Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 51 Complete Novel
*ASM Bk2051*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………….A razane duk suka mik’e ganin abunda ke faruwa Hajiya ta fara fad’in” gashi nan ai zaku kashe masu D’iya…” Gwaggo duk ta rud’e hannunta sai rawa yake daukarta Haisam d’in yayi yay hanyar fita parlon da ita duk suka rufa mashi baya, yana fita ya kira Amadu da k’arfi ya fito daga cikin shagon da sauri koda yaga abunda ke faruwa da gudu ya nufi Motar ya bud’e mashi baya ya sakata lokacin Hajiya ta fito ta nufi Motar itama ta shige bayan ta d’aura kan Fatuu akan cinyoyinta sai ga gwaggo itama ta fito tana kokarin sanya hijab hannunta ruk’e da wata hijabin da sauri Amadu ya tunkare ta cikin tashin hankali ya fara tambayarta abunda ke faruwa idanu cike da k’walla tace “Maganar da tsawo ka kula da gidan” daga haka ta nufi Motar Haisam yay mata nuni data shiga gaba tace to ta bud’e kopar ta shiga shima ya shiga driver seat ya tashi Motar bayan ya juyata suka tafi Amadu na tsaye jikin shi gaba d’aya ya mutu yabi Motar da kallo har ta 6ace ma ganin shi sannan jiki a mace ya koma shago, tunda suka hau hanya Hajiya ke sababi tana Fad’in “Wllh idan wani abu ya samu yarinyar nan duk sai nayi k’arar ku tunda kun d’auki aure abun wasa abu kamar a shirin film ko littafi ace wai Haisam ya auri Fateema ba tare da sanin mu ba Saboda bamu da amfani ke Dije da nike gani mai hankali amman kika goyi baya….” Dakatawa tay tayi k’wafa kafin ta maida idonta kan Haisam dake driving tace “ko ba abunda ya faru da ita sai na bi mata hakkinta hakanan kusa yarinya tay ta yawo da aure a saman kanta ba tare da ta sani ba kaman baku san darajar shi ba, sannan wllh kukan daka sani shima sai na bi hakki na hakanan kasa ni kuka share share ko mahaifin ka daya kwanta ciwo bamma shi kuka haka ba don iskan ci kasan yarinyar matar ka ce shine bazaka sanar dani ba da kazo sanar man da aika aikar da kayi mata ka nuna man raping d’inta kai kana ganin kuma yadda hankali na ya tashi na d’imauce amman ko a jikin ka Saboda shegen miskilanci wato in mutu ma kai ko a jikin ka ko bari dae Allah ya tashi Fateema dani kake zancen” tsit kowa yay gwaggo kanta na k’asa shi kuma idon shi na akan hanya yanata driving bai ko kalleta ba ta cikin mirror can ya kai hannu cikin aljihun jeans d’in shi ya fiddo wayar shi kokarin kiran Dr Habeeb wanda ya ta6a duba Fatuu da ya kaita har yasan ta fara period ya shiga yi saidae layin nashi baya shiga kusan 3 times yana jarabawa but isn’t available Abbas ya koma kira ringing biyu ya d’aga tun kafin yace wani abu Haisam d’in ya riga shi ta hanyar kiran sunan shi Abbas d’in ya amsa yace mashi Don Allah idan yana da wani phone no d’in Dr Habeeb ya kira shi yaji in yana Hospital gasu nan kan hanya zasu kai Zarah and is Emergency, hankalin Abbas d’in ne ya tashi ya hau tambayar shi abunda ya faru da ita yace mashi yana driving ne zasu yi Magana pls ya kira Dr d’in yanzu daga haka ya katse Hajiya ta kya6e baki tace “ai da sai kayi mashi bayani yarinyar mutane zaku kashe tunda shima da sa hannun shi” still bai tanka ta ba sai dae ya d’an kalleta ta cikin mirror suka had’a ido ta wurga mashi uwar harara ya maida idon kan hanya yana cigaba da driving.
YADDA HAISAM YA AURI FATUU,
