Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 52 Hausa Novel

A nan gidan Hajia ya ajiye motarsa ya samar musu taxi wadda zata kaisu airport, ya shiga gaban mota ita kuma ta shiga baya. Suna kama hanya ta zaro wayarta ta lalubo lambar Anti Wiyya ta tura mata sako ta wahtsapp tana sanar da ita an saki Khadeeja. Bayan sun gama hirarrakinsu na murna da nuna jin dadi Anti Wiyya ta turo mata sako kamar haka “Kije kiyi ta addu’a Allah ya sa kada kuna dawowa ya dawo da ita. Nan ma in sha Allah akwai wani malami da zan kaiwa abin sadaka yayi miki aikin da ba zata taba dawowa gidan ba, kin ga ki ci gida se yanda kika yi.”Ta turo mata emoji na dariya ta rufe wayar, ta mayar da hankalinta kan hanya zuciyarta fes cike da fatan Allah ya sa kada ya dawo da Khadeeja tunda ya ce saki daya ne; in ya so sai ta ji da yaran kawai.………A hankali Khadeeja ta baje kayanta a gida; ta sanar da Baffa ko da ya dawo ma ba zata koma ba domin ko ya mayar da aurenta to kotu zata kaishi ya saketa. A haka dai aka bar maganar domin shi Baffa gani yake kamar idan aka bata lokaci ta huce zasu yiwa kansu sulhu ita da shi.Tun Baffa yana sa rai zai ji kira daga wajen iyayen Mustapha sun biyo sawu har ya fitar da rai. Saura kwana biyu babbar sallah suna zaune a parlor shi da Mommy suna hira yace ‘Mutanen nan dai shiru, babu wanda ya biyo sawun Dije. Na san dai babu yanda za ayi suce basu san ya saketa ba tunda ai zasu ga ba ita ya barwa yaransa ko?’‘Uhm, ni abun har ya isheni ma wallahi. To amma ko tuntubarsu zaka yi ka ji, tunda ai ba zamu taru mu zama daya ba ko?’ Mommy ta bashi amsa.Yayi ‘yar dariya yace ‘Babu wanda zan tuntuba tunda ai da zan basu aurenta ba ni na tuntubesu ba su suka zo har gida suka tuntubeni. Idan na tuntubesu hakuri zan basu ko me? Ni aka yiwa wulakanci aka saki ‘yata ko ma don wanne dalili ne amma kuma ni ake jira nayin magana? To su cigaba da zamansu kada ma su zo inda nake.’A haka suka bar zance domin Mommy ta san in dai Baffa ne yanda ya kafe ba zai yi magana ba to tabbas ba zai yin ba.Suma daga can gidansu Mustapha a tunaninsu Baffan Khadeeja ne ya kamata ya nemesu don ya kamata idan ta je gida a bincika a ji, sai dai har aka shiga hidimar bikin sallah babu wanda ya neme su. Sai suka bar maganar kawai suna jiran Mustaphan ya dawo su ji ko shi yayi magana da iyayen nata…………Suna daga cikin na farko-farkon dawowa a alhazai. Tun kafin su baro masaukinsu ta gama magana da shi a kan ba za adauko yara ba sai tayi kwana biyar tana hutawa, don Rukayya ma tace kada a dawo da ita sai bayan sati biyu. Abokinsa ne ya daukosu daga airport ya kaisu har gida, da yake ya saka Habib ya bude gidan an gyara tsaf suka sami ko ina.Da safe suka sauka don haka kafin su shiga gidan sai da suka yi order din abincin rana. Sai can da yamma bayan sun gama hutawa sannan ya shirya ya wuce gidan Hajia. Nan ya zauna suka yita hira a wajen Hajia. Duk da ya gaya musu ba yau zai tafi da su ba amma Shukra ta kafa a kan ita a ranar take son ta bisu, don haka yace su shirya tare da su zai tafi.Sai bayan sallar magriba sannan Alhaji ya dawo, bayan sun gaisa suka cigaba da hirarrakinsu. Alhaji yace ‘Yauwa, ya wajen Khadeeja kuwa? Kun yi magana ne?’Yace ‘A’a ni ban nemeta ba kuma ba zan nemeta ba Allhaji, itace fa tace na saketa kuma na saketan, taje ta dana zaman gidan.’Alhaji ya dan bata rai yace ‘Kai! Ba a yiwa mata haka, idan jira kake ta nemeka to ba lallai ta nemeka ba gara ma kaje idan da wani abu ka yiwa iyayenta bayani su yi mata fada ka mayar da aurenta.’Ya jijjiga kai ‘Alhaji ni ba inda zan je, idan tana son auren nata zata nemeni tunda ai da kanta ta nemi sakin.’Haka Alhaji ya saka shi a gaba yayi ta yi masa nasiha, daga baya yayi musu sallama ya kwashi yaransa suka wuce.