Novel Document

Jeji Girl Complete Novel Document By Autar Alheri

Description/Story:

Jeji Girl Complete Hausa Novel Document Written By Autar Alheri

 

Description

“Wata motace kitafiya acikin dokar daji daga Legos zuwa Ibadan tafiya takeyi hankali kwance mutanen ciki sefira sukeyi ahankali cikin nishad’i da kaunar juna daga Gani base katambayaba kasan cewa mata damijine

 

Da jinjirar yarinya ahannun matar tafiya sukeyi suna yankar Jeji sosai sukayinisa cikin tafiyarsu,,,hadarine yataso Babu kama hannun yaro me iska da tsawa,,cikin tsoro matar tace “Alhaji hadarinnanfa yataso sosai Kuma gashi dareyayi inajin tsorofa musamu mutsaya harya lafa..dubanta yayi cikin murmushi kana yace shikenan hafsat yafad’a taredayin perking d’in motar agefen hanya,,kana yakarb’i yarinyar Dake hannunta kyakkyawa da,ita Yana mata wasa,,sunjima ahakan kamun ruwa sukece kamarda bakin k’warya ruwa akeyi sosai kamar zasutada garin abun har zabban tsoro,,itadai hafsat inbanda addu,a babu abunda takeyi yayinda megidan nata kuwa ko, ajikinshi,,,anjima sosai anaruwannan kamun Kuma sud’auke d’if kamar ba,ayiba se walk’iya kawai da,akeyi jefi jefi,,,motar yatayar kana sukaci gabada tafiya Ammafa garin yayi Baki kirin ga duhun hadari gana dare gakuma sanyin damuna

Sunyi tafiya medan Nisa kana hafsat tadubi megidan nata tace wlh ni banasan tafiyar dare seda nace mubari mutafi Ido naganin Ido Amma kace aa…murmushi yayi kamun yace to ai allah yakaddari yanzune zamuyi tafiyar Kuma bakisan manufarsa tayin Hakanba..berufe bakiba suka d’auki salati atare sabida fad’awa dasukayi cikin Wani katon ramen dayacika tab daruwan sama jikakeyi tsum,dummm motar tanutse duka acikin ruwan..hasbinallah😥

Washe gari dasanyin asuba haske yad’an fara fitowa nahango jaririyarnan kwance agefen wasu manyan ruwan gadukkan alamu tekuce anan,,abunda yafaru ajiya motar nafad’awa ruwa allah yabawa hafsat iKon bud’e gabun motar tafito itada jinjirarta sedai Bata iya ruwaba kamun tayi Wani yun kurin tuni igiyar ruwa takarb’e yarinyar tayi gabada,ita itako akayi gabada,ita..to shine ruwan suka wullo yarinyar anan.

Yarinyar jinjira abun tausayi se cilla kafafunta takeyi sama tana kuka,,,Wani katon kada🐊ne yafito abakin ruwan yahangi yarinyar cikin zumud’i yanufota domin yunwar safece tafito dashi,,daga gefe Kuma zakine🦁 kwance Yana kallanta nesa dashi kad’an tawagar giwayene🦣 sukazo Shan ruwa daga Saman bishiya kuwa Wani katon gwaggon birine Wanda akekira gorilla 🦍ke zaune Yana Hangen yarinyar,,,cikin Isa datak’ama irinta sarakunan namun dawa zakinnan🦁yafara nufota Shima,,Dede lokacinda giwayennan suka,Iso suka mazajen suna rigangan wurinyin lak’um da baiwar allah,,,,adede lokacinda suka k’araso wurintane Wani irin haske yabaibayeta Wanda duk yakashe musu idanuwa dukkansu suntsorata domin kowacce halitta akwai tsoro acikin rayuwarta.

Bayan wasu sakanni wannan hasken yab’ace b’at kamar bewanzuba,,,abun mmki haskennan nab’acewa se way’annan manyan halittun masu razana D’an Adam suka fara zagayen yarinyar suna shinshinarta sunjima ahakan sunata zagayenta ba Wanda ya,iya yimata komai…sayin wurinne yafara ratsata sosai Hakan yasa tafara tsandara Kuma tana wulla kafafuwanta sama…cikin sauri giwarnan tasaka jelarta tanad’ota tadayin sama da ita,,,Ganin Hakan yasa wannan gwaggon birin saukowa daga Saman bishiya takarb’eta daga hannun giwar tareda yaye kayan jikinta da towel d’inda aka nad’eta ciki yayi mata tsirara,,kamin yagama tubeta tuni zaki yasaka kohotunshi Yana had’a karanda kewurin Yana tarasu wuri d’aya,,,shiko birin yagama cire mata gayan kenan Sega k’waguwa🦑tafito kamar abunda akaturo tahad’a jelunanta tarik’a bugasu aiko Sega wuta takama cikin sauri birinnan yafigo wata katuwar kunnen bishiya me fad’i sosai yad’ora yarinyar Akai kana yazo kusan wutarnan da,ita yanad’an jigata alamar rarrashi,,atake kuwa tayi shiru.

Itakuwa giwarnan katuwar bishiyar lemu Dake wurin tarik’a girgizawa tana kad’o yayan tana Saka kafarta tana dansu kad’an sunayin laushi,,, birinnan na hud’eshi Yana matsa mata abaki tanasha harta k’oshi se bacci…kallan kallan sukatsaya yiwa juna ga dukkan alamu kowannensu soyakeyi yayi renon yarinyar Amma bahali tinda basuda hannun d’aukarta Hakan yasa suka barwa birin dole Badan sunsoba Amma fa anan kan katuwar bishiyar rini Dake bakin ruwan suka aminta yazauna da,ita yagano hakanne tahanyar zagayenshi dasukayitayi Kuma suna zagaya bishiyar.

Atake yahaye Saman bishiyar yashiga had’a sanyunta da hakinta Yana had’a Dan k’aramun bukka kamar gije,,seda yagama had’awa kana yashiga cikin jeji shida giwa dakuma Wani shirgegen maciji🐉 daya take musu baya..kad’a da zaren tunfafiya birinnan yashiga had’awa Yana murjesu gu d’aya idan ya murje seya majininnan yanad’eshi ajikinshi kana giwa tarik’a janshi da jelarta kana birin yadawo yarinka sak’ashi atake suka had’a mata zannuwa irinna kayan jeji Dade abunda zasu rik’a nad’eta dashi kana suka dawo inda sukabar basawan nagadinta.

Abakin babbar tekun Legos Wani matashin saurayine Dan kimanin shekaru 22 tsaye yake Yana d’aura igiyar shiga ruwa,, kyakkyawan saurayine ajin farko gashi fari tass kanar ka kwanta jini yafito yanada manyan idanuwa masu firgitarwa Kuma inada tsayi Dede gwargwado Dan k’aramun bakinshi medaukeda pink lips Wanda kananun Suma baka tayi liflif azagayenshi,,,yanada fad’ad’an girji medaukeda lallausar suma Masha allah irin k’irar jikinshi itace akekirada namujin zaki abun gwanin ban Sha,awa..Yana gama d’aura igiyar kawai yayi supa daga cikin katon jirgin ruwan🚢 se acikin tekun..!

Download Jeji Girl Complete Novel Document By Autar Alheri

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button