A Lokacin da Alhaji Lawal yazo wurin Ard’o ya sanar da batun janye Maganar auran Khalid da Fatuu Saboda yarinyar bata so tana da wanda take so kamar yadda Abbas ya sanar mashi firrr Ard’o yaki amincewa yace sam baza’a fasa auren ba su Yaya suka harzuk’a suka hau tunzura shi kan baza’a fasan ba nan Abbas ya shiga nuna masu da gaske ne tana da wanda take so baya K’asar ne shi Aminin sa ne kuma da ya dawo zai zo a d’aura masu auren, lokacin Alhaji Lawal ya shiga nuna masu illolin dake tattare da auren dole tunda har bata so to a kyaleta Ard’o fa ya hau sama ya tuma yace muddin yana raye hakan bazai faru ba wllh dole abi Maganar shi ai ba itace ta farko da aka fara za6a ma miji ba lokacin Alhaji Lawal ya k’ara nuna mashi ita baza’a had’a ta da yaran nan ba tunda a birni ta taso kuma a birni in hukuma taji za’a ma yaro auran dole bai so to kuwa d’aukar kwakkwaran mataki suke don har kotu ake zuwa mutumin k’auye da tsoron hukuma jin haka yasa Ard’o cewa yaji za’a fasan amman saidae a d’aura mata auren da Wanda take so don tayi girma da yawa ba aure nan fa cikin Abbas ya d’uri ruwa a rud’e ya shiga yi masu bayanin shi wanda take son baya K’asar ai yaje yin wani aiki ayi hakuri ya dawo amman Ard’o ya kafe har da cewa ai ko miji bayanan za’a iya d’aura mashi aure kuma tunda shi yace Aminin sa ne ba sai ya amsar masa ba sosae Abbas ya rud’e suka shiga kallon kallo shida gwaggo Alhaji Lawal yasa baki yace ayi hak’uri ya dawon kafin nan sai ita yarinyar taci gaba da karatunta aifa zancen suke so shine abunda Ard’on yace ya kafe kan ba’a isa yayi yadda ake so ba tunda daga yarinyar har uban nata shike iko dasu, su Yaya aka hau Kumfar baki ana zuga Ard’o don ita bata ma so ya janye da Khalid d’in k’arshe ma sai Ard’on ya fashe masu da kuka wiwi yana fad’in tunda yake nuna iko da ya’yan gidan ba wanda suka ta6a watsa mashi k’asa a ido sai iyalan Muhammadu don haka in dae ba’a d’aura da wanda take son ba to dama k’arya ne kawai so ake a yaudare shi to kuma Wallahi tallahi da kwarankwasa sai an d’aura da wanda aka za6a mata in ba haka ba a yau d’in nan ba gobe ba saidae Muhammadu ya tattare iyalin shi su bar mashi gida ya yafe su tunda basu da wani amfani a wurin shi sai saka shi jin kunya yana rufe baki ya hau yin tari aikuwa kan kace mi fadar ta rikice aka hau fad’in Baffan Fatuu da Gwaggo zasu kashe Ard’on hankalin gwaggo yayi matuk’ar tashi haka ma Abbas don yasan mutumin k’auye da iya jan sharri a rud’e ya hau lalla6a su yace a d’an jira zai kira shi ya sanar mashi sai a d’aura masu auren sai lokacin Ard’on ya d’an sassaukko yace ya bashi kafin gobe Juma’a Yaya ba haka taso ba tamkar zata fashe nan ta kawo Maganar a ba Khalid d’in Mino Chairman ya nuna itama a barta tay karatun ta k’arshe tasa aka fiddo masu da akwatunan lefen su, bayan an watse waje Abbas da gwaggo suka nufa suka tsaya jikin Motar Abbas d’in fuskokin su d’auke da matsananciyar damuwa Abbas yama rasa mi zai ce Gwaggo ce tay k’arfin halin cewa “d’ana Abbas ai da baka ce zaka yi ma wanda take son magana ba tunda dai babu dama an tsara hakan ne don asamu mafita kawae” cike da damuwa yace “amman muddin ba’ai yadda yake son ba saidae fa a d’aura mata waccan mutumin” yar ajiyar zuciya gwaggon ta sauke tace “in hakan Allah ya k’addaro mu bamu isa mu hana ba kuma koma dae miya faru ai harda laifin ta tun farko da anyi ma tufkar hanci tun da wuri ai kaga da