Hausa novels

Halysaah Page 10 By Khaleesat Haydar

✨✨ HALYSAAH ✨✨By _Khaleesat Haiydar_✍🏻10…..Khaleesat ta gyada masa kai tana rufe bakinta da hannunta murya can kasa tace “Plss i have a visitor, i want u to plss pretend you are not staying here, just pretend u came to drop some books for ur Female friend living here plssss” Kamar zata yi kuka ta kare maganar tana kallonsa, yayi shiru shima yana kallonta at first, sai kuma yace “As in how Halysaah?” Ta marairaice masa tace “Kawai dai kayi kamar ba a gidan nan kake ba don girman Allah ka rufa min asiri, u know my former housemate mace ce, act as though u are her friend, kayi kamar wajenta ka zo pls, don Allah ka taimake ni” Bata jira cewarsa ba ta mike ta juya da sauri ta fice daga dakin kafin Abdul ya biyo ta, ya bi ta da kallon mamaki baya ko kiftawa, can kawai yayi murmushi ya zauna ya ci gaba da abinda yake yi a Laptop dinsa, parlor Khaleesat ta dawo suka kusa cin karo da Abdul da ya nufo corridor yace “Me kika je yi a ciki? You didn’t even get me something to drink” Ta ɗan yi murmushi a hankali tace “Why didn’t you let me know u are coming? Me yasa baka gaya min zaka zo ba?” Yace “Sai na gaya maki in zan zo? Ko ke zaki biya min ticket din jirgin?” Ta girgiza kai cikin sanyin murya tace “Aa ba haka nake nufi ba, ya hanya?” Yana kallonta daga sama har kasa yace “What is wrong with you, why were you sick?” Ta sauke manyan idanuwanta kasa a hankali tace “I don’t know too, but i am much better now, naji sauki Alhamdulillah” Yace “Rashin lafiyar ne yasa kika dena daga kirana all this while?” Ta marairaice masa tace “Don baka san yanda nake ji bane a sannan, let me get you water to drink” Daga haka ta wucesa da sauri, ya bi ta da kallo har ta shiga kitchen, Khaleesat ta jingina jikin cabinet din kitchen din ta dafe kirjinta that was heaving so fast, after few seconds ta sauke numfashi sannan ta dau tray ta bude fridge ta dauko ruwa da lemo da glass cup sannan ta fito daga kitchen, zaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, ta karasa ta duka gabansa ta ajiye masa ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai tunda ta fito kitchen din yake bin ta da ido, ta zauna kan carpet ta tankwashe kafarta ba tare da ta bari sun hada ido ba tace “Ya su Mumy da Daddy?” Jin yayi shiru ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta kawai yake, a hankali ta sauke idonta kasa, yace “Duk kwana biyun nan kin canza Baby, you don’t look critically ill da har zaki kasa daga kirana, menene yasa kika dena kirana kuma idan na kira ki ki dagawa? Common WhatsApp kin dena min magana yanzu” Ta kasa kallonsa, tana wasa da gefen hijab dinta a hankali tace “To kwanan nan sai kayi ta min fada ta waya baka considering dina, ga kuma course dinmu da wahala ka sani” Ita kanta ta rasa dalilin da yasa hawaye ya cika idonta, He let out a sigh har a sannan yana kallonta, sai kuma ya dagota sitting her down by his side, gabanta ne ya fara faduwa, in da akwai abinda ta tsana kuma take fargaba a rayuwarta bai wuce Abdul ya zo America wajenta ba, duk da yawanci zuwan da yake it’s either tare da Mom dinsa or his Dad, amma duk da haka a dar dar take da shi saboda wasu abubuwan da ya tsira wanda a baya baya mata haka, duk zuwansa kasar sai ta kirko wani abu da zai maidata unhealthy wani lkcn har sai an kai ta hospital, ita da tasan zai kamo hanya ya taho da bata fara ce ma Safiyyah tace masa bata da lafiya ba, yana caressing fingers dinta yayi kasa da murya yace “But you know i love you Khaleesah, ke ce