Uncategorized

Maciji Ne Page 87-88 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 87/88

_______________Cikin wani irin mugun bugawar zuciya, abie ya bude bakinsa dake rawa yace “wa…..z..ii..rr”sai kuma ya kasa ƙarasawa, sakamakon numfashinsa daya dauke.nan ya zube gurin asume.

Cikin hanzari Adeeb da su Sultan Habeeb,sukayo kansa.

“Abie !abie!!Adeeb ya kira sunan Sultan yana jijjigashi.amma ko motsi bayayi,da hanzari suka zareshi suka nufi part dinsa dashi,suna zuwa likitocinsa suka rufu akansa.

Zulaihat ma asibitin cikin masarautar aka nufa da ita kai tsaye,sosai ta galabaita,dan jini sai zuba yake ta bakinta,kamar ma aman jinin take,

Queen Suhaimat,na riƙe da hannun ɗiyarta  gam, dan bazata ƙara bari,fattu tayi nisa da itaba in Sha Allah.

Amma ma tabi su Adeeb dan ganin ya jikin Sultan ɗin.

Dan haka nanny ke tura keken Rashad suka fice daga ɓangaren Ammi,kai tsaye bangaren Sultan suka nufa suma,dan hankalinsu yaki kwanciya,suna buƙatar ganin ya jikin nashi.

Download>>> Kwarata Complete Document

Cikin ikon Allah kuwa aka samu Sultan ya farfaɗo,saidai banda hawaye ba abinda idanunsa keyi.

Damuwarsa ta ninka ta farko,wannan cin amana da me yayi kama?ace dan uwanka ma baka wuce ya cutar da kaiba,yanzu dama za’a iya hada baki da waziri acutar da rayuwarsa,dashi ake ƙoƙarin kashe masa gudan jininsa?lallai yau da iyayensu suna raye tabbas ba abinda zai hana zuciyoyinsu bugawa.

Duk irin so da ƙaunar daya nunawa waziri,amma ƙarshen halaccin da zaiyi masa kenan?yana tare dashi, komai nashi waziri,ko wace shawara dashi yake,ashe shikuma yana amfani da wannan damar ne yana cin dunduniyarsa?kai rayuwa Allah ya shige mana gaba.

Adeeb ne ya,zauna kusa da mahaifin nashi, tare da riko hannunsa yana kallon idonsa,cikin tattasan lafazi yake rarrashin  Sultan”abie dan Allah ka kwantar da hankalinka,Ni dama najima ina zargin uncle,kuma koda muka shiga part din Ammi,Ina kallon lokacin daya zare jiki ya bar part din,Dan haka nayi saurin bada umarnin akamoshi dan dama tuni na shirya komai,yanzu haka yana hannu”Adeeb ya faɗa cikin sanyin murya yana murza hannun abie cikin nutsuwa.

Ajiyar zuciya Sultan ya sauke tare da lumshe ido,kafin ya buɗe su.

“Habeebee mutanen dana yarda dasu,su suka cutar dani,nayi dana sanin kasancewarsu makusantana,kuma na gode Allah dayasa bani da zuri’a da Ammi,da ta gurbatamin zuri’a da mugun iri,Allah Sarki matata Nazli,Allah ya jiƙanki yayi miki rahama,tare da yarana da kuma amintaccen driverna”abie ya faɗa cikin zubda hawaye yana jin zafi cikin zuciyarsa.

 

Haka su Adeeb da baban fattu sukayi ta rarrashinsa akan ya kwantar da hankalinsa,karya sanya damuwa cikin ranshi har yazo ya samu matsala babba.

Barcine ya dauke Sultan,dan haka suka fito zuwa babban falo,suka zauna dan tattauna yadda za’ayi.

Fattu na zaune kusa da mahaifiyarta,ta ɗora kansa akan cinyar innarta,wani irin nishaɗi da jin dadi takeji cikin ranta,wai yau itace tare da mahaifanta, lallai duk wanda ya mika lamuransa ga Allah,to tabbas zai ga daidai arayuwarsa.

Queen Suhaimat ma cike take da farin ciki,zuciyarta fess,ahankali take shafa kan fattu cike da tsantsar ƙauna,itakam tayiwa Allah godiya da wannan ni’ima da yayi mata,yau gata ga zaranta bayan shuɗewar shekaru masu yawa,ita dama bata taɓa cire rai da tsammani ba.

Suna nan zaune saiga su Adeeb sun fito daga cikin dakin,yana tura keken da Rashad ke kai,dan suna zuwa falon shima ya shiga gurin mahaifin nasu.

Tunda suka fito idon Adeeb yana kan fattu,kamar yadda itama take kallonsa,tana jin wata irin kaunarsa na ratsa dukkan sassan jiki da jininta,haƙiƙa Adeeb ya zame mata alkairi,haduwa dashi nasarace,kuma in sha Allah zata kula dashi,zata nuna masa soyayya ta gaskiya cikin amana da girmamawa.

Download>>> Tayi Min Kankanta Complete Document

Murmushi Adeeb ya sakar mata tare da dan shagwabe fuska,irin na nayi kewarki ɗin nan,itama murmushin ta sakar masa tare da lumshe ido alamun rarrashi,kamar yadda yake mata.

Zama yayi kan kujerar dake saitin wacce Queen suhaimat ke zaune,ta yadda zai rinƙa kallon fattunsa.