ba’a ma kawo yanzu ba da lokaci ya riga da ya k’ure ni dama nasan fasa wannan auren ba abu bane mai sauk’i a wurin wanccan kafaffen tsohon” hannu Abbas yasa ya dafe fuskar shi yama rasa tunanin da zai yi can ya yanke kiran Haisam don ya sanar dashi halin da ake ciki Saboda yasan da Maganar zuwan shi garin kallon gwaggo yay yace mata ta shiga ciki in sha Allahu za’a samu mafita zai yi mata magana cike da damuwa tace mashi kar yace zai takura kan shi don ba samun mafitar za’ai ba kawae suje a sanar da Ard’on wanda take son yace bai shirya ba sai a d’aura mata da wanda suke so d’in kawae, girgiza mata kai Abbas yay yace a d’an dai jira ta shiga ciki tace mashi to kawae ta nufi komawa cikin gidan a ranta tana tunanin taya za’a samu mafita bacin ita Fatun bata da wani wanda take so da har za’a d’aura masu aure, bayan tafiyar gwaggon ya shiga kiran Haisam saidae sam wayar tak’i shiga Saboda rashin Network mai kyau k’arshe dole ya yanke komawa Jimeta ya juya ya bud’e Motar ya shige bayan ya tashe ta ya ja ya tafi, a can cikin gidan bayan gwaggo ta koma sukai zaune jugum harda Baffan Fatuu cike da damuwa ya tambayi gwaggon dama da wanda Fatun suke son juna, ba tare data 6oye mashi ba ta sanar mashi babu wani wanda suke soyayya don karatun ta tasa a gaba kawae shi Abbas yasa a fad’i hakan ne don a samu mafita yanzu kuma ga yadda abu ya kasance Yadikko dai sai bin su da ido kawae take ita tasan Fatun nada wanda take so to amman shi ba lalle in yana son ta ba balle aje ga zancen aure bacin ma bai dad’e da yayi aure ba, k’arshe shima Baffan ce ma gwaggon yay kawae ayi hakuri a k’yale shi ya aura mata wanda yake so sai su bita da Addu’a tace itama tayi ma Abbas Maganar hakan amman yace a jira shi sai su jira suga abunda Allah zai yi duk suka ce Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi.
Cikin mintuna talatin ya isa jimetan bayan ya shiga gari ya samu wani ya tambaye shi ko akwae wani Hotel mai kyau yace mashi eh yay mashi kwatance, bayan ya isa ya kama d’aki aka bashi makulli ya nufi d’akin wanda d’an madaidaici ne akwae duk abun buk’ata na cikin bedroom da yake Hotel d’in ba wani babba bane, toilet ya fara shiga ya watso ruwa daga baya ya fito daga shi sai singlet da d’an short ya aje kayan daya cire a saman gadon shima ya zauna daga gefe ya kai hannu ya d’aukko wayarshi da ya aje lokacin da ya shigo ya shiga kiran Haisam saidae duk iya kokarin da yayi layin nashi yak’i shiga har mik’ewa yay ya d’an zagaye d’akin ko ya samu kiran ya shiga amman da yay dialing sai ya yanke k’arshe dole ya dawo bakin gadon ya zauna had’i da cillar da wayar asaman gadon ya had’e hannuwan shi ya d’aura ha6ar shi abun duniya duk ya dame shi yama rasa tunanin da zai yi, maida bayan shi yay saman gadon ya kwanta yana kallon ceiling sai sak’e sak’e yake a haka bacci yay awon gaba dashi, ba shi ya farka ba sai bayan Azahar lokacin har angama salla jiki a mace ya mik’e ya nufi toilet saida ya k’ara watsa ruwa ya d’auro Alwala sannan ya fito ya zura wandon shi ya kabbara salla anan cikin d’akin, bayan ya gama ya d’aga hannu yana Addu’a aciki ya rok’i Allah daya kawo masu mafita a Al’amarin nan ya za6a abunda yafi zama Alkhairi, bayan ya gama ya mik’e ya koma kan gadon ya shiga duniyar tunani ga yunwa ya fara ji can yaji wayar shi ta fara ringing ya juya ya kai hannu ya d’aukko