kike jawowa nake maki fada a ko da yaushe” Ita dai bata ce komai ba hawayen dake makale idonta ya gangaro bisa kuncinta, ya kai hannu yana goge hawayen a hankali yace “Ohk, but you know i love you so much right?” ta gyada masa kai kawai, a hankali yace “Housemate dinki fa? Is she around?” Sosai taji gabanta ya fadi, taki barin su hada ido tace “No ban sani ba, i saw she had a visitor daxu ya zo nemanta, probably her friend….” Yana kallonta yace “Friend? Namiji kenan?” Khaleesat ta gyada masa kai, lkci daya ya hade girar sama da ta kasa yace “Yaushe ta fara kawo namiji gidan? When did that start?” Khaleesat tayi karfin halin cewa “Dama tana kawowa time to time ai but not frequently, sai in kilan sun kawo mata reading materials ko bata da lafiya sun zo dubata” Yace “Kuma mazan na kwana a nan?” Khaleesat ta hadiye wani abu da kyar tace “Ni ban sani ba gaskiya, tunda ina dakina always a kulle ai” Kallonsa tayi to cut short the conversation tace “Na dafa noodles yanzu bari in kawo maka kar ya huce” Tana fadin haka ta mike da sauri zuciyarta na bugawa, dai dai nan Housemate dinta ya fito daga dakinsa, Khaleesat taji zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tsabar kidimewa, tayi saurin dauke kai tayi hanyar kitchen, Abdul ya juya jin an bude kofar daki, hada ido suka yi da Housemate din nata da ya shigo parlon yana tafiya slowly waya kare a kunnensa duk da ba magana yake a wayar ba hannunsa daya rike da wani Textbook, idonsa kuma na kan Abdul, hannu ya daga masa calmly yace “Hello” Abdul ya bi sa da kallo babu ko kiftawa without replying to his Hello, shi dai Housemate din nata yana tafiya calmly ya nufi kofa ya fita daga parlon, tuni Khaleesat har ta shige kitchen hankalinta a tashe ta dafe kirjinta tace “Na shiga uku…..” A haka dai ta fara zubo noodles din a plate, cike da karfin hali ta dawo parlon, Abdul dake ta kallonta yace “Who is he Baby?” Khaleesat ta ɗan yi fari da ido tace “Ni ban ma taɓa ganinsa ba sai yanxu, Nancy ya kawo ma littafi ina ga” Abdul ya mike yace “Ta yaya zaki dinga rayuwa under same roof da wani gardi Baby? Yaushe Nancy din ta fara shigo da samari gidan nan? All this while dama yana cikin gidan nan?” A hankali Khaleesat tace “Na fa ce maka ban taɓa ganinsa ba, i have never seen him before sai yanzu” Ajiye abincin hannunta tayi cike da karfin hali tace “In dafo maka black tea?” Komawa yayi ya zauna yaki cewa komai, kana ganinsa kasan he is boiling inside, ita dai ta juya tana tafiya kamar munafuka ta koma kitchen, mikewa yayi ya bi bayanta har zuwa kitchen din yace “Ta yaya wani banza can zai dinga shigowa yana kalle min ke anyhow Khaleesah?” A hankali Khaleesat tace “Ya Abdul kar ka manta communal living muke a gidan nan, this is America…. this isn’t my apartment alone, bazan iya cewa ga wa enda za su shigo gidan ba tunda ba gidana ni kadai bace” Tsawa ya mata yace “And so what??? An gaya maki bazan iya kama maki hayar gidan ke kadai bane? Banda kince kina tsoron zama ke daya a gida do you think u will be sharing an Apartment with anyone in America? Do u think I can’t afford a full apartment for you??” Har jikin Khaleesat ya fara rawa ganin how fiercely he was speaking to her yana huci, ga idanuwansa sun fara sauya launi, sosai take jin tsoron Abdul ita kam, hawaye ya fara gangarowa idonta muryarta na rawa tace “Ka fara kuma ko?” Kamo hannunta yayi fuskarsa a murtuke suka fito daga kitchen din, ta fashe masa da kuka a hankali har suka dawo cikin parlon, cike da fada yace “Ya bazan fara ba naga wani