Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 46 Complete Novel

*ASM Bk2046*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

……….Tana d’aga labulan d’akin ta sauke idanunta akan gadon dake wayam ba kowa da d’an mamaki ta k’arasa shiga don ta tabbatar da abunda take gani, tabbas ba Fatuu kwance tsaye tay ta fara ayyana ina taje ne acikin ranta can tace ko tana band’aki ne, sai kuma ta raya anya dae tana can tun d’azu fa tana kitchen kuma bata ga fitowar ta ba in ba dai tun kafin ta fara aikin girkin ta shiga ba to amman mi zai sa ta dad’e har haka ta jefa ma kanta tambaya, can dae ta juya ta fita daga d’akin ta nufi hanyar toilet don ta tabbatar tun ma kafin ta k’arasa ta hango kopar shi a bud’e alamar ba mutum d’an tsayawa tay sai kuma ta juya ta nufi hanyar fita daga gida, a bakin k’opa ta tsaya ta fara k’wala ma Amadu dake cikin shago kira ya bud’e ya lek’o ganin itace yasa shi k’arasa fitowa ya nufo inda take ya tsaya yana kallonta yace gashi tambayar shi tay ina Fatuu da d’an mamaki yace “bata ciki ne?” Gwaggon ta d’aga kai tace mashi bata nan ta duba har toilet d’an jimm yay kafin yace “gaskiya ni banga ta fito ba tunda na bud’e shagon” shiru gwaggon tay tana tunanin to ina ta shiga Amadu ya katseta da tambayar ta kira wayar ta ta girgiza mashi kai alamar a’a yace to bari ya kirata ya juya ya koma shagon, bayan ya fito ruk’e da wayar ya dawo gaban gwaggon ya fara k’ok’arin kiran Fatuu lokacin da kiran ya shiga tana ta sharar bacci har kiran ya yanke bata ji ba sai da ya k’ara kira ne can a cikin bacci ringing d’in ya kai mata ta fara motsi a hankali ta fara bud’e idanunta jin wayan nata k’ara yasa ta yunk’ura ta tashi zaune tana kai hannu zata d’auka kiran ya katse, bayan ta d’auka ta duba mai kiran nata har saida gabanta ya fad’i ganin sunan Kawu Amadu tana haka sai gashi ya sake kira tay shiru kaman bazata d’aga ba can dai tay picking ta kara ta a kunne daga can bangaren Amadun ya kira sunanta ta amsa a hankali ya tambaye ta tana ina ne tace mashi ta tafi Makaranta ya maimata abunda tace jin haka yasa ya mik’a ma gwaggo ta amsa ta kara a kunne ta kira sunanta itama ta amsa mata had’i da gaishe da ita tace “naji kin ce kina Makaranta lafiya kika tafi baki fad’a ma kowa ba?” Had’iyar abu tay ta fara tunanin k’aryar da zata mata cikin yar rawar murya tace “d..dama na manta ban fad’a maki ba da yake jiya baki nan na dawo akwae wani malamin mu to ba’a cika gane abunda yake koyawa ba ana ta mashi complaining shine ya ware mana lokaci a cikin wannan weekend d’in da safe yace zai yi mana lesson tunda lokacin da yake dashi cikin ranakun aiki bai isar shi ya rink’a yin bayani sosae yadda za’a gane” gwaggo dake sauraronta tace “to yanzu sai yaushe zaki dawo?” shiru Fatuu ta d’anyi kafin tace “sai Allah ya kaimu Juma’a”

 