ta yana kallon screen d’in yaga sunan da ya saka ma Haisam ya bayyana har bai san lokacin da yay murmushin farinciki ba duk da baida tabbacin za’a samu mafita a wurin shi, bayan ya d’aga suka gaisa yace mashi tun d’azun yake trying kiran shi amman yak’i shiga Haisam d’in ya tambaye shi yadda suka k’are da Mutanen cike da damuwa Abbas yace “Wllh H,Zakee bamuyi nasara ba k’arshe ma abun nema yay ya zama wani issue na daban” cikin cool voice d’in shi ya tambaye shi abunda ya faru nan Abbas ya kwashe komae ya fad’i mashi tun daga kan zuwa gidan Alhaji Lawal har zuwa zaman da akai d’azun a fadar Ard’o yace “Wllh kafaffen tsohon nan ya kafe kan lalle sai dae a d’aura mata auren da wanda nace suna son juna and ni na fad’i hakan thinking that za’a samu mafita ya amince kamar yadda shi Dad d’in yaron ya amince” shiru Haisam yay can yayi sigh yace “So what’s d way out now?” Yarfa hannu guda Abbas yay kan lap d’in shi yace “ban sani ba H,Zakee cos am completely confused abunda nasani dae shine muddin ba wanda nace d’in to tabbas wancan guy d’in zasu aura mata wllh don tsohon ya d’auki zafi da yawa nema ma yay ya suk’e mana fa yaja aka mana caa wai in ya mutu mune and yace muddin ba’a d’aura mata da wanda aka ce tana so ba kuma ba’a bari ya aura mata wanda ya batan ba to ya yafe Dad d’inta dole ya bar mashi gida a yau d’in nan sosae ya shiga tashin hankali abun ba dad’i but he’s in serious dilemma har ma da ita Zarah wllh, ni tsorona ma aje a aura mata shi ba fata ake ba wani abun mara dad’i yazo ya faru tunda ta nuna bata son shi ta tsane shi so everything can happen” shiru Haisam kaman ba zai ce komae ba saida ya d’an d’auki lokaci har Abbas d’in na fad’in “H,Zakee are u there?” Yay sigh yace mashi “yeah” Abbas d’in yaci gaba da fad’in “da akwae wanda take so sai a aura Matan kawae ba wani abu bane karatu ko a d’akinta ne sai tayi wannan ba wani problem bane har haihuwa in suna so zasu iya dakatar wa har ta gama karatunta to ni ta fad’a man ba wani wanda take so gaskiya Saboda karatu ta saka a gaba” still shirun Haisam yay can Abbas yaji yace “I think u should just marry her Abbas” har saida Abbas ya d’an zaro ido jin Maganar Haisam d’in yay d’an guntun murmushi a ranshi ya ayyana da ace ba wani a zuciyar ta tabbas da zai yadda ya aureta to amman yanzu ba zai iya auren ta ba gaskiya don yasan zuciyarta na wurin wani har saida Haisam ya k’ara mashi magana sannan yace “ba wai bazan iya auren ta ba H,Zakee saidae gaskiya itama ba lalle ta amince ba Saboda akwae shakuwa mai k’arfi tsakanin ta da Feenah hakan zai jawo babbar matsala azo a kasa samun kwanciyar hankali kuma” shiru Haisam yay yana nazarin Maganar shi can yaji yace to ko Yayi ma Najeeb magana yasan zai amince tunda yana sonta dama, yanayin fuskar Abbas d’in ne ya sauya da sauri yace “haba H,Zakee ban tunanin zaka yi wannan Maganar ba duk don mi ake gudun wannan d’in da za’a aura mata ba Saboda halin shi ba to miye marabar shi da Najeeb d’in duk abunda yake Najeeb ma nayi k’ilan ma ya take shi” sai lokacin ma shi Haisam d’in ya tuna da wannan yace “gashi Saleem was already engaged da sai in mashi magana” wani d’an guntun murmushi Abbas yay jin yadda Haisam d’in keta kawo mutane can yay ajiyar zuciya yace “H,Zakee kai why not ka aureta kawae dama kaga ance wanda take so bai K’asar kaga kenan kai ka