zakee bakuwa muka yi, daga ni dae sis d’inka ce ko?” tay tambayar tana kokarin zama ta nuna ma Fanan kujera tace ta zauna, maida kallonta tay kan Haisam tace “Zakee na tambayeka baka ban amsa ba” yace “Yea she’s my sis and My wife to be also” waro ido Nana tayi da sauri ta kalli fanan d’in sauran abokan aikinta ma suka kalleta ita dai sai faman sakin Murmushi take, kallon Haisam Nana tayi tace “Haba mana shiyasa ba wata mace dake gabanka ashe ashe hurul ayn zaka aura, kace duk kallon gwaggon birai kake mana Zakee” gaba d’aya suka saka dariya harda Fanan, taci gaba “Tubarkallah ma sha Allah, gaskiya had’in nan yayi ba’a Magana, duk kun dace abokan rayuwa wllh Allah yasa Alkhairi ya kaimu lokacin musha biki ya kuma maida mu damshin ku duk da dai ita Amaryar tamu bansan halinta ba” Fanan na dariya tayi mata godiya tace ai duk halinsu d’aya Nanar tace to ta zauna anan ta tantance in halinsu d’aya, dole anan Office d’in nasu ya barta aikuwa sun sha fira da Nana harda ma sauran yan Office d’in sun matuk’ar yabawa da halinta na rashin ji da kai, sai gab da za’a tashi sannan Nana ta rakata Office din Haisam wanda babban Office ne mai d’auke da duk wani abu da zaka samu a hadaddan Office na babban ma’aikaci yana da dan falo wanda anan Secretary d’inshi yake, ana yin la’asar suka baro wurin aikin saida Nana ta rakota har Mota tace tana jiranta tazo mata wuni gida tace in sha Allah Babe zai kawo ta, saida suka biya shopping mall suka yi shopping yawanci duk kayan ciye ciye ne suka siya kafin suka nufi gida.
Tun bayan da gwaggo ta tafi aiki take kwance tana ta tunane tunanen rayuwarta da Haisam, a yanzu ne komai nashi ke bala’en burgeta a hankali take kai hannu tana goge kwallan dake zubo mata wanda sam ta kasa tsaidasu ga wani irin kadaici da take ji don tasan da yanzu tana gidan Hajiya ba kaman da gwaggo bata nan, da ta tuna yana tare da Fanan sai taji wani irin kunci a zuciyarta har wani zafi k’irjinta ke mata da kyar ta yunkura tayi sallar la’asar ko Addu’a ta kasa yi don ta rasa wace Addu’a ma zatayi, mik’ewa tay ta cire hijab d’in ta koma kan gado ta koma duniyar tunani tana ta juye juye tana goge kwalla, tana cikin wannan halin Haulatu tazo gidan a bakin shagon Amadu daya bude bayan ya dawo daga Masallaci ta tsaya ta gaidashi ta tambayeshi Fatuu na nan ko ta wuce islamiyya yace mata tana nan ciki kwance ai bata Lafiya tun jiya jin haka yasa ta nufi cikin gidan da sauri har tana yin tuntu6e a bakin kopar shiga, d’akin Fatuu ta nufa tana zuwa ta fad’a ciki da sallama ta nufi gadon Fatuu na jin sallamarta ta yunkura da sauri ta tashi zaune fuska jage jage da hawaye ga gashinta ya kwance yay mata rumfa, a rud’e Haulat ta nufeta tana Fad’in”Subhanallahi, wai ciwon har ya kai haka k’awata, ni wllh bansan baki Lafiya ba tun d’azun naso zuwa to sai innarmu ta tafi unguwa tabar man kula da gidan, yanzu ma islamiyya zani inata tunanin k’ilan ma kin tafi ina tambayar Kawu Amadu shine yake ce man wai baki lafiya tun jiya baku ma samu zuwa Daurar ba ko?” kaman jira Fatuu take tana jin ta fad’i hakan ta fashe da kuka mai sautin gaske ta matso ta kama hannuwan Haulat cikin kuka tace “Haulat na bani munyi kuskuren fahimta wllh” a kid’ime ganin yadda Fatun take a hargitse tace “kuskuren mi?”
“Ya Handsome bai sona Haulat, bai ta6a sona ba wllh” zaro ido Haulat tayi murya na rawa tace “a..amman ke ya akai kika san hakan ko kin mashi Magana ne ya fad’i maki hakan?” cikin kuka tace “a’a ashe wai yana da wadda yake so kuma ma har ansa masu rana da ta gama karatu za’ai aurensu,yauwa ba kinsan wannan Aunty Fanan d’in ba yar uwarsu mai karatu a india to itace, jiya muna dawowa muka iske tazo baki ga yadda ta rungumeshi ba da suka had’u shima baki ga yadda yake farincikin ganinta ba, da daddare suka zo tare wai kawo man tsarabar da muka yo, da tayi ma gwaggo bayanin kanta shine gwaggon tace ko itace akai masu baiko tace mata eh ashe ita gwaggo ta sani sun ta6a yin Maganar da Hajiya, Wllh Haulat baki ji yadda naji ba wani abu mai zafi kaman wuta naji a kirjina ga kaina da yayi wata sarawa nan da nan amai ya taho man baki ga aman da nayi ba kaman yan hanjina zasu fito kuma su duk sunyi tunanin ban lafiya ne har allura suka je suka siyo ita da Ya Handsome tai man” kasak’e Haulat tayi tana sauraranta kamar gunki gabanta na fad’uwa don duk gani take itace sanadin shigar Fatun halin da take ciki…..