“Har sai Juma’a kuma ba da safe zaku rink’a yin lesson d’in ba in aka gama ai sai ki taho gida ko?” Fatuu tace “eh amman da yamma ma zamu yi group Assignment” sauke yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace “to amman shi yayan ki fa daya maido ki yace zai rink’a kaiki baki tunanin zaiga kaman kin k’i jin Maganar shi ko baki gode ba” d’an runtse ido Fatuu tay ta bud’e yanayin fuskar ta kaman zata yi kuka tace “Na fad’i mashi ai” gwaggon tace Shikenan Allah ya bada sa’a Fatuu na gumshe kuka ta amsa da Amin da sauri ta kife wayar akan katifa ta jingina da bango ta kifa fuskarta a tsakankanin cinyoyin ta wannan wace irin cin Amana ce sukai ma gwaggo gaba d’aya ta yarda dasu ji yanzu daga fad’i mata hakan har ta amince, da kanta ta rarrashi kanta bada jimawa ba aka kira sallar Azahar ta sauka daga kan gadon don tayi salla, wasa wasa har dare bata ga kiran Haisam ba balle tasa ran zai zo suyi Maganar da yace bayan taci indomie da ta dafa taje tay wanka ta zauna ruwa data dawo ta sha magungunanta ta kwanta saidae sam ta kasa yin bacci abubuwa ne da yawa ke mata yawo a rai ba kamar rashin zuwan Haisam duk da ba wai tana son zuwan nashi bane kawae sai take ganin kaman bai damu da halin da ya jefatan bane daga baya ta dasa tunanin yadda rayuwarta zata kasance nan gaba ba kamar in tayi aure, “anya ma ni zan yi auren kuwa?” ta ayyana a ranta sai dae itama tasan fad’a kawae take ba yadda za’ai ta rayu ba tare da ta yi aure ba tasan ai baza’a ma ta6a k’yaleta ba, tana ta tunane tunane sai can dare bacci ya d’auketa, Washe gari Lahadi haka taci gaba da jinyar kanta ranar ma har dare yayi Haisam d’in bai kira ba a lokacin Fatuu har ta gama yankewa ranta dama dad’in baki ne kawae yay mata ba wani abu ba, bayan sallar isha sai ga Fauzy ta dawo da mamaki ta shigo d’akin ganin kopar a bud’e idanunta suka sauka akan Fatuu dake kwance saman gado hannunta ruk’e da waya tana ganinta ta fara mata murmushi ta nufi gadon da take ta zauna a gefe surprisingly tace “wai da gaske ke ce?” Tana murmushi tace “a’a Aljana ce” gyara zama Fauzy tay sosae tace “amman ya akai na ganki anan bacin kin koma gida?” d’an yamutsa fuska Fatuu tay tace “to na dawo” waro ido Fauzy tay tace “Don Allah da gaske?” Kai ta d’aga mata alamar eh Fauzy tace “to ina Ya Haisam d’in yake da kika dawo ko har ya tafi” d’an shiru tay idonta a kanta ta rasa wace amsa ma zata bata can tace “Ya tafi Abuja” d’an tura baki Fauzy tay tace “to har kin siye mana zuciyar tashi ne da kika bari ya tafi” d’an murmushi kawae Fatuu tay a cikin zuciyar ta ta raya in ni ban siye zuciyar shi ba shi ai ya siye man Mutunci bin ta da ido Fauzy tay ta kalleta suka had’a ido duk sai ta tsargu can taji Fauzyn tace “ya naga kamar wani abu na damun ki har face d’in ki ta nuna?” damm k’irjinta ya buga tasa hannu tana d’an Sosa gefen kanta tace ba abunda ke damunta kawae bacci take ji kuma ta tsaya latse latsen waya tay Maganar tana niyyar komawa ta kwanta bayan ta kwanta Fauzy dake kallonta tace “amman yau kika dawo ne?” Kai ta d’aga mata alamar eh ta sake cewa taci Abinci ne Fatun tace eh taci d’azun gyad’a kai tay ta mik’e tana fad’in ga wani Abincin ta taho dashi ta tashi su ci ta tambaye ta minene tace tuwon shinkafa ne miyar d’anyen kubewa Fatuu tace to ta zuba masu, suna cikin ci Fauzy tace bata ba ta labarin dinner d’in data fad’i mata a waya zasu da Ya Haisam, d’an yamutsa fuska tay kafin ta d’an bata labarin sama sama bayan sun gama suka sha lemun data had’o masu dashi Fatuu na