dace matsayin wanda za’a aura mata” wani d’a murmushin gefen baki yay yama rasa wace amsa zai ba Abbas d’in har saida ya sake mashi magana kan abunda ya fad’a sannan yace “I thought k’arfi kowa sanin yaushe nay aure zaka k’ara man Maganar wani auren and Maganar shakuwa da kai itama Fanan d’in ai sun shak’u” Abbas yace “amman ai hakan ban tunanin zai hana ka aureta matuk’ar kana so ko don ka taimake ta duba da irin shak’uwar da ke tsakanin ku…..” Tun kan ya k’arasa Haisam d’in ya girgiza kai tamkar yana ganin shi yace “isn’t possible Abbas bansan yadda zan kawo wannan issue d’in ba just 3 months da yin aure na so let think of another solution” Abbas yace “H,Zakee Maganar aure fa ba magana bace mai sauk’i da kawae za’ai tunanin da anyi ma wani magana zai amince kuma yakamata ka rink’a tuna dalilin son fasa wannan auren nata, ni ina ganin in dae zaka amince ba wani abu bane zaka iya auranta ba tare da kowa ya sani ba just to help her ya zamana iya mu nan muka sani ko ita ba sai an sanar da ita ba kaga bayan an d’aura maku auran zaka iya rabuwa da ita ba tare da idda ta hau kanta ba” Haisam d’in yace “but baka tunanin still sunanta zai canza?” Da sauri Abbas jin kaman ya fara yin nasara yace “No, ai kaga yanzu su nan dama an sanar dasu wanda take son bai K’asar to in aka d’aura auran daga baya in tayi nisa a karatun ta sai a sanar masu ka warware auren don ba yanzu zaka dawo ba ita kuma kar tay ta zama da aure a kanta ba miji” wani kalan murmushi Haisam yay yace “what if suka maido Maganar auren wanccan din?” Abbas yace “ban tunanin hakan ai ba wai daka raba auren za’a sanar masu ba sai an samu kaman 2 years haka lokacin kuma nasan yayi auren shi tunda ba yaro bane kuma nasan ko don ya shirya da Dad d’in shi zai yi sauri yay aure in ma lokacin sun kawo zancen yi mata wani auren nasan k’ila bata rasa wanda take so then” shiru Haisam yay yana nazarin Maganar Abbas sai Addu’ar Allah yasa ya amince yake a cikin ranshi don yana da tabbacin ba lalle ya saketa ba in ya aureta don ya fahimci kamar shima yana son Zarah d’in kawae bai gane bane bayan wani d’an lokaci yace mashi shikenan in yana ganin hakan za’a samu mafita ba tare da wata matsala ba ayi hakan Abbas ya washe bakin farin ciki yace in sha Allahu ba wata matsala da za’a samu Haisam d’in yana murmushi yace shi zai zaman mashi Waliyyi kenan yace eh yana dariya ya tambaye shi nawa za’a bada sadaki Abbas yace ko nawa yadda yaga yayi mashi yace zai turo mashi 1 million ya bada 500k sadakin sauran 500k d’in ai abunda yakamata sosae Abbas yay mamaki jin sadakin daidai da na Fanan ya bada hakan ya k’ara tabbatar mashi da zargin shi na yana son Fatuu kawae ya kasa ganewa ne nan take ya d’auki aniyar sai ya yi yadda yay auren ya d’ore in sha Allah, suna gama wayar sai ga kud’in ya turo mashi murna a wurin Abbas har saida ya d’an taka rawa kafin ya d’aga hannu yay ma Allah godiya ya rok’i yasa hakan yazama Alkhairi, ba 6ata lokaci ya saka kayan shi ya d’auki wayarshi ya fice, ko ta kan ya nemi Abinci bai bi ba ya hau Motar shi bayan ya fito ya nufi komawa rugar akan hanyar shi zuciyar shi ta raya mashi yakamata yaje ya sanar ma da Alhaji Lawal don ya zame masu shaida sosae hakan yay mashi ya nufi hanyar zuwa gidan cikin sa’a ya gane kuma ya same shi yana gida, bayan ya shiga Parlon shi suka gaisa Abbas ya