katon banza under same roof with you? Me yasa tun tuni baki gaya min Housemate dinki na shigowa da gardawa cikin gidan nan ba in samar maki other alternative? Me yasa baki da hankali baki da tunani ne ke a rayuwarki?” Zaunawa tayi ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da kujera, ya zauna yana huci, ita dai kuka kawai take tana shessheka, after few minutes ya koma kusa da ita ya dagota drawing her closer to him kamshin turarensa ya cika mata hanci, nan da nan ta hadiye kukan da take tana zare ido, Gently yake caressing dinta murya can kasa yace “I am sorry Baby, amma da kin gaya min da na samar maki wani apartment din ai….” Ta fara kokarin komawa baya tana son kwace kanta daga hannunsa, kin saketa yayi a fusace yace “Why do u always act like a Bush gal Khaleesah? Har yanzu rayuwar Ghetto bazai fita a kanki ba? What is the meaning of this nonsense?” Ta ki barin su hada ido, da kyar tace “To ai… This is a promise you made, amma kuma sai ka dinga…” Cikin tsawa yace “So f what if i break the promise? Ko ance maki tsoronki nake ne? Ko kuma wani ne zai aure min ke dama?” Ta marairaice masa kamar zata yi kuka tace “Ni dae bari in kawo maka black tea” zata mike ya fixgota har sae da fado kansa, ya fige hijab din jikinta yace “Naga alamar kin ma maida ni wani gara don kinga ina biye ki” Ta takure waje daya wasu hawayen na taruwa idonta taki yarda su hada ido tana kokarin kwatar kanta daga grip dinsa, skirt karami ne sosai jikinta sai half vest shi sa ma take ta yawo da hijab tun daxu da ta dawo schl, ya sake fixgota sosai jikinsa, kuka ta fara yi muryarta na rawa tace “Don Allah ka bari plss, this wasn’t our deal, you are not keeping to ur promise” Kallonta ya dinga yi saboda yanda tayi provoking dinsa, duk da shi bai yi niyyar mata komai ba da ya wuce ya lallasheta amma tsabar yanda ta hasala shi sai ya fara kokarin kissing dinta, ƙin yarda tayi tana kiciniyar kwace kanta tana kuka, House mate dinta ne ya shigo parlon a lkcn, ya kalli yanayin da suke da kuma yanda take struggling din kwatar kanta daga jikinsa, direct ya nufi cikin parlorn har inda suke without a second thought ya cakumo Abdul yana kallonsa da kyau “Hey, this is America guy, what sort of molestation is this??” Mikewa Abdul yayi yana kallonsa da wani irin Expression na mamaki, bai yi wata wata ba kawai ya sauke masa fist dinsa a kirji har sau biyu, ya wani cakumosa yace “Are you insane? How dare you??” Khaleesat ta zaro ido ta mike cikin tashin hankali ta riko Abdul tana zaro ido with shock, lkci daya ta kalli Housemate dinta da ya tsaya yana kallon Abdul baya ko kiftawa kuma bai yi attempting rama abinda yayi masa ba, da kyar tace “He is my boyfriend, I don’t think u have any problem with this, who are you? And where do you know us from? You have no right to intrude!” Housemate dinta dake kallonta ya sauke idonsa kamar bazai ce komai ba, sai kuma calmly yace “My bad! And i am sorry, i thought u were in danger, i am only here to drop some books, sorry about that plss” Khaleesat ta wani kallesa tace “Do i know u from anywhere that warrant u intruding?” Ya girgiza kai yace “Not at all… I am sorry” Kallon Abdul yayi, bowing his head gently at the same time yace “I am sorry, dude” Daga haka ya ajiye book din hannunsa ya juya ya nufi kofar parlon ya fita waje, that was when Khaleesat realized she was half dressed all this while, dukawa tayi ta fara kuka a hankali ta hade kanta da kujera tana jin kanta na wani irin sara mata, wani kallo Abdul yayi mata yana huci, kawai ya