son tasha magungunan ta amman ta rasa yadda zatayi don tasan da Fauzy ta gani sai ta tambaye ta dalilin shan su tunda tasan magungunan na miye gashi ita ba wani rauni ke a jikinta da zata gani ba shiyasa ma ta bar su a cikin bag d’inta bata fiddo su waje ba gudun hakan k’arshe kawae sai tay kwanciyar ta Fauzy na ce mata bazata duba book d’inta ba tace mata bacci take ji. Washe gari Monday suka cigaba da zuwa class kaman ko yaushe ba laifi tafiyarta ta d’an daidaita in dae ba kallon k’urulla kai mata ba bazaka gane ba daidai take tafiya ba don sosae ta d’aure take tafiya yadda ba za’a zargi wani abu ba musamman Fauzy, wasa wasa sai gashi har Friday tayi ba Haisam ba dalilin shi balle kiran wayar shi bayan sallan juma’a suka fito tare don tafiya weekend saida aka fara sauke Fauzy Fatuu ta rok’i mai Napep zata d’an shiga yace to suka shiga gidan tare ta gaisa da Aunty Mareeya itama saida ta tambayeta Haisam tace mata ya koma kawae daga baya sukai sallama Fauzy ta rakota har bakin Napep suka k’ara yin bankwana ta tafi, a k’opar gida suka tsaya bayan ta fito ta biya mai Napep d’in ta nufi ciki don shagon Kawu Amadu a rufe yake, lokacin da ta shiga d’akin gwaggo ta nufa ta d’aga labule da yar sallama ta hango gwaggon kwance tana bacci d’an murmushi tay har zata juya ta fita taji ta kira sunanta ta juya ta kalleta suka had’a ido ta nufeta ta zauna a bakin gadon tana ta mata murmushi itama gwaggon tashi tay zaune ta jingina bayanta da kan gadon tace mata an dawo Fatun tace eh ta gaishe da ita ta amsa kafin ta tambaye ta Fauzy tace yanzu suka sauke ta a gidan Aunty Mareeya ta d’aga kai shiru ta biyo baya idon gwaggo a kanta ita kuma ta sunkuyar da nata still murmushi take can taji gwaggon tace taje ta zuba Abinci tace to ta mik’e ta nufi hanyar fita tana ruk’e da jakar goyon ta jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa A-shape ta yafa gyale dama ko ba don abunda ya faru da ita ba duk in ta san zata zo gida su had’u da gwaggo bata sa matsattsun kaya don tasan da gwaggon ta gani sai tayi fad’a kuma dama tunda abun nan ya faru da ita bata sa kayan da suka matse ta tafi zumbula doguwar rigar material, d’akinta ta nufa bayan ta shiga ta aje jakar a gefe ta nufi bakin gadonta ta zauna duk yadda taso kar ta damu da rashin kiranta da Haisam bai yi ba ta kasa abun ya matuk’ar d’aure mata kai tunaninta dama kenan k’arya yake mata, ita dama tasan ba wani abun da zai iya yi ya gyara laifin shi kawae dae ya cuceta, jiki a sanyaye ta mik’e tana kokarin maida k’wallan da suka tarun mata bayan ta fita kitchen ta nufa ta zubo Abinci, da daddare bayan tayi sallar isha ta watso ruwa ta zura doguwar riga yar kanti mai gajeran hannu ta saka hula akanta ta nufi d’akin gwaggo a zaune ta isketa akan kujera tana kokarin kunna Radio tana ganinta ta sakar mata murmushi itama Fatuu shi take mata ta zauna daga gefenta tace “wai gwaggo miyasa baki son zama a Parlor ne kullum indae kina gida kin fi son ki zauna a d’aki?” yar dariya tay tace “nafi sabawa da d’akin ne ni mantawa ma nike da wani Parlor” d’an tura baki tay tace “ga kayan kallo can maimakon kije ki kallo sai ki zauna kina ta faman jin radio