Daidai gidansu Fatuu ya parker bike d’inshi Fanan dake bayanshi ta saukko jikinta sanye da workout outfit da alama Gym zasu tafi tare, Cire Helmet din dake kanta tayi ta mik’a ma Haisam ya amsa ta juya zata shiga gidan Amadu dake cikin shago yana ganinta ya fito da sauri don jiya da daddare bayan ya shiga gida gwaggo ta bashi labarin zuwan nata harda allurar data yi ma Fatuu, da Fara’a ya gaidata ta amsa yayi mata anzo lpy tana ta sakar mashi Murmushi, bayan ta wuce ya gaishe da Haisam kafin ya koma shago, tana shiga ta kwad’a sallama da zazzakar muryarta jin ba’a amsa ba yasa ta k’ara yin sallamar tana shiga cikin gidan a lokacin suka ji sallamar Haulat ta mik’e tana bari ta duba ita kuwa Fatuu tana jin sallamar ta gane ko wacece hakan yasa ta kwanta da sauri ta juyama kopa baya ta lullu6e fuskarta tana goge kwallar fuskar, d’aga labulen d’akin Haulat tayi ta lek’a kanta tana amsa sallamar saidae a susuce ta k’arasa amsawar baki bud’e take kallon fanan dake mata Murmushi ganin tak’i ce mata komae yasa tace mata “Sannu Gwaggo fa” a dabarbarce don bata yi tunanin zataji tayi hausa ba cikin yar in ina tace “g..gwaggo ta… ina tunanin ta tafi aiki” tace “Ok Zarah fa” da hannu ta nuna mata cikin d’akin alamar tana ciki ta nufo dakin har saida tace mata zata shiga kafin da sauri taja gefe ta shige, gadon da Fatuu ke kwance ta nufa ta zauna a bakin gadon cike da kulawa tace “Sis Zarah” shiru bata amsa mata ba ta d’aga kai ta kalli haulat tace “ko tana bacci?” da sauri tace “e..nima ban dad’e dana shigo ba na ganta haka”
“Ok amman ina son nayi mata injection ne zamu fita bansan ko zamu dawo da wuri ba” haulat da tayi mata k’uri tace “to bari in tada ta” matsawa tayi ta fara kwala mata kira ba yadda Fatun ta iya dole ta yunkura ta tashi zaune a hankali ta d’an kalli Fanan din ta sakar mata Murmushi tace “Sannu sis Zarah hope u’r feeling better” dan daga mata kai tayi kafin kaman an mata dole ta gaidata ta amsa had’i da dafa kafadarta tace bari tai mata second dose d’inta kai kawae Fatun ta d’aga mata ba tare da 6ata lokaci ba ta fiddo allurar da syringe daga cikin jacket din data rufe jikinta da ita ta had’ata tayi mata, cike da kulawa tace “zamu je Gym da Babe do you need something?” wani abu fatun taji ya daki kirjinta hakan yasa ta d’an kauda kanta ta girgiza mata Fanan din tace to ta koma ta kwanta Allah ya bata lafiya daga haka ta juya har takai bakin kopa ta juyo ta kalli Haulat tace “U’r Haulat right?” da sauri haulat ta d’aga mata kai kaman kadangaruwa Fanan d’in tace “I heard u’r Zara’s best friend nayi farincikin ganinki” tayi Maganar tana mik’a mata hannu a d’arare haulat ta kama hannun wani kalan taushi data ji har saida ta had’iye miyau kutt, “zanzo gidanku in gaisa da mom naki in Zarah ta samu lpy” da sauri haulat tace mata to ta d’an yake baki ita ala dole Murmushi take, janye hannun tayi tace mata ta tafi, ai tana fita Haulat bata san lokacin da a zuciyarta ta furta “Bura ubannan Astagfurullah”, juyawa tayi ta kalli Fatuu suka yi ma juna k’uri da alama wutar kowa ta d’auke, a sanyaye Haulat ta koma ta zauna ganin kallon da fatuu ke binta dashi idanunta sun cika da kwalla yasa tace ” itace ko?” kai ta d’aga mata alamar eh, shuru sukai kowa da abunda yake sak’awa can Haulat taji Fatuu tace “Yanzu Haulat ya za’ayi” a d’an firgice Haulat tace “Uhyumm” matsowa Fatuu tayi ta kama hannuwanta kwalla suka fara zubo mata tace “Don Allah ki bani shawara Haulat yanzu ya zanyi, wllh inason Ya Handsome in ban aureshi ba zuciyata zata iya bugawa yanzu haka bakiji yadda nike ji ba kaman ana hura man wuta ga wani bugu da take man mara dad’i” tana kai Maganar ta d’ago hannun Haulat d’in ta d’aura kan kirjinta kwalla naci gaba da zubowa, wani wahalallan miyau Haulat ke had’ewa ta k’ura ma Fatuu idanu ba tare data ce mata komae ba,
“Haulat don Allah ki taimaka man kinga dama kin saba bani shawara in ina cikin mawuyacin hali kuma duk inkika bani tana man aiki don Allah ki fad’i man abunda zanyi yanzu?” nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace “kin yarda in na baki shawara tana maki aiki? Da sauri ta d’aga mata kai alamar eh, taci gaba “to zan baki shawara amman da farko ina mai baki hakuri akan halin da kike ciki don duk ni naja maki dana yanke hukunci ba daidai ba batare da nayi la’akari da wani lokacin ko a Novel d’in muna yin hasashe yazo bai zama gaskiya ba…..” katseta Fatuu tayi “ki bar d’aura ma kanki laifi ai dama kince nima ina sonshi kuma bazan gane ba sai naga ina niyyar rasashi to abunda ya faru yanzu kenan ni dai ki bani shawarar kawae” wata ajiyar zuciyar Haulat ta kara yi kafin cike da k’arfin hali tace “Shawarar da zan baki itace……………..
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.