tambayi ko ya gane shi yana fara’a yace ya gane shi mana ba duka d’azun suka rabu ba shima Abbas murmushi yake kafin ya sanar dashi yazo rok’on Alfarma ne yace to Allah yasa zai iya nan ya sanar dashi wanda take son ya amince a d’aura masu auren har ma ya turo da sadaki shine yake son don Allah ya shige masu gaba, sosae yaji dad’i yace ya taya Fatuu murna anan ya tambaye shi game da Haisam d’in Abbas ya sanar dashi sunan shi da kuma waye Mahaifin shi sosae Alhaji Lawal yay mamakin jin d’an Senator Alee Adamu Zakee ne wanda ba 6oyayyen d’an siyasa bane kusan ko ina an san shi ba kamar daya kasance shine Senator d’in daya fi kowane Senator kud’i a Arewa ba 6ata lokaci yace ya tsaya ayi sallar la’asar sai su koma rugar tare a shirya yadda za’a d’aura masu auren Abbas yace to nan Yasa aka kawo mashi Abinci yaci ya k’oshi daga baya yace zai d’an je cikin gari ya dawo yace to, kud’i yaje ya fiddo ana gama sallar la’asar ya dawo ba 6ata lokaci bayan Chairman ya dawo daga Masallaci suka tafi rugar Abbas na a Motar shi shima yana a Jeep d’in shi driver na tuk’a shi, lokacin da suka isa Ard’on na a kopar gida zaune da mutane suka nufi wurin su bayan sun zauna aka shiga gaisawa Ardon yace su shiga cikin fada Alhaji Lawal yace a’a nan ma lafiya lau tunda dama abunda ke tafe dasu ana son mutane su shaida nan Abbas yay ma Ard’on bayani game da amincewar da Haisam yay ya fiddo kud’i 500k ya aje a gaban shi yace ga sadakin ta sannan ya k’ara fiddo 200k yace wannan kuma na su ne su raba inji Angon jama’a zo kuga idanu baki bud’e kowa ke kallon kud’in Alhaji Lawal dae sai murmushi yake a rud’e Ardo ya hau tambayar wai waye wanda zai aure tan ko dai d’an yankan kai ne wannan iyayen kud’i a sadaki Alhaji Lawal ne yay masu bayanin ko wanene Angon Ardo daya gama rud’ewa harda cewa da tana da saurayi irin wannan tuntuni bata kawo shi an d’aura masu aure ba, Kamalu da Amadu da tunda suka ga isowarsu suka taso suka zo gefe don jin abunda zasu tattauna ai suna jin zancen Haisam ne za’a d’aura dashi suka nufi cikin gida da hanzari har rige rigen shiga d’akin suke lokacin su gwaggo duk suna a parlon tun bayan da suka gama sallar la’asar har saida su gwaggon suka tsorata ganin yadda suka fad’o masu Amadu na washe baki ya hau yi mata bayanin abunda ke faruwa a waje cikin d’aurewar kai ta maimaita sunan Haisam matsayin wanda za’a d’aura aure dashi yace mata eh wllh har sadaki ma an kawo Naira 500k zaro ido gwaggo tay tama kasa cewa komae Yadikko ko bata san lokacin data fara sakin murmushi ba Kamalu ne ya juya da sauri ya nufi d’akin baffan su ya sanar mashi lokacin yana kwance ya kasa fita Saboda damuwa ai yana jin zancen ya mik’e ba shiri ya nufi wajen anan aka shirya d’aura auren gobe Juma’a a Masallacin Juma’a dake Jimeta bayan gama Sallar juma’a Lokacin da Alhaji Lawal zai tafi har kud’i Abbas ya basu don su sha mai amman yak’i amsa yace da Haisam da Fatuu duk ya’yan shi ne k’arshe saidae yay ma driver d’in shi Alheri suka tafi kan sai goben, sam gwaggo ta rasa farin ciki zatai komi gaba d’aya kanta ya gama d’aurewa ta yadda akai Al’amarin ya kasance haka, sai bayan sallar isha sannan duk suka hallara a parlon Yadikko harda Abbas cike da damuwa gwaggo tace “d’ana Abbas ya akai hakan ta faru Saboda mi zaku takura kan ku har haka shi Haisam bai ganin bai dad’e da yin aure ba zai