sai kace wata tsohuwa” dariya sosae gwaggo ke yi tace to ai tsohuwar ce ko Fatun tace “a’a da sauran ki Allah” murmushi kawae tay sai kuma tana kallon Fatun tace “Oh ya mai jiki kuma” kallon rashin fahimta Fatuu ta bi ta da shi ganin haka yasa gwaggon cewa “Senator Alee na Hajiya nike nufi, ni kwata kwata ban sani ba sai ranar Laraba nan data wuce na shiga gaida Hajiyar anan Saude ke fad’a man wai ashe basu K’asar harda shi Haisam suna Germany nace ai ban sani ba ke kuma baki fad’a man ba ko ta waya” zuru Fatuu tay zuciyarta ta ayyana ashe bai K’asar muryar gwaggo ta katseta da fad’in “Bawan Allah, Allah ya bashi lafiya ya tashi kafadun shi” a hankali Fatuu dake ta kallon ta tace Amin suka d’an yi shiru can tace ma gwaggon miya ke damun shi ne, da d’an alamun mamaki tace ba dae bata san bai lafiyan ba Haisam bai fad’i mata ba a dabarbarce Fatun tace “….a’a na san bai lafiyan amman ban san abunda yake damun shi bane” gyad’a kai gwaggo tay da alamun damuwa tace “yanke jiki yay ya fad’i to an kaishi Asibiti nan Abujar daga baya likitocin suka bada shawarar ayi saurin fita dashi don ya kusa samun stroke Saude tace a ranar Juma’ar da ta wuce da Asuba aka kira Hajiyar ake sanar mata tun kafin gari ya waye suka tafi Kano ita da Haisam d’in daga can suka hau jirgin Abuja” gyad’a kai Fatuu tay tace Allah ya bashi lpy mai dorewa gwaggo ta amsa da Amin shiru tay da zuwa tayi taja gwaggon su je suyi kallo amman jin wannan Maganar yasa ta fasa ta mik’e tace mata bari taje ta kwanta taji bacci take ji ta d’aga mata kai tace Allah ya tashe su lpy, bayan ta koma d’aki zaune tay a gefen gado tama rasa tunanin da zatayi kenan wannan dalilin ya hana shi zuwa suyi Maganar kaman yadda yace can ta ayyana to amman ai ko a waya dai ya kirata tunda yanzu kwana takwas kenan da faruwar abun k’arshe dai ta yanke kawae bashi da abunda zai fad’a mata ne shiyasa bai kiratan ba a hankali ta kai kwance ta lumshe ido. Washe gari Asabar tana gama yin Breakfast ta gau gyara gidan tana cikin gyara d’akinta wayarta ta fara ringing ta aje bedsheet d’in da take kakka6ewa ta d’aukko wayar daga kan dressing mirror tabi kiran da kallo ganin bak’uwar lamba kuma da gani bata Nigeria bace bakin gadon ta nufa ta zauna ji take kaman kar ta d’aga kiran don tana tunanin ko Haisam ne gab da kiran zai katse tay picking ta kara a kunne tun kafin tay magana taji ance “Hello Kanwata kuma K’awata ya kike?” Zaro ido Fatuu tay ta washe baki jin muryar Haulat tace “Na’am Haulat ashe kece naga ba number d’in ki bace wannan” tace mata eh ta mijinta ce tana ta washe baki tace “to ya kike ya Nijar d’in?” itama Haulat bakin ta a washe yake tace mata nijar lafiya lou Fatun tace “kwana biyu sai inta trying layin ki bai shiga gashi tunda ki kai nauyi kin daina chat saboda ragwonci” tana jiyo dariyar Haulat d’in kafin tace “ashe ma ragwonci ne ba zan ce maki komai ba yanzu sai kema kin samu na Ya Haisam zan rama don nasan ke k’ilan ma ko wayar bazaki iya ta6awa ba” d’an yamutsa fuska Fatuu tay bata ce mata komae ba Haulat d’in ta tambaye ta Haisam tace mata yana nan bai dad’e da zuwa ba amman ya koma daga baya tace mata dama ta kira ne ta