Duk abinda sukeyi nanny na kallonsu,murmushi kawai tayi tare da girgiza kai.

Queen Suhaimat ce tace “ya jikin Sultan ɗin?”

“da sauki jikinsa kam,yanzu haka yayi barci ma”Adeeb ya bata amsa cikin girmamawa.

Wayar Adeeb ce tayi ƙara, ta jikin agogonsa, dagawa yayi tare da cewa ku “shigo dashi ciki”

Ya kashe wayar.

Ko minti  biyar ba’ayiba saiga wasu dakarun fadar sun shigo da waziri yana gaba suna binsa abaya,yayi tsilli tsilli  da ido,kunyar duniya ta gama lalata masa zuciya,

Durkushewa yayi atsakiyar falon kansa aduƙe,yana jin kamar ƙasa ta tsage ya shige ciki.

Kallonsa kawai suke cike da alhini da jinjina rashin amana irin na waziri.

Adeeb ne ya miƙe cikin nutsuwa ya nufi gaban waziri,tsayawa yayi tare da sanya hannu cikin aljihun wandonsa, ya kafe waziri da ido,na tsawon lokaci kafin ya nisa ya fara magana”uncle ka bani mamaki,ka sanya zuciyata tunanin cewar lallai mutane ba abin yarda bane,uncle me muka tsare maka arayuwa?me nayi maka kake son ganin bayana tare da mahaifina?uncle me ka nema agurin mahaifina bai maka ba?uncle yanzu da kai za’a hada baki ɗan ganin bayan dan uwanka? Uncle why ?yaushe kazama haka?yaushe ka bari shaidan yayi nasara akanka?har idanunka suka rufe kake cutar da wanda ya aminta dakai sama da kowa?”Adeeb ya faɗa cikin salon sa mai sanya mutum shiga taitayinsu.

Kuka kawai waziri ya sanya tare da kamo ƙafar Adeeb”kayi hakuri dana,ka yafemin wllh sharrin zuciya dana shaidan ne suka sanyani aikata wannan abubuwan,da kuma kwadaituwa da son hawa karagar mulki,dan Allah ku gafarceni”ya faɗa cikin kuka sosai yana riƙe da kafar Adeeb.

Lumshe ido Adeeb yayi zuciyarsa na masa zafi sosai haƙiƙa abubuwan da su uncle suka aikata shida Ammi,sun cancanci hukunci,dan haka dole ahukuntasu.

Download>>> Matan Asokoro Complete Document

Cikin salon sa na haɗe rai yake kallon uncle kafin yace “menene gaskiyar al’amari akan asirin zama maciji da akayi min ?”cewar Adeeb kenan yana kallon waziri.

Ɗago kai waziri yayi cikin zubda hawaye,yace “tabbas bazan boye maka ba,nine nan nasa akayi maka asiri ka zama maciji,domin farko nayi niyar ka auri yata Zulaihat,inyaso inbata guba ta sanya maka cikin abinci kaci ka mutu,sai kuma ka nuna rashin amincewa da auren Zulaihat,wannan shine ya kara tunzurani,naje gurin boka aka hada maka zazzafan asiri da kalolin macizai na duniyoyin aljanu da ban daban,wanda idan ka bar fadar nan,shikenan ka barta har abada,kuma nine da kaina na daukeka na kaika can yankin Nigeria,dan ko ganin ka bana sonyi kusa da fadar nan”waziri ya faɗa yana hawaye.

Salati gaba ɗayansu suka dauka,kowa yana Allah wadai da waziri,saboda son zuciya  da abin duniya,yake kokarin hallaka dan dan uwansa.

 Runtse ido Adeeb yayi cike da kumar zuciya,yama rasa me ya kamata yayi.

Daga bakin ƙofar dakin abie sukaji magana yana faɗin”waziri ka cuceni ka ci amanata ka yaudari soyayya irin ta yan uwan taka,me nayi maka haka da zafi ?kake son ganin bayana?duk irin kulawa da soyayya irin ta yaya da ƙani dana nuna maka,amma yau kaine ke son ganin bayana?kaje dan kanka,duniya zata koya maka hankali,kuma ko yanzu kasan Allah shine ke da iko akan kowa,dan gaka a ƙasa Ni kuma da iyalina muna samanka”abie ya faɗa cikin zubda hawaye yana dafa bango.

Download>>> Asad (The Arrogant) Complete Document

Da sauri Adeeb yayi gurinsa tare kamo hannunsa ya zaunar dashi akan kujera.

Cikin kuka waziri ya rarrafo gurin mai martaba yana bashi hakuri,

Suna cikin haka Tareeƙ ya shigo cikin dakin da sauri .

Duk waigawa sukayi suna kallonsa,

Cikin girmamawa yayiwa Sultan sannu da jiki,kafin ya isar musu da saƙon mutuwar Zulaihat .

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un,shine abinda Dukansu suka haɗa baki gurin faɗa.

Shikenan Zulaihat ta riga mu gidan gaskiya,Allah ya yafe mata kurakuranta.

Waziri kuwa daskarewa yayi azaune jin labarin mutuwar ɗiyar tasa guda ɗaya tilo,

Ihu ya sanya tare da faduwa agurin yana birgima…

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Mu hade anjima.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment

More typing.

Back to top button