Mijin Marigayiya Page 22 Hausa Novel
‘To ai kin ga shiryaki zata yi ki tafi school ko? Ko kina son ki makara Uncle ya koroki gida ne?’Yayi tsaki ya fice daga dakin ba tare da ya sake cewa komai ba.Ta lallaba Nasreen ta tura ta bandaki sannan ta juyo zata fito, kafin ta fito ta jiyoshi yana dawowa dakin yana cewa ‘Dankalin da kika bari a wuta ya kone, kije ki duba na kashe miki wutar.’Ta wuceshi ta karasa kitchen din da gudu inda ta sami dankalin ya kone, ta kwashe sannan ta sake kunna wutar ta dora. Ya karaso ya tsaya a kofar kitchen din, ya dan dauki lokaci yana kallonta tana zubawa yara abincin rana wanda ta sauke a babban flask. Jimawa kadan yace ‘Kin ga irin abinda yasa bana son ki barsu da yarinyar nan ita kadai ko? Ya za ayi ta iya kula da yara tunda gashi nan bata ma iya tashinsu daga bacci ba?’Ta kalleshi cike da mamaki tace ‘Nasreen ce fa, ko kaine ma ka tasheta sai tayi rigima, ko ka manta ne? Kuma kaine kace baka son Rashida ta dinga yi maka girki kuma ka ga dole abu daya zan yi a lokaci guda ba zai yiwu ina girka muku abinci ba kuma ina shirya yara.’Ya juya ya fice ba tare da ya ce komai ba.Ta ja tsaki ta share kwallar da ta taru a gefen idonta sannan ta cigaba da aiki. Bata ma san me take ji ba, kokari kawai take ta fita daga gidan idan taje makaranta ta samu tayi tunani ta fahimci me take ji.Bayan ta gama abinci ta wuce daki ta sameshi bayan ta zubawa yara abinci suna ci, yana kwance a gefen gado yana fama latsa waya ta wuce har ta kusa shiga wankan yace ‘Idan na kai yara dawowa zan yi kin sani, sai wajen 10am zan fita, ita wannan yarinyar taki haka zaki bar min ita a gidan daga ni sai ita?’Cikin halin ko in kula tace ‘Eh, ita da Shukra zasu zauna idan zaka fita kawai ka gaya mata don ta san cewa ka fita ta cigaba da aikinta.’Har zata shige bandakin yace ‘Gaskiya bana so, kuma kema kin san bai dace ba ki barni a gida daga ni sai mai aikinki mace. Irin hakane kuma idan an ce za a auri mai aikin kuce baku yarda ba.’Duk bacin ran da take ciki sai da ya bata dariya, duk da dai dariyar takaici ce tace ‘to ai gaka nan gata nan ka aureta mana, ai itama mace ce.’‘Ni dai na gaya miki bana son ki barta a gidan idan ina nan tunda ke bakya nan, ki sami inda zaki ajiyeta idan na fita sai ta dawo gidan.’‘Uhhm!’ Ta amsa sannan ta shige wankan cike da takaicinsa, har ji take kamar zuciyarta tana turiri. Zuwa makaranta lecture kawai ya zama wata drama.Nan da nan ta karasa shiryawa ta shirya yaran, ta hada tea ta zauna tana sha. A haka Mustafa ya fito ya samesu lokacin 7:15am. ‘Ku tashi muje.’ Ya fadawa yaran.Ta mike rike da kofin shayinta tace ‘Bari na dauko hijab dina na saka ku rage min hanya.’‘A’a zaki makarar damu ne fa, gashi ko shayi baki gama sha ba kuma kin san idan suka makara korosu za ayi.’ Ya juaya ga yaran wadanda sun riga sun mike kowa da kayansa a hannu yace ‘Mu je.’‘Anti sai mun dawo.’ Suka fada sannan suka juya suka fice ya bi bayansu.Ta bi bayansa da kallo cike da mamaki; ta kasa gane motarsa ce baya son ta dinga shiga ko kuwa tsabar bakin ciki ne a kan zata fita yake hanashi rage mata hanya. To amma kuma yana kaita unguwa, ko da yake wannan fita ce da shi ya ga dama kuma kusan duk inda zata tunda ta aureshi tare yake kaita da yaran suna biye da ita. To me yasa idan dai makaranta zata tafi sai ya san yanda yayi ya tafi ya barta ba tare da ya ko da rage mata hanya ba?Haka har ta gama shirinta ba tare da ta samo amsar tambayarta ba; ta fito ta sami Rashida a kitchen tace ‘Idan babansu ya dawo ki koma daki ki zauna in ya fita sai ki fito ki cigaba da aikin; idan Shukra ta zauna a wajensa shikenan idan kuma ta taho wajenki to don Allah kada ki bari tayi kuka yaji.’Tayi mata sallama ta fice tana sauri saboda 7:20am ta riga tayi kuma bata da tabbas din zata iya kaiwa BUK kafin 8:00am.Ta kusa isa titi Mustapha ya karyo kwana ya shigo layin, ta dauke kanta daga kallon inda yake; bata sani ba ko ya ganta ko bai ganta ba. Ta karasa titi cikin sanyin jiki ta hau Napep tambayoyi daban daban suna ta yawo a kanta; wai ina babe dinta ne? wanda yake son ta? Wanda kafin aurensu har so yake ya daukota daga makaranta ya kaita unguwa ko ya kaita gida don dai tana hanashi ne saboda ta san Baffa ba zai bari ba a lokacin.To shikenan soyayya ta kare ko me Mustapha yake nufi da ita? Shekara daya fa kenan da ‘yan watanni da aurensu.Kwanci tashi cikin wannan rayuwar da Khadeeja take a gidan Mustapha har ta gama level 2 a karatunta ta shiga level 3, kuma shekararsu biyu kenan da Rashida mai aikinta. Zaman dai haka ake yinsa cikin dagewa da dagiya; idan Mustapha yana son bukatarsa a wajenta sai taji kamar ba shi ba saboda yanda yake kwantar da kai ya samu bukatarsa ta biya. Amma kuma da zarar tayi maganar karatunta ko wani abu da zai sa ta fita daga gidan ba tare da ta tafi da yara ba to sai ya nuna bacin ransa. Domin a halin yanzu kowa a danginsu ya santa da ‘yayanta domin tare ake ganinsu ko bikin wa ake yi. Gidan Mommy kuwa sun mayar da shi kamar gidan kakarsu, kuma da yake sun sami karbuwa sai suka sake sakewa.Karatunta yana tafiya daidai tunda ta saka auduga ta toshe kunnenta daga duk wata mita ta Mustapha, sai dai kawai kullum a gajiye take daga aikin gida da kuma aikin tunanin abinda zata yi Mustapha ya daina nuna mata halin ko in kula. Yaran basu saba bata matsala ba a da, amma zuwa yanzu duk tana neman ta rasa kansu; musamman Afaf da Nasreen. Idan dai aiki ta saka su ba zasu ce ba zasu yi ba amma idan basu ga dama haka za suyi kunnen uwar shegu da ita sai dai ko ta yi aikinta ko kuma ta sa Rashida tayi mata. Sannan kuma yanzu Afaf ta kulla kawance da Samira ‘yar wajen Yaya Jidda, don haka kusan duk wani motsi na Khadeeja Afaf sai ta gaywa Samira wadda take kaiwa uwarta rahoto na kai tsaye; don haka ne ma matsawar da Yaya Jidda takewa Khadeejan ta karu.Sai dai a yanzu ba wannan ne damuwar Khadeeja ba, babbar damuwarta itace rashin haihuwa. Tun bayan da tayi bari a loakcin corona ko batan wata bata sake yi ba gashi ana neman shekaru biyu. Zaman gidan baya mata dadi, bata jin dadin yanda yaran suke mata, musamman Afaf wadda a da take tunanin sun zama daya. Tana fatan itama Allah ya bata ‘yaya wadanda zasu kalleta a matsayin uwa.Ta rigashi kwanciya kamar yanda suka saba saboda yanda ta kula idan ta zauna jiransa su kwanta tare ita ake cuta tunda dole ta tashi kafin asuba ta shirya yara. Sai wajen sha biyu saura sanna ya gama abinda yake ya kwanta a kusa da ita, ta juya ta gyara kwanciyarta. Yana kwance amma ya daga waya yana chattinga kamar yanda ‘yan kwanakin nan ta kula kullum kafin ya kwanta sai yayi chatting. Ta mike taje ta yiwo fitsari, ta sha ruwa sannan ta dawo ta kwanta, zuwa lokacin ya gama chatting din ya ajiye wayar yana azkar. Ta kwanta ta gyara kwanciyarta, bayan da ta kula ya gama azkar din ta lalubo hannunsa ta rike cikin sanyin murya tace ‘Abban Afaf.’