sanar da ita tayi D’iya Fatuu ta k’ara zaro ido ta rufe bakinta da hannu guda kafin tace “Don Allah Haulat da gaske kike ko wasa” tana jiyo dariyar ta tace Wllh ba wasa take ba ta haihu ran Alhamis da tsakar dare jiya aka sallamota yanzu haka ga babyn nan a hannunta da tsananin mamaki Fatuu tace “ikon Allah abun ba wuya ni wllh banyi zaton kin kusa haihuwa ba” Haulat na dariya tace “ashe abun ba wuya ki bari in lokacin da kema zaki haihun yayi zan tuna maki sai ki tantance” Fatuu na dariya tace ai ita haihuwar ne kawai bata yi ba amman tasan komai su da ke shiga Labour room kawae dae taga saurin abun ne daga lokacin da sukai wayar k’arshe, fira suka cigaba da yi har Fatuu na rok’onta ta turo mata picture d’in baby tace in suka gama zata sa ya turo mata ta tambaye ta zata dawo gida wanka ne tace mata eh amman sai an yi suna Fatun tace aikuwa dole su zo suna amman sai Haulat d’in ta hau rok’onta kan su barshi ba sai sun zo ba ai da anyi sunan zata dawo daga baya Fatun tace Shikenan tunda haka take so sukai sallama tace ta gaida mata gwaggo da Kawu Amadu, suna gama wayar cike da zumud’i taje d’akin gwaggo tana ta washe baki ta sanar mata zancen Haihuwar Haulat itama gwaggo tayi murna sosae tayi masu Addu’oi, bayan ta fito daga d’akin gwaggo hanyar waje ta nufa dama d’an gyale ne d’aure a kanta ta ciro shi ta yafa shagon Amadu taje shima ta sanar mashi yay murna sosae yayi mata Allah ya raya tayi D’iya sai faman washe baki take, saida ta amshi sweets da chocolate Amadun na fad’in komi take so ba zai hanata ba kar shima in tazo da kayan dad’i ta hanashi ta nufi gida tana dariya, da daddare bayan sallar Magrib ita da gwaggo suka tafi yin barka gidan su Haulat d’in, Ranar Monday da safe ta gama shirin ta tsab na tafiya Makaranta bayan tayi breakfast data fito d’akin gwaggo ta shiga tayi mata sallama tace mata sai yaushe tace Friday tasan zuwa lokacin k’ilan Haulat ta dawo tana murmushi tace mata to Allah ya kaimu ta amsa da Amin ta tafi, bayan taje Makarantar saida akai break take sanar ma Fauzy zancen Haihuwar Haulat ta hau murna tana fad’in zuwa suna Nijar ya kama su kenan Fatuu na dariya tace to murnar ta koma ciki da anyi suna zata dawo saidae su isketa gida tsuke fuska Fauzy tay tace ita gaskiya ba haka taso ba ta so zuwa Nijar don bata ta6a zuwa ba Fatuu nata mata dariya, a ranar da daddare suna cikin fira Fauzy ta kalli Fatuu tace “wai ni Zarah ina Ya Haisam ne kwana biyu ban ji kinyi Maganar shi ba?” bin ta da ido Fatuu dake zaune saman gadon tay tana tunanin abunda zata fad’i mata can ta sauke ajiyar zuciya ta fad’i mata halin rashin lafiyar da mahaifin shi ke ciki yanayin fuskar Fauzy ne ya canza cike da jajantawa ta yi mashi Addu’ar samun lafiya, Ranar Laraba da yamma Fatuu na zaune tana yin Assignment Fauzy kuma ta fita wayarta dake ajiye gefe tay k’ara alamar shigowar sak’o kallon wayar tay sai kuma ta aje biron hannunta ta d’aukko wayar ta shiga cikin messages d’in lokacin data bud’e sakon da ya shigon wani irin bugu k’irjinta yay da tsananin mamaki take kallon alert d’in 500k daga wurin Haisam lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya zuwa 6acin rai a ranta