k’ara wani wanda nasan ba don yana so bane kawae k’arfin hali ne irin nashi shiyasa ya za6i cire mu a matsala shi kuma ya jefa kan shi a matsalar aure ba ba k’aramin abu bane, gaskiya ni ban goyon bayan auren nan kwata kwata shima nasan bai yi nazari yadda ya kamata ba kafin ya amince, gaskiya ban amince ba kawae a k’yaleta ta auri wanda suke so hakan zai fi nima hankali na zai fi kwanciya fiye da ace Haisam ta aura” ganin yadda duk ta damu yasa Abbas warware mata komae yace shi yana ganin hakan zai fi kan ta auri wanccan da bata so kuma shima Haisam d’in hakan yayi mashi tunda ba takura shi yay ba ta bari kawae ayi yadda suka tsaran Allah yasa haka yafi zama Alkhairi” Yadikko itama tace “nima ina ganin hakan zai fi kawai ai dama Addu’ar abunda yafi zama Alkhairi duk muke tayi to hakan shi yafi Alkhairin” Baffan Fatuu dae ya rasa ta cewa su Amadu da Kamalu ma duk suka goyi bayan yadda aka tsaran gwaggo dae tay shiru fuskarta d’auke da damuwa duk da ta ragu sakamakon jin ba auren dundundun bane nan Abbas yaba gwaggo sauran 300k d’in yace ayi abunda yakamata tace yaba Baffan dama an bashi sadakin Fatun amman saida Ardo yasa aka bashi wani abu a ciki wai ai sun riga sun gama mata komae, Yadikko ta zubo ma kowa Abinci bayan an gama ci duk akai sallama kowa ya nufi wurin kwanciya Amadu har ya fita ya dawo yace ma gwaggo yana son magana da ita ta mik’e ta fito wajen jiki sukuku acan gefe suka ke6e ganin yadda duk ta damu ya shiga kwantar mata da hankali yace shi yana jin hakan wata hikima ce ta Ubangiji nan ya kwashe komae game da son da Fatuu kema Haisam d’in har ciwon da tayi acan baya suka zata na Aljanun ta ne tsananin mamaki ne ya kama gwaggo har saida tasa hannu ta ruk’e ha6arta baki bud’e ta shiga fad’in yanzu dama duk wannan halin data shiga Saboda Haisam ne Amadun yace mata tabbas don da bakinta ta fadi mashi ya bata labarin lokacin d’aya isketa cikin mawuyacin hali tana amai a d’aki har ta sanar mashi hakan tafa hannu gwaggo ta shiga yi tana salati Amadun yace don haka ta bi su da Addu’a kawae k’ilan Allah ne ya cika mata burinta, a daren ranar kasa runtsawa gwaggo tay sosae tausayin Fatuu ya mamaye mata zuciya biri yayi kama da Mutum ashe shiyasa tak’i sake ma Fanan duk da hakan ji take ba yadda za’ai auren ya dore abunda za’ai iya su ba tare da sanin dangin shi ba ita kanta bazata so Fanan taji zancen auren nan ba Saboda yadda ta d’auke su gani take hakan zai zama tamkar cin Amana ne, Washe gari Juma’a aka fara shirye shiryen d’aurin aure tunda safe Abbas da Baffan Fatuu suka tafi kasuwa suka yo siyayyar kayan Abincin da za’ai harda tunkiya da za’a yanka bayan sun dawo dole gwaggo ta washe suka fara hidiman Abinci da soyen nama bayan sallar Juma’a Mutane masu yawa suka shaida d’aurin auren Haisam da Fatuu sosae Alhaji Lawal yay kokari don kuwa shi ya kawo take aways na abinciccikan da aka raba ma Mutane, bayan sun koma gida aka ci gaba da hidiman biki saidae yawanci yaran gidan ba kowa ne yasan da Maganar auren ba sun dae ga anyi Abinci ga nama kuma an soya Yaya ranar wuni tay a d’aki tana ciwon bakin ciki tun bayan da taji da wanda aka d’aura ma Fatuu aure to ai dama ita Hassada ga mai rabo taki ce, Washe gari ana gama sallar Asuba suka kamo hanya harda su Yadikko aka taho Katsina……….
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.