dau wayarsa ya nufi kofa ya fice daga parlon kamar zae tashi sama, ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa tayi da sauri ta nufi window tana duba waje taga babu motar Housemate dinta har ya tafi, sae Abdul da ta hango yana tafiya down the street, dawowa parlon tayi tana goge hawayen dake sauka idonta ta dau Hijab dinta ta wuce daki da sauri, har wajen karfe tara na dare Khaleesat ta kasa tashi daga saman darduman da take zaune ga wani ciwo da kanta yake mata, jawo wayarta tayi a hankali, tun daxu take son kiran Abdul amma ta kasa kiransa saboda tsoro, daga karshe tayi gathering courage tayi dialing numbersa har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai ɗaga ba, tasan ba lallai ya ɗaga ba dama, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gado wasu sabbin hawayen na zuba idonta. Da safe duk da yanda Khaleesat ke jin ta wani iri kamar zata yi rashin lafiya haka nan tayi shirin makaranta ta saka Facemask dinta sannan ta bar gidan, ta kusa awa daya a makarantar kafin Safiyyah ta shigo, Khaleesat ta zauna gefenta tana kallonta tace “Why are you sitted here Khalee? Is the lecturer not around?” Khaleesat ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Safiyyah ta sauke Facemask dinta ganin swollen eyes dinta cike da damuwa tace “Subhanallahi, what is wrong Khaleesat? Kukan me kika yi? Ko jikin Mama ne?” Khaleesat ta girgiza mata kai hawaye na taruwa idonta, hankalin Safiyyah ya tashi tace “Innalillahi, don Allah me ya faru? Is everything ok?” Khaleesat ta girgiza mata kai tana goge idonta a hankali tace “Abdul ne ya zo” Safiyyah ta gwalo ido tace “Abdul kuma?? Yaushe? Kuma me ya maki kike kuka?” Khaleesat tace “He came yesterday evening” Safiyyah tace “Ji jaraba, to me ya zo yi? Kuma me ya faru da ya zo din?” Safiyyah na jefa mata wannan tambayar taji hankalinta ya tashi lkci daya, let it not be what just crossed her mind now, tunda tasan ko wanene Abdul, ta kamo hannun Khaleesat da sauri cikin tashin hankali tace “Ko ya maki wani abu ne? A gidanki ya kwana???” Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace “A’a” Safiyyah bata san sanda ta sauke wani ajiyar zuciya ba, can tace “Toh meye kuma na kuka don ya zo, ko rashin mutuncin da ya saba ya shuka maki?” Khaleesat na shessheka a hankali tace “He met my Housemate” Safiyyah ta bude baki tace “Kai don Allah, cikin gidan ya gansa? To ke ma dai wallahi baza ki iya karyan kare kanki ba kice masa kawai baƙon Housemate dinki ne shi tunda bai san Nancy ta tashi a gidan ba, to sai kika ce masa me?” Khaleesat na gyada mata kai tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace “Haka nace masa, amma ai kin sansa kinsan halinsa, he even fought with my Housemate” Safiyyah ta zaro ido tace “Fight? To akan wani dalili?” Khaleesat tace “Kema kinsan yanda yake yi ai Sophie, kawai wai zai yi kissing dina ni kuma naki yarda sai ga Housemate dina ya shigo shine yayi approaching dinsa seeing what he was doing to me, hakan da yayi ne yasa Abdul yayi fada da shi, he hit him so hard” Safiyyah tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, to Housemate din ya rama ne?” Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace “Bai rama ba, kawai hakuri ya basa” Safiyyah tace “Wallahi in ance min Abdul na shan giya ni bazan musa ba, cause his actions portray that, kawai daga ganin mutum ka fara fada da shi kamar wani ɗan daba, kuma in banda rainin wayo zai zo me yasa bazai ce maki zai zo ba kawai sai dai ki gansa kamar an jefosa a gidan?” Khaleesat tace “Wai fa ce masa da kika yi bani da lafiya shine yasa ya taso ya taho, da na sani da ban ce kice masa haka ba” Safiyyah ta bude baki tana kallon Khaleesat don ita ma sai a sannan taga da basu ce masa haka ba tunda ba isasshen hankali ke garesa ba, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace “To yanzu Housemate din naki fa? Hope he didn’t hurt him?” Khaleesat ta fara goge wasu sabbin hawayen idonta tace “Kinsan menene ya dameni?” Safiyyah ta girgiza kai, a hankali Khaleesat tace “Maganganun da na gaya ma Housemate din nawa, meanwhile he was just trying to be protective ganin kamar Abdul molesting dina zai yi, ni kuma abinda yasa nayi masa haka don kar Abdul din ya zargi mun san juna da Housemate din nawa, cause i told him frnd din Nancy ne kuma ni ban taba ganinsa ba” Safiyyah da ta kasa rufe baki tace “Wasu irin maganganu ki ka gaya ma Housemate din naki?” A hankali Khaleesat ta gaya mata duk bakaken maganganun da ta gaya ma Housemate din nata, Safiyyah ta dinga mata wani kallo cike da takaici, can tace “To shi katon banzan da kika fadi bakaken maganganun a kansa hope yayi considering dinki at the end of everything?” Khaleesat ta girgiza kai tace “He walk out on me, na kirasa sau biyu jiya yaki dagawa, kuma har yanzu bai kirani ba” Safiyyah ta ja tsaki tace “In ma ya ɗaga shi babban ɗan iska ne, kada Allah yasa ya daga, kuma shi Housemate din naki kun sake haduwa bayan abinda ya faru jiya?” A hankali Khaleesat tace “Shi ma tunda ya bar gidan jiya har yanzu bai dawo ba” Safiyyah tace “To wallahi ki kirasa don mutumin nan yafi karfin walakanci a wajen ki” Khaleesat ta fara wani hawayen tace “I don’t have his Number” Safiyyah tace “Ban gane baki da lambarsa ba?” Khaleesat tace “Wallahi, even when i was going to Nigeria kawai hadani yayi da wani mutum ya bani number mutumin amma bai bani lambarsa ba” Safiyyah tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace “Ki tashi kawai ki koma gida kilan Allah zai sa ya dawo sai ki basa hakuri, Abdul kuma kar ki kuskura ki sake kiransa in ba haka ba in tsine maki wallahi” Duk da bakin cikin da Khaleesat ke ciki sai da ta ɗan yi murmushi, a haka ta koma gida ta bar Safiyyah a school din bayan Safiyyah tace ta kirata duk abinda ake ciki, in ma Abdul din ne ya sake dawowa gidan ta kirata zata taho….. Throughout ranan Khaleesat bata ga Housemate dinta ya dawo gidan ba har karfe takwas na dare, ta rasa me yasa ta kasa samun nutsuwa hankalinta yaki kwanciya, ko tunanin Abdul bata saka a ranta ba tun bayan barin ta school daxu da safe da Safiyyah tayi encouraging dinta kar ta sake kiransa, but she was so restless ganin Housemate dinta bai zo gidan ba, she wish she had his number ta kirasa, wajen karfe goma saura wayarta ya fara vibrate ta jawo a hankali tana duba screen din taga Safiyyah ce, Safiyyah ta kirata yayi sau 6 daga barinta school da safe har zuwa yanzu, Safiyyah tace “Is he back Khaleesat?” Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace “A’a bai zo ba” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Kilan sai gobe zai zo gidan, ki kwantar da hankalin ki pls” Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace “Plss kar ki wani damu kanki da yawa kawata, hope kin ci abinci?” Khaleesat tace “Na ci” Safiyyah tace “To kiyi kwanciyarki, good night” A haka suka rabu, Khaleesat ta ajiye wayarta ta lumshe ido duk da tasan ba baccin zata yi ba…….*Continue making your payment before the end of free pages fanss, in ba haka ba aji shiruuu…*😃07087865788✍🏻

Back to top button