ta fara raya lalle ma Ya Haisam wato zai iya turo mata kud’i amman ba zai iya kiranta ba ita ga uwar son kud’i ko a tunanin shi zai siyeta da kud’i ne, a yadda take ji da tasan yadda zata maida mashi dasu da kuwa ta maida ranta ne ya bata ko ta kira Abbas ta tura mashi tace ya tura ma Haisam d’in sai kuma tay tunanin zai zargi wani abu tunda ai ba yau ya fara turo mata kud’i ba kuma har ta Account d’in Abbas d’in yana turowa cikin fushi ta fita daga cikin messages d’in ta wurga wayar gefe taci gaba da abunda take tana yi tana jan tsoki koda Fauzy ta shigo bata fad’i mata zancen kud’in ba don ta sa aranta bazata ta6a mashi kud’i ba, da daddare wuraren k’arfe goma saura sai gashi ya kira hakan kuma ba k’aramin tunzura ta yay ba wato ya turo kud’i shine ya samu k’warin gwuiwar kiranta k’in d’aga kiran tay har ya yanke wani ya sake shigowa k’arshe ma sai ta saka wayar a silent kawae, Ranar Friday da safe suna yin breakfast jikinsu sanye da Uniform ba tare da sun saka Hijab ba Fatuu ta fara kokarin tashi tana fad’in ta k’oshi Fauzy tay sauri ta gama su tafi, tana mik’ewa wani irin jiri ya kwashe ta da sauri tasa tafin hannunta na dama ta dafe goshinta tana yin salati hakan ya ja hankalin Fauzy ta kalleta ganin halin da take ciki yasa ta mik’e da sauri ta kamata tana tambayar ta lafiya, a gefen gado suka zauna Fatun na maida numfashi da d’an sauri Fauzy dake kallonta tace “What’s happening Zarah?” Sai lokacin ta cire tafin hannun tace mata ba komae kawae data mik’e ne taji jiri ya kwashe ta amman yanzu lafiya lau, d’aga kai Fauzy tay tace “Sannu Allah yasa ba Malaria ke son kama ki ba don kinsan yanzu haka take tai ta sa mutum jin jiri ga matsanancin ciwon kai” shiru kawae Fatuu tay tace mata ta k’arasa su tafi yau Friday yanzu sun makara tace to tama k’oshi bari su saka Hijab kawai su tafi, a saman gadonta ta d’aukko masu hijaban ta mik’a ma Fatuu ta ta itama ta sa ta nufi wurin kayan shafan su dake jere saman table ta d’aukko turare ta shiga fesawa bayan ta gama ta nufi Fatuu itama ta fesa mata koda k’amshin turaren ya d’aki hancinta da sauri ta kauda kanta Saboda wani irin tashin zuciya da taji, bayan Fauzy ta kauda komae da sukae amfani ta goya jakarta ta mik’a ma Fatun tata ta yunk’ura ta mik’e suka tafi, sosae k’amshin turaren da Fauzy ta fesa mata ke damunta ji take kamar zata yi amai a haka har suka k’arasa class d’in suna shiga Malamin su na Farko na shigowa, tunda ta zauna take yan juye juye tana yamutsa fuska sam ta kasa natsuwa wani irin tashin zuciya ne ke addabarta can malamin na cikin bayani taji wani irin yunkurin amai ya taho mata da sauri ta mik’e hannunta rufe da bakinta ta d’an bubbuga shoulder d’in Fauzy alamar ta bata hanya koda ta kalleta ganin yadda take yasa da sauri ta mik’e Fatun ta fita daga cikin seat d’in da gudu ta nufi hanyar fita gaba d’aya idanun yan class d’in ya koma kanta harda malamin nasu dakatawa yay ya bita da ido gaba d’aya Fauzy ta rud’e sai zare ido take can ta kalli malamin tace “Sir, pls let me help her” kai ya jinjina mata da sauri ta nufi hanyar fita ta bi bayan Fatuu………….

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button