‘Umm.’ Ya amsa yana kallonta duka da hasken da yake cikin dakin bai kai ya kawo ba.‘Uhm, gaskiya ina son zuwa asibiti naga gynae doctor.’ Ta fada tana wasa da hannunsa wanda ta rike.Ya rike hannunta a cikin nasa ya kara bata hankalinsa yace ‘Baki da lafiya ne?’‘No ba wani specific issue. Ka san dai kwanaki nace maka ina son naje a duba aga abinda yasa har yanzu ban sake samun ciki ba, kada naje wata matsala ce nayi ta zama gara naje a duba.’Ya gyara kwanciya ya kara matsowa kusa da ita ‘Kina dai so ki dorawa kanki damuwa, har yanzu fa ba a yi shekaru biyu da barin ba. Iya wannan ya isa ya sa ki san cewa lafiyarki kalau, kawai Allah ne bai kawo ba tunda wancan din ma ba asibiti kika je kika samo ba ko?’‘Na sani, amma dai gaskiya ina so naje a duba ni din na sami nutsuwa. Tunda ka ga idan naje aka ce min lafiyata kalau ai dawowa zan yi kawai na cigaba da addua’a, idan kuma matsala ce sa na nemi maganinta.’‘Babu wata matsala kina dai son tonowa kanki matsalar. Ke yanzu ma da kike neman ciki ido rufe ya zaki yi da karatun? Tunda gashi kin shiga level 3 kuma ke da kanki kina cewa ya fi wahala. Ya zaki yi da laulayi ga karatu? Ko har kin mata ne? ai zai fi sauki idan ma dolene sai kin je asibitin ki bari ki gama karatun kafin ki kwantar da kanki.’Suka yi shiru na dan lokaci, kowa da abinda yake tunani.Jimawa kadan tace ‘Ina son zuwa gaskiya, amma dai ina jin zan bari mu gama examsa din wannan semester in ya so kafin a koma hutu sai na samu naje.’‘To Allah ya kaimu.’Tana son ta haihu duk da dai Mommy ma tace mata lafiyarta kalau amma ita gaskiya tana so taje a duba ta. Kuma yanda Mustapha yake gwada mata halin ko in kula idan ana maganar haihuwa ya sa gaba daya ta fara tunanin ko bai damu da ta haihu ba; to ya ma za ayi ya so ta haihu tunda shi masoyiyarsa ta haifar masa yara har uku?Haka tayi ta sake-sake tana juyi, sai gefin asuba sannan bacci ya dauketa.______kamar kullum yana shiga office din yau ma damuwarsa ta yaye; musamman yanda kamshin turarenta ya yiwa kofofin hancinsa maraba bayan da ya shiga office din nasa ya rufo kofar. Wannan ya tabbatar masa da cewa ta riga ta zo office din watakila wani office din taje. Ya ajiye jakarsa a kan table ya karasa ya zauna a kan kujerarsa cike da farin ciki.Sabuwar sakatariyarsa Naja’atu Musa Bello; watanta uku da fara aiki amma soyayya mai karfi ta kullu a tsakanisu. Duk wata damuwa da Khadeeja zata dora masa da ya shigo office din ya ganta yake mantawa da ita, idan kuma an tashi daga office ko a ranakun da babu aiki ya kan je gidansu zance. Duk da dai manya basu riga sun shiga zancen ba amma dai yana ji a jikinsa Naja’atu tasa ce.Bai dade da zama ba ta turo kofar ta shigo, daga tsaye ta sakar masa kyakkyawan murmushinta wanda baya gajiya da kalla.‘Ranka ya dade barka da shigowa.’ Ta fada tana juya kwayar idonta.‘Good Morning my dear.’ Ya amsa yana ta faman murmushin da yake barazanar karawa bakinsa fadi…
