Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 120 Complete Novel

Father of soldiers

🔥TAKUN ƘARSHE🔥

Lokacin da Abusufyan ya fita a fusace ya shiga motarshi yayi mata key da gudun gaske ya fusgeta,shi kanshi baisan ina zai dosa ba,A Æ™arshe gefen bishiya yayi parking É—in motar Ya kifa kanshi jikin steering,tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,Bai ta6a tunanin Sgr zaiyi mashi haka ba,duk irin yadda yake treating É—insu,tun suna yara yake hawa jirgi daga Turkey zuwa U.s don kawai ya gansu,saboda Æ™aunar da yake yi masu shi da Omar Amma sai gashi yau Sgr Yayi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba,Tsananin damuwa ne akan fuskarshi,zuciyarshi sai tafarfasa take yi,Zufa tuni ta wanke mashi fuskarshi,cikin shessheÆ™ar kuka Ya furta”Why Rafayet!why!ban ta6a tunanin haka kake ba”lumshe idanuwanshi yayi,Anan Ya yini gefen bishiyar,

Duk ta damu saboda rashin ganin Sehrish ga wayarta dake ajiye saman side drawer tun safe,tun tana zarya acikin bedroom ɗin harta fara tunanin Zuwa nemanta,hijab ta zura ajikinta ta buɗe ƙopar ɗakin ta fito,miƙar hanya tayi tana tafiya,Adai dai ƙopar bedroom ɗinsu ta tsaya,Hannu tasa tayi knocking ɗin ƙopar,

Jahad ce ta buɗe mata ƙopar,jikinta na sanye da pakistan wando Burgujeje pink da Riga fara mai dogon hannu,daga ƙasan rigar anyi mata adon stones,Ta yafa mayafin a ƙafada,Yayin da ta saki sumar kanta,

Fuskarta É—auke da murmushi tace”Amrish”ta Æ™arasa maganar tare da yin hugging É—inta,Suka rungume juna,bayan sun kammala gaisawa Amrish ta soma tambayarta

“dama ina neman Sehrish ne,tun asuba dana farka banganta ba,bansani ba ko tazo wurinku ne,ko ta fita daga gidan,”

Gaban jahad ne ya É—an faÉ—i don ita kanta duk yinin ranar bata sanya Sehrish a idanuwanta ba,

“Gaskiya bansan inda taje ba,nima duk yau banganta ba,Amma abunda za’ayi bari na bincika cikin gidan may be ko tana wurin Aunty azeema ne,”

Juyawa Amrish tayi,da sauri jahad ta ce”Ki shiga mana,Ga Hosana can tana kallon drama,”.

Murmushi ta É—an saki tare da gyaÉ—a kai tace”okey,”Matsa mata hanya Jahad tayi ita kuma ta shige É—akin,A kwance ta samu Hosana ta baje saman gadon,Ga laptop agabanta ta Æ™ura ido tana kallo,wuri ta samu daga gefe ta zauna,

“Hosana,ya kike,”

Juyowa hosana tayi fuskar nan a yamutse tace”Lahiya,”ta mayar da idanuwanta kan laptop din,zama sosai Amrish tayi suka cigaba da yin kallon atare,

Tana Æ™oÆ™arin fitowa daga Toilet,tajiyo Muryar Mommy tana sallama,Ƙarasa fitowa Hajiya Azeema tayi jikinta sanye da bubu ta atampa ,fuskarta É—auke da murmushi ta amsa mata”Wa’alaikum salam,Aunty ki shigo daga ciki mana,”

turo Æ™opar mommy tayi jikinta na sanye da jallabiya fara,babu mayafi akanta,sam babu kwanciyar hankali atattare da ita,ganin fuskarta a hargitse yasa Hajiya azeema tace”Aunty Lafiya naga kamar akwai damuwa a fuskarki,”

Mommy tace”Ina fa lafiya,Rafayet yayi aika aika…

 Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 120 Complete Novel

 

Some of related Hausa Novels

Back to top button