Uncategorized

Wani uba ya cire nonuwan yarsa yar shekara takwas da haihuwa a duniya.

Wani uba ya cire nonuwan yarsa yar shekara takwas da haihuwa a duniya.

Al’amarin ya faru ne a jihar Legas idan rundunar ‘yan sanda ta cafke mahaifin da ake zargi da cire wa yarsa nono ta hanyar amfani da dutsen guga mai zafin gaske.

Bayanan da aka tattaro sun ce mahaifin ya aikata wa yar tasa wannan rashin imanin ne sakamakon takaicin yadda kirjinta ya fara cikowa da nonuwa, alamun ta fara balaga.

Jami’an tsaron sun dauki yarinyar sun kaita asibiti inda suka bayyana cewar tana cikin mawuyacin halin bisa aika-aikar da mahaifinta yayi mata mai suna Mista Banjo, wanda shi a tunanin sa yarinyar ta yi saurin balaga shi ya sa yayi mata haka.

Kungiyar kare haƙƙin yara da marasa galihu su suka yi ƙarar mahaifin yarinyar, inda kakakin Jihar Legas DSP Asijebotu ya tabbatar ta afkuwar lamarin kuma ya ce suna kan bincike a halin yanzu.

Mahaifiyar yarinyar ta ce kullum sai mijinta Mista Banjo ya doki yar ta su, kuma bata da damar hana shi, ta ci gaba da cewa a gabanta mijin nata ya aikata ta’asar”

Mista Banjo ya amsa laifinsa inda ya ce Shi abin da yafi bankanta mashi rai shine yadda yaga A’isha wato yarsa da bata wuce shekara takwas ba da nonuwa, shi ne shi kuma yayi amfani da dutsen guga mai zafi bayan ya saka tsumma a kasan shi ya goge mata nonuwan.

Back to top button