………..Ba shi kadai ba hatta yaran ma saida suka gane bata ji dadin dawowarsu a ranar ba, haka dai suka gaggaisa suka yi mata sannu zuwa kowa ya shiga harkarsa. Inda Allah ya taimaketa ma shine ya siyo musu abincin dare.Ta rigashi kwanciya saboda gaba daya bata ma jin dadin jikinta, sai da suka gama hira shi da yaransa sanan ya rufe gidan kowa ya tafi ya kwanta.Motsin shigarsa daki shi ya tasheta daga bacci, sai da ta bari ya gama shirins ya kwanta sannan ta gyara kwanciya tace ‘Kai da muka yi da kai ka bar yara sai mun huta shine ka taho da su?’Ya gyara kwanciyarsa yace ‘To sun ce zasu taho, suma fa ba dadin zaman suke ji ba a wani wajen kin san kowanne yaro ya fi son gidansu.’Ta kula idan dai a kan yaransa ne ba zai saurareta ba don haka ba tare da ta ce komai ba ta juya masa baya ta cigaba da baccinta; amma dai ta san tabbas dole ta dauki mataki don babu yanda za ayi ta bari ya kori kishiyarta kuma ya mayar da yaransa kishiyarta. dole ta dauki mataki.Sai da tayi sati da dawowa sanna taje gidansu ta taho da Rukayya, don ko ‘yan gidan nasu ma da zasu zo musu sannu da zuwa cewa tayi kada a zo da ita don idan ta zo ba zata yadda ta koma ba.Bayan ta gama hirarta a gidan ta wuce gidan Anti Wiyya; nan suka zauna tayi mata bayanin ayyukan da ka yi mata, sannan ta bata wasu layu guda biyu tace ‘Gasu nan hatimi ne aka rubuta da ayoyin Allah, ki sami waje ki konesu kurmus sai ki zuba masa tokar a miya. In dai ya sha miyar nan to ba zai sake yi miki musu ba. Wannan aikin bana haufisa kamar yankan wukane sai dai idan baki aikata ba.’Ta karba ta mayar cikin ledarsu ta kulle ta jefa a jaka tana cewa ‘Ai dai kin ce ayoyi ne ko?’Tace ‘Wallahi ayoyi ne, ke malamin fa har almajirai gareshi suna karatun allo. Ai idan kin haihu zamu je ki gani da kanki idan har kina da wata matsala.’‘Hmm! Ai dole ma nayi Anti Wiyya, daga dawowarmu ya fara neman ya nuna min iyakata a kan yaransa, gashi su baka isa ka saka su aikin komai ba sai dai kai ka kare a hidimarsu. Ai yau din nan zan aikata wannan layun kowa ya shiga hankalinsa. Ko nan ma fa da zan taho shi so yayi na taho da su wai saboda kada na barsu su kadai, ki ji don Allah sai kace wasu jarirai.’‘Ya zata kema Khadeejan ce.’Suka yi dariya gaba daya.Sai gefin magriba sannan ta dauko Rukayya suka dawo gidan. Tana zuwa tadora abincin dare imda ta dafa tuwo miyar kuka.Tsaf ta hade tokar layun nan ta juye masa a miya ta juya komai ya shige, tayi sa’a kuma ya sami tuwon nan yayi masa cin koshi.A hankali ta fara ganin kyawun aikin da Anti Wiyya ta yi mata. Cikin wata daya da dawowarsu ta tattare kayanta ta koma sama part dinshi, bata son tayi maganar part din Khadeeja sai ta bari wata uku ya cika saboda kada ma ta tuna masa yaje ya dawo da ita. Yanzu ta samu idan suna sama shi da ita ta hana yaran hawa kuma ya kasa yi mata magana. Ta san bai ji dadi ba don yana nuna mata a fuska amma wannan ba damuwarta bace, kuma idan shi ya zauna a kasan da zarar ta kirawoshi haka zai tashi ya bi bayanta su koma saman da shi da ita da Rukayya, sauran yaran suna kasa. Sai dare yayi idan zasu kwanta ne suke hawa saman da yake dakinsu yana can. Suna hawa sai ta kadasu su wuce daki su kwanta.………..

Back to top button